KHF 31
Sallama Fati ta fara musu, Umar ne ya amsa ya na kallon Aliyu. A tare su ka gaishe su dukkan su biyun, faran faran Umar ya amsa sabanin Aliyu da ke ta faman danna wayan shi kasa kasa ya amsa gaisuwan nashi.
Wani kallo Umar ya mai ba shiri ya sa wayan cikin aljihu sannan ya mike ya rufe motan.
"Sannun Ku fa, mun same Ku lfy?" Ciki ciki ya fada kaman an sa shi dole fati ya ke kallo kuma itan ce ta amsa mishi ga me da tmbyn shi aiki shi ma ya tmby karatun su.
Zahrau dai kanta na kasa kaman wurin Fatin aka zo ta rakota.
"Zahrau" Umar ya kirata, nisan da tayi a duniyan tunani ne ya sa ba ta ji kiran ba sai da Fati ta tabo ta. Firgigit, ta dago tana kallon fatin, nuna ma ta Umar ta yi "yana magana"
"Haka kike irin wannan tunanin ke da baki da lfy Zahrau, so kike ki jawo wa kanki wani matsala ko?" Umar ke maganan yana kallon Abokin shi da yayi shiru yana sauraren shi.
Murmushi ta yi sannan ta amsa "Yaya Umar ba fa tunani na ke ba banji ka ba ne" shima murmushin yayi sannan ya ce ma ta "to shknn tunda kince hakan, Kaman yanda kika sani wurin ki mu ka zo musamman dan mu baki hakuri, ko shakka bbu kowa ya San an dauki hakkin ki ba kadan ba. Maganar gsky shi aure ba abun wasa bane abinda ya ke sunnar mazon Allah (SAW) sannan kuma har iyaye su ka shigo ciki to wlh matukar kuna son ganin cigaba a rayuwanku sai kun ajiye makaman yakin Ku kun rungumi kaddarar Ku da hannu biyu, Nasan Aliyu ke da laifi Zahra sai dai ke ma kin matukar ba da gudunmowa akan laifinnasa. Dukkanku mu nan mun San gskyn zance kenan so is better you face your reality" Kaman ko yaushe Zahrau kan ta na kasa Aliyu ko lumshe idon shi yayi yana sauraran Amininsa.
Alama Umar ya ma Fati su ka je gefe su ka bar su su biyu a wurin.
Sun kai minti biyar a tsaye ba Wanda ya iya ma wani magana hasali ma kowa da wurin da ya ke kallo. Sake sake Aliyu ke ta faman yi a zuciyan shi yana kuncewa, har ga Allah bai san ran shi bai son abinda ya ke shirin aikatawa amma ya ya iya this his only option, ya riga yayi Na'am akan rungumar auren Zahrau ko dan samun Albarkar iyayen shi ba wai dan akwai ko digon son ta a zuciyan shi ba, gani ya ke an zubar mai da class in shi ne dan yafi karfin ya so wannan mitsitsiyar yarinyar amma ya zai yi this is his only solution.
A hankali yayi gyaran murya sannan ya juyo yana kallon ta tabbas ya San ba za ta yi magana ba don da alamun ta fishi miskilancin ma "Zahrau" a hankali ya kira sunan na ta ta yanda za ta jiyo.
Dan dago ta yi ta kalle shi sannan ta sadda kanta kasa, ita ma a hankalin ta amsa da" Na'am "
"Ki dago ki kalle ni za mu yi magana"
Sarai ta San shi da saurin zuciya hakan ne ya ke ja mata duka a wurin shi tun tana karama tsoron kar ya mata wani abu gaban mutane ne ya sa ta yi saurin dago da kanta tana kallon shi.
"Ba ki ga text INA ba ranar?" Shiru ta yi dan ba ta San me zata ce mishi.
Harara ya bi ta da shi sannan ya ce "sarai kin San hali na kar ki kaini bango, please ki yi hakuri ki bani amsa kafin a samu matsala" for the first time a rayuwan ta taji ya ambaci hakuri sai dai burin ta bai wuce ta daina ganin shi ba right now, jikin ta ko har rawa ya ke tsabagen tsoro da ke daman ita gwana Ce.
Sanin saurin zuciyan zai iya kai shi ya baro ya sa ya bata hakuri su rabu lfy already daman a wuya ya ke coz he hate what he is doing right now.
"Ban ban San kai ba ne" dariya ta bashi yanda ta yi maganan a tsorace amma kuma bai bar dariyan ya fito ba ya tsare gida "calm down magana kawai za muyi. firstly, kiyi hakuri da duk abinda na miki a baya kina kai ni bango ne and kinsan ban San raini shiyasa, maganganun da na fada miki kuma su ma cikin fushi ne haushi na nake hucewa akan ki so am sorry pls. Kaman yanda ki ka Sani both of us ba son auren nan muke ba but at least let us give it a chance ba mu San abinda Allah ya boye ba" a firgice ta dago tana kallon shi ko kadan ba ta taba expecting maganan zai iya fitowa daga bakin uncle Aliy ba.
Sarai ya gane abinda ta ke nufi hakan ya sa ya dan dara sannan ya ce "expect the unexpected life is always changing same goes to situations" shiru ta yi tana Satan kallon shi sai dai wannan karon ba mamakin abinda ya fada ta ke ba illa mamakin yanda ya ke gani duk abinda ya zaba shi za a yi, there is no doubt he is selfish. Ya gama ma ta wulakancin da ya ga dama yanzu kuma ya dawo yana tunanin su shirya lfy kalau, if he is okay with it ita an fada mishi she is.okay ko kuma shi kadai ke da feelings? Ba ta gaa tunani ba ta ji yana fadin "Maganan kenan daman dare nayi ba ra mu tafi, we will talk later"
Gaba daya daren tunanin halin Aliyu ta ke yi, shin in ma ta amince wani irin zama za suyi he is so selfish, infact she is not ready to accept him ma.
