KHF 14


  A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Su Zahrau har sun kai JSS3 suna extension in JSSCE, Kowaccen su yanzu jin dadin makarantar da take take yi sosai, anyi kawaye kala kala.

In ka gansu yanzu za ka sha mamaki in aka ce maka sune su kayi abubuwan da, yanzu kam basu da abinda su ka sa a gaba sama da Karatu, sosai su ke yin shi.

Duk Hutu ko tabbas sai sunje Kaduna wurin Anty Rukayya, sun saba da ita sosai ita ma ko tana ji dasu, ita ce uwar dakin su duk wani shawara da ita ake yi, Nanah ma kawance su yayi karfi sosai don ko basu je Kaduna ba zata je wurin su a Zaria.

Visiting ko raba shi ake yi kowa da Wanda zai je, Ummiy ce ma ta dan fi su morewa coz on weekend sometimes Anty Zee na zuwa ta duba ta.

***

Kwance ta ke akan gado da daurin gaba domin ta yi shirin wanka ne sai ta kwanta tana karanta wani Novel mai suna SON KOWA, Sosai ta ke jin dadin littafin hakan ya sa ta shagala da yin wankan.

Sumayya ce ta shigo kwanan da kulan Abinci da ta amso musu a dinning tana fadin "Zahra yanzu nayi waya gida su Yaya Abdoul sun dawo, sun ma ce zasu zo min visiting"

"Oh I will finally get to meet them" Zahrau ta fada tasan halin Sumayya in bata tanka ba ba zata barta ta cigaba da karatun ta ba.

  Dariya Sumayyan tayi, Yayyinta biyu ne da ke karatu a India suka dawo Hutu, sai dai dayan Cousin inta ne, suna shan labarin su kala kala gurin kanwar ta su, da alamun dai suna shiri Sosai.

Fatima ce tazo ta tadda su a kwannan, kallon Zahrau ta yi "wankan kenan, toh Albishirinka ruwa ya kare har an shiga rizaf"

Saurin ajiye littafin tayi tana fadin "bari mana, mu kadai a makarantar ma sai anyi rashin ruwa"

"Kar ki manta yan SS3 na nan, kince Sa'a naje naga ruwan ya na daf da karewa na ari bucket gurin Ummi na debo miki" Fatiman ta bata amsa

Ajiyar zuciya ta yi tana fadin "Amma gaskiya kin taimakeni, bari inje inyi wankan Ku jira in dawo sai mu ci Abincin" Soso da soap case ta dauka sannan ta nufi bayin.

***

Yau ne ranar Visiting insu, Ammah, Yaya deedat da Yusrah ne suka zo mata, taji dadi sosai musamman ganin Ya deedat domin yana ji da ita.

Sai karfe uku su ka tafi, kaman ko wani visiting sai da ta raka su har wurin inda malamai ke taru a kasan wani bishiya sannan ta juya.

Hostel ta koma, la'asar aka kira hakan ya sa ta fita Small tap dauro alwala domin ya fi kusa da hostel insu.

Tana shirin kabbara Sallah Sumayya ta shigo tana kwalla mata kira "Zahrau su Yaya Abdoul sun iso" haka kurum ta ji gabanta ya fadi, saurin kabbara Sallah tayi.

Ta so kin zuwa amma ganin yanda musamman Sumayyan ta jira ta ta idar duk yanda ta ke zumudin ganin yayyin nata ya sa ta hakura ta bita.

Zaune su ke akan fararen kujeru da aka tanada domin visiting in, itan kan tana nufu su taji bugun gabanta ya karu ta rasa dalilin hakan.

Sallama ta musu sannan ta gaishe su sabanin Sumayya da ta fada jikin su tana musu oyoyo.

Su Uku ne a zaunen " ga kawata Zahrau" Sumayyan ta fada tana nuna ta.

Dukkan su murmushi su ka mata, daya daga cikin su ta ke ganin kaman ta San shi, shi ma kallon sanin ko yake ma ta. "Kaman na sanki" ya fada

"Zaria kike koh? Kinyi Therbow School?" Ya tambaya, Kai ta gyade mishi alamun eh.

