KHF 25
Har tsakan dare ta kai tana tunanin mamakon rayuwan ta, ganin har Uku ya yi ya sa ta gabatar da nafilah tana rokon Allah ya zaba ma ta abinda ya fi zama alkhairi a rayuwan ta, ba ta San sanda bacci barawo ya sace ta ba a nan kan Sallayar sai da aka kira asuba ta tashi shi ma Dan ta saba tashin ne. Tana idar da Sallah ta koma bacci da ke a gajiye ta ke ba ta samu daman tashi ba sai karfe 11.
Ba ta yi tsammanin tym ya ja haka ba, a daddafe ta karasa bayi ta yi brush, cikin ta ne ya fara wani kuka ko shakka bbu yunwa ke damun ta tunda dai yunwa ba kanwar baban ta bane rabonta da abinci tun jiya wurin karfe biyu shi ma Anty Rukayya ce ta tasa ta sai taci da haka za ta kwana da yunwa Dan Sam Sam abinci bai mata dadi tun da aka sanar da ita auren ta, yunwan kara shigan ta ya ke sai dai ba za ta iya fita ba balle kuma batun zuwa kitchen in yana falon fa Allah ya gani tana tsoron haduwan ta dashi saboda ba ta San wani irin karba ya ma ta ba.
Umar ne yayi sallama a kofar falon , Aliyu na zaune yana kallo ba komai ya kawo shi gidan ba sai sanin abinda abokin shi zai iya aikata wa kuma ga dukan alamu zargin shi ya tabbata "frnd an tashi lfy?" Ya fada yana cicije wa "da ba lfy ai ba za ka ganni ba INA zahrau"
"Wannan wani irin tmby ne tana inda aka ajiye ta ma na"
Tsakin takaici Umar ya yi hade da girgiza kai "Allah ya shirye ka" ya fada yana dialling numba a wayan shi yayi ignoring "Ameen" in da Aliyu ya fada.
Nanah ya kira ta turo mi shi numban Zahrau sannan yayi dialling numban ta. Tana zaune kan gado tana juye juye Dan kirjin ta har ya fara ma ta zafi abinka da daman tun can tana Ulcer, New number ta gani hakan ya sa ta share ba ta dauka ba amma ganin ana ta kira ya sa ta picking. "Hello" ta fada cikin muryar ta da ta fara dishewa "Umar ne ki fito parlour pls" ya fada sannan yayi ending call din. Hijabin ta har kasa ta dauko ta sa sannan ta lallaba falon. "Bismillah zauna mana" Umar ya fada yana nuna ma ta wuri. Gaishe shi ta yi ya amsa sannan ya tmby ta gajiyan biki "Ya kuma kwanan bakun ta"
"Lfy kalau" ta amsa kanta a kasa tana wasa da yatsun hannun ta. "Ma sha Allah kaman yanzu kika tashi, kin karya kuwa?" Girgiza mi shi kai tayi "frnd ba Amina ta aiko muku da abinci ba". " yana dinning " ya fada hankalin shi kan kallon da yasa a gaba. "Ai da kin fito kin duba Zahrau ba dadi zama da yunwa sai ya miki illa, Dan Allah sai kinyi hakuri fa kin San ba wai zama kika zo for a mean time ba don mu fata mu ke ace kun fahimci junan ku domin duk abinda aka ce miki iyaye ne su ka hada to tabbas ana hangen alkhairi a cikin sa, In sha Allah wata rana dukkan Ku za Ku zo kuyi alfahari da hakan Dan wani hanin ga Allah baiwa ne wlh kar ki manta har tmbyn ki an je a gida amma da ya ke Allah bai yi ba sai abin ya juye a haka kinga KO kullum Abu mafi alkhairi mu ke Neman wurin Allah domin shi ya fi mu sanin dai dai sannan ya zaba mana abinda ke alkhairin gare mu gabadaya, auren Ku da Aliyu wlh hadin Allah ne Zahrau coz dukkan Ku da wadanda Ku ke tsammanin za Ku yi rayuwa da su sai aka samu akasin haka, pls and pls ki sauke komai ki rungume auren nan da hannu biyu ibada ne a wurin ki kuma shi zai kai ki aljanna, so i will like it in kika yi accepting destiny in ki kika karbi Aliyu a matsayin mijin ki na aure ko da ko shi bai yi Na'am da hakan ba you are a