Haka dai ta cigaba da bin shi duk yanda ya so duk bayan kwana biyu za aiko mata da text yana tmbyn lafiyan ta da karatun ta iya ka ta mai reply da lfyn ta kalau ta gode shknn.
2 months later
Zaune ta ke gaban Yaya deedat yana mata bayani "am so sorry sister ban fada miki ba amma industrial attachment inki Abuja na nema miki har sun yi approving"
A firgice ta juyo tana kallon shi "Yaya Deedat ina zan zauna a Abuja"
"Gidan mijinki" ya bata amsa hakan ya sa ta yi kasa da kanta tana cigaba da sauraron shi "Zahrau its high time you face reality, Nasan Ya Aliyu ya miki laifi but tunda yanzu ya nuna yana son ya goge laifin shi pls give him a chance aure ba abin wasa bane Zahra. Just get to know your husband he is so nice kuma lada ma zaki samu"
"Tohm shknn" ta amsa ba wai dan ta so sai Dan ba za ta iya mishi musu ba
"Shknn in kinje Abujan zai kai ki asibitin"
Zaune ta ke a falon mami tana karanta littafi a watt pad, Sallaman da taji a bakin kofan dakin ne yayi nasarar janye hankalin ta daga gun littafin. Ido hudu su kayi dashi saurin dauke idanun ta tayi "INA wuni" ta fada kanta a kasa "lafiya kalau Mami na cike ne" ya bukata
"Tana kitchen" ta bashi amsa sannan ta cigaba da abinda ta ke.
Hanyar kitchen in ya nufa, ya dade suna magana da mami sannan ya dawo falon "Ki zo Mami na kiran ki" ya fada yana kallon ta, ba yanda ta iya mikewa tayi ta bishi zuwa dakin mamin.
Dukkan su biyun a kujeran da ke dakin mamin su ka zauna, kallon ta bi su dashi dukkan su sannan ta mai da kallon ta gun Zahrau "ke kunyi da Aliyu za ki bi shi ne?" Mami ta tmby tana kallon ta, shima Aliyun kallo ya bita dashi yana jiran mai za ta fada, daga inda ta ke tana iya hango shi da ke kujerun na kallon juna, harara ya fara aika ma ta hakan ya sa tayi saurin canja zuciyan ta kan abinda ta yi niyyan fada daga farko tunda shi gani ya ke takaman shi ke yi mai komai "Aa Mami yau ma Yaya Deedat ya ke fada Abuja ya cika min IT letter na" ko kallon shi bata yi balle ta lura da irin kallon banzan da ya ke aika ma ta.
"Kai kasa shi ko Aliyu?" A duniya in akwai Wanda Aliyu ba zai iya wa karya ba to mahaifiyar sa ce"eh mami nine" ya bata amsa hade da sunkuyar da kai.
"Toh ban amince ba" A firgice ya dago yana kallon ta "Mami me ya sa?"
"Saboda ban yarda da kai ba Aliyu, ba za kaje ka hallakar min da Yarinya ba a gida ma ka illatata balle kuma ka kai ta inda daga kai sai ita"
Ajiyar zuciya ya saki "Sannan ya ce mami please wlh kuskure ne kuma ma ki tmby ta na bata hakuri"
Girgiza kai tayi sannan ta ce "ka ma bar zancen nan, Abbah ma ba zai yarda ba shi kanshi ya sauke sharadin da ya daura ma ka yace raba Ku zai yi"
"Innalillahi mami Dan Allah ki bashi hakuri" muryar shi na rawa ya ke maganar "wlh mami Abbah baki zai min in har ya rabu mu, kuyi hakuri mami wlh zanyi abinda kuke so"
Kallo Zahrau ta bishi da shi ganin yanda ya rude sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa ya ke ta bin ta sau da kafa ashe bacin ran iyayen shi ya ke gudu.
Sallamar da Abbah yayi ne ya katsewa Aliyu abinda ya ke shirin fada. Kallon su yayi daya bayan daya sannan ya amsa gaisuwan da Zahrau ta ke mai, Aliyu ne ya gaishe shi maimakon ya amsa harara ya bishi dashi sannan ya ce "Daman INA Neman ka"
Sunkuyar da kai yayi yana sauraran abinda Abbah zai ce "bani takardan Zahrau" wani irin faduwan gaba yaji "Abbah Dan Allah..."
"Dakata Malam" Abbah ya katse shi a zuciye da hannu "ban son wani magana, INA nina hada auren to na fasa tun farko ban San halayen ka bane that's why bincike ya ke da kyau" A fusace Abbahn ke magana, Aliyu zai iya rantse wa bai taba ganin bacin ran shi ba irin na yau ba har ko lokacin case in farida.
Zahrau dai kan ta na kasa ba zata iya cancance wani irin hali ta ke ciki ba farin ciki ko akasin shi ita dai yanzu shirye ta ke ta amshi duk abinda ya kutso cikin rayuwan ta.
Mami ma kallon su kawai ta ke amma ko kyar ba ta ji tausayin Aliyun ba ya kamata ace shi dansu ya rufa musu asiri amma maimakon haka sai ya nemi tozarta su.
Kasa ya durkusa gaban Abbah yana bashi hakuri amma ba ko kallon shi bai yi ba illa takardan da ya ke Neman ya bashi.
Hello dearies, hope you are all fine? Alhmdl if so. So am really really sorry for the late and short updates, sai a hankali ne but I will be trying in Sha Allah.
I've all seen your comments and I really really appreciate everything and I will try to change cause you guys motivates me
Thank you
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top