KHF 37

   Kala bai ce mata ba har su ka isa gidan ita din ma shiru ta yi har su ka Isa, a tare su ka karasa cikin gidan sai dai kowa hanyar dakin shi ya nufa, ita dai burin ta bai wuce ta ganta kan gado ba saboda gajiyan da tayi ranar gabadaya.

  Ruwa ya watsa sannan ya canja kayan jikin shi zuwa light jallabiya, Falo ya fita ya kunna TV, Wayar sa ya ciro yayi dialling numban ta.

  Har za ta kwanta ta ga Kiran nashi kaman ba za ta yi picking ba Kuma sai ta daukan.

   "Ki fito falo" kawai ya ce mata ya katse wayan.

  Dogon hijab inta da ta cire ta dauka ta Mai da sannan ta fita Falon.

  A hankali ya dago ya kalle ta bayan ta zauna ji ya ke kaman ya tashi ya rungumo ta tsabagen soyayyarta da ya ke ji Yana yawo a jinin jikin shi gabadaya.

   "Pls Ina son Shayi" ya fada yana Kallon ta ta kasan ido

   Ba ta ce komai ba ta nufi kitchen in ta dafa Mai shayin da ya ji kayan kamshi, kan stool ta aje Mai cup, flask da spoon.

    "Thank you" ya fada yana kare mata Kallo

  Ganin ta tafi daki ya sa yayi saurin kiranta "dawo Ina son magana da ke"

  Ba musu ta dawo ta zauna, kusa da shi ya nuna ma ta ta matso ta zauna.

"Fatima" ya Kira sunan ta, Dan dagowa ta yi ta kalle shi sannan ta sadda kanta kasa.

   "Me yasa na Kira ki ba kiyi picking ba"  shiru tayi ba ta ce komai ba don ko ba ta da abin cewa.

"Naga Alaman you don't even Miss me ko kadan ko?"

  "Dago kanki muyi magana Mana" ya fadi a hankali, dago kanta tayi Amman ba ta facing in shi.

   "Ba ki son Zama da ni ko?" Girgiza mishi Kai kawai tayi

"Dan Allah ki dinga bani amsa, kinsan i hate all this ban son ki yi provoking Ina inzo inyi abinda Zan zo Ina da na sani, help me pls"

  Tasowa yayi ya karasa inda ta ke, a kasa take zaune Daman, gab da ita ya je ya zauna, da sauri ta ja baya, Girgiza ma ta Kai yayi ya kara matsawa kusa da ita dab da dab ta yanda su kan iya jiyo numfashin junansu, Tsabagen tsoro ji ta ke kaman kirjin ta zai fito Shima ya fahimcin hakan sai dai Shima nashi kirjin bugawa ya ke sosai kaman zai fito fili.

  Hannun ta ya riko duka biyu ya zuba ma ta fararen idanuwan shi cikin na ta, saurin sadda Kai ta yi kasa ya sa hannu a fuskan ta ya dago ta ta yanda su ka fuskanci juna, "Fatima" ya Kira slowly da wani rin murya da shi kanshi bai San yana da ita ba.

    "Am sorry please kinji" ya fada cikin rawan murya, gyade kanta tayi da sauri saboda ita har ga Allah a takure ta ke ta kosa ya sake ta.

   "Na San ba kijin dadin Zama dani kawai ba ki da choice ne Amma ni Ina son kasancewa tare da ke, Dan Allah ki bamu Daman mu fahimci juna ko ma samu Daman albarkan wannan aure na mu da ya fita daban da na mutane" a hankali ya ke maganan ga wani irin rawa da muryan nashi ya ke daga ita har shi gabadaya jikin su rawa ya ke sai dai kowa da nashi dalilin rawan jikin, ita dai zallan tsoro ne da ya mata katutu daman Zahrau da tsoro balle ga dodon a gaban ta gabadaya, shi ko wani irin shauki ne yasa haka, zuciyar Shi sai harbawa ya ke, hannun ta da ya rike ba karamin affecting in shi yayi ba Yana Jin kaunar ta a kowani sashi na jikin shi, ji ya ke kaman ya jawo ta ya rungumeta kam kam inda dama ma ya maida ta jikin shi gabadaya. There is not doubt ya sa sakan yan abubuwan da ya dinga ma ta a baya ne ke bin shi, he don't even know how to confront her and confess his deep and endless feelings for her, Amma dai ya daukarwa kanshi alkawarin koya mata son shi.

