KHF 2

                      One week later

                  19th September, 2016

  Ba irin fadi tashin da Iyayen Sulaiman basu yi a fiddo shi ba amma a banza. Maganar Aliyu ce dai ta tabbata daya ce kaf fadin kasar nan ba mai iya fiddo shi.

  A bangaren Zahrau ko ikon Allah ne kadai ya kaita izuwa wannan lokacin, duk ta rame, abinci ma sai anyi dagaske ake samu ta ci kadan, in ko aka matsa mata dayawa da ta gama ci za ta amayo shi, Zazzabi ko dashi take kwana ta ke wuni har an daina irga ledan ruwan da a ka sa mata.

Ganin abin na ta bana Kare bane, anyi fadan har an gaji, ya sa aka koma yi mata wa'azin yarda da kaddara, ana binta da lallami kawai, ba Wanda bai ji da Zahrau kaf fadin gidan in aka cire mutum daya da shi gaba daya harkar su ne ma bai Shiga balle ya damu dasu, A fadar su Zahrau yar Amana ce a wurin su so dole taga gata.

                  20th September, 2016

                            Abuja

  Sulaiman ne zaune a dan dakin da aka ajiye shi. Duniya ta mishi zafi, bai taba tunanin irin haka zata taba faruwa dashi ba. Yayi dana Sanin rayuwar da ya tsabar wa kanshi wanda ya boye wa Yan'uwan shi da duk wani na kusa dashi, shi ya San da sa baki a kama shin da aka yi amma tun farko shi ya ja wa kanshi. A yanzu ya fi takaicin halin da ya sa iyayen shi da kuma Zahrau wanda ba wai an fada mishi bane amma ya San irin halin da za ta Shiga. Ya San irin Son da ta ke mishi shi ma kuma hakan ne domin kaf duniya ita kadai ce macen da ya taba wa soyayyar gaskiya. Ya San bai mata adalci ita da iyayen shi ba, he wish za a bashi dama yaje ya roki su gafara.

Yau gabadaya wani iri ya ke jin shi tunda ya tashi, Sati daya kenan banda ruwa ba abinda yake iya kai wa cikin shi. Kaman kullum Abinci da suka sa ba bashi da ko kallo bai ishe shi ba aka kawo mai, Yunwa yake ji kaman ya mutu da sauri ya jawo abinci ya fara kai bakin shi. Sai da ya cinye Abincin tas sannan yaji cikin shi ya fara wani irin mahaukacin murda, tun yana daurewa har ya kasa, wani irin kara ya Saki Wanda ya jawo hankalin police in da ke wurin. Da farko sun dauka iskanci ne amma ganin yanda ya ke ihun a gigice yana neman dauki ya sa suka kira Emergency aka tafi dashi asibiti.

  Ba karamin galabaita yayi ba kafin a karasa, da gudu aka wuce dashi A&E. Sama sama ya ke hango Leelah da Samira (Last yarinyar da ya yaudara)

  "Sulaiman kenan ka dauka ka ci bulus, ka gama shan abin sha ka yadda kwalba ko, to kayi kuskure dan baka San wacece Samira balle mutanen da take hulda da su, Leelah kuma Aminiya tace  muka hada baki domin ganin mun kawo karshen ka" Wani irin mahaukaciyar dariya ta sheke da

Leelahn ce ta kalle shi yana ta kokarin tashi ya zauna, ture shi tayi ya koma kwance "kwanta mana yanda poison in zai bi jikinka da kyau ka tafi kowa ma ya huta"

Bin su yake da ido kawai dan yawun bakin shi ma ya kafe balle ya iya magana.

"Da polices, da likitoci kai manyan kasan nan gaba daya ba ta inda bamu da hanyan samun abinda muke so akan ka, So Sman a huta lafiya sai munzo ko"  tare su ka fada suna daga mai kira sannan suka fita su ka bar dakin.

