KHF 33
Text ya turo mata yana jiran ta a falo zasu je wani wuri.
Gyalenta kadai ta dauka ta fita falon "Sannu koh ya gajiyan hanya?" Ya fada hankalin shi na kan wayan shi.
"Lafiya kalau, ya naka" ta amsa mai a hankali
"Nima lfy muje ko" ya fada bayan ya dauki keyn Motan.
Bata tmby shi ina za su je ba shi ma bai fada mata. In less than 10 minutes su ka isa gidan Salim daman ta yi suspecting can za su.
"Oyoyo Amaryar mu ta dawo"
"Ina wuni Maman khalipha"
Da gudu khaliphan ya zo ya rungumeta yaron yayi girma sosai haka yar kanwar ta shi ma tayi wayau.
Hira yayi dadi sosai sai karfe goman dare su ka nufi gida. Zahrau kan ba ta ma ki su kwana a nan ba.
A gajiye likis ta shiga cikin gida, saukin ta tayi Sallan isha'i dan haka ruwa kawai ta watsa ta yi haramar bacci.
Ba ta iya bacci da kaya masu nauyi ba dan haka wani yololuwar half gown ta sa shara shara a na iya ganin komai na jikinta. Gashin kanta ta baza tana tajewa lokacin da taji Sallama a kofan dakin ta.
Kafin ta yi wani kwakaran motsi har ya shigo cikin dakin. Saurin sadda kanta kasa tayi cike da kunya jikin ta sai karkarwa ya ke.
Ganin haka ya sa Aliyu saurin barin dakin yana mai cike da mamakin tsoro irin na Zahrau, abu kadan jikin ta ya dau rawa.
Ribbon ta sa ta kama gashin na ta sannan ta dauko dogon hijab inta har kasa ta bishi falon.
Still dai jikin na ta rawa ya ke, kanta na kasa har ta karasa inda ya ke, dan nesa dashi kadan ta tsaya "Uncle ga ga ni" ta fada cikin siririn muryan ta dake rawa.
Kallon gefen ido ya bita dashi sannan ya ce "Na kira ki ne?" Saurin Jan baya tayi a firgice a sanadiyar yanda yayi maganan.
Zaro idanun shi yayi sannan yace "seriously tsoron ki yayi yawa, ki rage"
Shiru ta yi kawai kanta a kasa "Je ki abinki daman Nazo in duba Amanan Abbah ne" Hankalin shi na kan waya ya ke magana. She wonder me ya ke yi da waya 2/4/7.
"Sai da safe" ta fada ta yanda zai iya jiyo ta bayan ta mike
"Tsaya, kayan da ki ka bar min a nan ba ki so ne?"
Rashin sanin amsan da za ta bashi ya sa ta yin shiru.
A hankali ya ja tsaki "kinsan fa banson ina magana a share ni"
"Ina so" kawai ta fadi sannan ta nufi dakin ta.
....
Kwance ya ke rigingine a dakin shi, bacci ya ke son yi amma ina ko alamu baccin ya ki zuwa sai ma wasu shirmen imaginations da ya fara zuwa mai rai, kaman da wasa surorin Zahrau ya fara fado mishi a rai tun yana kokarin cire a rai har dai ya ga alamun rashin yiwuwan hakan.
Ganin bai da mafitan hana zuciyan shi tunani abinda ya ga dama ya sa shi janyo Qur'an yana karanta a haka har ya fara jin bacci sannan ya samu ya kwanta.
Da safe ko da ya tashi bai bi ta kan ta ba office ya shirye ya wuce daman ba satin za ta fara zuwa IT ba.
Ita ma ko da tashi ba taji alamun duriyan shi ba kitchen ta nufa straight ta samu abinda za ta ci.
Kwana Uku kenan Zahrau ba ta sa Aliyu a idon ta ba. Ko kadan hakan bai dame ta ba sanin cewa daman fushin Abbah da Mami ya sa shi dauko ta ba wai dan wani abu ba. Abinci ma ko kadan ba ta taba tunanin ajiye mishi ba iyaka komai ta ke nema tana samu daman ta taammaci hakan saboda sojan ba wai yana wasa da cikin shi bane.
Shi kanshi ya San Abinda yayi bai kyauta ba sai dai yayi hakan ne ba dan komai ba sai dan ya samu ya cire wa zuciyan shi tunanin Yarinyar. As he claimed Zahrau ba sa'ar shi bace ta mishi karanta yana dai tausayin ta ne kawai amma kuma ita ma ai bata neme shi ba that means ba ta damu dashi ba kenan? Haka kurum yaji bai ji dadin hakan ba.
Dakin ta ya nufa already har ta kashe wuta alamun ta yi bacci. Har zai juya sai kuma ya tsinci hannun shi da kunna Switch in wutan.
Baccin ta ta ke cikin kwanciyar hankali ka ganta kasan ba ta da matsalan komai a rayuwa. Gashin kanta a baje yake kan pillow ta kunce ribbon in.
Sha'awa ya ji ta bashi, gashin na ta ya bi da kallo yanda ya baje, a rayuwan shi yana matukar son mace mai gashi.
Kishi kuma ya fara ji ganin cewa ya dade rabon da yayi baccin cikin kwanciyar hankali haka.
Saurin kashe wutan yayi ya bar mata dakin gudun kar ya kara dasa wa zuciyan shi wani abun dan kwanan nan Zahrau da ya raina zuciyan na neman bashi Kunya a kanta.
Washegari, da safe bai fita aiki da wuri ba yana wanka yaji kaman motsin mutum na kaiwa da kawo wa. Nan da nan ya gama wanka. Yana cikin shiryawa ya tabbatar da itan ce jin kamshin da ke tashi a gidan.
