KHF 36
Yayi kwana biyu sannan ya warware gabadaya ya koma bakin aikin shi, still ba wani abinda ke shiga tsakanin su sosai yawancin ma gaisuwa ne sai ko in shi ya ja ta da lbr.
A haka azumi ya riske su, zuwa yanzu Aliyu ya sadakar dacewa Hakkin yaran nan ne ke bibiyar shi, haka kurum ya dauki kin duniya ya sauke a Kansu, hantara da kyar hade da duka ba Wanda ba su sha a wurin shi ba, hakan yasa su ke mugun tsoron shi har ya kai dacewa ba sa yarda su zauna inuwa daya dashi.
Da farko ya San kiriniya da rashin jinsu ya Fara kawo rashin jituwar su daga baya kuma shi kanshi ba zai ce ga dalili ba illa ya San cewa gudun shi da suke ma ya taimaka sannan ko kadan bai son raini kuma ya ga alamun hakan a tattare da su.
Ajiyar zuciya ya saki yana tunanin hanya da zai bi ya goge laifin shi a wurin su duka, ni dai nace Allah ya ba da sa'a.
Yan barrack insu sun zo shan ruwa gidan nashi sosai farkon azumi, haka Zahrau ke dawo wa daga asibiti a gajiye ta hau aiki gashi shi sai da Yamma ya ke samu ya dawo gida so ba karamin wahala ta sha ba.
Ranar da aka kai azumi na Tara ya same ta a dakin ta bayan sun dawo asham, a mota kullum yake daukan ta su tafi though banda gaisuwa ba abinda ke shiga tsakanin su.
"Zan yi tafiya Fatima kuma zan kai Sati daya ko fi ma, in bar ki a nan ne"
Ya fada yana kallon kasa ita ma kasan ta ke kallo kaman masu kunyan juna ko ince surukai.
"Ka kai ni Zaria" ta bashi amsa
"Zaria Kuma? IT in naki fa?" Dan jum yayi Yana tunani "ki shirya zan Kai ki gidan Salim"
Fuskan ta yake kallo yaga reaction Inta sai dai ya kasa karantan komai.
"Ko bakiso?"
Girgiza kai tayi kafin ta amsa "ba matsala" amma zuciyan ta tunani ta ke kaji min bawan Allah bayan ka gama yanke shawara kuma.
Flight insu karfe sha dayan safe ne so tun karfe Tara su ka kama hanyar gidan Salim in. Su uku za suyi tafiyan so already Umar yana can.
•••
Taji dadin zaman ta da Maman Khalipha kasancewar ita mutum ce mai son mutane game da Jan su a jiki, ga Khalipha yaron yana birgeta sosai ya kan tuna mata khaliphan Anty Rukayya.
Kasantuwar maman Khalipha na da mai aiki nan da nan su ke gama aikin su.
Kullum za ta je Asibiti ta dawo ba abinda ta sa a ranta bare ya dame ta sanin irin matsalan da ta ke dashi. Tunda ya tafi ko sau daya bai kirata ba itan ma ko a jikinta dan ko ba ta daura a ka ba, har ba ta so ya dawo ma Dan ta fi jin dadin zaman ta a gidan.
•••
A gajiye driver ya sauke ta a gida, gabadaya yau a asibitin ta wuni ga ayyuka dayawa da tayi hakan ya sa tafiyan da tayi ma zuwa cikin gidan na karfin hali ne.
A parlour ta iske mai aikin Maman Khalipha ta fito da fruit a hannun ta tana kokarin sawa a fridge "yau kam nayi lattin dawo wa ba dai har kun gama aikin ba" ta fada bayan ta gaishe ta.
"Ai ko dai kadan ya rage"
Murmushi tayi ta nufi kitchen in tana kiran Maman Khalipha, sai dai maimakon ita wata kyakyawar mace ta gani tana kokarin hada soup. "Sannu da aiki" tayi saurin fada ganin sun hada ido da ita
"Yauwa Sannu" ta amsa tana smiling.
Hakanan Zahrau ke ganin kaman ta Santa amma she can't really remember how.
Ganin komai ya kammala ya sa ta wuce dakin da take zaune domin ta watsa ruwa.
"Besty Ina Kika samo kyakyawa" fareeda ke tmbyn
"Kyakyawa Kuma? Ina Kika ganta?"
