KHF 28

  Ko da su ka gama shiryawa su uncle Aliy ba sa falon da alamun masallaci su ka tafi saboda an shiga Sallah, an gama shirya ko mai so nan da nan aka fara program ba African time, its all ladies event so komai ya zo da sauki sai da aka fara kiran magariba sannan aka watse.

  Washegari ana shirin tafiya kamu ta je dauko Abu a gidan Babban yaya nan ta iske taron mazan family insu da abokanan su ba ta so wuce wa ba am she is in hurry ana jiranta Allaha ya taimake ta ta roki fati ta raka ta da ke ta zo bikin da hakan nan za ta koma, ta gefe ta lallaba ta wuce dan ba ma ta so su lura da ita  sai dai me sun fito kenan za su wuce Yaya deedat ya kwala ma ta kira, ba yanda ta iya haka nan ta karasa gaisuwan da ba ta so dai sai da ta yi shi As usual Umar da Salim su ka sa ta a gaba da tsokana "INA Maman khalipha" ta tmby Salim, "tace ba ki da Kirki ai ba kya nementa". " Ayyah pls ka ba ta hakuri I will call her" Gogan na ta ko hankalin shi gabadaya na kan waya ta fi jin dadin hakan Dan ba ta cika so abu na shiga tsakanin su ba, sakon da Ya deedat in ya ba ta ta kai wa Ammah ta amsa su ka wuce da Fati.
  ***                      ***                    ***

    Sai da ta tabbatar kowacce ta samu motan da za ta wuce dinner sannan ta yi cikin gida ko ta huta "Aa Antyn mu ke ba za kije ba ne na ga ko shiryawa ba ki yi ba" Hamza ke magana "Wlh ko hamza a gajiye na ke"  "Aa fada min gsky ko dai ya Aliyu ne ya hanaki" Girgiza mi shi kai tayi sannan ta yi hanyan sassan Ammah  "Zahrau" ta ji an kwalla ma ta kira hamza ne dai still "Ana miki magana" ya fada sannan ya wuce, direction in da ya nuna mata ta kalla, four eyes su ka yi da Uncle Aliy ganin bai da niyyan dauke idon shi ya sa ita tayi saurin dauke na ta, alama ya mata da hannu ta karaso ita abin ma mamaki ya fara ba ta. "Me ya sa ba ki je ba? Ban son karya". " Ammah ce ta hanani wai sai na tmby "
   "Ke kuma kin fi karfin tmby ko?"
  Shiru ta yi tana kallon shi cike da mamaki "je ki shiryo in kai ki ba za su ji dadi ba in ba ki je ba" ba musu ta wuce cikin gidan ta shiryo. Ba Wanda ya ce ma wani uffan har su ka isa ya sauke ta, tana fita ya ja motan shi ya dawo gida ba komai ya sa shi yin hakan ba sai gudun Abbah ya ji lbr rashin zuwan ta ya ce shi ya hana ta a tunanin shi kenan.
   Washegari aka daura aure sannan aka shirya kai amare gidan su, sun ci kuka kaman ba su ke son auren ba rungume junan su kayi suna kuka da kyar aka raba su Dan ganin lokaci na tfy, kano a kai Ummiy sharadda phase 2 Maijidderh kuma Kaduna Nasfat village saukin su ma Anty zee na kano while Kaduna kuma Anty Rukayya, ita dai Zahrau ba inda ta je a cewan ta sai bayan kwana biyu za ta je ta ga gidan na su saboda har ga Allah ba ta son wa za ta raka ba they are all equal to her. Sai kuma gidan ya zama shiru saboda kowa ya watse su Yusrah ma sun tafi school boarding hamza ma ya koma, yaya deedat Tun safe ya ke fita aiki daga ita dai sai mami da Ammah sai kuwa Adnan, Uncle Aliy ma tun bayan bikin ba ta gan shi ba kuma ba ta tmby ba "Anty Zahrau Abbah na kira" Adnan ya katse ma ta tunanin da ta ke "Yana parlor?" Gyada kan shi yayi ya wuce.
   Abbah da Mami ta tarar a falon sai da ta zauna ta gaishe su cikin fara'a su ka amsa ma ta "Yaushe za Ku koma makaranta". " December" ta bashi amsa kanta a kasa "Nan da one month kenan" "eh" ta amsa still kanta a kasa "me ye sa ba ki bi Aliyu ba" wani irin Abu ta ji a zuciyan ta ko tunanin komawa gidan ba ta so ma, shiru ta yi Dan ba ta San me za ta ce mishi ba "ba ki ma San ya tafi ba ko?" Gyade mishi kai ta yi Dan ba ta San me za ta ce mishi ba "Good, fada min wani irin zama kuke yi dashi, kuna ma magana da shi kuwa"

  Abbah mutum ne mai hikima ga iya karantar mutum abinka da tsohon lauya duk yanda ta so boye mishi sai da ya fuskance ta, yanayin fuskan ta kadai ya tabbatar mishi abinda ya ke zargi "tashi ki tafi zan neme ki"

