KHF 22

Da yammaci Kowa na harkan gaban shi, kokarin daura girkin dare su ke a kitchen sai musun abinda za a dafa su ke wannan ta ce tuwo wata tace pasta kowa dai da ra'ayin shi. Khalipha na ya leko kitchen ya gan su "to kai kuma me ya kawo ka nan sarkin iyayi" Nanah ke magana tana hararan shi wai Dan yaji tsoro.

Cewa yayi "Sorry Anty Nanah ba gunki nazo ba" Da ke yaro ne mai wayau straight gun Maijidderh yaje ya jawo hannun ta yana fadin "Favorite Anty zo kije"
Ummiy ce ta harare shi "ji yaro da gulma za ka yi bayani" ita dai Zahrau faman gyara kayan miya take daman ba wai ta cika magana bane.

Har gaban Ibrahim ya ja hannun ta ya kai ta "Uncle IB gata toh"
"Thank you khalee boy ga chocolate ko"
"Thank you Uncle" rugawa yayi cikin gida yana murnar chocolate in da aka bashi.

Kallon sha'awa Ibrahim ya bi shi dashi har ya shiga parlour. "Haka kake son yara" Maijidderh ke tmby.
"Hauwa kenan ban ki inyi aure yau ba in zan samu cute babes"
"Yara ai akwai shiga rai amma lokaci ne"
"Haka ne gobe za Ku tafin"
"Ehmm za mu koma schl akwai shirye shiryen da zamu yi"
"Allah taimaka"
"Ameen"

"Maganan mu Allah ya sa zaki iya cika Alkawari"
"In sha Allah"
"Yauwa toh, Hauwa'u"
"Na'am" ta fada tana Dan Satan kallon shi.
"Zan so ki bani aron hankali da natsuwar ki kuma zan so ki ma abinda nazo da shi fahimta mai kyau."

Shiru tayi tana mamakin abinda ya ke nufi da har ya ke wadannan maganganun "Hauwa Allah ne ya kadarta min ba ni na daura wa kaina, ban kuma San ya zaki dauki zance na Amma still zan fada miki Ina sonki" saurin dagowa tayi tana kallon shi "Nayi karfin hali ko? Pls am sorry it just happen" Daman Ibrahim zai iya speaking fluent English haka? Kai anya bai da wani boyayyen sirri?

"Nagode" ta tsinci kanta da fada "Amma ni ban San me zance maka yanzu haka ba kawai dai nasan ina son taimakon ka"

"Na Sani, taimakon da kika min ne ya fara Jan ra'ayina gare ki at your young age kin burge ni, amma bara in tmby ki, ace ina da rufin asirin da zan iya ciyar da ke in kuma kula da ke zaki iya zama dani?"

"Me zai hana?" Ta fada kanta a kasa

"Zan tafi in nemo sana'ar da zan iya rike ki Hauwa za ki iya aure na"

Kai ta gyade mi shi hade da rufa fuska alamun kunya. "Alhamdulilah I S A bazan baki kunya ba, ki ban numban da zan same ki, zan neme ki in na gama settling"

Numban ta rubuta mishi sannan su kayi sallama, ba ta ce tana son shi ba Amman ya ga alaman hakan a tattare da ita, sai godiyan Allah ya gama mission a dai dai.

*** *** ***


April 2015
A ranar su ka gama jarabawar su ta WAEC bayan extension da yan makaranta su ka bar su suna yi, a washegari su ke sa ran tafiya gida Hutu duk da dai PC sai kokarin ja musu rai yake yi.
Da Yamma ya mu su announcing tafiya gidan tuni su ka hau ihun murna, ga Zahrau murnar ta biyu saboda Satin Abdulrahman biyu kenan a cikin Nigeria duk sun kosa su hadu, bayan magriba ta kira shi ta sanar mi shi dawo wan ta Zaria a washegari, yayi murna kwarai coz ya kosa ya sa ta a idanun, princess inshi ta canja? Though koya ta ke itan dai kawai ya ke so," jibi ni kuma in sha Allahu zan shigo Zaria" ya fada mata abinda ya sa ma ba zai zo a washegarin ba saboda ya bar ta ta huta.

A gajiye ta isa Zaria ta iske su Ummiy da Maijidderh har sun dawo nan fa su hau murnar ganin juna, Yan Uku kenan.

Da yammacin ranar su kayi Waya da jaanam din ta ya kara tabbatar mata da zuwan na shi a washegari. Da dokin murna ta yi hanyar dakin Deedat "Zahrau yan SS3 wannan farin ciki fa?"

"Ya Deedat Abdulrahman zai zo gobe" sai da ta fada tayi realizing me ta aika ta, Deedat bai San tsakanin su ba "Ya fada min, me ya faru?" Bbu tace sannan ta yi saurin barin dakin "okay in tayi tsami naji" ya fada da karfi ta yanda zai iya jin ta.

Da dare Abdulrahman ya kara kiran ta hakanan ta ji gaban ta ya fadi ba Dan komai ba sai Dan ganin sau daya su ke waya dashi a rana, saboda fahimtar da ya mata bata cika son magana bane? Ko Dan shi ma ba mai son maganan bane?.
Sun ko dade suna wayan, yana kara tabbatar da irin son da ya ke mata ita ma sai ta tsinci kanta da bayyana mishi sirrin zuciyan ta, duk ko kunyan ta yau ta kauda shi ko me ye sa hakan? Yanayin ne kawai ya zo mata a haka ta rasa dalili.

Haka da asuba shi ya tashe ta Sallah sannan karfe Taran safe su ka kara waya yace mata by 11 ya ke son barin KD. 11 din ya kira ta akan Baban shi ya sa shi wani aiki zai yi kokarin gama zuwa 2 ya taso bayan da ba ta yi ba akan ya bari sai gobe ya ki dalilin shi kuwa gani ya ke in bai sa ta a ido ba a ranar komai zai iya faruwa.

