KHF 21
Weekend ne na karshen month kuma karshen shekara, kaman yanda su saba duk karshen shekara su ke meeting a family house insu na Unguwar Alkali cikin garin Zaria. Yan uwansu kala kala na cikin Nigeria da wadanda su ke zama abroad ma gaba daya suna haduwa a cikin wannan rana.
Tun ranar Alhamis su ka tafi Zaria har Anty zee da ke kano ma a ranar ta iso uncle Aliy ne kadai bai zo a cewar sa aiki ne ba zai bar shi amma duk da hakan sai da Abbah ya ce mishi lallai lallai dole ne ya baro Abuja ko Saturday ne tunda ranar Sunday za a gabatar da taron. Hakan ba karamin dadi yayi ma mutanen shi a cewar su saci Karen su bbu babbaka.
Taro yayi taro in kaga mutane sai ka dauka gaba daya jama'an Zaria ne su ka taru a wurin. A nan ake sanin yan uwa yawancin musamman matayen da aka auro kafin lokacin taron nasu da sai mai tsawon rai ne zai gani. Bayan nasihohi da fadakarwa da aka yi da kuma tarihi kala kala tare da ma wadanda su ka rasu addu'a kusan na awawowi dayawa sannan aka yi addu'a. Lokaci ne na ganawa da ciye ciyen da ba irin abinci da za ka nema ka rasa a wurin.
"Kai amma wancan Brother inku ya hadu just my dream guy" Wata cousin insu Khadija ta fada tana pointing direction in da Aliyu ya ke, da yake mutane dayawa ya sa ba Wanda zai iya cewa shi ta ke nunawa. Kallon ta suka yi a tare dukkansu ukun sannan su ka juya kai "sai dai it seems like kaman bai magana gashi ni kuma am the noisy type ya za ayi kenan"
"To fah miss dream guy har kin fara hango Ku tare" Wata cousin in ta su ta fada cikin tsokana.
"In dai Yaya Aliyu ne kya yi ki gaji don ko kallo ba ki ishe shi ba I doubt in yana da budurwa, miskilancin shi yayi yawa" Nafisa ta yi magana da ke ita suna zumunci Sosai da gidan su Zahrau.
"Ehm ehm wlh An gaya miki miskilancin namiji na hana shi love ne? Bar su kawai inda kika bar su"
Ummiy da Maijidderh a tare su ka tashi "I don't belong here kunji bari in shiga ciki" Ummiy ta fada tana tafiya bin bayan ta Maijidderh ta yi
"Are you jealous Dan ana son yayanku" Khadeeja ta fada tana musu dariya.
Zahrau kam hankalin ta na ce wurin su Rukayya suna lbrn Novels daman inda tafi karfi kenan.
Ko da za su tafi da yamma hamza ne ya zo ya Kira ta su ka wuce.
*** *** ***
Manya makaranta, Senior of the seniors and the juniors kuma masu makarantar da kanta wato Yan SS3. Zaune su ke a hostel yayin da su ka tattara yan makarantar gaba daya su ka kora prep in ka cire kalilan da ke class domin ra'ayin Kansu sai kuma yan SS2 da su ka zame musu karfen kafa domin ba daman Koran su saboda Immediate bullying in da ba ayi a girl section.
Wanka ta fito daure da zani da dankwalin shi iri daya bayan ta gama shiryawa ne ta daukko dimbin notes in da ke gaban ta ko ta ragewa kanta aiki, hakanan ta ji ba ta son zuwa class din ai ko ta samu yan uwa zama hira dayawa duk dai SS3 ke fada musu karya, inda Allah ya taimake su ba malamin da ya zo kora ranar ba ko karamin sa'an hakan su ka ci ba. "Zahrau na Abdulrahman, Abdulrahman na Zahrau" Asma'u ta fada cike da tsokana. Ko kadan ba ta iya holding blush inta matukar an ambato sunan shi, tafiya ta ke taji ance Abdulrahman sai ta waiga ta ga waye ne ballan tana ta San da Abdoulh in nata ake. Har cikin zuciyan ta ta ke ji dadin sunan ko kadan farin cikin da ke kwance a fuskanta bai boye ba duk yanda ya so boyewan "oh ni Zahra wai wani irin So kike wa bawan Allahn nan, ko dai za a daura ne ranar da aka yi grad kawai ki tare" Asiya ta fada "Wlh ni ban ki hakan ba, just wait to fall in love you will know how it feels" ta fada tana lumshe ido. "Ehm ehm anya Zahra, fada min me ya ke fada miki? Wasu kalamai ne su ka ruda ki haka" wata ta kara tmby. Ita dai shiru ta yi tana jin su. Sunga laifin ta? Abdulrahman is the perfect definition in Husband material da duk wace mace za ta so, Tattali, kulawa, kyauta da kuma nunawa mace so ba Wanda bai iya ba kalan su ne in suka so yaudara za suyi saurin yin nasara.
Wayan da su kayi jiya dare ne ta tuno. "Mera princess" ya fada bayan sun gaisa. "Naam jaanam" ta amsa su a dole indiyawa. "Ina So in ganki Soon", " ba kun kusa graduation ba ina last year ka ke"
"Ehm Amma kinsan Allah ji na ke kaman in jawo lokaci Wlh yayi min nisa"
"No jaanam kar ka damu Zahrau will always be waiting for you, ko yaushe ka dawo ma am already yours"
"Shknn princess Allah da na dawo zan turo gidanku yanda da na samu aiki sai ayi ko? Ko ya kika gani"
Wani farin ciki ne taji ya mamaye zuciyan ta jin abinda ya ambata.
