KHF 23

  Kallon Lafiyan ki kalau Ummiy ke bin Maijidderh da shi bayan ta gama labarta ma ta abinda ke tsakanin su da Ibrahim, sau dayawa ta sha tunanin canja numban amma in ta tuna Ibrahim din ya amsa numban ta sannan za iya kiran ta at anytime sai ta fasa hakan, tun tana sa rai har ta gaji.

  Kwatsam kiran Ibrahim ya shigo wayan Maijidderh ya na mai sanar ma ta ya gama komai na shi soon zai zo wurin ta. "Ke yanzu rayuwan da zaki zaba ma kanki kenan Maijidderh akan So?" Kallo Zahrau ta bi ta tashi tabbas Ummiy ba ta San so ba ne shiyasa ta ke fadin haka amma ita ji ta ke za ta yi abinda ya fi haka ma in dai kan soyayya ne, a kullum rashin da ta yi dawo ma ta yake sabo fil a zuciya in ta ji ana maganar Soyayya, ko kadan ba ta ga laifin Maijidderh saboda da sanar da su irin son da taji tana ma Ibrahim din, shin ma ina ruwan so da matsayi?

   Anisa kanwar Khalipha ce ta tashi yau ba lafiya zazzabi ya rufe ta kirif, NNPC industrial clinic su ka nufa da Anty Rukayya sai Ummiy da Nanah su ka bar Zahrau da Maijidderh a gida da ke da rana su kaje duk likitocin Sun fita break sai doctor  daya consultant ne ya zo musamman daga Aminu kano teaching hospital kuma ma sai anyi booking ake ganin shi, jikin Anisa ko yayi tsanani sai rawan dari ta ke gashi daman tana da Pneumonia sai wani nishi ta ke sama sama,  Shi ko doctor din ya Dade a ciki suna magana da wani probably ba abinda ma ya shafi ciwo bane ga patients dayawa sai complain su ke tashi  Ummiy ta yi ta cincibi Anisa ta yi office in doctor direct ta bude "Sorry Madam da kin Dan jira ni for some minutes zan fara kiran suna"
  "Sorry doctor Alfarma nima nake nema my patients is suffering she is a young girl" ta bashi amsa kai tsaye, kallo ya bita dashi jin yanda ta ke magana kai tsaye cikin tsiwa
"Okay come in " ya fada.
  Sai da ya gama duba Anisa Sannan ya dago ya kalle ta to yan Neman Alfarma hope nima in na nema za a min? Murmushi ta mai duk tsiwan na ta sai taji ya tafi yau. Doctor Kabir Saraki, Can I have your number?
   Wannan ne  mafarin Alakar Ummiy da Doctor Kabir, sai ko abin nasu yazo daya domin BUK ta cika a Jamb form inta. Nanah da Maijidderh KASU sai Zahrau ABU Zaria.

  "Ke ashe Ibrahim inki SSS ne" Abinda ya sauka kunnen Maijidderh kenan Anty Rukayya ke maganan, dukkan su su ka juyo suna kallon ta cike da mamaki, "Baban Khalipha ke fada min Kusan Alhaji Nakowan layin can?"
  "Custom in nan Anty?" Nanah ta tmby
"Shi fa shi aka turo yin bincike akan kasuwancin shi"
  "Tab to ke Anty ya aka yi kika Sani?"
  "Jiya ya je office in baban khalipha ya mishi godiya, ya ce kun daidai ta haka ne?"
  Hankalin ta a tashe tace "Anty ni wlh ban Sani ba sai yanzu"
   "To Maijidderh ai daman is part of their job so no way zai gaya miki".

    Wuni su kayi suna mamakin lamarin kaman shirin film su ke ganin abin. Kiran shi Maijidderh ta yi tana mai complain in me yasa ya mata haka? Hakuri ya bata akan yanayin aikin nashi ne he have no choice.

    Admission in su ya fito kowaccen su ta samu abinda tayi applying, sai shirin fara registration.

                  *2 months later*

     Sun yi nisa a karatu war haka sai kokarin copping da yanayin University din, Tare su ke zaune daki daya da Fateemerh ita ma ABU in ta ke sai dai ita Biochemistry ta ke karanta wa Zahrau kuma Microbiology.

   Sanye ta ke da dogon hijab inta har kasa mai hannu mai hannu, kanta a kasa ta karasa Electrical Engineering Department in da Yaya Deedat ke lecturing. Dai dai za ta shiga office in ta ci karo da maza biyu sun fito daga office in, ganin yanda su ke kallon ta ya sa tayi saurin shiga office in. " Ya dai" Musa ya tmby Sulaiman ganin har ta rufe kofa amma bai daina kallon wurin ba. "Am in love" ya fada a hankali gami da dafe jikin bango sannan ya lumshe ido. "Hey Guy stop acting wannan ba kalan yaudarar ka ba ce , Kanwar Deedat ce fa" Wani irin ajiyar zuciya Sulaiman ya saki "Alhamdulilah abin ma zai zo da sauki kenan"
  "Au har iskancin naka ya kai nan Sulaiman Kanwar Abokin ka fa ai inda kara Karen gidan siriki ma uba ne"
  "Musa kenan kaman yanda ba ta ma ka kama da kalar yaudaran ba nima ba yaudarar ta zan yi ba, kyakyawan Niyya na ke dashi this time"
  "Yau ka fara fada Sman? Kar ka manta ..."
   Dakatar da shi Sulaiman yayi "Dan Allah ya isa haka ba lallai ka yarda ba daman"
  
