KHF 16

                   20th August, 2013

                            5:30 pm

Da  sauri da sauri su ke tafiya sanadiyar hazon da ya mamaye sararin samaniya, shakka bbu ruwa na daf da sauko. Anty Rukayya su kaje amsowa a sauko a nan cikin kinkinau sai dai da dan nisa amma duk da haka sun zabi tafiyan a kafa, a cewarsu ana tafiya ana hira hakan ya fi dadi.

Wani irin guguwa ne ya fara tashi, da ke unguwan akwai wadataccen yashi, kasa ne ke tashi kaman ruwan sama. Dukkansu durkusawa su kayi domin kare idon su.

Kofan wani gida da ke wurin kwanar layin da za a je gidan Anty Rukayya su ka tsaya kafin kuran ya raguwa. Sai dai me kuran na tsayawa aka tsuge da ruwa kaman da bakin kwarya, duk da dai sun fake amma ruwan mai hade da iska ne yana iso su. "Oh mu yau daman sai da Anty ta fada" Maijidderh ce ta yi magana cike da nadaman fitan da suka yi a kafa duk da antyn ta gargade su. "Saukin ta ba mu fito da wayoyin mu ba" Nanah ta fada. "Mtswww" a tare su ka ja tsaki su duka ukun suna hararanta. Ummiy ce ta ce "ke dai wlh ina ga ba abu mai mahimmanci a rayuwar kaman waya"
"Da mun zo da wayan ma ai da ko malam Ado ma kira" Zahrau ta fada.

Sun dan jima a fake ganin ruwan ya dan tsagaita amma bai da alaman daukewa gaba daya ya sa su ka lallaba hakanan su ka karasa gida.

A bakin gate in gidan su ka hadu da wani saurayi ya fake a wurin sai faman rawan dari ya ke ga numfashin shi na neman seizing.
Sanye ya ke da 3 quarter ash colour, tsa tsaf ya ke amma kallo daya za ka mishi ka gane ya kwode dan har colour in ya fara fading, sai bakin riga mai guntu hannu ba laifi bai kai wandon kodewa ba. Kallo su ka bishi da shi kaman yanda ya bisu dashi.

"Ai da ka lallaba ka tafi malam dare nayi gashi kuma ruwan bai da alaman daukewa" Ummiy ta fada cike da rashin yadda.
"Ehm ehm Ummiy ki ka San nisan da yake dashi gashi unguwan nan ba a samun abin hawa da dadin rai, kuma daga ganin alama sanyin nan na mishi illa. Ina laifin ya shiga dakin IB in yaso ko shayi ya sha sai ya wuce din."
 
  Kallon hankali dayaUmmiy da Nanah su ka bi Maijidderh da shi sabanin Zahrau da ta shiga ciki ta bar su a wurin don tun ainihi itan mutum ce mai jin sanyi sosai.
"Malam bismillah koh" Maijidderh ta fada tana mishi murmushi. Ganin da gaske ta ke yasa su Ummiy su ka shiga gida su ka barta a wurin.

Dakin IB mai gadinsu ta kai shi bayan ta ma IB din bayani, Wurin Anty Rukayya ta kara zuwa ta mata bayani ita dai bata ce mata komai ba.
Ruwan zafi ta tafasa hade da kayan shayi ta kai mai. Gogon naka kuwa daga kai kawai yayi yana kallonta da kyar ya iya bude baki yace "nagode" da ke ita Dan Allah tayi ba Dan godiyan na shi ba ko kadan hakan bai bata mata rai ba.
"Bara inje ko akwai abinda kake bukata?" Ta tambaya tana nufan kofan dakin.
"Man zafi" kawai ya ce mata yayi shiru.

  Man zafin ta je ta dauko mai ta same shi yana sallah, jira tayi ya idar sannan ta bashi ya amsa wannan karan ko arzikin godiyan ba ta samu ba sai da zata fita yace mata "Zan tafi, ina zan samu chemist"
"Eh akwai ba nisa IB Dan Allah raka shi mana"
"Toh" Ya amsa hade da mikewa

Saurayin ne ya juyo ya kalleta a hankali yanda za ta iya ji yace "Sannu fah  nima sunana Ibrahim, kin taimakeni da pneumonia ya tashi" sai kace dole yanda yake maganan

"Allah ya kara lfy am Maijidderh"

"Nagode Hauwa'u" ya fada cike da murmushi sannan ya bi IB su ka bar gidan.

***********************************

  Zahrau da Maijidderh ne a kitchen suna faman hada lunch, na yau din special saboda guest da Anty Rukayya ta ce musu zata yi ga kuma Sumayya za ta zo wurin zahrau, hakan ya sa suka zage wurin hada abinci na musamman, cuisines kala kala. Basu farga ba kayan salad ba sai da su ka gama dafe dafe su hakan ya sa suka yanke shawaran fita su siyo.

