KHF 30


  Abuja, Nigeria.

Idanuwan shi kar akan TV in da ke gaban shi, a hankali hankali yana daukan kayan marmarin da ke gaban shi yana kai wa baki. Duk Wanda ya gan shi zai yi tunanin gabadaya hankalin shi ya tafi ga tv din da ya ke kallo amma ko kadan ba hakan ba ne domin idanun shi kawai ke gun amma hankalin shi gaba daya ya tafi ga Neman mafita a kadararren auren da aka mai kaman yanda ya ke ikirari.

"Kar ka kara zuwa wuri na da sunan Neman in yafe ma har sai ranar da ka dauki auren da na maka da mahimmanci Aliyu in har na isa da kai" abinda Abbah ya ce mai kenan da su kaje wurin shi tare da Umar.

Mami ko fada ta rufe su dashi daga shi har Umar in da bai San hawa ba balle sauka, har gwara ita ma ta hakura daga baya nasiha ta musu sosai tare da sharadin zai gyara rayuwan auren shi.

A yanzu haka bai da mafitan da ya wuce ya gyara rayuwan auren na shi ba dan komai sai dan ya faranta ma iyayen shi ta hanyar cika musu burin su.

Sai dai bai san ta yanda zai fuskanci yarinayar ba bayan irin maganganun da ya sha fada ma ta ma rasa dadi duk da dai ba wai har zuciyan shi hakan ya ke ba Aa yayi hakan ne kawai dan ya ba ta ma ta rai sai dai har ga zuciyan shi bai jin yana son ta.

Bai so ta raina shi ko kadan bai son raini shi ya sa ya ke kama girman shi wurin kowa amma matsala zai iya takun shi dole ya San abin yi.

Numban ta ya bukata gun Umar don shi kadai ne zai iya amsan numban ta wurin shi ba tare da ya tuhume shi ba, Nan da nan Umar ya turo mai numban tare da farin ciki abokin shi da gaske ya ke zai canja.

"Fatima" ya tsinci kanshi da ma ta saving, sai kuma ya ji sunan ya mishi dadi kuma yayi kama da mai shi din.

Har yayi dialling numban sai kuma yayi saurin katse wa gwara ya turo ma ta text zai fi.

"Hey, how is ur body And school? Hope you are good? Its Aliyu ur brother"

Zaria, Nigeria.

Littattafai ne dayawa a gaban ta kala kala da note book da text book duka, Assignment gare ta na pharmaceutical microbiology, washegari za su yi submitting gashi yana da yawa ga research kuma printed one ya ke so sai tayi typing tukunna bayan haka kuma a washegarin ranar suna da test in biochem duk abubuwa sun hade ma ta dan ma Allah ya taimake ta kullum cikin karatu ta ke.

Searching ta ke yi a different kind of websites da kuma text books tana Neman convenient amsan da za ta ba lecturer in, karan shigowan text ta ji a wayan ta, tsaki ta ja cike da takaici tana fadin "MTN in nan su in shi mutane su bar mutum ya ji da abu daya mana"

"Wai miye sa da mutum yaji karan text a wayan shi sai ya ce MTN Ku duba mana sai Ku yi ta musu sharri" Fatima ta fada ita ma tana karatun test in biochem in da za suyi gobe da ke akwai courses dayawa da su ke yi tare.

"Duba ki gani mana su kadai ke da tym din banza"

Jawo wayan fati tayi sannan ta duba text in "ai ko kin dauki hakkin don ko numba ne ya miki text" shiru Zahrau ta ma ta Dan ta yi tunanin tsokanan ta tayi sai da taji ta fara karanta text in sannan ta dago tana kallon ta kaman daga sama taji tana fadin "its ur brother Aliyu" mamaki ta fara yi wani yaya gare ta Aliyu kuma "Aliyu kuma brother na" ta tmby fati

Hararan ta fati tayi sannan ta ce "a gidanku ba Aliyu ne" girgiza kai tayi "okay, ki duba true caller"

"Aliyu Abubakar Tafida" ta gani a rubuce, mamaki ne ya mamaye ilahirin ruhin ta gabadaya me zai sa uncle Aliy ya turo ma ta mssg.

"Yanzu kin gane kenan" fati ta tmby ta kai da gyada ma ta sannan ta ce "ni nafi sani Uncle Aliy ko kuma Yaya Aliy"

"Ehm yanzu da ki gane ai sai ki mai reply" tsaki ta ja ta cigaba da abinda ke gaban ta Girgiza kai fati tayi tana kallon ta cike da mamakin irin yanayin auren kawar ta.