Sunan Allah Sulaiman ke kira jin wani abu dake tasowa a cikin nashi sai time in munafukan doctors in da aka hada baki su ka shigo, daga musu hannu yayi alamun kar su taba shi, Abu daya kawai yake ta fadi "Dan Allah Ku rokan min gafara wurin Iyaye na da Zahrau"

Wani irin Amai ya fara yana kiran Sunan Allah, Kafin kace kabo har yace ga garinku... Kulli Nafsin za'ikatul Maut daman kowa nashi ya ke jira.

Gawan shi ma da kyar aka bada, aka mai Sallah sannan aka kai shi gidan shi na gaskiya.

A gidan su Zahrau ko ba karamin tsinkewa su kayi da Al'amarin ba barin ma Deedat da yake aboki a wurin shi. Zahrau lokacin da labarin Mutuwan ya iske ta ba karamin kidima tayi sai ma ta nemi kukan ta rasa, lokacin ta yadda lallai kukan ma rahama ne. Ta rasa Abdulrahman sannan a karo na biyu ta kara rasa Sulaiman ita kan bata da Sa'an Soyayya a rayuwa. Ta bawa yan gidan nasu mamaki domin yanda suka yi zaton zata karbi labarin mutuwan Sulaiman ba haka tayi. Juriya tayi ba Kadan ba ta fawwala wa Allah komai, Ko yaushe cikin mishi addu'a ta ke dan wasu halayen nashi ma sai bayan rasuwan shi su ke ta fito, Kai jama'a Allah yasa mu dace kawai. Har sauka tayi a matsayin sadaukarwa gareahi Allah ya kai ladan cikin kabarin shi. Tana dai kokarin Danne komai amma kai da ka ganta kasan tana cikin damuwa duk tayi baki ta rame abinka da farar mace. Allah ya sa mu dace kawai.

                  One  month later

Shirye Shiryen bikin Captain Aliyu ake wadan za ayi karshen shekara, ending December kenan. Sosai da Sosai ake shirya wa bikin Dan last bikin da aka yi a gidan shi ne na Anty Zainab Wanda yanzu haka take da ya'ya' Uku, Babban su na da shekara Tara.

  Farida Ibrahim Kabir diya ce ga Wani Babban Dan kasuwan da ake damawa dashi a harkar Siyasa na jahar Kaduna garin gwamna.

  Sun hadu ne da Aliyu a bikin wani Abokin shi, ita kuma kawar Amarya. Babanta Mutum ne Wanda bai yadda mu'amala ta hadashi da Talaka ba ko da wasa hakan ya sa tun wuri ya gargadi ya'ya'nshi a kan hakan.

Ko da Faridan ta zo mishi da labarin Sojan hannu biyu ya karba ganin cewa Matashin Saurayine Wanda kudi ke shigo mai ta kowani hanya amma ya so samun fin hakan. Sai dai ance wai da babu gara ba dadi.

Three Weeks to bikin kusan an gama komai sai jiran lokacin biki, anyi organising events kala kala daga both side na amarya da angon, haka anko ma kala kala an fiddo su.

Su Zahrau yan mata sai murna da rawan jiki ake, amma asali ba wai auren bane a gabansu, A'a barin gidan da zai yi gaba daya har Weekend ba zai dinga zuwa ba ke sasu farin ciki domin ganin shi kadai ba abin alkhairi bane a wurin su "Allah ya sa daidai dashi ce wacce zata gasa shi" Ummiy tana fada tana tabe baki, Maijidda ce ta katse zancen da cewa "ke a ganinki Ummiy akwai macen da zata iya gasa sojan nan, tabdi " "Haba Hauwa kulu Maijidda sai dai in Soyayyan bai kama shi ma wlh" Zahrau ke fadi hade da girgiza kai tana murmushi.

