KHF 41
Hey, ya kuke? Fatan dai lafiya? Almdlh if so. Well, I didn't even plan of updating kwana kusa but my close friend (ayshatou) urged me to so I have no choice. Please check her stories Down hearted and I was created like this. Don't worry you will all thank me later.
Akan faffadan royal bed in shi ya ajiye ta Yana bin ta da lustful eyes in shi da ya can zuwa ja izuwa yanzu, cikin ido ya ke Kallon ta direct hakan ya matukar kashe ma ta jiki gabadaya jikin rawa ya ke yi, gam gam ta runtse idanuwan tana jiran Jin step In da zai dauka next.
Sai dai har ga Allah ba ta Jin za ta iya barin Aliyu ya aikata Abin da ya ke so a gare ta, Dan ita Kam ba ta shirya bashi hadin Kai ba sai dai ko inta karfi zai Mata hakan ko ba shakka zai tabbatar Mata da zargin ta wato jikin ta ya ke so ba wai inta yake so ba.
A hankali ya fara sarrafata, ita kanta yanayin da ya ke Mata ba karamin rikitar da ita yake ba har ta so ta bada Kai bori ya hau sai dai Kash, wani Abu ta ke ji a kasan zuciyan ta Yana fada jikin ta fa ya ke so, rintse idon ta ta Kara yi dam dam zuwa lokacin ko gogan ya riga da ya fita hayyacin shi, a hankali zagin da musgunawan da ya dinga Mata ya fara dawo Mata kaman a mafarki, Abu Daya da Aliyu Bai sani ba a waccan lokacin mugun rikon matar tashi hakan ba abin mamaki bane in aka yi la'akari da jinin fulanin da ke yawo a cikin jikin ta, Har kwanta da ke a asibiti fa yayi Amma still hakan Bai hana ya dai na kyarar ki ba, tunowa ta yi da alkawarin da ta wa kanta na ba za ta taba son shi ba Haka Kuma ta hakura da rayuwan aure in dai da shi ne.
A hankali ta fara kokarin janye jikin ta duk da jikin na so ya bada ita yanda ya ke reacting ga ko wani action na mijin na ta Amma Kash abunda ta ke ji a ranta ba zai bari, wani irin karfi ta ji yazo Mata Nan da nan ta janye jikin ta ta koma gefen gadon yayin da gabadaya jikin ke rawa.
Nufo ta yayi Yana so ya jawo ta ganin hakan yasa tayi saurin Mikewa ta nufi bakin kofa ta tsaya tana kyarma, idon ta ko har ya kumbura saboda kukan da ta fara tun dazu.
A hankali ya iya dago kanshi ya kalle ta gabadaya jikin shi yayi sanyi, idanuwan ko kace garwashi ne a ciki "Fateeeeema why" ya fada a hankali more like whispering.
Girgiza mishi Kai ta fara yi tana fadin "am sorry bazan iya ba" da hannu ya ma ta alamun me ye sa, Kai tsaye ta ce "zuciyana na tsargin jikina kake so Uncle ba ni ba" galala ya saki baki yana Kallon ta da kyar ya bude baki yayi magana "Zahrau ni?" Ya fada ya nuna kirjin shi, Banbarakwai ta ji sunan saboda ba ta taba Jin hakan a bakin shi ba "sharrin da Zaki min kenan Koh? Well, tunda jikin ki na ke so tashi ki fitan min a daki" a zuciye ya ke magana har Bai son lokacin da hawaye masu zafi su ka fara digowa daga idanuwan shi ba, wannan wani irin soyayya ne? Ita ma tsayawan ta yi tana kuka ba ta motsa ba, "Ki fitan min a daki kafin in illata ki ko" runtse idanuwan shi yayi gam har ga Allah Bai son ganin na ta a yanzu, wani irin zafi kirjin shi ya ke mishi ko da wasa Bai taba expecting kalman Nan daga gun ta ba, jin sheshekan kukan ta ya tabbatar mishi da ba ta fitan ba, wani irin tsawa ya daka ma ta "Ki fita nace ko" Ba shiri ta ruga ta bar dakin, Kan gadon ta ta tsaya direct ta cigaba da kukan ta "hakan na nufin da gaske jikin na ta ya ke so kenan?"