"Bata dade da shigowa ba ai da lab coat a hannun ta"
"Oh Zahra ta dawo kenan, IT ta ke zuwa"
"Ban San ta ba"
"Haba Matan Aliy ce fa"
"Oh really she looks familiar"
"Maybe kin Santa wurin tsohuwar Zuma"
"Kai Besty ai ya Zama history"
"Au you finally let it be kenan"
"Is not like I have a choice" ta cikin rawar kaman za ta yi kuka. Lura da hakan ya sa Maman khaliphan saurin canza hiran nasu gabadaya duk da dai jikin ta ya riga ya yi sanyi.
Ruwan zafi ta watsa saboda ta samu jikin ta ya warware don kam ta gaji sosai, nan da nan ta shirya ta iske su already a falo suna jiran a kira sallah don they are already done.
"Sannun ku da aiki" ta fada bayan ta zauna
"Sannu Zahrau yau dai an Sha aiki"
"Hmm ai ba a cewa komai, Su khalee boy yau azumin ake yi ne"
Daga kan Shi yayi hade da rike cikin Shi Yana bata fuska kaman da gaske azumin ya ke. Dukkan su sai da su ka dan dara.
"Ehmm Zahra Captain ya ce numbanki is not going through, in ce miki sun dawo but za su Sha ruwa a gidan Brigadier so ki shirya in yazo za ku wuce"
Shiru tayi jikin ta duk yayi sanyi coz har ga Allah ba ta son tafiya Kuma ba ta San wainan da zasu toya da Aliyu ba, ya kikirata ba tayi picking ba.
Dan Bata fuska tayi kafin tace "Kai Shi ko daga dawo wa? Gsky ni Maman khalipha ban son tfy gidanki da Dadi"
Murmushi ta yi "Ina ruwan Zahrau nima ban son ki tafi ammaba zan iya wa mijinki fashin ki ba kwanan da yayi Shi kadai ma ai ya Isa ko?" Ta fada tana daga mata gira
Sunkuyar da Kai tayi cike da kunya still dai ba ta son tafiyan
"Mommy wai Anty tfy za tayi" Khalipha yayi saurin mikewa
"Eh my boy Uncle Aliy zai zo ya dauke ta"
"Zance mishi ya barta Muna son ta ai yana da kirki zai bar Mana ita, Zaki zauna ko Anty"
Daga mishi Kai tayi tana murmushi, yayi saurin zuwa ya haye cinyanta kaman yanzu aka ce za ta tafin.
Ita dai Farida kala ba ta ce musu illa ma danna wayanta da take ta faman yi.
A haka a ka Kira Sallah, su kayi Sallah kafin su ka yi buda baki su kayi haramar tafiya Asham.
Fareeda da Zahrau kadai su ka je saboda Maman khaliphan ta ce zata zauna kar su Salim su dawo basa nan.
Driver ya sauke su a mosque in duk da dai ba nisa da gidan, sai da aka idar gabadaya su ka dawo Amma ba wani magana sosai ya shiga tsakanin su ba.
•••
Karfe Tara dai dai ya musua gidan Salim, burin Aliyu kawai ya ga Zahrau sosai yayi kewan ta, ko da ya ki kirat ba ta dauka ba hakura yayi ya kyaleta but ko da yaushe tana cikin ranshi, da azaman neman soyayyarta ko ta halin Kaka ya dawo.
Ko da su ka Isa falo su ka iske Matan Salim kawai ji yayi kaman ya tambayeta Ina ta ke, dube duben hanyan bedrooms ya dingayi har sai da ta dago Shi ta sanar mishi sun tafi masallaci, nan fa su ka hau mishi tsiya Shi dai yake kawai yake nan ta ke sanar mishi tare ma da Fareeda su ka tafi, he just blushed yana tuno old memories, Allah sarki he will never forget about her sbd da irin tsaftataciyar son da su ka wa junan su but Allah bai yi ba.
A haka Mijin Faridan ya iso daukan ta but still ba su dawo ba. Aliyu na ganin Shi ya gane shi, Shima Yana ganin Aliyun ya shaida shi, a tare Suka sakan wa junan su murmushi sannan su kayi shaking hands.
Tun daga haraban gidan su ke Jin voices na tashi hakan ya tabbatar musu dawowan su Aliyun.
A tare su ka shiga Falon "To Frnd finally duba kofa ya kare" dare su kayi dukkan su, Aliyu na hararan Umar din da yayi maganan.
