KHF 39


  Sun fi minti goma a hakan kowannen su na sauke numfashi, a hankali ya cire ta daga jikin shi ya hade goshin su Yana Kallon cikin idanun ta Yana aika mata sakonnin daga nashi idon, kaman Mai jin bacci haka idon na shi su kayi gani tayi ba za ta iya jure eye contact in ma ta yi saurin lumshe idanuwan ta.

  Idanuwan na ta ya bi da kallo ya ga sun mishi wani irin kyau na daban hannu ya sa Yana shafa idanuwan kafin yayi faking in su da lips, tsigan jikin ta taji Yana tashi Kara lumshe idon ta yi da kyau gabadaya jikin ta sai rawa ya ke.

   A hankali lustfully eyes in shi su ka sauka kan lips wani irin abu ya fara ji Yana fisgan shi Amma Kuma Yana gudun ta yi mishi mummuna zato, ya fiso ya bi komai a hankali, Yanda zai ma ta proving son da ya ke mata kaman yanda ta bukata.

  "Za ki kwanta a nan ko mu tafi can gidan" ya fada Yana referring da gidan shi na Zarian.

   "Can gidan" ta bashi amsa sannan ta bude idon ta

  "Tashi mu je toh" Ita ji tayi ma tana kunyan shi hakan yasa ta sadda Kai kasa tana wasa da hannu black abayan da ke jikin ta.

  "Ko in dauke ki ne?" Daga giran shi yayi sannan ya kashe mata ido Daya.

  Smiling kawai tayi sannan ta Mike a ranta tana fadin "Namiji bashi da kunya"

   "Kaya na na dakin Mami"

    "Mu je mu dauko?". Saurin girgiza Kai tayi tana zare idanu, ya gane kunyan mamin ta ganshi da ita ta ke ji.

  "Shknn Zan sa Shahida da Yusrah su dauko ko Kuma Hamza"

Gyade Mai Kai tayi sannan ta bishi, Yana gaba tana baya ganin ba ta sauri ya sa ya rike hannun ta su ka nufi gidan nashi tanan cikin gida su ka wuce da ya ke akwai hanya.

  A hanya su ka hadu da Deedat zai tafi dakin shi tun zuwan su sai yanzu su ka hadu.

  "Ah ah ah Malaman makaranta" Aliyu ya fada cike da tsokana

  "Ina wuni Yaya" ya fada yana sadda Kai kasa.

  "Lfy kalau, ya students"

Amsawa yayi sai sannan Zahrau ta gaishe a kunyace ci ke da jin kunyan yanda ya gansu da Uncle in.

  "Baby sis yau Kuma kunyata ake ji ne?"

Saurin sa Daya hannun ta tayi ta rufe idanun ta, hararan shi Aliyu yayi "Mata ta kake tsokana? Toh maza find your way"

  "Kai Yaya Nima dai nayi zuciya auren nan Zan yi"

  "Da ka kyauta Mana sosai"

Sallama su kayi ya wuce su ma su ka tafi.

  a Falon gidan su ka yada zango, tana zama wayarta ya fara ruri. Sumayya ke kiranta, kunyan daukan wayan ta ji saboda ta Dade ba ta nemi sumayyan ba sai dai ita ta neme ta. "Pick the call Mana" ya fada Yana kare Mata kallo, Daurewa tayi tayi picking "Sumyyyy" ta fada a hankali.

   "Zahraaah ba ki da kirki Allah"

   "Sorry Sumayya nasan nayi laifi Amma Ina neman gafara"

   "Au sorry fa na manta Matan aure na Kira at this time of the night"

  Murmushi kawai tayi sannan tace "Allah ya shirye ki"

  "Hmm Anyway, na Kira in fada miki ansa ranar biki na ne"

  "Serious? Yaushe? Wa ye angon?"

"Dagaske na ke, December ending, da Al-ameen"

"Allah sarki toh Allah ya nuna Mana Amaryar Al-ameen Allah yayi" dariya Sumayyan tayi sannan tayi ending call in.

  Juyo ta yi taga Yana Kallon ta, Abin ma mamaki ya ke Bata, kadan daga cikin ikon Allah kenan. Ta ayyana a ranta.

    Tana fara Jin bacci ta fuske ta Mai sai da safe, kala bai ce Mata ba illa dai sanyin da jikin shi yayi, shi kanshi bai da niyyan wani Abu ya shiga tsakanin su yanzu sai ya koya Mata yanda za ta so Shi.

  Ba laifi ta kan Dan sake kadan su yi hira Amma ba Dan ranta na son hakan ba, shi ma ya fahimci hakan shiyasa lokuta da dama ya ke kyaleta sbd Bai son takura ma ta duk da hakan ba karamin ciwo ya ke Mai ba, da Yana da dama da ya cire zuciyan shi ko ya huta da kaunar da ke addaban shi.

