KHF 42
Sakin baki tayi tana Kallon shi a tsorace "me za muyi a Zaria? Karata za ka Kai?" Murmushi Mai ciwo ya saki "Haba Fateema yanzu ni kaman ni Sai inje Kai kararki? In laifi Kika min ni da kaina na Isa in miki hukunci, a gaba na fa aka haife ki" ya karasa zancen nashi da murmushi "Baffah ke son ganin ki Kuma ai Sallah ya Zo ko?" Sai a sannan ta saki ajiyar zuciya but still tana mamakin me ye sa Baffah ke neman ta after all suna yawan waya Amma Bai fada Mata ba, Anya ba Abu a kasa? Haka kurum taji gaban ta na faduwa saukin ta kawai through out ranar su na tare da Unclee Aliy.
Washegari, Sha biyun Rana a Zaria ta musu straight can su ka wuce. Zaune su ke a falo bayan an idar da Sallan la'asar su na hira tare da Mami da Ammah sai ko ya Deedat da ake ta labarin shirye shiryen auren shi, idon Mami ne ya sauka akan Zahrau tun dazu ta ke Kallon ramar da tayi tasan Zahrau da sa abu a rai ba shakka akwai abinda ke damun ta, kasa shiru tayi sai da ta tanka "Zahrau me ke damun ki? Kinyi rashin lafiya ne?" A tsorace ta juyo tana kallan mamin "Ma Mami me Kika gani?". "kin rame of course"
"Ni lfy na kalau" ta bada amsa tana Satan Kallon Aliyu.
Lura da hakan da mami tayi ya sa ta Kara zargin sosai Kallon Aliyu tayi "Aliyu ka ji tsoron Allah, in cutan yarinyar Nan kake wlh Allah ba zai barka ba" Sakin baki yayi Yana Kallon mamin ya ma rasa ta yanda zai fara amsa ma ta, idanuwan shi su kada sunyi ja domin ko ta tabo Mai abinda ke Mai kaikayi, Ganin reaction ya sa Mami ta yi tunanin zargin ta gsky ne "kaga ni nagaji wlh, ai ba a abun Dole ko bara Abbah da Baffah su Zo gwara a raba auren Nan kowa ma ya huta, Abu ya ki ci yaki cinyewa" da Mami za ta ga halin rudin da Zahrau ta shiga ciki ba za ta Kai ga karashe zancen ta ba, Kallon mamin ta yi da sauri ta fara girgiza Kai sai ta hawaye Sha, daga Mami har Ammah sun dauka juriyan ta ne ya Zo karshe Jin maganan da ake sabanin Deedat da ya ke hango rashin gaskiya a idanuwan ta kiri kiri, mutuniyar shi ce sosai tun tana karama hakan yasa duk wani move inta ya riga ya karanta. Jawo ta Mami ta yi tana Bata hakuri, "kiyi hakuri Su Baffah su dawo anjima yau za ayita ta kare" ganin Mami na nema Kai ta ta baro ya sa ta bude baki ta fara magana cikin sheshekar kuka "Mami Dan Allah ku yi hakuri ni wlh ba abinda yake min Allah" harara mamin ta sakan Mata "Tsoron shi kike ji ko? Ban son karya"
"Mami wlh da gaske na ke, Dan Allah Kar KU raba ni dashi wlh bai min komai inma akwai Mai laifi nice Allah..." Kallon da Aliyu ya Mata ya sata saurin rufe bakin ta.
"Mami, Ammah kuyi hakuri please, karamin issue ne but za muyi solving and please Mami ki daina batun raba mu, ba za mu iya rabo da juna ba muna son junan mu Allah"
"Wai Haka" Mami ta tmby Zahrau, ba kunya ta daga idon ta. Gabadayan su jikin su sanyi yayi Deedat dama tuni ya bar dakin, Mata da miji sai Allah.