    Sarai Sulaiman ya San Musan ba zai taba yadda da shi ba, kafan abokan shi na Zaria shi kadai ya San waye shi gabaki daya saboda duk kanwan ja ce, halin su daya sai dai shi MUSA a bayyane ya ke abin shi.

   Deedat Sulaiman ya samu da maganar Zahrau, Kallo ya bi shi da shi daga sama har kasa yana son gano  gaskiyan lamarin abinda ya fada din, ya San halin da Zahrau ta shiga ranar da aka wayi gari ba Abdulrahman ba zai so hakan ya kara faruwa ba domin ba karamin jinya su ka sha ba "Ka tabbatar da abinda kake fada? But why her?" Ya fada yana mishi kallon tuhuma. "Its just happen daga lokacin da na sa ta a idanu so pls save a friend" Dalilin da zai sa ya hana Sulaiman Hulda da Zahrau ya ke Nema sai dai ko ta ina ya bullo sai ya ga Sulaiman bai da makushi a wurin Dan a ganin shi Sulaiman ya fi shi riko da addini, duk a cikin abokanan su ba Wanda ya kai shi kokarin azumin Nafila da Salloli . lokacin su na karatu a ABU shi ke matsa mishi sai ya tashi Sallahn dare ga haddar Alkur'ani da kuma kiyaye dokokin sunnar manzo S A W. Har halaye Sulaiman halaye ne da za ayi koyi da su Unknown to him Sulaiman irin mutanen ne da ake kira Sumamman kasau macijin boye domin bai abin shi inda ya San ana ganin shi da mutunci Samun aikin shi a Abuja ya kara fidda true color in shi shi kanshi MUSA sai a nan ya gane waye Sulaiman din. Shaye Shaye, Neman mata, gidan rawa sai da yayi kaurin suna a wuraren nan hakan har ya kai shi ga shiga hanyar Smuggling, Mata kala kala ba wacce Sulaiman bai yaudara ba daga na kirki zuwa yan iskan amma fa duk abin nan the moment da aka ce ya bar Abuja zai juye kaman ba shi ba.

Gun Abbah da Baffah ya fara zuwa kafin ya gabatar da kanshi wurin ta, Daman tun asali sun San shi da Deedat kuma sun Amince da tarbiyyar shi hakan ya sa suka amshe shi hannu bi biyu amma kafin nan sai da su ka sa aka musu bincike akan shi.

    A ranar da Abbah ya sanar da Zahrau anzo Neman izinin auren ta a wurin shi wuni ta yi tana kuka domin sai ranar ta kara tabbatar wa ta rasa Abdulrahman rashi na har abada. Da farko kasa sakin miki ta yi gabadaya amma ganin yanda ya ke nan da Family inta ya sa ta Dan sake mai. Hakurin shi game da addinin shi ya fara Jan ra'ayin ta akan shi. A hankali sabo ya fara shiga tsakanin su ta wannan daman yayi nasarar fara sa ma ta son shi ko da ziyaran da ya ke kawo mata inko yana Abuja har video call ya ke kiran ta tun bata sakin jikin ta har ta saba. Wa'azi sosai ya ke mata sannan shi mutum ne kwarai da ya iya tafiyar da mace ta yanda ba za ta kara kallon wani Namijin ba. Gashi da fara'a, raha da kuma saurin sabo ta haka ya siye yan gidan nasu gabadaya, lokacin da wani aiki ya kai shi kano sai da ya biya gidan Anty zee ba adadi Anty Rukayya kuwa ya sha kai mata ziyara, komai na Zahrau mai mahimmanci ne a wurin sa yanda ta fi duk matan da ya yi alaka da su mahimmancin.

***                      ***                     ***

  Bakin cikin MUSA a kullum bai wuce yanda Sulaiman ke sa mun cigaba a rayuwa ba musamman da ya ga yanda a ka amshi shi hannu bi biyu a gidan su Zahrau ya San cewa da sun San waye Sulaiman da ba su yi gigin bashi yar su ba.

   Deedat ya je ya samu a office ya sanar mishi duk abinda ake ciki sai dai ko kallon arziki Deedat in bai mishi ba ya mishi tattas sannan ya kore shi daga office in. Daman tun can kyamatar shi ya ke shi kanshi Musan ya San da hakan "Good banga laifin ka ba amma you are surely gonna regret this" tsaki yayi ya cigaba da aikin da ke gaban shi hakan ya matukar kara kular da Musa fita yayi yana kwafa.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top