Kitchen su ka shiga ita da Yan uwanta su ka hada mai abinci na gani na fada duk Wanda ya tmby su sai su ce baki za su yi. Hamza daya dawo daga Unimaid yana 100 level kadai su ka fada ma gskyn abinda ke faruwa ai ko sun sha tsiya.

2:00 pm in ko ya taso da za su zo da Faroukh amma ya bar shi ya kara sa musu aikin, gudu ya ke sosai a hanya burin shi ya isa da wuri ya samu ishashen lokacin zama da Zahrau saboda bayan isha'i zai dawo KD.

Cikin mintuna kalilan ya isa jaji, wani irin kulle wa ya ji cikin shi nayi sauran kadan kan motan ya kubce mishi yayi saurin lallabawa ya koma gefe, kusan shekara kenan ya na fama da ciwon cikin nan duk ya taso ba karamin wahala ya ke. Gadan gadan ciwon ya taso mai rike wurin yayi yana mai kiran sunan Allah.

Jin shiru ya sa Zahrau ta kira numban shi kusan sau biyar amma bai daga ba, hankalin ta ne ya tashi da sauri ta lalubo numban Faroukh ta kira.
Bayan sun gaisa ne ta ke fada mishi ta kira Abdoulh bai dauka ba ce mata yayi bara shi ma ya neme shi yaji.

Kusan 2 hours ba kiran Abdoulh kuma ba na Faroukh gaban ta sai dukan Uku Uku ya ke.
A bangaren Abdulrahman kuwa ya kai kololuwa wurin galabaita tun yana iya magana har ya kasa. Ganin mota ya Dade a wurin ya sa mutane su ka yanke shawaran su duba su ga lfy. Suna bude motan su ka ganshi ya saki wani numfashi mai karfi sannan ya fado kasa, caa su kayi akan shi wani daga ciki ya taba shi ya ji ba ya numfashi, wayan shi su ka dauka su ka kira numban Faroukh da ya mai missed call last domin sanar da shi halin da ake ciki.

Mintuna Ashirin su kai Faroukh da Wani yayan su jaji a rude su ka sa shi a mota akan za su wuce dashi asibiti, dayawa daga cikin mutanen kyale su su kayi kawai amma sun San rai ya riga yayi halin sa.

Wannan karan Sumayya ta ke ta dialling don har ta gaji da kiran Abdulrahman da Faroukh dukkansu ba sa picking sai dai Sumayyan ba ta dauka ba, kara kiran dai tayi ganin shi ne dai mafita.
Sheshekar kukan Sumayya ne ya katse ma ta maganar da ke bakin ta. "Me ya faru" kawai ta tmby Dan ko jikin ta ya riga da ya ba ta abinda ke faruwa "Wai Ya Abdoulh ya rasu" wani irin karkarwa jikin ta ya fara yi, wayan da ke hannun ta sa kan shi ta yi a kasa kafin ita ma ta bi shi.

Sai Washegari a ka samu ta far fado already lokacin an Riga an kai Abdoulh gidan shi na gaskiya, gidan da ko ranar zuwan nashi ya ke jira Kulli nafsin za'ikatul maut, Abdoulh kam sai godiya domin yayi cikan shahada. gaba daya dakin ta bi da kallo ta tunanin me ya kawo ta asibiti, Deedat da ke gefen ta ta bi da kallo sannan abinda ya faru ya dawo ma ta "da gaske wai Abdulrahman ya rasu" ta tmby shi, gyada ma ta kai yayi kawai saboda bai ga amfanin boye ma ta abinda ta riga ta Sani ba. Gani ta ke karya kowa ke mata duka duka yaushe ya kira ta ma ace ya mutu kai ba zai yiwu ba, cikin yan awanni kalilan ace mata ya mutu ba ciwo ba komai ba kuma accident yayi ba.

Wani irin gigitancen kuka ta fara tana girgiza kan ta "wlh karya ne Dan Allah Ku ce min mafarki na ke" Mami ce ta kama ta tana rarrashin ta ga me da mata nasiha, abinda mamin ba ta Sani ba ko kadan ba ta jin ta karshe ma kara sumewan ta yi.

Da kyar likitoci su ka samu daidaituwan numfashin ta saboda shock in da ta shiga, sati biyu tana kwance a Asibiti ba ehmm ba Aa ganin ta fara warware wa Ya sa aka sallame ta ga me da daurata akan magunguna, ita dai bin su kawai ta ke Dan ji ta ke komai na duniya ya tsaya mata cak. Schl ma sai ana gobe za su fara jarabawa ta koma, sai dai komawan na ta Ma kaman taso mata da ciwon mutuwar shi yayi domin hatta kwanar ta duk sunan shi ne a jiki, yan mate insu sun tausaya ma ta sosai sanin irin soyayyan da ke tsakanin su. Jinya yau gobe sauki a haka su ka gama jarabawar da yawancin yi mata ake, haka su ka yi Grad ita dai gata nan a duniyan ne kawai ba Dan ta na fahimtan komai na ciki ba. Duk ta rame ta yi wani iri ko da su ka koma asibiti likitoci sun tabbatar da zuciyan ta na gab da buguwa saboda halin damuwan da ta kasa fita a ciki.

Sai dai Iyayen ta su ka zauna da ita musamman su ka mata nasiha mai ratsa jiki Deedat ma ya mata sannan ta fara kokarin dawo wa yanda take game da bata rabin ranar ta tana ma Abdulrahman addu'a Dan gani ta ke har karshen rayuwan ta ba za ta iya cire shi a ran ta ba.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top