KHF 3
Birnin Zazzau
Daga Abbah, Baffah har Mami ba Wanda ranshi bai yi mugun baci jin irin cin mutuncin da aka musu.
Ammah ta so boye zancen ta fada musu zancen daga bikin da suka nema kawai amma kafin ta ce uffan ma Anty Zainab ta sanar musu duk abinda ya faru ba abinda ta rage.
A zuciye Abbah ya nemi a hada mi shi family meeting har ko da Aliyun da tun da ya ga bikin ya karaso ya ke Zaria da Aminin shi Umar.
Cikin mintuna kalilan aka hadu gaba daya, haka kawai Aliyun gaban shi ke fadi yana jin kaman zaman Dan shi aka yi. Baffah ne ya katse mai tunanin na shi "Kai Aliyu gidan kanana nan mutane kaje neman aure ne, ba kayi bincike ba halan"
Das das gaban shi ke fadi "Baffah lafiya me ya faru ne?"
"Me ya faru kake tambayan mutane, sakarkaru zaka mai damu ma kenan" A hassalce Abbah ke magana Dan lamarin ba karamin bata mi shi rai yayi ba.
Mami ce ta kalleshi sai keta zufa ya ke "Haba Aliyu da hankalin ka da Tunaninka, ko an gaya maka saboda Soyayya kadai ake aure" Umar da ke zaune kusa dashi kanshi a kasa ta cigaba wa magana "Kai kuma Umar kana ina ya je irin wannan gidan neman aure"
A hankali ya amsa mata "Mami a iya sanin da mu ka wa Farida mace kamilaliyya mai addini sai dai kuma in akwai boyayyen abu wanda Allah bai bamu ikon sanin shi ba" Kusancin shi da Aliyu ne tun suna kanana ya sa suka dauke shi tamkar Dan gidan haka kuma ko abu ya taso kan Aliyun to wurin shi suke samun Karin bayani.
"Kuna da labarin neman daga auren da shi mahaifin faridan yayi" Baffah ya fada yana kallon su dukansu biyun.
A firgice duk suka dago su ka kalli Baffahn gani suke kaman kunnuwan nasu basu jiye musu da kyau ba.
"Ba daku ake magana bane wai" Abbah ya fada yana musu kallon sama da kasa.
"Aa wlh Abbah ko kadan ba mu da masaniya a kai hasalima yanzu naji daga wurin ku" Aliyu ya amsa mai cike da girmamawa.
Mami ce ta karbe zancen
"To bayan Zancen daga auren ma, har da rashin mutunci aka zabga wa iyayenka da yayyinka ga Zainab da Ammah nan duk a gaban su aka yi komai"
Inalilahi Wa'ina'ilaihi raji'un kawai Aliyu ya ke ambato a cikin zuciya domin labarin ba karamin gigita shi yayi ba.
"Ba akanka muka fara aurar da Ya'ya' ba haka kuma ba akan ka zamu bari ba. Ga Muhammad ga Zainab ba tarzoman da ya taso a nasu sai naka?" Abbah ke maganan yana girgiza kai.
"Don haka ba zamu daga aure ba saura sati biyu biki, Don haka kaje ka nemo matan da zan aura maka aure da ita zuwa wannan lokacin ko kuma in zaba maka duk wacce naga dama"
Da sauri ya dago kanshi yana kallon Abbah, da kyar ya iya bude bakin shi domin magana "Abbah ina zan samo mata a kwana Goma Sha biyar?"
"Wannan ya rage ruwanka kuma, tashi ku bamu wuri."
Sadaf sadaf su ka tashi su ka bar falon. Tun daga lokacin Aliyu ya rasa natsuwan Dan ma Umar na tare dashi, Ya San halin Abbah mutum ne mai zuciya kuma baya magana biyu, tunda har ya furta a gaban kowa to ba makawa ya San sai yayi abinda ya fada din. Tsabagen takaici ma kasa kiran Faridan yayi domin jin ainihin abinda ke faruwa sai Umar ne ya kira ta.
