KHF 32


Kiran Sallahn da aka yi ne ya katse musu draman da su ke yi, masallaci su ka nufa mami da Zahrau ma sallahn su ka tafi yi.

Zaune ta ke akan sallaya tana azkar bayan ta idar da Sallah a dakin da ya za ma nata yanzu a side in mami.

Sallaman da akayi a bakin kofar ne ya sa ta dagowa dan ganin wa ke magana...

Uncle Aliy ne, "wa'alaika Salam" ta amsa but still tana zaune akan sallayar "Ba za ki bani wurin zama ba" ya fada yana ma ta murmushin da ya zama bako a gare ta hakan ya sa ta jin abun banbarakwai. "Bismillah" ta fada tana nuna mishi kujeran dake dakin.

Kujeran da ke kusa da ita ya zauna yana fuskantan ta. "Zahrau Dan Allah taimakon ki nake nema" ya fada yana kallon ta alamun amsan ta ya ke jira, tana mamakin yanda Aliyu ke iya komai ya ga ya samu abinda ya sa a rai. Daga mishi kai tayi alamun tana jin shi.

Kallo ya bita dashi ganin yanda gaba daya jikin ta ke rawa, ko shakka bbu ya sa Zahrau matsoraciya ce sosai musamman ma shi da ya ke kaman dodo a wurinta. Ko ma ta ya za suyi zaman?

Ganin at anytime Abbah zai iya shigowa ya sa ya kauda duk wani tunani ya fara mata magana "ke kadai ce zaki roka min Abbah ya sauko da wuri so pls ki bashi hakuri" a hankali ta juyo ta kalle shi sai kuma ta yi saurin kauda kai "kinji" ya fada yana kallon reaction inta.

A hankali ta fara magana though da kaji muryan ta kasan a tsorace ta ke "kayi hakuri Pls Amma ba zan iya gardama da hukuncin da Abbah ya yanke a kaina amma in har ya tmby ni zan nuna mishi ba komai" tausayi Aliyun ya bata ganin yanda har ya sauko kasa yana Neman tainakon ta kwanan ba shakka yana gudun duk wani Abu da zai hada shi da mahaifan shi ita ma kuma ba zata so ta zamo sila.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dan ja tsaki, shin me ma ya kawo shi gun Zahrau bayan ya San ko da Deedat ya ce abu ba ta tsallake shi balle kuma Abbah.

"Zahrau, Aliyu" Mami ke kwalla masu kira, juyowa su ka yi duka suna kallon ta "Ku fito falo" kawai ta ce musu sannan ta wuce.

Ba hakurin duniyan da Aliyu bai ba Abbah amma INA ko kadan Abban bai sauko ba.

Yau dai duk jarumtar sojan sai da idon shi yayi ja yayi tagumi sai zufa ya ke hadawa. Daga Mami har ita kanta Zahraun da ake son kwato wa yanci ba Wanda bai ba tausayi ba.

Gashi Baffa ba ya nan balle ya sa baki.

"Abbah Dan Allah ka yi hakuri wlh ni bai min komai ba" kaman daga sama su ka ji siririn muryan na ta. Dukkansu kallon mamaki su ka bita dashi She hardly talks balle kuma a irin situation in nan.

...

"Ka ga ni ko tsakanin Mata da miji ai sai Allah" Mami ke fada wa Abbah bayan ya sallami su.

Wani ajiyar zuciya yayi sannan yace "ya dauki hakkin yarinyar dayawa gata Amana ce gare mu, wlh ba Dan ta sa baki ba sai na raba auren nan"

"Allah ya kyauta" kawai mami ta ce

Zaman musamman Mami tayi da Dan ta, nasiha ta mai sosai game da mai tuni da Zahrau amana ce a gare su. Jikin shi yayi sanyi sosai, kwata kwata ya kan mance da iyayen Zahrau n su rasu, gabadaya yaran gida a zaton su Ammah ta haife ta hadda itan ma haka ta ke gani. Babban Yaya, Anty zee, Aliyu da Deedat kadai su kasan zance.

Wani irin tausayin Yarinyar yaji yana shigan shi, Ga ta Allah ya bata hakuri. Amma shin yaushe Mami su ka shirya fada ma ta ne, ko sun manta yakamata ta dinga ma iyayen ta addu'a. She deserves to know gsky amma ya San me zai yi.

A washegarin ranan ya nemi koma wa Abuja tare da Zahrau n Abbah ya so ya hana shi sai da mami ta bashi baki sannan.
Safiyar ranar da zasu wuce Abujan kuka tayi ta wa Ammah da Deedat, rarrashinta su ka yi ta game da mata nasiha. Ba ta son bin shi Abujan amma ba yanda ta iya hakanan ta saduda.

Shi ke tuki ita kuma tana seat in mai zaman banza. Tunda ta gaishe shi ba ta kara magana ba shima din shirun yayi hankalin shi na kan tukin da ya ke.