Cikin Uniform ya shirya bayan ya gama shafe shafen turaruka da mai, sosai Uniform in ke amsan shi da ka ganshi ka ga kaga hadadden Sojan da ya dace da matsayin shi.
Sanye ta ke da kayan bacin ta Riga da wando ta daura kimonan kayan a saman shi, black veil ta daura a kanta amma still gashin ta ya fito ta baya.
Ya dade a tsaye yana kallon yanda ta ke ta faman soya golden yam In da ke gaban ta a gefe daya kuma tana pepper soup in kayan ciki Wanda ya wadatu da kayan kamshi dan kuwa kamshin sai faman tashi ya ke.
Jikin ta ne ya bata ana kallon ta da sauri ta juya, four eyes tayi dashi da sauri ta sadda kanta kasa sannan ta gaishe shi.
"Ba zan amsa ba, wato kin manta da yayanki ko?"
Sanin ya tsani a share shi ya sa tayi saurin girgiza kanta.
"Eh mana, you are not even sure if am well 3 days amma you are here enjoying"
"Am sorry " ta fada kasa kasa
"Shknn INA jiran breakfast INA ko ba dani aka daura ba?"
"Okay" kawai ta ce sannan ta mai da hankalin ta kan aikin ta.
Ganin hakan ya sa shi zuwa dinning yana jiran ta, haka kawai ya tsinci kanshi da son cin abincin na ta da ko kallo bai ishe shi ba kafin a hada su aure.
Aikin ta take a zahiri amma cikin zuciyan tunanin sabon halin Uncle Aliy ta ke ko kadan bai yi kama dashi ba shi ne har da Jan ta da wasa gsky abin da mamaki INA ma twins na nan su ga abin alajabin nan.
Allah ya so tayi niyyan yin abinci har rana ne da ba zai ishe su ba dake tana son doyan since from time.
Cikin 15 minutes ta gama komai cikin warmers ta shirya mishi komai sannan ta kai mishi plates hade da flask in tea da sauran kayan.
"Thank you" kawai yace mata sannan ya fara kwasan gara. Gsky ya dade yana missing abinda ya dinga ayyanawa a ran shi kenan har ya gama cin abinci.
"Zan wuce office"
"Allah ya kiyaye hanya" ta amsa
"Ba za ki rakani ba?"
Toh fah har ga ranta ji tayi abin Aliyu na neman ya fi karfin ta. Rakiya kuma.
Ganin still ita ya ke kallo ya sa ta tashi ta bi bayan shi.
"A haka zaki fita akwai fa masu aiki a gidan" wannan karan ran shi hade ya fadi maganan zuwa yanzu saurin canja mood in shi ya far daina ba ta mamaki.
Har ga Allah ba ta ga laifin shigan ta ba gaba daya jikin ta a rufe yake amma da ya ke ba ta son magana ya sa ta shiga daki ta dauko dogon hijabi ga mamkin ta yana nan Inda ta barshi yana jiranta.
Har bakin Motan ta raka shi sannan ta dawo cikin gidan ta fara tattarewa.
Nan da nan ta gama ta afka duniyar da tafi karfi wato karatun novel.
Zaune ya ke a office ya yi jigum yana mamakin tunanin Zahrau da ya ke yi ba gaira ba dalili, wani siririn tsaki ya ja yana fadin OMG wannan wani irin rayuwa ce? Shin me ke damuna ne? Karan wayan shi ne ya katse shi daga zancen zuci da ya ke. Text message ne " an Bayan Sallah da Sati biyu" kallo ya bi text in dashi Sam bai gane inda ya dosa ba, ko me zai sa Umar turo mai text in nan. Tsaki ya ja sannan ya ajiye wayan.
Shiru yayi kaman ya tuno wani abu kuma yayi saurin dauko wayan ya kira Umar. Bai dauka ba sai mssg in da ya kara turo mai "sorry Frnd ina tare da baba, will call you later."
Ba shi ya koma gida ba sai bayan Sallan isha'i, meeting ya tsaya har magariba da ya shiga Sallah kuma sai ya jira har bayan isha'i.
Ba ta falon so straight dakin shi ya wuce yayi wanka sannan ya sa jallabiya Mara nauyi har zai kwanta saboda gajiya gashi gobe suna da tafiya wata zuciyan yace ya je ya dubo Zahrau. Ya lura kwata kwata bai gaban yarinyar and bai jin dadin hakan.
Zaune ta ke kan sallaya tana karatun Al-qur'ani cikin suratul Yasin lokacin da yayi sallama. Sai da ta kai aya sannan ta dago ta amsa sallaman nashi. Murmushi ya sakan mata hakan ya sa tayi saurin sadda kai kasa "Ya aiki" ta fada tana wasa da yatsun hannun ta "aiki lfy Malama Fatima ba za a cigaba da karatun ba"
Tab banbarakwai taji fatiman da ya ce mata sau daya ta kan manta sunan ta kenan in ba malamai su ka kirata ba. "Na gama" ta bashi amsa.
"Shknn tunda kince haka, Abinci na fa?"
"Ban yi abinci ba" Zaro idanu yayi yana kallon ta "me kika ci da rana?"
"Na sha tea"
"Keh wasa kike da lfyn ki ko?" Saurin girgiza mishi kai tayi.
"Ko kiwiyan girkin kike" yanzu ma dai kara girgiza kan tayi.
"Ki daina girgiza min kai Fatima. Ni gidana ba a zama da yunwa so zan miki afuwan na yau. Me zaki ci in samo miki?"
"Allah am okay"
"Ki sameni a mota" kawai yace ya fita dakin.
She have no other choice haka nan ta bishi Motan.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top