Zaune su ke gaban iyayen nasu duka hudu daga ita sai shi, a wurin ita kadai CE ba ta San makasudin Kiran da aka Mata ba don a tunanin ta maganan su da Aliyu ne duk ta tsargu.
Baffah ne ya Kira sunan ta da sauri ta dago tana Kallon shi, Nasiha ya fara Mata sosai, gabadaya Yan falon sai da jikin su yayi sanyi, ita Kam duk a tunanin ta fada za su Mata akan Unclee Aliy sai da Abbah ya fara magana sannan ta fara shakkun hakan. Tariha rayuwan su ya fara ba ta har zuwa rasuwan mommy da Daddy da Kuma jaririyar da su ka bari, shiru Abbah yayi ya kasa karasawa, 'to meyesa ita kadai za a ba lbrn? Shin Ina jaririyar da Abbah ke magana akai"
"Ki yi hakuri Zahrau hakika ba mu kyauta Miki ba sai dai munyi niyyan fada Miki tun tuni Amma ganin kaddarar ciwon da Allah ya saukar Miki ya sa mu ka kasa don gudun barazana ga ciwon ki" a firgice ta ke Kallon Abbah Dan Bata fahimci inda zancen shi ya dosa ba. "Ke ce jaririyar da suka bari Zahra" Baffah ya karasa zancen Abban. Shiru ne ya biyo dakin Dan bbu Wanda zai iya cancance halin da Zahraun ke ciki. Tashi tayi a hankali ta nufi gun Ammah ta riko hannayen ta "Ammah da gaske dama ba ke Kika haife ni" hawaye Ammahn ta ji ya fara zubo Mata ta Dade tana tsoron zuwan ranar da Zahrau za ta gane hakan. "Da gaske ne kenan ko Mami" jawo ta Mami tayi jikinta ta na rarrashin ta Amma abinda ya fito bakin ta ya ba kowa mamaki "bakomai Mami na yadda da kaddara ta, Infact Kun min rikon da ba ta yanda Zan yi in fuskanci hakan bakin ciki na Daya Addu'a da ban tabawa iyaye na ba Amma In Sha Allah daga yau na fara" ta fada tana share guntun hawayen da ke fita daga idanun ta ganin haka ya sa Aliyu ya Mike ya Isa gare ta hannun ta ya ja zasu bar falon. Abbah ne ya dakatar dashi Yana fadin "Allah ya Miki Albarka Zahrau, hakika nayi matukar farin cikin yanda Kika dauki zancen Nan, Iyayen ku kullum suna cikin addu'an bamu, ko da su ke raye mutane da Basu da hali mara kyau sai Wanda ba a rasa ba, Mahaifiyar ki mutum ce Mai matukar kirki, kawaici da sanin yakamata, Mahaifinki ko mutum ne natsatse Mai ilimin addini sosai hakika ya samu matukar yabo bakin Al'umma, suna sonki sosai Amma Allah Bai yi Zaku rayu tare ba, abinda Kika yi ya tabbatar mun da tarbiyyan ki hakika da iyayenki na alfahari da ke, Allah ya baki iyaye na gari kema"
"Ameen Abbah nagode" ta fada sannan ta bi bayan Aliyu su ka bar falon.
Direct gidansu su ka wuce a falo su ka zauna. "Haba Fateema kin San tunanin da kike yi zai iya tado Miki ciwon ki Koh?" Ya fada Yana binta da idanu. Forcing murmushi tayi har sai da hakoran ta su ka fito "Wai Uncle me ye sa kake ce min Fateema?" Ta fada tana kukan manya wato yake. Shima murmushin ya Mata duk da ya San na ta na Dole ne "Fateema the name suit you best and I like it"
"A school ne kadai ake ce min Fateema"
"Na sani but am unique remember?"
Wannan karon ma murmushin tayi.
