KHF 35
Karfe takwas na safe ya gama shiryawa ya fito falo, a nan ya same tana jiran shi. "Ina kwana" ta fada tana danna wayan ta "lfy" kawai yace yana kallon ta ta kasan ido. Wai shi yau tunanin kanwar kanwar bayan shi ke garawa a cikin gidan shi lallai wannan shi ake kira kaddara "shall we" kofan falon ya nufa, mikewa tayi sannan ta juya ta kalli dinning table "uncle akwai abinci"
"Am okay" ya amsa yana cigaba da tafiya, as he expect bata damu da rashin cin abincin nasa ba duk da ta San shi mutum ne da bai son wasa da ciki, basarwa ma tayi ta bishi wajen.
Ba Wanda ya ce ma wani kala har su isa Hospital in da za tayi industrial attachment inta, sai da ya tabbatar da komai intact sannan ya wuce barrack insu.
Ita ko Zahrau a tunanin ta halin shi na asali ya dawo shiyasa ma canjawar shi ba ta Dada ta da kasa ba inda sabo ai yaci ace ta saba.
Kullum da safe shi ke kai ta asibitin in an tashi ya je ya dauko ta su wuce gida, ba wani maganan arzikin da ke shiga tsakanin su banda gaisuwa.
Ko da wasa ya daina sake ma ta fuska a tunanin shi hakan da yayi zai sa ya dena damuwa da tunanin sai dai kash maimakon abu yayi baya ma gaba ya ci, shin wai ya zai yi da rayuwar shi ne?
Sati daya su ka dauka ba sa wani magana a tsakanin su, iya ka ta mishi girki daga baya ma driver yasa yana kai ta asibitin.
Jiki da jini, Da wani irin zazzabi da ciwon kai ya tashi safiyar ranan ko falo bai iya fito wa ba. Tara su ka yi zasu hadu da Umar amma har shadaya shiru, Umar in yana ta Kira shi bai daga waya ganin haka yasa shi zuwa gidan ya ga ko lfy.
Zaune ta ke a kan gadon ta tana kallon wani Korean film descendants of the sun, Sallama da taji ne ya sa ta sako hijabin ta domin ganin waye. Tana ganin shi ta saki murmushi sannan ta gaishe shi, sai da su ka dan gaisa sannan ya tmby abokin shi. Kallon hanyar dakin shi tayi sannan ta ce "ko za ka duba shi yau gabadaya ban ma ji duriyar shi ba" Kallon mamaki ya mata yana ayyana abu a ranshi sannan ya mike ya tafi dakin.
Kwance ya same shi kan gado ya lullube jikin shi da bargo sai rawan dari ya ke, da sauri ya karasa inda yake bargon kanshi ya dau zafi ballantana jikin shi da yayi kaman wuta.
Bargon yayi kokarin janyewa ba shiru Aliyu yayi saurin kankame jikin shi gaba daya jikin shi rawa ya ke yi idon shi yayi ja, A fili Umar ya nuna tsoron shi saboda ya manta rabon ya ga abokin shi a a haka, shi mutum ne mai dauriyar ciwo so ba karamin jin jiki yake ba.
Da hanzari ya shiga toilet ya debo ruwa da towel, da kyar ya bari ya Dan goga masa ruwa ko za a samu zazzani ya ragu. Abokin su doctor ya kira game da gaya masa halin da Umar in ke ciki sannan ya fita wurin Zahrau.
A dinning ya same ta tana shirya abinci. "Sannu madam" ya fadi yana kallon ta, Murmushi kawai ta mai game da cigaba da abinda ta ke yi. Kan stairs ya sauko ya karasa dinning ya zauna "zauna INA so muyi magana" ba musu ta zauna tana sauraran shi.
"Haba haba Zahrau a gsky kin ban mamaki" yayi maganan yana girgiza, ita ko sakin baki tayi tana kallon shi "ban ce frnd bai da laifi but ke fa mace ce yaka mata ace yanzu ba wani sauran matsala tsakanin ku, ba ki tunanin Ma Allah zai tambaye ki? Duba fa ki gani Aliy bai rage ki da ci ko sha ba kina da sutura basu kirguwa ga gida nan kina zaune cikin rufin asiri, kinga ko kenan in za a wa Aliyu adalci ya sauke hakokin shi dayawa Amma ke fa Zahrau? Nayi tunanin ke ce za ki bi hanyoyin da za Ku zauna lfy, Duba fa ki gani tun safe ba kiji duriyar shi ba ai kya duba halin da ya ke ciki ko dan zaman tare" ajiyar zuciya yayi sannan ya ce "anyway, Dan Allah ki canja kika kawo mana Abincin daki bai da lfy ne" Da mamaki ta dago ta kalle shi sai dai bai tsaya sauraron ta ba ya koma dakin.
Jiki a sanyaye ta tattara warmers in kan tire ta nufi dakin nashi, wannan ne karo na farko da zata fara shiga dakin tunda ta zo gidan, Da siririyar muryata tayi sallama a hankali Umar ya amsa ma ta yana fadin shigo mana Zahrau.
