KHF 4
December 2016
Abbah ne ke magana rai a bace, bai taba jin an mi shi raini wayau na karshe ba irin yau, an mai da shi karamin Mutum mara kima da daraja duk a sanadiyar Neman aure, kaman an rasa diyar aure a duniya sai yar wadanda ba su San kima, mutunci da darajan dan Adam ba.
Zuwan Baffah da Babban Yaya Kaduna kiri kiri Dad ya nuna ma su ba zai bada diyar shi ba in har basu daga auren ba, abinda ke basu bai wuce ganin Dad din ba talaka bane balle a daga mishi kafa, yau aka ce za a aurar da diyar shi zai iya mata komai a ranar kuma bana kushewa. Take taken shi suka gano inda ya dosa. Ba karamin fusata su kayi ba sai dai inda abin ya zo da sauki daga Baffahn har Babban Yaya duk masu hakuri aka tara.
Abin duniya suk sun taru sun ma Abbah zafi ta ya zai fara kallon duk dimbin mutanen da ya gayyata ace an fasa aure, shi za a kunyata a idon duniya kan abun duniyan da za a barta. Kafa ya karkadawa ya na Neman mafita sai dai ya rasa ta ina zai fara ma.
Lura da tashin hankalin da Baffah ya lura dan'uwan shi ya Shiga ba karamin damunshi yayi ba. Damuwar shi tashi ce shakka bbu. Murmushi yayi ganin Alamun mafitan da ya samo musu zata iya fisshe su.
"Abbah ga shawara sai dai kafin mu yanketa zan so a kira Aliyun mu tambaye shi ko akwai wacce ya samo a bisa sharrudan da ka sa mai"
"Baffah kenan ka fada min shawaran, ina zai samo mata cikin yan kwanakin nan na sa masa sharuddan ne saboda lokacin ina tunanin akwai hope in gyaruwan Al'amarin"
"To shknn, me zai hana kawai mu hada su da Fatima tunda a yanzu haka ita kadai ce muke da ikon aurarwa"
Murmushin da bai San lokacin da ya fito ba Abbah yayi, ji yayi sakayau damuwar shi ta kau "Alhamdulilah Gsky kayi tunani mai kyau, Allah ya sa alkhairi zamu kulla"
Ghen Ghen yau ake yinta.
••••••••••
Mami shiru tayi tana sauraren Abbah inda yake labarta mata hukunci da suka yanke shida dan'uwan na shi. Sai da ya kai aya sannan ta dube shi "haba Abbah Aliyu fa da yan matan gidan nan ko kadan ba jituwa su ke ba Dan in za a daka ta tasu cewa suke ya tsane su, anya ba ka ganin da matsala a hada su da Zahrau, bama shi yace yana so ba."
Murmushi mai sauti Abbahn yayi sannan ya ce "Mami kenan ina tsangwa man da ya musu kan karatu ne kafin yaran naki su yi hankalin Kansu, ina da yakinin Aliyu zai kulan min da Fatima in Sha Allah, ke dai kawai kuyi addu'an hakan alkhairi ne"
"Shikenan Abbah tun da kace haka Alkhairi ai kullum shi muke nema" Ba wai dan ranta ya so ta fadi hakan sanin cewa ba abinda zai sa Abbah ya canja ra'ayin shi.
A bangaren Ammah ko da aka fada mata fatan alkhairi ta wa abun domin ita dai bata da haufi akan Aliyu mutum ne nagarttace gashi kuma tuwo na maina za ayi.
Babban Yaya ma yayi Na'am da abin Wanda haka yake wurin Anty Zainab da Anty Rukayya ma. A cewar su Aliyu zai kula musu da Zahrau ko shakka babu. Ni dai nace anya kuwa?
••••••••••••••
Zaune ta ke tana karanta English Novel a wattpad, kwannan duk shi ke debe mata kewa sai ko karatun da ta kanyi a gidan cause tunda aka koma school day take yi bata yadda ta koma school din ba ta kafe akan sai January bayan mid semester.
Shahida tayi Sallama sannan ta sanar mata da Abbah na nemanta a Babban falo. Haka kurum taji gabanta ya fadi "lafiya Abbah ke nema na" ta tambayi kanta, tunawa da tayi ba kyau bad thought ya sa tayi saurin kauda duk wani tunani da ke ranta ta dauki gyalenta ta yafa sannan ta bi hanya Babban falon domin amsa kiran iyayenta.
Gab da zata karasa falon ta hango Aliyu da Abokin sa Umar sun fito daga falon. Rashin a hade yake kaman wani mayunwacin zaki, haka ba wani Sabon abu bane a wurin ta, Sunkuyar da kanta tayi sai da ta zo gab dasu sannan ta dube su ta kasan ido. A hankali ta furta "INA wuninki"
"Lafiya kalau Malama Zahra" Umar ya amsa, Aliyu kam harara ya bita dashi. Ita kam ko a jikin ta wai an tsikari kakkausa. Gab da za ta Shiga falon ta ji Umar na ce mishi "Bawan Allah ba fa ita ta maka laifin ba da kake nema ka huce akanta"
Sallama tayi suka amsa Mata, kaman yanda ta zata su biyu ne a falon. Zama tayi ta gaida Abbah sannan ta juya ta gaida Baffah.
"Fatima ya makaranta?" Baffah ya tambayeta
"Lafiya kalau" ta amsa
"Ma Sha Allah, Allah ya bada sa'a"
Kanta a kasa ta amsa da Ameen "ki bamu aron hankalinki nan Abbah yi mata bayani"
Gyaran Murya Abbahn yayi sannan ya dube ta "Fatima natsu ki saurare ni, mun yanke hukunci akan ki Wanda mu ke fatan zaki mana biyayya"
A hankali ta furta "In Sha Allah Abbah"
"Mun hada ki Aure da Yayanki Aliyu nan da sati biyu..." Dif taji gabanta ya fara dukan Uku uku , A firgice ta dago tana kallon Abbahn, gani ta ke kaman kunenta ba su ji da kyau, ko dai mafarki take aure ita? Uncle Aliy? How can that even be possible kuma ma wai in 2 weeks time. Maganganu taji Abbah da Baffan nayi Wanda yayi kama da nasiha sai dai ita ko fuskanta ba tayi. "Ta shi kije shikenan"
Da sauri ta tashi ta nufi side in Mami dan ita zata tabbatar mata da abinda kunnenta yaji.
A falo ta iske Mamin na kallo, jikinta ta fada sannan ta saki wani irin razannen kuka da ya rikita ita kanta Mamin. Dago tayi tana lallashin ta cause ta gane Zahrau n taji maganan auren nata ne "Mami Dan Allah kice min su Abbah wasa suke" Maganar ne ya katse saboda sheshekar kukan da take yi.
Deedat da Hamza ne suka shigo falon suka iske su a haka.
Taruwa sukayi su kayi suna bata baki game da yi mata nasiha abinda basu gane ba binsu kawai take da kallo ba wai tana fahimttan abinda su ke fada ba Tana Neman yiwuwar abin ne dai dai ko ta INA bata gani ba. Shi kanshi Hamza sai da ya jinjina abin cause kusan a gaban shi komai ke faruwa.
A ranar da labarin ya iske Maijidda lokacin ta shirya ita da Nanah suka wa Zaria tsunke saukin abin ma an kusa mid semester break. Ummiy ma Dan dare yayi ne ta Bari washegari tayi asubanci saboda ba zasu iya barin Zahrau ita kadai cikin situation in ba a cewar su they will did everything possible su ga auren bai yiwu ba.
Yau ake yinta...
Ni dai na ce mu je zuwa
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top