  Ranar jajibari da safe ya kawo ma ta dinkunna da yasa aka Mata har kala biyar, tayi mamaki ganin tana da sabbin kayan da aka sa Mata a lefe wadanda ba tayi using ba, ta dai yi godiya kawai ta amsa.

  Haka ma washegari Sallah, aiki ta yi sosai na kala kalan abinci da abin Sha su Yusrah su ka Taya ta da ke su Ammi na da masu aiki ga Kuma Ya'ya'n yan'uwa dasu ke gidan yanzu.

  Aiko abokan shi na cikin Zaria sun zo sosai hadda wasu daga kaduna. Sai Ranar yawon Sallah su ka je Kallon Hawa tare da su Hamza da yaya Deedat gabadaya, ita dai Sallahn ba wai ya Mata Dadi bane saboda ba su Ummiy sai ta ji wani iri, ya zagaya da ita gidan Yan'uwa da abokanan shi karshe su ka je Family house insu da ke Unguwan alkali aiko sunyi farin cikin ganin su sosai.

  Zuwa yanzu Zahrau ta gama amincewa Uncle Aleey na son ta da gaske ganin yanda ya ke kokarin kyautata ma ta ita in ma tana kokarin yin hakan sai dai har yanzu ba ta gama sakin jiki dashi ba ga zancen son shi da ba ta ji har yanzu, ta lura gudun raini ya sa ya ke share ta sometimes, ita kanta tana so ta canja but she just can't.

   Some days bayan Sallah su ka tafi kaduna tare da Ummiy da ta zo Zaria, da ke an fara shirye shiryen bikin Nanah, Gidan Anty Rukayya ya sauke su direct sannan ya wuce ba tare da wani maganan kirki ya shiga tsakanin su ba, ta lura kwana biyu fushi ya ke da ita but she choose to ignore it.

  A can su ka iske maijiddah cikin ta ya fito sosai, nan fa Ummiy ta sa ta a gaba tana tsokana duk da ita ma tana kunshe da na ta karamin cikin.

  Biki yayi mutane Kuma yayi armashi, Bridal eve su ka fara yi ranar Wednesday a gidan Anty Rukayya sai washegari aka yi kamu a guest house in Baban Nanah, Komai su ke bukata Ya Aliyu ke Kiran Zahrau ko su Ummiy su sanar dashi.

  Ranar Juma'a bayan an sauko daga masallaci aka daura auren a nan kinkinau, Babban Yaya ne waliyyin Amaryar.

  Da yamma motocin daukan Amaryar su ka isa gidansu da ke Unguwan rimi, bayan la'asar aka Kai ta can domin yin sallama da iyayen ta.

  Yan matan amaryan da yayyin ta so su kayi su Bata musu lokaci a cewan su haka ake yi a al'adance.  In akwai abinda Aliyu ya tsana ya biyo bayan African time, ga Yamma na Kara yi ga Kuma Shirin event da za su yi. Wayan shi ya ciro ya Kira numban Anty Rukayya ya na Mata complain.

  Su na zaune su na hira abin su fuskan Amarya a rufe an ga ma Mata nasiha sai gani su kayi Anty Rukayya ta shigo dakin ta dago ta sun dauka wani magana za suyi sai su kaji tana fadin "In ba za kuje yanzu ba kuyi zaman ku mu kam munyi gaba" habawa da gudu kowa ya taso su kayi waje.

 
  Daman a motan Aliyun za a Kai Amarya direct can Anty Rukayya ta nufa tare da wasu Aunties inta.

  Gidan iyayen shi aka kaita da ke a Abuja za ta zauna.

  Dinner za ayi a crystal garden by 9 pm za a fara, Gudun ba ta tym ya sa Amarya da kawayen ta su ka shirya da wuri, Aiko 8:30 dai dai Abokan angon su ka iso sunji dadin rashin African time in da aka yi.

  "Alhmdlh yau ba za mu Sha mita ba gun oga" Salim ya fada cike da tsokana Yana kallon Aliyu.

  Murmushi yayi "Ba kaman bikin wasu ba bah"

  Dariya Salim in yayi ya na fadin "Zan Rama"

  Bayan motan Salim aka budewa Amaryan ta shiga ita da angon ta, kawayen ko Motoci su ka nema su na shiga.

  "Ke zo muje mu shiga motan mijin ki" Ummiy ta ja Zahrau su uku su ka nufi motan.

  Murmushi ya sakan musu sannan ya bude seat in Mai zaman banza "Bismillah madam" ya fada Yana Kallon Zahrau.

Ita abin ma mamaki ya Bata ganin ta manta when last ya sakan Mata fuska sosai haka.