Kiran Ahmad Sulaiman ya sa a motan yana bi. Kafin su karasa Kaduna har tayi bacci ba mamaki dadin karatun ne tun da ya kunna ta lumshe ido daman.

Kallo ya bita dashi ganin yanda numfashin ta ke sauka a hankali, wani irin tausayin ta yaji yana ratsa shi. Yasan ba kowace mace za ta iya juriyan da tayi. Bayan duk abinda ya mata ta kareshi gun Abbah duk kawaicin ta da rashin magana. Ba shakka Zahrau ta cancanci a jinjina mata.

Har zai dau hanyan Abuja ya fasa ya yi hanyan gidan Babban Yaya, Sai da yayi parking a kofar gidan sannan ta farka, kallo ta bi gidan shi cikin mamaki. "Mu shiga mana ko in zagayo in bude miki kofa ne?"

Saurin girgiza kai tayi sannan ta bude kofan ta fita, Murmushi yayi ganin yanda ta yi saurin girgiza kai cike da tsoro.

Khalipha da kanen shi na tsakar gida su ka shiga da gudu gaba dayan su su kayi kanta "oyoyo Anty Zahra" daya bayan daya ta daga su banda khalipha da ta ce shi ya girma, baki ya turo yana shi bai yadda ba suna ta mishi dariya "Ina wuni Uncle" Anisa ta fada tana kallon Shi
Hararan ta yayi sannan yace "ba ruwana da dukkan Ku Antynku kadai kuka gani koh"

Hannu khalipha ya hada yana "sorry Uncle Wlh Anty Zahra ce ta ja munyi missing inta sosai" Sauran kannen ma dauka su kayi suna fadin "eh mana Uncle"

Yaran ba dai wayau ba, suna birge shi sosai.

Da gudu Anisa ta yi cikin gidan tana fadin "Mommy Anty Zahra da Uncle sun zo"

Cikin Sauri Nanah ta fito ta rungume Zahrau sannan ta gaida Aliyu.

"Oyoyo Zahra na" Anty Rukayya ma fito wa tayi ta tarbe ta shi dai Aliyu sai kallon su ya ke ba sa ma ta kan shi sunyi kewan ta ba kadan ba.

Falon su ka karasa suna masu farin cikin ganin juna.

Da gudu Maijidderh ta fito daga daki dan daman Sallah ta ke yi "oyoyo Yaruwa" kanta gabadaya tayi tsaban farin ciki saura kadan dukkan su su zube kasa.
"Ah ah miye haka da auren naki ma ba za kiyi hankali ba" Aliyu ke magana cikin bacin rai.
"Sorry, nayi farin cikin ganin ki ne Sister. Ina wuni Uncle"

Hararanta yayi ba tare da ya amsa ba.
Daki Nanah da Maijidderhn su ka kai ta. "Au ni Uncle Aliy ba zai taba canjawa ba" Maijidderh ta fada.
"Kinga laifin shi? Da auren ki kya kama gudu so kike kima Mijinki asara abinda ke cikin nan ko?" Nanah ta fada cike da tsokana.

"Ke wai Wa ya ce miki ina da ciki" dukkan su biyun harara su ka bita dashi "ana ganin ki an gane Hauwa'u" Zahrau ta fada tana kare mata kallo.

Ummiy su ka kira, ji tayi kaman ta yi tsuntsuwa ta ganta a kadunan amma ba hali.

Suna cikin cin Abinci Anisa ta leko dakin "Anty Zahra Uncle ya ce kizo Ku tafi"

"Daga ina kuke wai" Maijidderh ta bukata

"Zaria"

"Abuja za Ku wuce"

Kai kawai Zahrau ta gyade mata game da mikewa.

"Ki bari mu gama cikin Abincin mana" Nanah ta fada.

"No am okay"

"Shknn muje mu raka ki kar Uncle Aliy ya ce mun rike mai mata daman na samu arzikin tsawa da na dade ba a min ba"

Murmushi kawai Zahrau ta mata suka fita.
Karfe hudu dai dai su ka isa Abujan, gidan su ka nufa kai tsaye.

Gidan na nan yanda ya ke sai fenti da aka canja da kuma furnitures.

Kai tsaye dakin ta na da ta nufa daman Aliyun bai shigo gida ba masallacin ya nufa.

Abin mamaki akwatunan ta gani ajiye ta yanda ta barsu haka gado da sauran kayan daki duk suna nan.

Bayi ta shiga ta dauro alwala sannan ta gabatar da Sallan La'asar tana me rokon Allah ya zaba mata dukkan abinda yafi alkhairi a rayuwan ta.

Ko wani irin Zama za ta yi wannan karon? Abinda ke ta fado mata kenan a rai tana tuno irin zaman da tayi da.

Kuyi hakuri ban son na muki alkawarin yanayin yanda Zan dinga  updates ne Kuma a zo a samu matsla, kunsan school and all sai a hankali. But Zan kara kokari as promised earlier.

Nagode kwarai.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top