KHF 17

Wayar Zahra da ke gefen ta ne ya hau ruri, tana kallon call har ya tsinke wani ya kara shigowa still bata dauka ba har ya tsinke.

"Ba dai kyau wulakanci" Nanah ta fada tana kallon ta.

"Kinsan Allah ba wulakanci bane kawai dai maganin kar ayi kar a fara" Zahraun ta bata amsa.

Ummiy ce ta tanka "wlh Zahrau ban San me ya sa kike wa Abdulrahman haka ba bawan Allah tun muna Nursery fa yake ji dake"

"Sumayya na son shi Ummiy, shi kuma naga take taken shi ya kira ni jiya da dare mun gaisa fa to gsky ni yau bansan me yake son in mishi ba"

"Ke kuma ke kika mishi kawai ta hakura" Nanah ta fadi

"Wai rufa min asiri" Zahrau ta fada tana rufe baki "ba ki San kishin Sumayya ba"

"Ke dai wlh anyi matsoraciya " Ummiy ta kara fada

"Hmm ke ni ta karatu na ma nake duka duka SS2 fa zamu shiga"

"Ba sai kiyi candy marriage ba" Maijidderh da tun ta su ke maganan ba ta tanka ba sai yanzu ta fada.

Tsaki Zahrau ta ja hade da barin wurin.

Zaune su ke suna jiran babban Yaya ya dawo, yau za su koma Zaria saboda Hutu yazo karshe. Hira suke tayi ana raha amma banda Maijidderh da hankalinta gabadaya bai wurin su. Ummiy ce ta dafa kafadanta "Hajiya Hauwa tunanin barin Saurayin ki kike ne?" Hararanta Maijidderh ta yi sannan ta daure fuska.

Dariya su ka kwashe dashi dukkan su

"Nima naga alaman haka ai" Nanah ta fada cikin tsokana.

"Anty kin gansu dai ko" Maijidderh ta fada was Anty Rukayya dake dan nesa dasu amma tana jin duk abinda su ke tattaunawa.

"Ehm ehm kun ga dai Ku kyaleta ko, Taimako kawai ta yi kuma lada zata samu don haka Ku dai Ku bari" Anty Rukayya ta gargade su

"To Anty ki ce mata mu dai ba za mu kai Amarya ba in dai kauye za a" Ummiy ta fada.

"Kaniyanki kauyen ba mutane bane"

"Shi fa So ba ruwan shi da wannan, Ku muka San wa zaku So koh Maijidderh" Zahra ta fada ita a dole za ta kare wa Maijidderh

"Ce miki nayi ina son shi"

Nan fah su ka hau mata dariya wai an gwale ta.

Anty Rukayya ce ta shigo ta sanar dasu dawowan Babban Yaya, fidda kayan su suka yi.

Kaman kullum yana zaune kan benci a gefe guda yana duba jarida, kallon shi Ummiy ta yi ta girgiza kai "wai wannan me ya ke yi da jarida tsakini da Allah"

Dariya su ka kara yi Maijidderh kam ko tanka su bata yi don tasan ita su ke wa tsiya.

***                           ***                    ***

A gajiya su dawo daga shopping in makaranta dukkan su washegari za su koma School, a falon Mami su ka yada zango. Yusrah ce ta shigo da wayan Zahra a hannun ta tana gudu "Anty Zahra wayanki na ringing" ta mika mata.

Abdulrahman ta gani akan Screen in wayan, girgiza kai tayi hade da fadin "ikon Allah" karfin halin daukan wayan tayi kar ya ga kaman tana mishi wulakanci.
"Hello" ta fada a dakile
"Zahrau kina lfy"
"Lafiya kalau"
"Madallah na shigo Zaria ne pls ina son ganin ki in ba matsala"
"Ganina kuma? A ina kenan " ta fada cike da mamakin request in shi
"Gidanku mana zan zo gun deedat, pls fa"
"Shikenan sai ka zo"
"Thank you" ya fada sannan yayi ending call.

Unguwar Alkali su kaje gaishe da yan uwa ba su samu dawo wa ba sai bayan la'asar.

Duba wayan ta Zahrau tayi taga Abdulrahman ya mata missed calls har 5, kwata kwata ta manta da yace mata zai zo gidan su. Call in Deedat ne ya shigo wayanta.
"Hello ya Deedat" ta fada cike da shagwaba
"Zahra na ina kika je ne, Abdulrahman ya ce min ke ya ke jira"
"Unguwan Alkali mu ka je amma mun dawo yanzu"
"To kiyi sauri ki zo he is on his way, ke ya ke jira"

  Veil ta yafa kan plain bakar doguwar da ke jikin ta ta nufi dakin Yaya Deedat in.

Sallama tayi a kofar dakin nashi sannan ta karasa ciki. Abdulrahman in kadai ta iske zaune kan single chair in da ke dakin yana danne dannen waya.

Yana ganin ta ya saki murmushi sannan ya ajiye wayan nashi a gefe. "Sannu da zuwa Zahra" ya fada cikin husky voice in shi da ya ratsa kunnen ta gaba daya.

