KHF 29
Accident and Emergency aka shiga da ita, sun dauki kusan 5 hours akan ta sannan aka fita da ita zuwa wani dakin, a rude su ka bi bayan likitan zuwa dakin da aka kai ta "Alluran bacci mu ka mata please a bar ta ta huta" Dr ya fada sannan ya juya ya kalle su daya bayan daya "is she married?" Ya tmby mami ganin duk ta fi su damuwa so he just assumes she is her mother, gyada mi shi kai tayi "fine, if the spouse is around I will like to meet him and you in my office". Aliyu da Mami su ka bishi office in, sai da su ka zauna sannan ya bisu da kallo, a hankali ya fara magana "she had an attack due to sudden frightened, I guess this is not the face time kuma hakan na barazana ga zuciyan ta, she is just young please kar a mata ruining rayuwa more especially you the husband ta kai stage in da kiris zuciyan ta ya ke jira ya buga so you have to be careful Dan Allah" Godiya su ka mai sannan su ka bar office in.
Ko da su ka koma dakin Ammah ce kawai a wurin sai hamza, Zahrau kam ba ta farfado ba "kai ba yau za ka koma ba?" Mami ta tmby hamza "eh daman wai naga Zahraun ne"
"Kai za ka ba ta lfy" girgiza kai yayi "to maza tafi gida ka shirya ka wuce" sum sum hamza ya fita ya bar dakin sannan Mami ta kalli Ammah "Ammah da kin je gida kin hutu, tun da dai zahrau n ta farka"
"Mami sai kuma na bar ki ke kadai?"
"Aliyu zai zauna"
"Haba Mami INA namiji INA zaman Asibiti?"
"Shi ya nemi zaman ai Dan Allah kuje Ammah kya dawo ko anjima"
"To shknn" ta fada
Wani kallo Mami ta bi Aliyu dashi da sai da yaji gaba daya jikin shi na rawa "me kayi wa Zahrau Aliyu" kasa magana yayi sai in INA da ya ke ta tayi da kyar ya ce "ma Mami ba ba abinda na na mata" harara ta bishi dashi da yasa shi saurin sadda kanshi kasa "tmby ka nayi ka ban amsa " wlh Mami magana kawai mu ka yi da ita shi ne fa tana fita naji maganan ki kina Neman ruwa"
"Maganan ma kala kala ne ai, ita ta maka laifi da za ka sauke fushin ka kan ta, shatin fuskan ta fa? Tunda na gan ta tana rike da wurin"
"Mami to ba INA mata magana bane ta min tsaki ni ban ma San na mare ta ba tsabar takaici"
"Inalilahi wa'inna illaihi raji'un Mari Aliyu, har yanzu ba za ka dena saurin hannun ka ba Ashe duka mace za ka dinga yi, yarinyar da daman ba ishashen lfy gare ta ba za ka buga"
"Ki yi hakuri Mami ba zan kara ba" ya fada kan shi a kasa.
"To in dai akan Farida ne ya sa ka dukan ta to wlh Aliyu bazan taba baka goyon bayan auren ta ba, ba da yawuna ba" wani irin faduwan gaba yaji jin abinda mamin ta ambata Duke da dai ba yau ta fara ambatan ba.
Abinda ya faru shi ne bayan auren Aliyu da Zahrau fir Farida ta ki yadda ta auri Wanda babanta ke so, juyin duniyan nan aka yi ta ki, karshe baban ya rufe ido ya aura mata shi a dole, ko sati daya ba ayi da auren ba ta daga wa mijin hankali, wulakanci kala kala karshe ya gaji ya sake ta. Tun da ta dawo gida ta fara Neman Aliyu tun yana doje ma ta har ya hakura a haka su ka cigaba da soyayyan su, wannan karon mahaifin ta da kanshi ya nemi ya turo mahaifin shi, shi ne ya zo fadawa Abbah bai San daman yana kule dashi ba kaca kaca ya mai sannan ya haramta mishi sakin Zahrau da kuma auren Faridan, wurin Mami ya je ita ma fir ta ki amincewa shi ne ya sauke haushin shi akan Zahrau baiwar Allah.
Satin Zahrau daya a asibiti ba laifi ta Dan warware, Aliyu kuwa har yanzu bai koma bakin aikin shi ba, fir mami ta hana shi a cewarta sai Zahrau ta warke sannan za ta bar shi ya tafi, ba yanda ya iya haka ya zauna ba dan yana so sai dan mami ce ba yanda za ayi ya mata musu. Zahrau tun da ta farfado ba abinda ta ki jini irin ta farka ta ji muryan Aliyu ballantana Kuma ta ganshi da idanun ta, wani irin kiyayan shi ta ke ji yana yawo a jinin jikin ta dan she even doubt ko soyayyan yan uwa tana mishi, ita ma ta tsane shi kaman yanda ya furta ma ta ido da ido ba kunya balle tsoron Allah.