A bangare Aliyu ko kwana yayi Yana juye juye, kirjin shi ko kaman zai fito Tsabagen zafin da ya ke Mai, Ya Kai awa biyu Haka gabadaya jikin shi rawa ya ke yi jin da yayi zazzabi na niyyan zuba Mai ya sa yayi na maza ya tashi ya yiwo alwala Dan ko ba zai iya baccin ba. Ya Dade Yana rokon Allah akan matsalan auren shi, in Zahrau ba alkhairi ba ce a gare shi Allah ya cire mishi son ta ya raba su cikin lafiya Amma a lokacin ma wani irin soyyayan ta ya ji Yana Kara shigan shi, shi kanshi ya San fitan shi ba Abu bane Mai sauki saboda ba farat Daya ya fara son ta ba soyyayarta a hankali ya dinga shigan shi ta yanda shi kanshi bai Ankara ba har ya mishi illa, Sai dai Kam ya samu natsuwa sosai.
Ita ko tuni bacci yayi awon gaba da ita bayan ta gama kukan ta, Dama ba wani tada Mata hankali abin yayi ba, har yau ba za tace ta fara son Aliyu ko Aa ba ta dai San tana tausayin Kuma tana son kyautata mishi ga Kuma Sabo da tayi dashi na Yan kwanakin nan ba karya ta na jin shi a ranta Amma fa ko kwatan abinda ya ke ji Bata ji a ranta.
Bacci soyayya yayi bayan Sallan Asuba a dalilin natsuwan da ya samu hakan ya Bata Daman shiga kitchen ta hada musu abinci. Sai wurin 11:30 ya farka ya fito falon akan dinning ya same ta ta ci kwalliyan ta tana cin abinci hankali kwance, tabe baki yayi ya karasa Falon "Ina kwana". "lfy" kawai ya ce ya Mai da hankalin shi Kan TV da ya ke Shirin kunnawa.
"Ga abinci"
Ko tanka ta bai yi ba ita Kuma ta yi zaton Bai ji bane ya sa ta Kara magana "Bazan ci ba" ya amsa, shiru tayi jiki a sanyaye ta karaso Falon da niyyan bashi hakuri, daga ma ta hannu yayi Yana fadin "its okay, ban ji ci ne kawai" marairaice mishi da ta ke Shirin fara yi ne yasa ya tsallake ta ya nufi dakin shi don har ga Allah haushi ta ke bashi, sai yau ya tabbatar da Zahrau ba ta da tausayi ko kadan don ba zai Kira abinda ta Mai da yarinta ba sai ko zallan rashin hankali, Bathroom ya nufa direct yayi wanka ya shirya ko daya fito falon samun ta yayi a rakube a kasa jikin kujera sai kuka ta ke ko Kallon ta Bai Kara yi ba ya nufi kofa.
Ba tare da wani tunani ba ya tada motan da niyyan nufan Zaria, Yau kawai Mami ya ji Yana son gani, saboda ta Sha fada mishi abubuwan da ya ke ma Zahrau watarana sai yayi da na sani shiyasa ko tantama Bai yi ba akan maganan ta ke bin Shi.
Ko da ya Isa side inta ya nufa direct Yana ganin ta ya fara rokon ta Dan Allah ta yafe Mai duk abinda yayi Mata har ya Bata ma ta Rai, sosai mamin ta tsorata da yanayin shi tuni ita ma hankalin ta ya tashi, uwa da da sai Allah, rudewa tayi tana tambayan shi me ke damun shi, ita bata taba rike shi ba, kin sanar Mata komai yayi illa dai ya ce Mata yana cikin matsala ne ta Taya shi da addu'a Kuma ta yafe mishi. Karshe dai ita ta dawo ta na bashi hakuri a gunta ya wuni gabadaya ranar tana mishi nasiha sai dare ya nufi dakin shi.
Bashi ya koma Abuja ba sai ranar Monday, direct wurin aikin shi ya nufa, inda aka tura su kwas oyo na kwana hudu ba musu ya amince domin ko zabi aka basu, ko da ya je gidan ya San ba ta Nan domin ko ya sa driver ya dinga Kai ta asibiti hakan yasa Nan da nan ya hada kayan shi ya nufi Ibadan.