   Sati biyu kenan da maganan su da Abbah amma bai kara Neman ta da maganan ba ba kuma Wanda ya taba ma ta maganan Aliyun ita har ga ranta tafi jin dadin hakan ma. Ita da hamza ke kallo a falon mami suna musun siyasa kowa da Wanda ya ke bi wa baya, ko sallama ba su ji ba sai ganin mutum su ka yi akan su yana tmby INA mami "yanzu ta shiga" hamza ya amsa, ko gaisuwan da ya ke mishi bai bi ta kai ba ya yi hanyan daki "toh fah wa ya tabo mutumin naki ne Antinmu" hararar shi ta yi sannan ta mai da hankalin ta kan kallon da ta ke yi, ya kai 30 minutes sannan ya fito har yanzu dai ranshi a bace ya ke  "Ki same ni a dakina na cikin gidan nan" ya fada ba tare da ya kalle ta ba sannan ya yi hanyar kofa itan ma kallon ta ta cigaba da yi sai da hamza ya tabo ta "ke mijinki na Neman ki ba za ki tashi ba ko? Haka aka koya miki" "Allah hamza ka sa min ido INA ruwan ka ne wai?" Dariya yayi sannan ya ce "Allah Zahrau ku shirya kanku da Ya Aliyu za Ku dace sosai" banxa ta yi dashi ta cigaba da kallon ta sai bayan kaman mintuna Ashirin sannan ta tashi ta dauki mayafin ta tafi ta daga falon tana jin hamza na tsokanar ta "Za a amsa kiran mijin kenan bayan an gama Jan aji" bazan ta yi dashi ta wuce abin ta.

   Zaune ya ke ya hade girar sama da na kasa sai kofa ya ke ko da tayi sallama banza yayi da ita sai da ta zaune sannan ya bita da harara "tun yaushe na neme ki?"
   "Tun dazu" ta bashi amsa kai tsaye
   "Okay raini ya hanaki zuwa" shiru ta mai "ba magana na ke miki ba?" Tsawa ya mata da sai da ya sa ta yi baya dan tsoro jikinta har kyar ma yake, wani siririn tsaki ya ja sannan ya ce "ke ga shegen tsoro ga kuma rashin kunya, me da me kika je kika ce wa Abbah na miki?" Kallon mamaki ta bishi dashi sai kuma ta yi saurin sadda kai kasa "Tmby na yayi ya alakar mu da kai ni kuma na fada mai?" Ta fada a hankali though da kaji muryan ta kasan a tsorace ta ke dashi "saboda kina son alakar ya fi haka? Ko kuma ki na son hadani da mahaifina" girgiza kai ta yi cikin sauri "kace in nemon hanyan da bazan kara komawa gidan ka ba shiyasa" "karya ki ke yi to albishirinki INA mai taya ki farin cikin Abbah ya ce duk ranar da na sake ki ba zai taba yafe min ba, INA son in gama da duniya lfy so sai ki shirya damarar zama da ni da dukkan halaye na da za ki tarar gaba but FYI I will never see you as a wife so is good ki shirya rayuwa cikin kunci da wahala da kuma rashin so" sheshekar kukan ta da yaji ne ya sa shi dakatawa ba komai ya sa ta kukan ba sai jin hukuncin da Abbahn ya yanke "Dakata malama ki dena min kukan munafunci, na fi ki tsanar labarin da na ke baki, upon all matan duniya ma me zan yi da mace irinki?" Girgiza kai yayi cike da kunci sannan ya ce " wlh an cuce ni amma Aliyu wlh ya fi karfin ajin ki, I will never love you in my life" tsakin da ta buga ne ya katse mai maganan da ya ke yi this tym around, ya tsani a mai tsaki ko da wasa wani irin mari ya kife  ma ta a fuska ba shiri ta zube a kasa "Na tsaneki wlh" ya furta ya na bin ta da kallon tsanar da ya fada yana mata, a zabure ta tashi ta fita waje da gudu.

  Mami ganin yanda Aliyun ya fita ya sa hankalin ta bai kwanta ba tuntuni, dakin shi ta nufa domin tana son su tattauna dashi amma sai dai me? Zahrau ta hango ta fito da gudu daga dakin tallabe da fuskan ta da sauri ta karasa gun ta tana tmbyn lfy? Ganin idon ta ya fara rufe ta yi kasa ya sa ta saurin rike ta tana girgiza ta amma ina b ta ma San ta na yi ba. Jin maganan Mami ne ya sa Aliyu fito "ruwa ruwa" mamin ke ta kira, da sauri ya dauko bottle da ke kan study table in shi ya mika mata, sai da aka yayyafa mata sannan ta saki ajiyan zuciyan mai karfi kirjin ta sai buga ya ke da karfi, "dauko key mu tafi asibiti" Mami ta fada a rude hijabin ta ma hamza ne ya dauko ma ta.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top