"Amma su Ummiy da Maijidderh ba Wanda ya shirya and tare mu ka taso"
"No princess don't start it Allah I can't risk loosing you gwara tun ina da chance"
"Are you doubting me?"
"No just ban taking chances ne, ki kwanta pls kar kije kina bacci a Class"
"Ehmm Gud nyt"
"Thank you, luv yhu"
"Bye" ta fada yayi saurin katse ta "tsaya ma naki wayon baki taba cewa kina so na ba"
"Kai Jaanam wannan ma ai sharri ne"
"Let's just balance the equation"
"Zahrauuuuuu INA son ki" ya fada hade da Jan sunan ta, INA aljanna a sa Zahra, ji take ta fi kowa Sa'a a duniya. "Kinji" ya kara fada a hankali da voice inshi da ke mugun affecting inta. "Naji"
"To baki ce komai, I love you"
"I love you too" ta fada hade da saurin katse wayan saboda da kunya. A daya bangaren Abdulrahman smiling yayi yana kallon wayan cike da farin ciki, kunyar ta na matukar burge shi. Fake yayi wa screen in wayan sannan ya rungume a kirjin shi. Faroukh da ke gefen shi ne ya kwashe da dariya "man bi a hankali electronic ke hannun ka ba Zahrau ba Mr lover boy" shi dai lumshe idon shi yayi yanda ta furta I love you too na kara sauka cikin kunnen shi.
Hutun nan ba su je Kaduna ba saboda Mami da Ammah sun yi kememe akan duk Hutu can su ke zuwa su ka hana su zuwa ba Wai dan sun so ba suka hakura Sai Nanah ce da su khalipha su ka zo Zaria hutun.
Maijidderh ko Ibrahim ne a ranta shi yasa duk tafi su haushin rashin zuwa Kadunan, ga abinda ya ce zai fada mata na taimakon da zata mishi kullum yana yawo a ranta, kasa jurewa tayi ta kira khalipha a sirrance tana tmbyn shi. Abinda ya sanar mata ya matukar kidimata. Yana nan amma yace yana son komawa garinsu nan da wata Uku, me ye sa zai bar aikin da ita a ganin ta da wuya ya samu aikin da za a biya shi irin shi ba saboda ba makaranta yayi ba, to wai ma meye sa ta damu da lamarin shi ne? Ta tambayi kan ta, taimako mana wani zuciyan ya bata amsa.
Sai ana sati daya su koma school ne Mami ta ce suje su musu kwana biyu, ba karamin farin ciki su ka yi ba ko Dan yanda su kayi missing Antyn nasu, sun saba da ita sosai Dan ko wani abu ya taso to da ita ake shawara.
Ita kanta tayi murnar ganin su dan tayi kewan su, bayan sun Dan huta ne ko abinci ba su ci ba Maijidderh ta faki idon su ta fita dan ba ta so su mata tsiya. Wurin mai gadi ta je ta tmby shi Ibrahim din "ya dan fita wlh amma INA ga ba nisa yayi ba, kina son wani abu ne" maigadin ya bukata. Girgiza kai tayi tace "Aa kawai INA son ma sa magana ne" tana cikin magana sai gashi yayi sallama ya shigo gidan "kinga gashi nan ma" Maigadin ya fada.
Kallon ta yayi sannan ya Dan saki murmushi "Hauwa ashe zaku zo naga har Hutu ya kare na dauko sai wani hutun ai". Shi ma yana kewan ta kenan? Wani sashe na zuciyan ta ya fada tayi saurin kauda zancen " Eh wlh ba mu samu zuwa bane, mun same Ku lfy?"
"Lfy Kalau, da ko ba za ki same ni ba"
"Khalipha ya ce min kace za ka bar aiki Why"
"Family na suna bukata na kinga ko dole in koma"
"Hakane amma kana da wani aiki a can ne?"
"Kala kala ma a can kauye ai ba a rasa abin yi"
"Hakane Allah ya taimaka"
Shiru su kayi yana kallon ta ita ma kallon na shi ta ke sai dai a sace, lura yayi da magana a bakin ta "fada mana" ya ce mata. Murmushi tayi tana mamakin yanda a kayi ya gano ta "daman so nake inji taimakon da kace kana so in maka ko ka fasa"
"Aa INA bukata ai, Yaushe zaku tafi"
"Jibi". " Zan neme ki gobe" ya fada hade da shiga dakin da yake mallakin shi a yanzu.
Cikin gida ta koma ta iske duk sun shirya cin abinci ita ake jira "Halan wurin mutuminki kika je koh" Anty Rukayya ta tmby bayan ta zauna.
"Naje mun gaisa ne" ta fada cike da kunya.
"Ni dai Maijidderh na sa ma wannan zumuncin alamar tambaya" Nanah ta fada cikin tsokana.
"Hauwa'un kauye ba" Ummiy ta fada
"Aa ba a mutunci balle Ibrahim ma bai da matsala gashi bai da hayaniya banji dadin barin aikin da zai yi ba" Anty Rukayya ta fada
"Daman Anty ai ba sa zama kila aure za su mishi tunda kika ga haka" Zahrau ta fada.
Wani harara Maijidderh ta bi ta dashi "wai Zahra kinga hararan da kika sha kuwa" Nanah ta fada
"Baki ga na kama baki na ba, Afuwan Maijidderh na tuba"
Dariya su ka kwashe da shi dukkansu ita dai Anty Rukayya girgiza kai tayi tace "Allah ya shiryeku"
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top