KHF 20

Yau Sati daya cib da wayan su na karshe da Abdulrahman, haka kawai ta ke ji ta kaguwa ya kira ta domin nuna mishi amincewar ta. Anya kuwa ya damu da ke yau har sati daya bai neme ki ba? Wata zuciyar ta kimtsa mata, Saurin yi mishi uzuri tayi. Ai da tana gida yana yawan kiranta kila Dan yaga tana school ne.

  A wunin ranar ko ya kira ta da dare, har ga ranta ta yi farin cikin kiran amma kuma sai tayi kokarin fuskewa ba ta nuna hakan ba. Bayan sun gama gaisawa ne ya tambaye ta "Toh princess na kira inji Hukuncin da kika yanke". Shiru ta yi domin ta na kunyan abinda zai fito bakin ta. Jin shirun na ta yayi yawa ya sa shi sake mata wani tambayan "Yadai? Kinyi shiru".

  " Ehmmmm " kame kame ta fara yi "Shknn na Amince"

  "Ehm banji ba" Ya tmby domin ji yake kaman kunnen shi karya ya ke shiyasa ya ke son ya kara tabbatar wa.

  "nace maka na amince"

   "Dan Allah princess da gaske kike? Pls kar kice min wasa ne" har muryar shi canja tayi tsaban farin cikin da ya tsinci kan shi

  "Da gaske na ke na Amince" ta kara maimaitawa.

    "Alhamdulilah Allah kai ne abin godiya, Princess ina zuwa" Ya katse wayan, murmushi ta yi sannan ta ajiye wayan a gefe domin jiran kiran nashi.

  Alwala Abdulrahman yayi sannan ya gabatar da Sallah raka'a biyu domin godewa Allah da ya sa burin shi cika.

  Kiran ta ya sake yi, sun dade suna waya ya na nuna mata farin cikin Amincewar ta da yayi hade da tabbatar da ba son wasa ya ke mata ba. Ita dai bin shi ta ke da ehm ko Aa saboda hakan sabon abu ne a wurin ta sannan ba ta San abinda za ta ce mishi ba, ranar har Faroukh da wani abokin Abdulrahman din sai da su ka Kira su ka nuna mata jin dadin su haka Sumayya ma tayi ta murna duk da Zahrau tana ganin kaman Yake Sumayyan kawai ke ma ta ba Wai dan hakan bai kona mata rai ba.

***                         ***                        ***

Duk da dai ba wani waya su ke ba shakuwa ta shiga tsakanin su sosai, A ganin Abdulrahman zai takura mata in har yana yawan kiran ta a schl kar ma yayi distracting inta hakan ya sa yayi limiting kiran nashi. Zuwa yanzu sosai ta ke jin Abdulrahman ya shiga ran ta saboda yanda yake nuna mata kulawa da So.

  A haka har aka yi hutun schl, kaman ko wani hutu Sati daya kawai su kayi a Zaria su kayi wa Kaduna diran mikiya.

  Zuwa yanzu mutumin Maijidderh wato Ibrahim ya zama dan gida, Maijidderhn ta cigaba da kula da Alamarin shi kaman farkon zuwan shi gidan, su kam yan gidan mamakin ta su ke gani ganin yanda ta ke nan nan da Alamuran shi amma godiya wannan da kyar ya ke mata ba Wai dan bai jin dadin abubuwan da take mishi sai dan naturally haka ya ke miskili, bashi dai da karanta jarida kullum da ear piece a kunne, kullum da yamma ya kan Dan fita inda su ma basu San ina bane.

  A kule Maijidderh ta fito daga cikin gida saboda da haushin da yan uwan na ta su ka ba ta, Recharge card ta ke son siya urgently amma duk sun ki yarda su rakata gashi su khalipha na islamiyya, zaune ta iske shi akan kujera sai dai wannan rubuce rubuce ya ke maimakon jaridan da su ka saba ganin yana karantawa.

