KHF 24
Kaman yanda ta saba tafiya weekend cikin Zaria duk Friday wannan satin ba ta samu dama ba saboda test in da ta ke dashi ranar Monday gashi sai 6 na yamma su ka samu fitowa Physics practical ranar Friday din don haka a gajiye likis ta nufi North gate domin karasa wa gidan su da ke off campus su ke zama ita da Fatima ba su samu hostel ba.
Napep ta hau ganin in tace za ta karasa a kafa ba karamin wahala za tayi ba, A shago ta tsaya ta saya ma Fatima sakon da ta ba ta, Tabbas Uncle Aliy ta gani a gaban ta bin shi ta yi da kallo shi ma itan ya ke kallo amma me? Ta bude baki za ta gaishe shi taga ya dauke kai ya karasa motan sa ya tafi, girgiza kai ta yi cike da takaici, shin wannan wani irin mutum ne da zai dauki tsanan duniya ya daura musu alhalin jinin su daya, abin har ya Kai nan kenan. A ganin su Mami da Ammah rashin jituwa ne kawai tsakanin su basu cika zama ba in yana gidan shiyasa ba su fuskanci ainihin abinda ya ke faruwa ba.
A ranar Sulaiman ya shigo Zaria jin ba ta zo gida ba yasa shi zuwa nan Samarun ganin ta.
Though a gajiye ta ke lallabawa ta yi ta fita saboda in ba ranar ba Saturday da Sunday she got a lot to cover. Yana Zaune cikin motan shi ya hango ta tafi to, dube dube ta fara yi dan ba ta ganshi ba ganin haka ya sa ya fito cikin motan, tsaf ta hango shi amma ta ki karasa wa don a ganin ta shi ya kama ta ya karaso din fahimtan da ya mata ne yasa ya karasawa "muje ko"
"Aa mu zaune a nan mana" ta nuna bencin da ke can gefen su "kaman motan zai fi nake ga"
Girgiza kan ta tayi "okay mu je din" ya fada sanin ba za ta shiga ba tunda ta ki tun farko.
"Ya hanya Gentle? Gsky kana kokarin zuwa garin nan ko gajiya ba kayi?"
"Haba Smart how do you expect me ba zan zo ba after all na ajiye ki" murmushi ta yi "To thank you amma pls a rage kar Stress ya ta damun ka"
"To ai baki Sani bah ganin ki ya na sa duk Stress in tafiya, Wai Smart yaushe zan tura gida ne am eager to have you forever" kallon ta ya ke cike da shauki ta yanda za ta iya ganin zallan soyayyan ta a cikin idanun shi ba alaman karya bare yaudara.
"Ko 100 level ai a bari in gama ko"
"Smart kenan just promise me you will be with me a cikin ko Wani hali"
"In Sha Allah Gentle"
Wayan shi ake ta kira amma yana rejecting ganin an ki daina wayan ne ya sa ya hakura ya dauka "am doing something important please zan kira ki later" ko me aka fada mishi sai ji tayi yana fadin "Allah zan kira ki trust me, OK bye" Kallon tuhuma Zahrau ta bi shi dashi sannan ta sunkuyar da kan ta kasa, Allah yayi ta da mugun kishi Mara misaltuwa hatta kawar ta tana kishin ta gan ta da sabban frnds balle kuma saurayi "Abin har ya kai da ayi a gaba na kenan" ta fada a hankali da kaji yanayin maganar ta kasan abun ya bata mata rai. "Oh no Zahrau na isa she is just a coworker akwai aikin da muke tattaunawa ne"
"Aikin ne har da dare?" Ta girgiza kai "bazan iya gasan ba sai in bar ma ta kai" da kaji muryan ta kasan kiris ya rage ta fashe da kuka
"Haba Zahrau ke Kinsan ba zan miki haka ba ko baki yarda dani bane?"
"Me yasa tun farko kaki daukan wayan?"
"Saboda gujewa irin haka"
"Gentle kenan" kawai ta fada sannan ta yi shiru.