"Baki ganeni ba koh princess? Kina primary one mu kayi relocating Kaduna, you used to be my little sister back then"

Sarai ta gane shi, ya ma za ayi ta manta Abdoul dinta Wanda idan Uncle Aliy ya basu assignment ya ke koya mata, amma ganin irin kallon da Sumayya ke mata ya sa tayi kaman ba ta gane ba, Sarai tasan halin Sumayya mutum ce mai kishin tsiya ballantana ta San yanda su ke da Abdoul din, farouk ne blood brother inta amma sun fi shiri da Abdoul, ta dade da sa wa relationship in question mark shiyasa gudun kar Sumayyan ta zargi wani abu tayi pretending ba ta gane shi ba.

Tun daga wannan visiting in Abdulrahman ke yawan kira wayan Ummi kawar su da sunan za su gaisa da Sumayya, zasu dade suna waya da Sumayya sannan yace ta bawa Zahrau su gaisa, ba wani hira ta ke tsayawa suyi ba zata ba Sumayya wayan saboda kar ta zargi wani abun.

Ranar hutu Abdou in ne ya zo daukan Sumayya, ganin ba a zo daukan ta ba yace ta zo su sauke ta, ta yi mamakin rashin zuwa daukan ta da wurin da aka yi domin ko irin haka bai taba faruwa hakan bai sa ta bisu ba saboda gudun sabani.

Fatima anzo daukan ta daga kano amma Zahrau shiru kake ji, har ta yanke shawaran kiran waya domin hakan bai taba faruwa ba.

Admin ta nufa gun wani teachern su zata shiga office in kenan ta hango Uncle Aliy da abokin sa Saleem. Gabanka ta ne ya yanke ya fadi don har ga Allah ta manta when last ta ganshi da sunji zai zo zasu tattara su tafi Kaduna.

Karfin halin karasa wa wurin su tayi "kaga gata nan ma kana ta mitan yanda za ayi muganta" Saleem  ya fada

Gaishe su tayi Saleem kadai ya amsa gogan naka kuwa ko a jikin shi, wurin form master ajin su suka nufa ta amshi news letter da ke extension tayi ba result, sai da suka jira Saleem ya ga gaisa da malaman su da ke shi ma school in ya gama sannan su ka tafi.

Ita kadai ke zaune a baya abinta ta kulla wannan ta saka wancan, ta saba duk tafiyan da za tayi sai tayi ciciye kala kala amma banda na yau da ruwa ma Saleem in ne ya bata amma Uncle Aliy ko a jikin shi sai danne danne waya kawai yake yi.

Ko da suka isa Zaria ta iske har an dauko Ummiy daga makaranta, Maijidda kam ta na Kaduna akan Babban Yaya zai zo Zarian washegari sai ya taho da ita.

  Banda harara ba abinda ke shiga tsakanin su da Aliyu ko abu yake so sai dai ya aiki Shahida ko Hamza tsabagen kin da yake musu.

Su ko zaman su a inda yake ma ba so suke ba hakan ya sa suka yanke shawaran bin Babban Yaya Kaduna in ya zo washegari domin sun takuru da kallon banzan da ake musu kallon tsana da kyamata.

Yanke shawara su kayi akan maijidda ta yi zamanta in yaso sa tafi mata da kayan ta. Da kyar Abbah da Baffah su ka amince da zuwa kadunan nasu Mami ce ta sa musu baki sannan aka barsu.

Washegari da safe sun gama hada breakfast suna karyawa a falon Ammah, Aliyu da deedat su ka shiga falon.

Sanin ce wa ko sun gaishe shi ba amsa wa zai yi ba yasa suka gaida Deedat kawai, hakan ba karamin fusata Aliyu yayi ba.

Wani matsiyacin kallo ya bisu dashi sannan ya ce "Ku wasu irin kazamai ne? Ko mai masu aiki za su muku koh? Da kun gama breakfast Ku tabbata kun share ko ina na gidan nan"

Haka ya sa su a gaba sai da su kayi aikin da su ka manta rabon da suyi shi bayan ga masu aiki kiri kiri ya hana su yi, ai ko Babban Yaya na iso jikin su har rawa yake su ka kimtsa kayan su da zai tafi su ka bi shi.

Shi kanshi Aliyun sai da ya fuskanci shi su ke gudu amman ko a jikin shi hasalima shi ma din ba son ganin su yake ba.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top