Mai da idon shi yayi kan maijiddah "ke Kuma a hakan zaki fita da dare" saurin sunkuyar da kan ta tayi "Mata dai akwai bidi'a Zan nemi mijin naki ai, ku shiga mu tafi"

  A whatsApp group in su Ummiy ta tura message Uncleeee will never change.

    Maijiddah: Allah ma ya taimake mu Manyan veils mu ka sa.

   Ummiy: Wai Gsky Zahrau kina kokari, ko da yake na ga wani Kallon so yake bin ki da shi mu ma ya raina wa wayau.

  Zahrau: me ya Miki? Daga fadin gsky? Tausayin ku ma yaji shi.

  Maijiddah: Eyyeh!! Love tin tin su Zahrau an kamu

Ummiy: I can see, na yi shiru tunda depending mijinki kike Antynmu.

 
  Parking yayi wurin da Motocin da suka iso su kayi sannan su ka fita, 11:45 pm su ka bar wurin dinner in ba wai Dan an tashi Aa Aliyu ne ya sa ka su a gaba hakanan su ka hakura su ka biyo shi.
 

   Washegari, aka shirya Kai Amarya gidan ta da ke Abuja, bayan azahar aka tashi Nan da nan ko su ka isa, Gida yayi gida Ma Sha Allah komai ya ji, Amarya dai ta Sha kuka rabuwa da gida.

  A nan su ka kwana gabadayan su hadda Zahrau ga mamakin ta Aliyu bai ma ta magana ba, Sai Washegari bayan sun tafi ita ma ta shirya komawa gidan ta.

  "Wai ke ma tafiya Zaki yi?" Nanah ta tambaya kaman za ta yi kuka ganin Zahraun na hada akwati.

  Dariya ma ta Bata "Nanah Aisha kenan, Nima gida na Zan koma"

  "Kai Dai ba ki da kirki Allah Ina ba nisa ki bari sai anjima Mana"

  Girgiza Kai tayi "Akwai abinda Zan yi gobe Zan je asibiti" ta fada tana danna wayanta da alamun Kira ta ke.

  Sallama aka yi daga dayan bangaren ta amsa.

  "Fatima..." Ya fada alamaun Yana sauraron ta

  "Nace Daman Ina son tafiya gida ne". Jim yayi kafin yace "okay, I will be on my way"

  Cikin minti Ashirin ya iso gidan ya Kira ya shaida Mata.

  "To Amarya ni Zan wuce" hararanta Nanah tayi "Umma ta gaida Ashha tun da baki da kirki"

  "Sorry, kawata Gobe in na dawo asibiti Zan zo in Sha Allah, Daman Maman khalipha tace Zan kawo ta kinsan ita ma suna da biki a kano ne so ba ta sa mu zuwa naku ba sai yau ta dawo ita"

Tabe baki Nanah tayi "Na tmby ki ne"

  "Allah ya huci zuciyan Amaryar Umar faroukh ni dai na tafi"

Murmushi Nanahn tayi "Shknn Zahrau"

  Ko kafin ta karasa ya bude Mata motan, sallama ta mishi kafin ta gaishe shi, Yana murmushi ya amsa Mata "Har an gaji da gidan Amaryan ne?"

  "No akwai abinda Zan yi a gida ne"

  "Okay, Allah sarki baiwar Allah kin barta da kewa ita kadai"

Tabe baki tayi "Sabawa za tayi kaman yanda na Saba"

 
     Some weeks later

Zuwa yanzu Zahrau ta gama amincewa da son da Uncleeee ke mata ta gani a idon shi, a aike ce sannan Kuma ta ji da kunnen ta sai dai me? Tausayin Shi ma ta koma tana ji Still ta kasa sakin jikin ta gabadaya dashi though dai akwai improvement sosai.

  Sai dai me? Kwatsam kwana biyu ta fuskanci canjin yanayi daga wurin shi, Fuskan shi kullum a sake ya ke Amma kwana biyu gabadaya ya koma ta Uncleeee in da ta sani da Wanda take tsoro kaman Azra'ilu, ya daina Jan ta da hira ya Kuma daina shi shige Mata magana ma sai ya Kama ya ke hadasu.

  Haka kurum ta ke Jin hakan bai Mata Dadi ba ko ba komai ta farawa Sabawa dashi sosai, to ko dai wani Abu ke damun shi?

  Hello my people, Let me apologize first, am so so sorry.
Dukkan ku na ga messages inku ku ma ina godiya sosai sosai sai dai Kuma Ina Mai ba ku hakurin rashin samun update akai akai, Am in school, things are getting complicated, free time in kalilan ne and I have many other schedules. So ban mu ku alkawarin update akai akai ba sai dai na San I will be trying best. Hope you will all bear with me? Thank you once again.
  

Happy Eidul Kabeer in advance

And have a blessed and great Arfah day.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top