  A hankali ta yi kokarin zare hannun ta daga nashi Amma ba ta yi succeeding ba "Uncleeee" ta fada tana Kallon cikin idanun shi, ganin irin Kallon da ya ke mata ne ya sa ta dauke idon na ta  saboda there is no way za ta yi believing abinda ta ke gani cikin idon shi, ajiyar zuciya Mai karfi ta sa ke sannan ta ce "Am sorry but you are selfish" a razane ya dago Yana Kallon ta, gyade mishi Kai ta yi "Na San kana komai ne saboda gudun fushin Ammi da Abbah akan ka Amma ba matsala Kila kaddara ta ce hakan" ta fada kafin ta saki wani irin kuka Mai sosa rai.

  He is speechless, ya ma rasa abinda zai yi ga kukan ta da ya ke Jin har cikin zuciya, Handkerchief in shi ya dauko ya Mika mata bayan ta yi calming kan ta ta rage kukan, he feels so guilty Dan tunda har ta iya bude baki tayi magana abin ba karamin cin ta yake ba Sarai ya San halinta, she hardly talks ma sai Kuma da alamun za ta yi riko"

  Ba musu ta amsa ta share hawayen ta "Bakomai as Always za ka samu abinda kake so" ta fada tana kokarin tashi.

   Riko hannun ta yi ya maida ta zaune "No let's talk please, spill it out Dan Allah ba Dan ni ba"

   Ba musu ta cigaba da magana "Tun tasowa ta you are always harsh on us, ka nuna Mana kyama da hantara kaman ba jinin ka ba unfortunately aka aura ma ka ni, Knowing well tsoro da fargaba ma kadai sun ishe ni Amma ba ka banni da wannan kawai ba, Ka tsangwame ni ka yi hitting Ina several times, zagi da cin mutunci ba wanda ba Ka min ba Uncleeee bayan kasan ko kadan ba laifina a ciki, har asibiti ka sa na kwanta" ta fada tana lumshe idanu cike da nuna jin zafin abin. "After all this, ban San me Mami da Abbah su ka ce Maka ba but nasan su Suka say ka same ni har ka bani hakuri, hakuri da ba Ka damu nayi ko banyi, it was not even genuine Kai Dai kawai burin ka in hakura in biyoka mu zauna ba tare da kayi la'akari da halin da Zan shiga ba balle Kuma ra'ayi na akan hakan Kai Dai kawai kayi fulfilling na ka burin, haka zamana gidan nan duk abinda kake so shi kake so ya faru sai dai da kaman wuya faruwar hakan abu Daya na sani Zan jure Zama har karshen rayuwata Amma Kuma ba Zan iya kara binka a duk yanda kake so ba, ni ma mutum ce kaman kowa, I have my worth, feelings and dreams"
Kara lumshe ido tayi tana expecting ta ji ya kwashe ta da Mari kaman yanda ya Saba.

  Kallon ta ya ke har ta gama bai taba ganin ta yi dogon magana ba sai yau, a jiyan zuciya yayi a hankali ya jawo ta jikin shi ya sa hanky Yana goge ma ta hawayen da ke fitowa daga cikin idanun shi, mutsutsu ta dinga yi tana son kwace wa daga rikon da ya mata "Duk abinda Kika fada haka ne ba kuskure ko kadan a cikin Shi Amma ki sani dukkan Dan Adam ajizi ne, Dan haka gani a gabanki Ina Mai rokon yafiya a gare ki Fatima Dan Allah ki yafe min am so sorry"

   Kallon yanayin fuskan shi tayi da idanuwan shi, Saurin Girgiza Kai tayi a zuciyan ta tana fadin "no hakan ba zai taba yiwu ba" Nadaman da take gani cikin idanun shi is fake ba abinda ke cikin zuciyan shi da ya wuce zalunci da mugunta, he have his reason for doing this. Ko kadan bata karyata zuciyan ta ba.

  Kafin ya ankara har ta ruga ta bar wurin, Wani irin sarawa yaji kanshi nayi da sauri ya rike Yana fadin "Ya Allah! Help me" a daddafe ya karasa dakin shi, Ranar daga ita har shi ba wanda yayi sahur.

  Washegari, ya Kama Friday. Bai da aiki sai Monday saboda course in da su ka je. Sai dai zaku su hadu da Umar akwai tattaunawan da zasu karasa akan shirye shiryen bikin shi Umar in.