Damuwar shi Farida itama ba ta da lfy, a cewarta tun daman yaudarar ta ya ke yi tunda yanzu ance ya fito ya ki, ya sha fahimtar da ita amma ta ki fahimta, zargin ta bai tabbata ba said da aka kwantar da ita a asibiti ya kasa zuwa ya dubo ta. Gaba daya ya susuce banda rama ba abinda ya ke zubawa, ga tunanin makomar aikin shi da aka hana shi komawa, banda hantara ba abinda ke hada shi da mami, Abbah ko ko kallo bai ishe shi ko gaishe shi yayi bai amsawa ga kuma farida, gabadaya yana cikin tsaka mai wuya ya rasa mafita.
Tsaki ya ke ta bugawa ya rasa mai ke mishi dadi gabadaya a duniyan, abinci da ke gaban shi ya bi da kallo amma me? Duk rashin wasansa gun ciki yau ko kara kallon abincin bai son yi, a hankali ya bi wayan shi da ke ta ringing tun dazu da kallo, mostly abokan shi na Abuja ke ta kiran shi bai San me zai ce musu ba shiyasa ya kasa dagawa.
Sallaman da yaji a kofan dakin shi ne ya katse mai tunanin da ya ke ciki said dai kafin ya amsa har mai sallaman ya shigo, Umar ne kallo ya bishi dashi kaman yanda shi ma ya ke kallon sa "ba ka da lfy ne frnd" kai ya girgiza mai "ka rame ka yi Baki, you are not picking your calls"
Ajiyar zuciya Aliyun ya sake sannan yq nuna wa Umar wuri alamun ya zauna su yi magana, "INA jinka"
A hankali ya labarta mishi abinda ke faruwa har karshe, kallon tausayi ya bi abokin na shi dashi, ko kadan Aliyu bai daukan shawara ne tun farko da hakan bai faru dashi ba "Aliyu gsky ba zan boye ma ka dole iyayen ka su yi fushi da kai ganin yanda ba ka dauki auren da su ka ma ka da mahimmanci kaga tun da Kai ba ka faran ta musu ba suma ba zasu faranta ma ka ba, the best solution kawai ka rabu da farida INA ga tun farko ba alkhairin ka bane shiyasa hakan ya faru, ka samu mami da Abbah ka ba su hakuri sannan ka rungumi auren ka hannu biyu ba ka San alkhairin da Allah ya boye a ciki ba kuma in kayi hakan dukkan matsalar ka zai kau ko ya ka gani" shiru yayi yana bin abokin nashi da kallo tabbas duk abinda ya fada gsky ne and it's the best way out.
"Frnd Wlh ban taba kallon yarinyar nan da sunan mata ta aure ba bansan yanda za ayi na sa zuciya ta ta fara kallon ta a matsayin hakan ba sannan kuma farida za ta ga kaman yaudarar ta na ke Dan man yanzu haka zargi na ta ke. Girgiza kai Umar yayi sannan ya fara magana " Zahrau mace ce da ko wani da Namiji ke burin ya samu fahimtar kawai za kayi Aliyu, she lacks Nothing sai dai abinda ba a rasa ba daman Dan Adam ba zai taba cika goma ba please frnd give this marriage a chance, Allah kadai ya San dalilin shi na yin hakan. Farida kuma ka barni da ita zan ma samu Salim da madam in shi akan magana su zasu iya fahimtar da ita ta yi hakuri ta koma gidan mijinta don shima yana son ta ta dai ki zaman ne, in kuka yi hakuri dukkanku sai Allah ya ba Ku abinda za kuyi alfahari dashi kilan ma jarrabawa ce yanzu dai mu fara da su mami" murmushi Aliyu yayi Wanda ya manta rabon da yayi irin ta "ko ruwa ban baka frnd" hararan shi yayi sannan ya ce mishi "yau kuma bako na zama a gidan nan" kallon shi yayi alamun au haka ne fa dariya su ka kwashe dashi dukkan su harda tafa hannu "yaushe ka zo?"
"Yanzu nan daga Abuja direct nan gidan na iso ka daga min hankali shi ne na zo inga lfy"
"Allah sarki abokina Allah ya ba ka matar da za ta kula da kai irin haka"
Hararan shi Umar yayi sannan ya ce "au tsiya za ka min to sha kurumin ka har na fada wa Baba ina neman aure yanzu ma muje in fadawa Abbah"
"Kai fa ba ka da kunya, wai kai yanzu da gaske kanwar Anty Rukiey nan za ka ke so"
"Tsaya nan kwanan za ka ji anje Neman aure ne"
"Allah sa alkhairi" ya fada yana tabe baki hararan shi Umar yayi sannan ya fita daga dakin ya bishi.
Thanks for all the votes and comments.
I do appreciated.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top