  Dukkansu shiru su kayi, tausayin yar'uwar su na ratsa su, sun San ko shakka babu tana tuno masoyanta da ta rasa ne. Nanah ce ta katse shirun "haba Ku ko yayanku ne fa amma kullum mugun fata kawai kuke mai, Allah ba kyau." Ummiy ce ta daga mata hannun cike da tsiwa "Wai ke Nanah Dan baki San waye wannan mutumin bane shiyasa ki ke kare mai kina ganin jiya fa dan muna murnar ganin Hamza yaushe rabon da a hadu ya fara zaginmu, mu dolayen ina ne, mahaukata, wawaye da baza mu taba girma ba, Fisabililahi kuma a gaban wannan Abokin na shi, yanzu fa ba da bane"
"Ni ko banga laifin Abokin ba, hana shi ma fa yake" Nanah ta fada tana murmushi
"Tabdi jam, Wlh na ciki na ciki asalima dariya yake mana in ana mana fada" Maijidda ke magana tana hararan Nanah
"Hmmm Ku barta, ni na ganota ai ba kuga yanda take acting a gaban shi bane" Zahrau ke tsokanarta. "Aa fa Zahra banda sharri" Nanah ta fada tana murmushin da daga gani kasan har zuciya ne.

  Yau aka shirya kai kayan lefe Kaduna gidan su farida. Anty Zainab, Anty Rukayya, Ammah da wasu yan'uwa ne suka tafi kadunan.

  An karbe su hannu bibiyu cikin mutunci da kamala. Sai dai me kamar yanda Al'ada ya gada su Anty Zainab ne suka mike domin fara bude akwatunan lefen. Kanwar Dad ce ta katse su da fadin "A'a ba sai kun bude ba ma, Baban  Faridan ma ya bada Sakon yana so an daga bikin don kawai shirye shiryen da ba a karasa ba.

Wai tashin hankali ba a sa mishi rana ba su Ammah kadai ba har mahaifiyar Farida sai da ta Shiga firgici. " Nace ba mu gane ba dai naga kaman abinda kike fada ba maganar mu bace" Anty Rukayya ce tayi karfin halin maganan.

"Ni dai yar sako ce" Matar ta fada hade da juya Kai.

Yan kawo lefen duka jikin su yayi sanyi, shakka babu sun San akwai makarkashiya a abin.

Mahaifiyar Farida ko in ranta yayi dubu ya baci, ba tun yau ba dangin mijinta ke mata irin abubuwan nan amma yau sun kai ta makura. Sun dauka kudi shine rayuwa shi yasa duk abinda Dan'uwan nasu ya fada to daidai ne. Bakaramin kunyata ta suka aka yi ba ko dan yan'uwan ta da suka zo amsan lefen kuma  tabbacin ya San ba za ta taba amincewa ba shiyasa bai yi shawara da ita ba, yanzu haka wani mai kudi ya samo.

"Ku tashi mu tafi ko" Ammah ta fada saboda ita ba ta ga amfanin zaman ba.

"To sai anjiman Ku, mun kuma gode da irin wannan karrama war" Anty Zainab ta fada cikin habaici

Hararta Ammah ta yi sannan ta mata Alaman ta zo ta wuce.

"Ai daman kun da akwatinan kawai" wannan karan ma matar ce ta kara maganan.

Tsabagen kunya mahaifiyar faridan kasa magana tayi, kuma abin haushin wa'inda su ka girmeta na wurin amma ko a jikinsu.

"Haba ke ko, auren yarki fa suka zo nema ai da mutunci" Daya daga cikin dangin Maman ta fada a hasale

"Ai daya ke su  ma ba zasu rasa Namiji kuma kayi ayi maka ne abin" Anty Rukayya ce ke magna an cikin zafi. Sannan Anty Zainab ta kara da cewa "kuma mata nawa ne a gari"

Abin dai fada koma musu sai da mahaifiyar faridan da dangin ta suka basu hakuri sannan fa Ammah ta sa su suka kwaso akwatunan su ka wuce.

To fah...

Mu je Zuwa...

Juma'at kareem

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top