Lady you know your ways". Mtseww, wani wawan tsaki Aliyu ya ja sannan ya bi both Umar da Zahrau da harara "for God sake ya za ayi ya zauna ya na fada ma wannan yarinyar irin talks in nan she is not wise enough for that ai duka duka yaushe ta gama secondary school, karatun ma he doubt in akwai abin arziki a kwakwal war bare ta yi wayewar da zai iya zama da ita a matsayin matar shi" Kashe TV yayi sannan ya wuce hanyar dakin sa ya gaji da jin abin takaicin haka nan. Murmushi Umar ya mata "sorry please go and get yourself some food na cika ki da surutu." Ya fada yana nuna mata dinning din. "Ehmm Nagode" ta amsa dinning din ta nufa saboda yunwan ya shige ta sosai shi ko Umar dakin Aliyun ya nufa ya iske shi ya kwanta yana kallon silin "frnd me ye haka, tsakin na menene kuma fisabillilahi ya za ayi ka bar yarinyar mutane da yunwa ta hakan za ka sauke hakkin da ke kanka da ban zo ba fa? Kuma kai kafi kowa sanin darajan Abinci Dan ko ba ka wasa dashi"
"Umar ya za ayi ka tadda wannan yarinyar ka na mata irin maganganun nan ba ta yi deserving ba Wlh" kallon mamaki Umar ya bishi dashi "au shi nasihan ne sai Wanda aka zaba". " I mean ka San dai ita ba tsari na ba ce kuma ba ta kai ajin mata da zan iya Hulda da su ba so banga dalilin da zai sa ka zauna kana hada ta dani ba har da CE mata ta San ways ta fa ja hankali na kenan kake nufi gsky ka cuce ni wlh me zan yi da wannan abin" tafi Umar ya mai "bravo, ka fi San wayyayu Wanda da ake damawa da su a duniya Wanda idon su a bude su ka San me ake ciki a duniya" "No atleast mace wayyaya wacce za ta iya tafiyar da Alamuranka na jama'anka da kuma yayanka wacce ba za ka ji kunyar nuna wa ba somebody educated, mai tarbiyya, amma wannan ka na ganin tana da courage in da za ta iya fuskantar mutane na in ma tana dashi me zata ce musu, she is not serious in her studies fa kawai zuwa schl din ta ke kaga ko wurin speaking a samu matsala kullum tana kunshe cikin dogayen hijabai banda shiririta ba abinda aka iya, kai ni physical appearance in ta ma is not good for my liking"
"Naga alama, amma tarbiyyan da kayi mentioning bai sa ka jin wani iri ba, gida daya kuka taso mutane daya su ka muku tarbiyyah kaga ko in har kana da shi to tabbas ba ka da shakku akan ta, karatu kuma ai kai ka mata jarrabawar shiga University ko? Batun wani kyau kuma da kake ambata Wlh karya kake kace ba ta da kyau ko da ko za a tara maka kyawawa in fact abinda ke boye shi ne mai kyau ba Wanda ke bude a duniya ba, atleast give her a chance wacce ka ke ma wa dai an riga an aurar da ita so gara ka wa kanka fada" tsaki ya ja sannan ya bar gidan gabadaya.
Bayan la'asar Amina matan Salim ta zo wurin ta, har dakin ta shigo ta same ta, taji dadin ganin domin ko kadan ba ta kaunar halin kadaicin da ta ke ciki, yaron da ke hannun ta ta amsa daman tana son yara barin ma maza "Ya sunan shi?" "Khalipha" "Kai amma dai ya fi kama da Yaya Salim" dariya Aminan ta ma ta domin ko ba gun ta ta fara jin comments in ba. Ganin she is trying to be free with her ya sa ta saki jikin ta sosai da ita, kafin ta tafi sai da ta mata nasiha sosai akan Aliyu domin ta San komai la'akari da faridan kawar ta ce. Ba ta so su ka tafi ba Dan dai ba yanda ta iya ne barin ma khaliphan ya shiga ranta sosai.
Ramadan Mukharram!!
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top