Kaduna
Kwance take a rigingine tana kallon silin a zahiri amma zuciya da ruhinta tuni suka cika da fargaba hade da Shiga matsanaiciyar damuwa ganin abun ta ke kamar a mafarki wai Dad dinta ya raba ta Aliyu a bisa wani dalili nashi Wanda har yanzu ba Wanda ya Sani daga ita har mom. Ba abinda ke kara tada mata hankali sai irin abinda taji ance kanwar Dad ta wa yan'uwan Aliyun, Tana Son Aliyu Soyayya ba na wasa ba bata San da wani baki zata iya bashi hakuri balle kuma ta daga ido ta kalle shi. A takaice dai ranar wuni tayi tana kuka da kyar mom ta rarrashe ta.
Sau biyu wayar nata na ringing amma ba ta ma yi attempting duba wa balle ta dauka. A karo na Uku wayan nata ta ya kara daukan ruri, sai lokacin ta dauka wayan ganin Umar ne ya sa fargaban ta ta ke ji karuwa, sai da tayi bismillah kafin ta dauka game da yin sallama.
"Wa'alaiki Salam Sister hope dai kina lfy"
A hankali ta bude bakinta "lafiya brother" kawai ta iya cewa tayi shiru
"Sister mun ji abinda ke faruwa daga shine na kira inji me ye ainihin abinda ke faruwan"
"Wlh brother in nace maka ga abinda ke faruwa nayi karya, Dad in dai ya birkice ya ki zancen mun rasa gane kanshi gaba daya wlh. Dan Allah ka ba mine hakurin abinda aka wa su Anty Zainab wlh ba laifina bane and mom ta wa Wani Aminin Dad inma magana in Sha Allah komai zai dai dai ta."
"Ba wani abu Sister just keep praying, Allah ya zaba mana abinda ya fi alkhairi"
"Ameen brother mine in fa"
"He is frustrated call him later"
"Shknn, Dan Allah ka bashi hakuri"
"Karki damu, kinsan halin mutumin naki da ya sauko shi da kanshi ma zai neme ki"
"Tam brother nagode, sai anjima ko"
Zaria
Zuwa yanzu gaba daya gidan sun samu labarin abinda ya faru. Sai dai har yanzu Abbah yana nan kan bakanshi na ba zai daga auren ba. Tausayin Aliyun ya sa Baffah da Babban Yaya su ka yi tattaki har Kaduna wurin mahaifin Farida...
Yan matan gidan ne zaune a falon suna tattauna abinda ya farun, duk rashin jituwan su da yayannasu bai hana su jin bakin cikin abinda ya faru ba. Maijidda ce ta kalli Ummi da ke ta fama danna waya tana murmushi "Halan da likita kike chatting, wannan murmushin ba haka nan kawai ba" Ummiyn ce ta amsa ma ta Dan da ma ta San ba kyaleta za tai ba "Ya son ranki, Wani abin ma sai Next Year Officially Mrs Kabir Saraki Kanon dabo za ta yi diba" nuna kanta tayi tana blushing. "Ehmm fa Ummiy abi dai da Addu'a ga biki saura 2 weeks da kwanaki ance an fasa balle ke da ya rage kusan wata Tara" Nanah ke maganan tana hararta. Kaman jiran ta take ta gama maganan ta karbe da fadin "Ehm ehm dai Nana Aisha bari wannan maganan, shima Wanda kike maganan ai mai damu yayi low class to ga yan high class nan sun Nuna mi shi nasu halin though na ji wai yarinyar na son shi babanta ya kawo matsalan still na ji mai haushi kinsan wai ance hannunka ba zai taba rubewa ka cire ka yar ba to ya zamuyi tun da Allah ya hada mu da iri" "ke dai bari" Maijidda ta fada hade da mika wa Ummiy hannu suka tafa. Nanah kallo ta ke bin su dashi cike da mamaki in all her life bata taba ganin masu kushe yan'uwan su irin su ba "nikam Kuna bani mamaki gsky abin na Ku ma na lura kara yawa yake". " baki San waye mutumin nan ba" a tare su ka fada in aka cire Zahrau da ke gefe tana saurarensu. Itan daman ba mai yawan surutu bace sai kuma abin ya kara hadewa da abinda ya faru da ita month back.
Dan dan dan...
Wa ya dago abinda ke shirin faruwa?
Mu cigaba da gashi
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top