Daga nesa ta hango shi a gefe guda ear piece a kunnen shi yana duba jarida mutumin da Maijidderh ta taimaka jiya ne Ibrahim. "Wancan kaman mutumin ki na jiya" Zahrau ta nuna ma Maijidderh suna isa wurin mai sai da kayan Salad in.
"Ai ko shine" ta amsa

Kayan salad in da suka rage a wurin kadan ne kuma duk sunyi wani iri "Sannu Malam Dan Allah nace ba wani ne sai wadannan" Maijidderh ta tmby

"Yanzu za a kawo min daga kasuwa ko za Ku dawo nan da mintuna Ashirin" Mai saida kayan ya fada

"Kash Wlh da dan nisa ne anya Maijidderh ma zamu fasa ba kawai" Zahrau ta fadi tana ya mutsa fuska saboda nisan wurin da take gani.

"In ba matsala to Ku bar kudin mana inyaso wancan ya kawo muku Ku biya shi" ya fada yana nuna Ibrahim "sai kuje dashi yanzu ya ga gidan"

"Baba to shi kuma aikin shi kenan?"
Maijidderh ta bukata

"Allah sarki yarinya shi hanyan con abincin shi kenan, ya zo gari cirani bai San kowa ba da wannan yake Dan lallabawa kafin ya samu wani aiki mai dan karfi haka"

"Allah sarki" su ka fada a tare

Kiran shi tsohon yayi ya fada mishi aikin da zai musu, daga kai yayi ya kalle su sannan ya kalli tsohon yace "shikenan Babah na San gidan zan kai musu" gurin da yake zaune ya koma ko kara kallon su bai yi ba.

Ko da suka koma gidan har Sumayya ta iso. Da gudu su kayi hugging juna da Zahrau suna murnar ganin juna.
"Yaya Abdoulh yace in gaisheki shi ya sauke ni" Zahrau dai murmushi kawai ta Mata.

Tare su ka ciga da aikin suna hiran schl, har Ibrahim ya kawo Salad in, Dari biyar Maijidderh ta bashi wai ya dauka duka, godiya ya mata ya wuce abin shi don da alamu yana needing kudin.

Anty Rukayya ta sa su kai ma bakin nata abincin, was zasu gani? Uncle Aliy da abokan nashi wato Umar da Salim.

Bakin ciki kaman ya kashe Zahrau da Maijidderh haka su ka cije su kayi sallama "INA wuninku" su ka fada a tare. As usual su biyun ne suka amsa banda Aliyu.

  "Bismillah sauko ko kai ke ta babatun yunwa" Umar ya fada yana taba Aliyu.

Hararan shi yayi sannan yace "na maka kama da Wanda zai iya cin abincin kazaman yarannan? Ku dai da zaku iya Ku min sauri Farida na jira na"

"Eh lallai Aliyu kai mai budurwa wato ta maka girki ba za kaci na kannen ka ba ko?" Saleem ya fada cike da tsokana.

Su dai suna gama abinda ya kawo su su ka bar wurin su kaje suna ba Ummiy lbr takaicin wahalan da suka sha Ashe kan shi ne sunyi Allah ya isa ba adadi ita ko Ummiy har Sujjada tayi ta godewa Allah da bata sa hannu a girkin ba.

Suna falon su ka zo wa Anty Rukayya Sallama sannan suka wuce, ni ma nace Allah ya raka taki gona.

  Da Yamma Abdulrahman ya zo daukan Sumayya, dukkansu su ka je rakata hadda ya'ya'n Anty Rukayya.

Duk a tare su ka gaishe ya amsa sannan yace "Aa Sumy haka kika yi jama'a ne?" Murmushi kawai su ka yi dukkansu tace "yaya Abdoulh kasan daman ni mai jama'an ne"
"Naga alama kam, Zahrau ba kirki ko? Ko Neman mutane ba kya yi"

Faking murmushi tayi tace "no ba haka bane"

Yace "to menene? I need ur number"
Wayan shi ya mika mata.

Ba musu ta amsa ganin yanda Sumayyan ke smiling ya sa ta rubuta mishi numban.

"Thank you" ya fada sannan su ka wuce.

  Anty Rukayya ce ta zo ta same su a falo suna hira ta musu complain akan malam Ado zai bar aiki nan da 2 weeks wai zai koma garin su. "To wa zai dinga kai su khalipha schl Anty" Ummiy ta tmby.

"Gashi kuma babban Yaya bai so kina driving" Zahrau ta kara

"Akwai wani sai dai bansan ko ya iya driving ba" Maijidderh ta yi saurin fada.

"Ina kika San shi Maijidderh" a tare duk su ka tmby

"Wanda na taimaka rannan"

  Anty Rukayya ta so hana Maijidderh yi ma Ibrahim magana amma ganin yanda ta dage ta na son taimakon shi ya sa ta barshi.

Ko da taje ta same shi bai mata boye boye ba yace mata shi bai iya driving ba amma Sam Maijidderh ta dage wai Malam Ado sai ya koya mishi kafin ya tafi.

Ba musu Ibrahim ya yadda saboda shi ma yana son aikin, a haka suka fara fita koyan tuki da Malam Ado kullum maijidderh sai ta ajiye mishi abinci hakan ya sa suka dan saba saboda shi ba mai son magana bane.

A cikin 2 weeks hannun shi ya dan fada saboda daman ba lokacin ya fara koyan mota ba a yanda ya fada kenan.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top