"Kai ne da sannu kai da kazo daga wani gari"

"Allah ko? To ai ni na zama Dan gida"

Shiru kawai ta yi don ko bata da abin cewa. "Gobe za Ku koma school ko?"

"Eh" ta bashi amsa

"Okay, nima goben zan koma ke nazo wa sallama"

Dago kanta tayi cike da mamaki tana kallon shi, wani irin Kallo ya mata mai cike da ma'anoni dayawa daya sa ta saurin sadda kai kasa.

"Kina mamaki ne Zahra, ai kin wuce hakan a wurina"

"Kinyi shiru " ya fadi still dai bata tanka din ba "ko kunyata kike ji princess"

Bata San sanda ta Saki murmushi ba hakanan ta tsinci kanta da jin dadin sunan daya kiratan, abin mamaki ba yau ya fara kiranta da hakan ba. "Aa" ta ce mishi tana wasa da yan yatsunta.

"To dago kai ki kalle ni" haka kurum ta ji nauyin hada idon dashi take.

"To Zahra bara in tafi yamma nayi ban son driving in dare"

"Okay Nagode" a hankali ta fada kaman mai rada

"Ni ke da godiya sai na kira ki"

Bayan tafiyan shi Deedat ya tsare ta sai ta fada mishi me ke tsakanin su da Abdulrahman din, ce mishi tayi mutunci ne kawai tsakanin su.

  Da dare kawai sai ta tsinci kanta da expecting call din Abdulrahman din Amma shiru kake ji kaman an aiki bawa garinsu. Wani sashe na zuciyan ta ne yace mata anya Zahra inda Amana ruwa ya dafa kifi, wannan yarinyar fa amana da yarda ya sa ta kwashi sirrinta ta fada miki in kika mata haka anya kin mata adalci? Saurin girgiza kai tayi hade dayin au'uziyya.

Washegari da sasafe suka dau hanyar katsina, tun a bakin gate wurin biyan school fees ta hadu da Fatima ta dawo , sunyi murnar ganin juna sosai Sumayya kam sai bayan Azahar ta iso.

Daukin SS2 su ke tayi yanzu ba su da seniors in da za su dinga takura musu dake ba a immediate bullying a girl section.

Wanki su ke a rizaf ita da kawayen nata guda biyu, Sumayya na basu labarin wani saurayi da tayi Al-ameen koma wansu Hutu, har waya su ke dashi a schl yanzun. Zahrau ce ta katse ta "Wai Sumy lafiyanki Yaya Abdoulh in fa, ya za kiyi dashi?"

"Hmm Wlh Zahra sosai nake jin Ya Abdoul a raina, sai dai Allah ma ya gani I can't confess"

"Amma yanda kuke din nan ba kya ganin shi ma yana son ki" Fatima ta tmby

"Anya da kyar wlh, da fa na bashi lbr Al-ameen har shawara ya ke bani kinga ko ni ke haukana"

Ummi ce ta leko ta window din tana kwallawa Sumayya kira tazo ana Neman ta.

Kara ta buga tana "my Al-ameen ya kira ni"

"A nan zaki yi wayan ko, sai malama binta ta fito kija mana case gun malam Adams gobe a Assembly" Zahra ta fada

Fatima ta ce "wooh Zahra tsoro"

Maimakon yanda Sumayya ta yi tsammanin Al-ameen sai taji muryan Abdulrahman, sai farin cikin ma ya wuce na da tace "Allah sarki ya Abdoul yanzu mu ke lbrn ka da su Zahra"

"Lah Sumy gulma ko to me aka ce a kaina"

"Secret ne Yaya, ya schl"

Sun Dan Dade suna hira da kanwar ta shi kafin ya nemi ta ba Zahrau, da ke yasa tmbyn ta yasa bata kawo komai ba, cikin zumudi ma ta bata wayan.

Bayan sun gaisa ne ya nemi ya San secret in da Sumayya ta ce sunyi magana akan shi. Bata fada mishi ba duk nacin shi haka ya hakura, hira ya jata Wanda take amsa mai da ehm ko Aa ganin ta ki sakin jiki ya sa ya ce mata "shikenan princess gud nyt, ki kulan min da kanki pls" ba abinda ya fada bane ya tsaya mata a rai A'a yanda ya fadan ne ya mata dadi. Ita kam tana ga zata dena amsan wayan shi inba haka ba to tabbas zuciyan ta zai sa tayi betraying Sumayya, Wanda ko kadan bata fatan haka she can sacrifice everything for her love ones nd Sumayya is included.

Sumayyan ce ta nemi ta San me Yaya Abdoul ke ce mata su ka Dade a waya, ce mata tayi makaranta kawai ya ke tmbyrta. "Karfa Sumayya ta fara zargin wani Abu?" Ta fada a ranta dole ta yi yaki da zuciyar ta don ba shakka Abdulrahman ya fara samun wurin zama a wurin ta.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top