  A falo ya iske ta tana zaune, shaf ya manta da zata asibiti a rana da alamun Kuma da Shirin ta ta fito "Ina kwana" ta gaishe tana facing kasa.

   "An tashi lfy?" Ya fada yana mata murmushi sai abin ma ya so ya Bata tsoro la'akari da yanda su ka rabu jiya.

  "Meyesa baki kirani ba? So kike kiyi latti?" Girgiza mishi Kai tayi, he hates body language in da ta ke mishi but bai da wani choice a yanda ya ke ji ranshi ma gabadaya zai iya sadaukar ma ta.

   "Mu je in sauke ki, ya fada yana sa links"

   Sai da ya fita gidan sannan ya kalle ta hakan yayi dai dai da juyowan ta, Four eyes, Murmushi ya sakan ma ta hade da kashe ma ta ido Daya.

  "Fatima na nemi yafiyan ki ba kice komai ba". Shiru tayi ba tace komai ba

  "Baki yafe min ba ko? Shknn fada min me Zan miki ki hakura ko ma mene zanyi saboda ban son inta Zama da hakkin ki a kaina" a hankali ya ke maganan hankalin shi na kan driving in da yake.

  "Ni ba komai Kuma bani kadai ma kayiwa abubuwan ba ai" Kaman daga sama ya ji siririyar muryar ta.

   Juyo yayi ya kalle ta  in shock "da su wa? Su Ummiy"

   Daga mishi Kai tayi

"In su ka yafe min kema Zaki yafe min" kan ta kara daga mishi

Daganan Bai kara cewa komai ba har yayi dropping inta ya wuce gidan Umar.

Ba komai ya sa ta yin hakan ba sai tunanin da tayi in dai da gaske Nadaman yayi ai su Maijidda sun yi deserving ya basu hakuri coz dukkan su ya takura wa rayuwar su, a ganin ta ba zai iya ba Amma za dai ta gani.

  Bin shi da Kallo Umar yayi har sai da ya Kai aya "Ai ga irinta nan Aliyu da nake ce ma ka ka daina takurawa rayuwansu gani kake kaman bayan su nake bi yanzu wa gari ya waya? Call them kannen ka ne duka biyun uwa Daya uba Daya ko ba komai ka goge tabon da kake dashi a wurin su, taimaka ma tayi"

   "Ko numban su Banda shi Fa"

   "Kira Mami ko Ammah" ya bashi amsa.

"Yes Ammah is the best solution" ya fada a fili, nan da nan ya Kira ta bayan sun gaisa yayi requesting numban su, har tsiya ta mishi kafin ta tura Mai.

   Maijidda ya fara Kira sanin cewa ta fi saukin Kai. Yana magana ta gane muryar shi "Uncleeee Ina wuni" ta fada a daddafe there is not doubt har yanzu tsoron shi bai barta ba

Amsa gaisuwan na ta yayi hade da tmbyn Mai gidan nata "Ya akayi Kika gane ni ko Daman kina da numbata"

  "Aa fa muryar ka na gane"

   "To Shknn just call to say Hi tunda ku ba kwa neman na at all ko har yanzu Muna fadan ne" Girgiza kan tayi kaman Yana gaban ta "Aa ban San za ka so na Kira ka bane"

  "Saboda har yanzu Kuna rike da ni right? Anyway, we are siblings Kuma Yan uwa ba sa fada so am sorry" ita dai gani ta ke kaman a mafarki, she still couldn't believe it.

  "Lah ba komai Uncleee and we are also sorry"

  "So are we good?"

    "Yes we are"

   "Ko kefe, I will be expecting your call" ya fada kafin su yi sallama.

   Ummiy ya kira, the same process da yayi na Maijidda ya mata sai dai ita ta kasa shiru sai da ta ce.

  "Kai Uncleee ni dai am so suprise gsky, In my entire life ban taba tunanin za ka Kira ni ba"

  "Why? Ke Kika dauki abin da zafi ai, hope my apology is accepted"

    "Sure, Ina Zahrau?"

  "She is fine"

   "Alhmdlh now I feel comfortable she is in safe hand"

  Dariya yayi Yana fadin "Ummiy kenan ba ki da dama"

    Ko da su ka Kira Zahrau su ka fada ma ta she is so shocked Amma sai ta ji zuciyan ta na fada mata he is definitely up to something ba a banza yayi ba...

    
  

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top