Sai ranar Saturday ya dawo da Rana, sallama yayi Amma ba a amsa ba Hakan ya sa yayi tunani kila tana bacci a daki ne, wanka ya shiga yayi sannan ya nufi restaurant ya siyo abinci. Har dare Bai ji motsin ta ba ji yayi ya kasa jurewa ya je dubo ta dakin ta ya duba sai dai wayam ya gani ba kowa da sauri ya leka bayi Nan ma dai shiru dayan dakin da ke facing na ta yayi saurin budewa, a can jikin bango ya hango ta ta takure sai kyarama ta ke yi da sauri ya karasa wurin ta ya yaye bargon da ke kanta.
Tana ganin shi ta kankame shi tana kuka, zafin radau ya ji jikin na ta, "Tun yaushe Kika fara ciwon" ya tmby Kai tsaye. Shesheka ta fara yi tana magana "yau yau kwana uku". "meyesa to ba ki ga doctor ba a asibiti?" Girgiza Kai kawai tayi sannan tace "shine kayi tafiyan ka ko? Kuma Ina ta neman ka a waya Bai shiga" murmushi Mai ciwo kawai yayi sannan yace "tashi mu je asibiti"
Kirjin ta ya gani tana dafewa ta wurin saitin zuciya hakan ya sa shi tsorata sosai cincibota yayi sannan ya ja hijabin Daya gani a gefen ta ya sa mata takalmi ma shi ya sa mata su ka nufi asibitin da ta ke Siwes in.
Fada sosai Doctor ya mishi akan a guji baccin ranta saboda halin da za ta shiga sanin yanayin ciwon na ta sai a dinga gudun matsala don ko kiris ya rage ciwon na ta ya dawo gadan gadan Allah ne dai kawai ya rufa asiri.
A gida shi ya dinga Kula da ita ta ci abinci sannan ya bata magani ta Sha da su ka Zo kwanciya ma ki tayi Wai ita sai dai ya kwanta a Nan shi ma ba musu ya gyara yayi kwanciyan shi duk bayan mintuna sai ta farka ta lalubo shi ta ji Yana Nan ko ya fita ganin haka ya sa ya jawo ta jikin shi ya rungume kawai, da farko jikin ta ya fara rawa Amma Jin ba abinda ya ke Shirin ma ta ya sa ta kwantar da hankalin ta yi baccin ta.
Tun ko daga ranar ta fara like mishi ko Ina ya ke tana kusa dashi har ko da dare Inka ga ta kyale shi to wurin aiki su ka fita dukkansu ba yanda ta iya ba, abinda ba ta sani ba Aliyu dauriya kawai ya ke yi Amma abinda ya ke ji ba ma a magana kwanciyar hankalin shi Daya ganin yanda ta damu dashi yanzu sosai ya San ba shakka ko da ba ta son shi har yanzu ba tantama ba za ta iya rabuwa dashi ba.
Amma Kuma duk ya Zama wani iri yayi baki ya rame Kai kace ya dade Yana ciwo.
Ranar dai da abin ya Kai shi makura ya nemi ta bashi hadin Kai ta zame mishi kaman gunki daga karshe ma Kara ta sakan Mai ba shiri ya kyaleta ya bar ma ta dakin, Ranar in ka ga yanda ya koma Kai kace ba soja ba rasa abinyi ma yayi duk ya fita hayyacin shi, ko washegari da safe da tazo dakin nashi ko Kallon ta Bai yi ba tunda ga ranar ya fara share ta domin kuwa ba za ta dinga hada Mai zafi biyu ba ba yanda za ayi ace kullum tana jikin shi Kuma ta hana shi hakkin shi ai shi ba dutse bane Yana da feelings, da gaske ya Mata ta yanda ita kanta tsoron ta je kusa dashi in ta ke ba ma Kuma wani maganan kirki da ke shiga tsakanin su saboda kullum fuskan shi a daure ta ke ba wurin yin wargi.