"Kaga laifin sa? Kwana nawa bai ga abun sa, ko da ya ke bari sai kayi Aure za ka gane what I mean" Salim ne yayi maganan Yana kashewa Umar ido
"Dadin ta ma na kusa, sai Kuma in ga Wanda za a wa gori again" dariya su kayi.
Sai a sannan su ka samu su ka gaishe su game da musu ya hanya. Zahrau daki ta nufa while Umar da Salim sai Jan Farida su ke tana maidawa wani Sa'in ta yi dariya kawai. Farida ce ta kalli mijin ta "sorry dear na barka kana ta jira ko" smiling yayi sannan ya ce "Ina Kika bar wayanki? Ammah na ta fada"
"Oh Yana jaka bara in dauko mu tafi ko?" Ta fadi hade da nufan dakin.
Ko da ta dawo already mijin na ta ya musu sallama ya fita waje, ita ma Sallaman ta musu, Amina na ce mata to "besty thanks, sai na zo kafin ku bar Abuja" A hankali ta Isa wurin kujeran da Aliyu ke zaune Wanda ya ke daga Shi sai kofa, he is totally busy with his phone, Kallon shi tayi sannan ta dan buga kujeran ya dago su kayi four eyes, Saurin dauke idon shi yayi "are we fighting?" Ta fada in a very low voice. Girgiza ma ta Kai yayi "sorry, I don't know anything deserve to say" shrugging shoulders inta tayi "You are right" shiru ta danyi sannan tace "she is pretty" nodding head in shi yayi in approval sannan ya ce "thanks"
"All the best" ta fada tana heading out
"Besty haramun" Amina ta fada while Umar cewa yayi "Daki da waje dai ba nisa" giggling ta yi tana musu waving hand Shi ko Umar Mai da hankalin shi yayi kan waya kafin can ya dago ya kalli Amina. "Mommyn boy please Kira min ita mu tafi its getting late"
Ko da ta shiga daki sakan baki tayi domin ganin Zahrau ta yi bacci hadda ko kayan bacci a jikin ta, tada ta tayi.
"Kai Dan Allah please ki ce Mai ya banni Mana gobe sai in koma"
"Ehm ehm Zahrau ayi haka? Nikam ba ruwana ki dai tashi kwana nawa ko kewan mijinki ai Kya yi" tabe baki tayi tace "Allah am sleepy ya barni kawai gobe sai in koma"
"Shknn fito ki fada mishi da kanki, maybe ya yadda Amma ni ai har daki ya biyo ya zo ya fiddo ki"
Ba yanda ta iya hakanan ta tashi ta daura dogon hijab har kasa kan night gown in da ke jikin ta sannan ta fita, Maman khalipha na ganin ta fita ta yi saurin hada mata kayan ta hatta brush inta da ke toilet sai da ta fiddo ta sa mata a trolley sannan ta jawo shi Falon.
Ko da ta fito shi da Salim kadai ta tadda coz Umar na sauri ya tafi, Gabadaya attention in shi na waya so ta ma rasa ta yanda za ta mishi magana sai da Salim ya tabo shi. Kallon ta yayi sannan ya ce "ba dai har kin fara bacci ba?"
"Ehh nace da da ma ka banni a nan kawai tunda dare yayi gobe na dawo" habawa me Salim zai yi in ba dariya ba hadda rike ciki. Kallon takaici ya bishi dashi hade da Jan tsaki sannan ya juya wurin ta wani irin harara ya bita dashi ba shiri tayi saurin koma wa daki ta dauko kayanta luckily ta hadu da Maman khaliphan ta jawo kayan.
Kallon Salim da har yanzu bai dena dariyan ba yayi sannan yace "Kai fa ba fa na son iskan ci Allah"
"Yi hakuri ba ni na kar zoman ba" ya fada still Yana dariyan.
Maman khaliphan ta ja mata trolley in har motan Aliyn Yana ji Salim na fadin "madam sai Kuma a maida min mata Mai Jan trolley" banza yayi dashi.
Hugging inta Amina tayi tana fadin "nagode Zahrau sai na zo ziyara na musamman, toh Captain mun gode fa da Zumun ci"
"Nine da godiya Mommyn boy zan zo ma ai specifically "
Cewa tayi "haba Captain bakomai ai"
Ita dai Zahrau shiru tayi coz har ga Allah ba ta son tafiyan da kyar ta iya masu waving.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top