Kan ta na kallon kasa ta shiga ta ajiye tray in sannan ta dago kan ta, Four eyes su kayi dashi coz shi in ma ita ya ke kallo, Jallabiya ke jikin shi kallon ruwan kasa buttons in gaban a bude hakan ya bata daman ganin bakin gashin da ke kwance a kirjin shi kaman bargo saurin dauke idon ta tayi "Sannu Uncle Ya jikin?" Muryar ta na rawa ta masa magana, Gyada mata kai kawai yayi "Allah ya kara sauki"
"Ameen" ya amsa a takaice.
Karan wayan Umar ne ya katse shirun da ya biyo baya cikin dakin, Doctor ne sun dan yi magana kadan sannan ya katse wayan "serve him Bara in shigo da Doctor" gyada mishi kai kawai tayi sannan ta fara kokarin bude warmers in.
Faten dankalin turawa ne da ya sha kayan lambu da kayan ciki kamshi sai tashi ya ke tayi sannan kunun gyada. Tana kokarin zuba dankalin ya dan kalleta "kadan za ki sa" ya fada yana lumshe idanu dan shi kadai ya San radadin da ya ke ji. "Sannu" ta fada gami da mika mai abinci ganin rawan da hannun shi ke yi ya sa ta jawo study table in da ta gani ta daura abincin. Ya fi shan kunun akan dankalin da ke tafi ruwa ruwa "Doctor na jiran ka a falo" Umar ya fada bayan ya shigo dakin. Gyada kai yayi hade da kokarin tashi ba shiri ya koma zaune saboda wani jirin da ya debe shi kanshi ya mai nauyi. Umar ne ya rike shi da kyar su ka karasa falon. Da sauri doctor ya nufe shi yana mishi sannu ya fara aune aune "Captain ma ba zamu asibiti ba kuwa? Your temperature is high" Girgiza kai Aliyun yayi, "shknn tunda ba ka so bara muga yanda za ayi, Bara inje clinic in dawo tunda ba nisa" Gyade mishi kai Umar yayi.
Ba a cika mintuna Ashirin ba ya dawo da abubuwa a hannun shi, drip yayi kokarin sa masa sannan ya dura allurori a ciki bayan nan ya debi jinin sa da niyyan ya masa test in ya koma asibiti, Magunguna ya mishi prescribing sannan ya mishi fatan Samun saukin sannan ya wuce.
Gabadaya magungunan sai da Umar ya nuna wa Zahrau sannan ya bar gidan da niyyan zai dawo anjima kasancewar baccin da Aliyu yayi.
Ba yanda ta iya haka ta dawo falon ta zauna tana Reporting IT NATA. Dai dai karewar drip in ya farka, idanuwan shi a kanta ya fara sauka tana rubutu kallon na ta ya cigaba dayi ba kakkautawa, jikin ta ne ya ba ta ana kallon ta dagowa tayi su jayi ido hudu saurin janye idon tayi ta mishi sannu da jiki, murmushi kawai ya sakan mata hade da lumshe idanu "pls in za ki iya ki cire min INA son nayi wanka" Ya fada ya na nuna hannun shi. Zuwa lab in da tayi kwana biyu ya sa ta iya Jan coka allura ta ja jini, a hankali ta rike hannun nasa, duk Kansu sun ji reaction in haduwan hannayen nasu amma sai su kayi choosing ignoring, A hankali ta zare plasta in sannan ta cire aluran.
Ba lefi ba kaman dazu ba yanzun ya Dan samu karfi tunda har ya iya takawa zuwa daki.
Ya dauki mintuna dayawa yana shiryawa har Umar ya dawo, wannan karon a dinning ta shirya musu abinci, bayan sun gama ne Umar ya ja shi waje su sha iska da ke zazzabin ya dan sake shi.
Sau Uku Umar ya na mishi magana amma gabadaya hankalin shi bai wurin sai da ya tabo shi sannan ya dago a zabure yana tmbyn shi me ya ce "Tunanin me kake frnd?" Wani irin ajiyan zuciya yayi sannan ya kai hannu kan kirjin shi "Zuciyana na min zafin frnd akwai matsala?"
"Subhanallah me ya faru?"
"Zahrau"
"What about her?"
" Frnd na kuma da son ta wlh ban San ya aka yi ba"
"She is your wife already, ai abu mai sauki ne" Girgiza kai yayi yana kallon Umar in "ba ka fahimceni ba, Yarinyar nan ba ta so na, ba ta damu dani ba kwata kwata in ba zan mata karya ba amma kaman ina ganin kiyayyata a cikin idanun ta, tana zama dani saboda is her only choice" murmushi Umar yayi sannan yace "Haba captain sai dai kace ba soja ba Allah ni ka ban kunya, Mace ce fa kai za ka tafiyar da ita ka koya mata son ka da damuwa da kai balle ma Zahrau ba wata mai rigima bace INA ganin hakan zai zo da sauki"
"Hakane amma frnd ba ka ganin ta kullace ni ne? Kasan abubuwan da suka faru dai"
"Ranar irin ta yau tuntuni daman nake guje maka amma ba ka jiba, da ga ganin ta akwai riko ba shakka. Aiki ya zame maka biyu kenan ka fara goge wannan bakin tabon da kake dashi a wurin ta shi ne sannan ka fuskanci dayan"
Sun dade suna tattauna yanda za su bullo wa lamarin sannan su ka shiga batun shirye shiryen bikin Umar, sai gab da magriba ya tafi.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top