"Fateeeeema pls let it out barin shi cikin da Kika yi shi zai haddasa miki matsala fa"
Kaman jira ta ke ya Kara sa maganan kawai ta fashe da wani kuka Mai Kara da ratsa zuciya duk Wanda ya ji kukan ya sa abinda ke damun ta ba karamin Jin shi ta ke a zuci ba, saurin karasawa yayi gare ta ya rungumota Kan kirjin shi har cikin zuciyan shi ya ke Jin kukan na ta na ratsa ko wani sashe na jikin shi. "Uncleeee ni marainiya ce Banda uwa Banda uba" ta fada da karfi. Saurin rufe ma ta baki yayi Yana fadin "haba fatee ki godewa Allah cikin gata Kika taso wasu akan titi su ke kwana wasu da iyayen nasu Amma ba su samu kaso Daya daga cikin dari akan gata da wadatan da kike ciki ba, ki godewa Allah kaddarar ki ce haka" wa'azi ya mata sosai Amma Kuma Bai hana ta kukan nata ba har sai da ta gaji Dan kanta ta fara sauke ajiyan zuciya a haka bacci ya kwashe ta akan kirjin nashi.
Lallabawa yayi ya tafi da ita dakin shi su ka kwanta, shigewa ta Kara yi jikin shi sosai, gogan naka ko na maza yayi ya kyaleta ba abinda ya shiga tsakanin su sai dai Kara rungumeta da yayi kikam kaman ance za a kwace mishi ita.
A tare su ka farka da Asuba ya tafi masallaci ita Kuma ta gabatar da nata. Baccin safe ta ke Shirin komawa ta ganshi ya shigo cikin track suit blue Yana kokarin sa ka Trainers in da ke hannun shi, bin shi tayi da Kallo ya sakan Mata da killer smile in shi "kallon fa" ya karashe zancen da daga gira.
"Fita zaka yi?"
"Training, are you going?"
Girgiza mishi Kai tayi kafin ta tabe baki "sai ka dawo"
"Za ki sani ne yarinyar ki gama tabe bakin ki, I will let you today but soon tare zamu dinga zuwa" bargo ta ja ta rufe fuskan ta Kar ma yayi tunanin za ta bishi.
Ko daya dawo ba ta tashi ba, sai ma knocking da yaji ana yi, Yusrah ce the kawo musu abinci inji Ammah, amsa yayi ya na godiya a ranshi ya na fadin sai kace wasu sabon aure, wani zuciyar ne tace mishi and what's the difference? Saurin kawar da tunanin yayi ya ajiye abincin sannan ya koma dakin.
Patting Gashin ta ya fara yi har sai da ta farka "oyya tashi gari ya waye"
Turo bakin ta tayi tana kumbure kumbure, shi dariya ma ta bashi sai Kuma ya ga ta birge shi, Bai ta ba witnessing that side of her ba sai Yan kwanakin nan da ta zame mishi chewing gum. Hannun shi ya Kai Kan small lips in nata ya shafa lightly, tuni jikin ta ya fara rawa, Murmushi ya saki sai ji tayi ya cincibeta kaman bayi ya dire a toilet "oya brush your teeth"
"Albishirinki" ya fada bayan sun shiga kitchen
"Goro" ta amsa tana kallan shi kasa kasa
"Fari ko ja?" Shi kanshi dariya ya ke da ya fada
"Fari Kal Kal"
"Naki me Zaki ban goron albishir"
Shiru tayi alaman tunani sannan ta bude baki "me kake so?" A hankali ta yi maganan and there is no doubt yanda tayin yayi affecting in shi.
Folding lips in shi yayi kafin ya kalle ta directly into her eyes Yana Mata wani irin kallo da ke bayyanar da irin tsantsanr kaunar da ya ke mata, kasa cigaba da hada ido dashi tayi saboda abinda ta hango a idon na shi da sauri ta saukan da idon ta kasa.
"Za ki bani?" Wannan Karan a skin inta ta ji maganan daga kanta tayi ta ganshi tsaye a gefen ta dab da dab.
Daga mishi Kai kawai tayi don ba xa ta iya magana ba she can't believe he is affecting her har Haka.