Abin mamaki wani irin rama ya ga ta fara yi har duhu tayi har ta so ta fishi ma saboda ya fi nunawa a jikin ta kodan shi Yana da karfin hali ne? Daga baya Kuma ciwon na ta ya fara barazanar tashi tuni ya sauko ya fara jawo ta a jiki Yana lallashin ta ta fada mishi me ke damun ta Kai tsaye ta ce mishi shine, shiru yayi Yana mamakin wannan alamari na Zahrau, ya ma rasa ta inda zai bullo Mata Wai shin me ke damun ta ne Haka?
"Me kike so in Miki fateema?"
"Ni ka daina share ni ka na daure min fuska ban so"
"Dole ne ta sa haka wlh ba yanda Zan yi ne" ya fada yana girgiza Kai.
"To Mena maka?"
"Ke ma kin sani, let me be straight forward to you ma, kingane ba yanda zanyi in barki kullum kina jiki na Kuma kice ba abinda zai shiga tsakanin mu, I mean ni ba dutse bane ko katako Fateema ina da feelings tun da dai ni Dan Adam ne sannan Kuma in na neme ki ki ki bayan kinsan da cewa tsinuwan mala'iku ne zai sauka akan ki ni kuma banson hakan ya faru da ke, After all claiming kike jikin na ke so ya kike so inyi? So this is the better solution kawai na bar Miki jikin ki Nima please let me be Kuma ki daina tada hankalin ki da kin damu Dani ai ba Haka ba" kuka ta sake kawai ya saki baki Yana Kallon ta ko da wasa bai taba expecting Haka ta ke ba, kowa yabon halayen ta yake yi da alamun Shi kadai ya san that side of her.
Hakuri ta fara bashi still tana kuka sannan ta fara fada mishi dalilin ta Daya sa ta kasa sakin jiki dashi gabadaya Wanda ba akan komai bane illa yanda zuciyan ta ke yawon tuno Mata da abubuwan da su ka gabata tsakanin su su biyun.
"Fateema ke ba Kya yafiya ne" girgiza Kai ta fara yi tana fadin "Wlh Uncleeee na yafe sai dai na kasa manta da abun Yana yawan fado min sai inji gabadaya ma haushi kake bani"
"Karya kike ba ki yafe ba da ba Haka ba ai za ki manta"
"Wlh wlh Allah na yafe maka, Nima ban San yanda Zan yi ba ne kawai, halina ne riko tun Ina karama bansan yanda Zan yi yaki dashi ba ko na yafe in mutum ya min abu sai in dinga Kallon shi da shi ko da yaushe sai inji Yana bani haushi wani lokacin Allah kuwa kaga kaman yanzu Summy kawata ta taba min abu akan Ya Abdulrahmah da yace Yana so na, tun a lokacin ta bani hakuri Kuma na hakura Amma wlh har yau da ya rasu Ina Kallon ta da abun sai in dinga Jin Ina Jin haushin ta shiyasa ma ban cika neman ta sosai ba" ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Amman kinsan babu kyau ko"
"Nasani"
"So Dole ki nemo hanyan da za ki gyara ki dinga yawon Addu'a ni ma Zan dinga ya Miki don wlh ba Zan boye Miki ba Ina cuta sosai, Dan har na fara Jin kaman in hakura da ke duk da ko soyayyan da na ke Miki zai fi akan kiyita kwasan zunubi" da sauri ta juyo tana kallan shi, Saurin rungume shi tayi tana fadin "Dan Allah ka yi hakuri wlh ba Zan iya rabuwa da Kai ba" shi ma rungume tan yayi Dan ko ya San da hakan. "Its okay" ya fada Yana shafa kanta "ki shirya kayanki gobe za mu tafi Zaria"...
Okay, I know, I know, na sani sosai most of you are disappointed with me ko? Let me say it am sorry saboda tun can I didn't plan on letting it be in this chapter, maybe the next one or even in two chapters to come. Miye ma na damuwa? If can I remember ku ke bani advice akan ya kamata Zahrau ta rama so ra'ayinku na bi tun farko. Sorry dai still...
Till we meet in next chapter soon, currently I've start working on it.
Nagode
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top