"Sannu da hutawa" ta fada hade da kutsa kai waje

Bai amsan sannun da tayi mishi ba sai ma tambayan da ya jefo ma ta "ina za ki je da ranar nan? Ko ke ba ki jinshi?"

  Kallon mamaki ta bishi dashi domin ba ta saba jin yayi dogon magana haka ba inba sako zai fada ba shi ma yanayi kaman matse bakin shi ake yayi magana.

"Kati zan siyo a shago" ta amsa mishi

"Kawo in siyo miki"

"No ka barshi kaga Abu kake kar in katse ka"

"Karki damu kawo"

"Allah ka bar shi nima tafiyan na ke ji"

Wani irin kallo ya bita dashi da ya sa ta sadda kan ta kasa ba shiri "Hauwa" ya fada cikin wata irin sigan murya da ta ke ji har cikin jinin jikinta "ki kawo nace ko, ban cika son musu ba"

Saurin mika mishi ta yi tana fadin "Nagode" ko kallon ta bai yi ba ya tattara littatafan shi sannan ya fita.

   Tana tsaye a tsakar gidan har ya siyo katin ya dawo "Da kin shiga ciki ai sai na aika a kira ki" ya fada yana mika mata katin. "Ba komai Nagode Sosai" ta fada bayan ta amshi katin. Shi dai murmushi ya mata hade da mika mata sauran canjin ta da ke hannun shi "ka bar shi kawai" Kallon ta yayi cikin idanu sannan ya ce "ayi haka?"
  "Allah ka rike ba komai". " Tohm Nagode " ya fada a hankali sannan ya sa kudin cikin aljihu.
   Cikin gidan ta nufa haka kawai ya tsinci kan shi da bin ta da kallo yana murmushi "I think i got her" ya fada yanda shi kadai zai ji. Har za ta shiga kofan falo ko me ya zo kanshi sai yaji ya kira sunanta "Hauwa" ya fada da muryar shi da ke sa ta rasa natsuwar ta dan har cikin kwakwal war kanta muryar ke sauko sannan ya zaga ye jikin ta gaba daya. Juyowa tayi tana kallon shi kallon da ya bita dashi ya sa ta janye idonta "Abu na ke so na tmby ki" ya fada sannan ya sadda kanshi kasa kaman ba shi ya mata magana ba, tsintar kanta tayi da isa wajen ta kaman ita ke aiki a gidansu maimakon shi.
 

Dakalin da ke gefen shi ta yi ma kan ta matsugunni sannan ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta "Hauwa" ya kira ta, ta rasa dalilin da ya sa duk lokacin da ya kira ta sai ta ji wani Abu, ko dan shi kadai ke kiran ta da sunan bayan malaman ta na makaranta "Naam" ta amsa mai a hankali  "Shekarun ki nawa" ya bukata. Tayi mamakin dalilin da zai sa ya tambayi shekarunta amma hakan bai hana ta bashi amsa ba "am 16".
" aji fa"
"SS2"
"Great Allah ya taimaka, zan so tambayanki me ye sa kika taimake ni baki sanni ba" Shiru tayi don har ga Allah ba ta da reason in da ya sa ta taimake shi kawai taji tan son taimakon nashi ne. "Kinyi shiru"
"Ban Sani ba kawai naji ina son taimakon na ka ne"
"Haka kawai? To in na cutar da ke fa ko yan gidan nan"
"Ni saboda Allah nayi ai kuma ya ga zuciya ta"
"Haka ne kam, toh Allah ya biya ki saboda ni ban da abinda zan biya ki dashi, Amma ga wani taimakon za ki yi min?"
"Matukar bai fi karfi na ba"
"Ko kadan just ki min alkawarin za ki min"
"In sha Allah"
"Ina ga mu bar shi zu wani rana, ki Shiga gida kar su neme ki"
***                         ***                    ***   

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top