•••••

Tun Aliyu na tsammanin reply in Zahrau har ya sadakar, "ita har ta isa ya daga waya ya mata text amma ba za ta mai reply, what the hell do she think she is? Ita har ta kai matsayin nan?" A fili ya ke magana sai dai shi kadai ne a falon, tsaki ya ja yana fadin duk su Abbah su ka ja min amma ba komai zai yi komai dan ya faranta musu sai dai ba zai dau raini.

Share ta yayi bai kara bi ta kanta ba. Weekend su ka tafi Zaria shi da Umar, yayi tsamanin ganin ta a gidan amma sai ya ga sabanin hakan Yusrah ya tmby ta ce mishi ba ta zo ba.

Umar ya fadawa komai akan fa shi fa ba zai iya daukan raini ba gwara kawai a barshi "haba Aliyu daga text daya sai ka yanke hukunci, in ba ta gane Kaine ba fa, bayan haka ka ma yarinyar abubuwa dayawa kasan mata da riko so matukar ka na son ganin ka cika wa mahaifanka burin su to ko shakka bbu sai ka sauke son girman da komai ka shawo kan ta tukunna"

Wani siririn tsaki ya ja cike da takaici "kar ka manta ba Wanda ya taba ce maka ta taba son ka balle ta ma ka abinda kake so, kai ke son abu so dole ka sauke kai ka nema Aliyu"

Ajiyar numfashi yayi sannan ya ce "this is totally annoying wlh, miye abin yi yanzu?"

"Pay her a visit" harara Aliyu ya juyo yana bin shi dashi alamun ka sha wani abu ne? "De na harara na kalau na ke"

"Sai dai in tare zamu" ya fada ba don zuciyan shi na son abinda ya ke shirin yi ba "ba matsala na raka ka yawon banza ma balle inda lada zan samu"

Murmushi ya saki Wanda akan fuskan shi kadai ya tsaya sannan ya ce "When are we going?"

"Tomorrow of course sai dai in you are eager sai mu je yau"

Hararan shi ya yi sannan ya ja tsaki "na Shiga daki ni" girgiza kai yayi sannan ya bi shi.

Washegari, a samaru su kayi Sallahn magariba. Sun zabi dare ne ganin irin ranar da ake yi da rana. Umar ke driving Aliyu ko yana gefe tunanin shi kawai inma sun je me za su ce Mata, "ka ma fada ma ta kuwa"

Dan dakata da tukin Umar yayi sannan ya ce "au ba ka fada ba ma kenan ka sa mu ka taho, in ba sa nan fa?"

Kallon takaici Aliyu ya bishi dashi, tsaki ya ja don bai jin yin magana ballantana ya maida wa Aliyu amsa.

Wayan shi ya ciro yayi dialling numban ta for the first time a rayuwan shi sai dai har ya katse ba ta dauka ba. Citson yatsa yayi cike da takaici hakanan ya hakura ya kara dialling numban na ta, sai da ya kusa katsewa sannan aka dauka.

Shiru yayi haka ita ma ba ta tanka ba ta kuma kashe wayan ba "Assalamu Alaikum" Ya fada a hankali "Wa'alaikasalam" ita ma ta fada a hankali, har cikin jikin shi ya ji saukan muryan na ta ko da yanda ta yi maganan a hankali ne kila "kina gida ne?"
"Ehmm"
"Okay, ga mu nan zuwa"
"Emhmm" kawai ta ce sannan ta yi shiru ganin haka ya sa yayi ending call in.
Sai sannan Umar in ya cigaba da driving da ke da man ya taba kai su Nanah gidan.

Kallon Fati tayi sannan ta ce "Wai Uncle Aliy ke ce min gasu nan zuwa, ko dai wani Abu ya faru ne"

"Daman sai abu ya faru Miji ke zuwa gurin matarsa"

Tsaki Zahrau ta ja sannan ta ce "to ni me zai min? In ba zuwa yayi ya bata min rai ba wlh ni ban son ganin shi"

"Ai da kin fada mishi a wayan"

"Fati me ye haka ina fada miki abu kina fada min magana"

"Me kike so ince miki Zahrau? So kike in biye miki ki kashe auren"

"Muna waje" ya turo ma ta mssg

"Sun iso wai, I can't go alone"

"Ya za ayi kenan"

"Kin zuwa zanyi mana"

Dariya fati tayi sannan ta ce "tashi mu je in raka ki"

Ajiyar zuciya ta yi sannan ta mike.

Umar na tsaye jikin mota shi ko gogan ya na zaune a ciki ya sa ko kafafun shi ta waje.

Da ke dare ne hasken da ke wurin ne ya haska fuskan Umar hakan ya sa su ka gane idan su ke.

  Nagode

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top