"Shknn za muyi maganan" a hankali ya matsa kusa da ita gabadaya kanshi ya Kai kunnen ta "Maijiddah ta haihu"
Da sauri ta juyo ta kalle shi, daga Mata Kai yayi ba ta San sanda ta rungume Shi ba tana tsallen murna.
"Bari muyi breakfast muje please me Zan dafa maka?"
"Karki damu Mami ta hutashe ki tun safe su Yusrah sun kawo breakfast in"
Tsalle ta Kara bugawa kaman wata yarinya sannan ta ja hannun shi su ka tafi dinning in, Shi Kan kallo kawai ya ke binta dashi "so Haka ta ke in tana cikin farinciki?" He is getting to know everything about her little by little.
Bayan azahar su ka shiga kaduna, direct gidan Maijiddan su ka nufa bayan ya tsaya yayi Sallah a masallaci. "Mai jego Mai jego" Ta shiga tana kwalla kira
Nanah na ji ta ce "Zahrau ta iso"
Kaman Wanda aka tsungula tana shiga wurin Mai jiddan ta yi ta rungume ta tana Mata sannu sannan ta amshi babyn tana kallo "She looks like her dad Mom" gwalo ta yi wa Maijiddah, ita Kam Maijiddan abin dariya ma ya Bata "Wai Zahrau yaushe Kika yi baki har Kika koyi tsokana?" Nanah ta fada tana girgiza Kai.
"Hey Hajiya Aisha sorry na ganki na San matsalan kenan" dariya aka kwashe dashi gabadaya.
Tsaki Nana ta ja tana fadin "bakomai na San duk influence in Yaya Aliy" wani irin blushing tayi da duk Yan dakin sai da suka Dara.
"Inalillahi Yana ma waje wlh"
"Yayan nawa Kika bari a waje? Amma ba ki da karki" maijiddah ta fada tana binta da hararan wasa.
Ita ma miyar mata tayi kafin maijiddah ta Mika Mata key "bude Falon bakin ce please ki shigo dashi am coming"
Da kyar Aliyu ya yadda yadda shiga, a cewar shi shiga gida kanwa ba nasu bane sai da Zahrau ta Bata Rai sannan ya bita.
Kayan motsa baki aka fara kawo mishi kafin Zahrau ta kawo mishi baby "Uncle kalle ta so cute" murmushi yayi sannan ya amshi babyn ya tofa ma ta Addu'a "she is cute sosai Fateema, kina sonta?" Ya fada ganin farin ciki na daban da ta shiga since da ya fada mata news in haihuwan, Gyada mishi Kai tayi tana fadin "Kai sosai ma infact am obsessed with them" murmushi ya Kara yi "then ya kamata ki samu naki Kinga Kya dinga kallo everyday kina Jin Dadi ko?" Rufe fuskan ta tayi da tafin hannun ta tana dariya ita a dole she is shy. A Haka Maijiddah ta shigo ta same su, ta ji dadin daidaita kansu da suka yi though ta ji kunyan yanda ta tadda sun. Zama ta yi su ka gaisa da yayan nata sosai ya Mata barka da sawa baby Albarka.
250k ya ciro ya daura Kan showel in babyn sannan ya Mika ma Zahrau "oya Kai musu Dan su muma mu Nemo namu" Kai Uncle ta fada tana dariya. Lokacin Ibrahim ya iso xa su gaisa, fita Zahrau ta yi ta basu wuri suna tattaunawa, Mutunci ke tsakanin su sosai, All of them are Uniform men of course.
A gidan Aliyu ya bar Zahrau a Kan sai da yamma zai Zo ya dauke ta, ita dai a makale da baby ta wuni.
Musamman su ka Kira Ummiy suna Mata tsiya, kaman ta yi kuka da ke Dr Kabir na neman hanata zuwa da ke ita ma tayi nauyi, kaman ta yi kuka haka su kayi sallama bayan an tura Mata hoton baby ba adadi.
Nagode.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top