Hakuri ya dinga ba ta yana tabbatar ma ta zargin da ta ke mishi ba haka bane
"Allah za ki sa inyi dana sanin zuwa kuma zan ga kaman next time ma in nazo similar thing zai iya faruwa"
Kallo ta bishi dashi "Saboda kasan zai iya faruwan ko"
"Ki fahimceni mana, shin Kinsan illan zargi kuwa? Bai kamata mu daura alakar mu da zargi ba Smart saboda zai zamo ba yadda tsakanin mu gaba daya kuma kinga ba amfani kenan, in har ko muna son cin ma nasara aure dole mu ture wannan mudinga wa junan mu kyakyawan zato" tuni ya cika ta da kalamai da wa'azi har ta yadda ba abinda ke tsakanin su da wacce ta kira shi ganin dare na yi ya sa ta kira Fatima su ka gaisa sannan su kayi Sallama ya tafi.
Bayan ya bar wurin ne ya kira Samira ya mata ta tas hakan yayi sanadiyar rabuwan su. Ba karamin kuluwa tayi ba ganin ba abinda ta mishi so ba ta San dalilin da zai sa ya mata haka ba. Shi ya fara sanin ta a matsayin Ya mace gabadaya ta gama saudakar mishi da kan ta da soyayyan ta gabadaya ta ya ma za ta iya kyale shi bayan shi ya bude mata idanu though bai San ta zarce idan ya ke zato ba. Kawarta leelah ta samu cike da tashin hankali nan su ka fara kula kulan yanda za su rama abinda ya ma Samiran sai dai a binciken da su kayi ne su ka gano yaudaran matan ya zama kaman sana'ar shi ne nan su ka dauki aniyar ganin karshen shi. Trap su ka mishi ya fada da leelah sai dai ita tun farko ya San idon ta a bude ya ke, Sun kai 3 months kafin su ka gama shirya planning insu sai kuma komai ke tafiyan musu yanda su kayi planning.
A ranar da aka kama shi kafin ya fita ya kira Zahrau ta Skype as usual daman system in ta na gaban ta shi ta ke jira, she is kinda obsessed with him apparently. Dariya ta fashe ta fashe dashi tana ganin face in shi akan screen in laptop in ta, he doesn't have idea me ta ke ma dariya amma ganin yanda ta ke dariya bbu kakautawa ya ji ya burge shi, komai na Zahrau burge shi ya ke, wani murmushi ya saki saboda wani farin cikin da ya ziyarci zuciyan shi bai ta ba ganin ta tana irin dariyan ba so it memorable to him. "Haba Gentle wannan yashe hakoran fa kaga kanka kuwa?" Ta fada tana sasauta dariyan na ta. Shafa kan shi yayi sannan ya gane abinda ta ke nufi, Askin da yayi ta ke wa dariya Wanda saboda birthday in besty leelah yayi ace warta they have to look beautiful saboda su ne guest of honour "Trying to act social? To bai ma ka kyau ba ma gwara ka je kayi askin gabadaya" He feel sad the moment da tayi maganan cause da ta San dalilin da ya sa yayi askin da ba zata fada ba. Anya ya na wa Zahrau adalci kuwa? Girgiza kan shi yayi "I will change soon coz of her" ba zai iya mata karya ba so sai ya ma ta murmushi kawai sannan ya canja topic in. "Smart pls pray for me kinji?" "But why?" Ta tmby ganin face in shi he looks serious.
"Zan fada miki wani time for now kawai ki tayi ni da addu'a, its late ki kwanta ko" ya fada yana daga mata gira hade da kallon shi mai rikitarwa.
"Shknn Allah ya kawo mana sauki, Gud nyt"
"Nyt smart promise to be with me whatever the situation pls"
Faduwar gaba ta ji jin abinda ya fito daga bakin masoyin nata.
"You are my always and forever In sha Allah"
"Thank you smart, I love you, sweet dreams"
Back to the story...
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top