KHF 13

Har anyi Common entrance tun tuni amma haka Baffah ya je ya nemi alfarmar a karbe su, ya ko taki sa'a domin duka makarantar sun amince suje suyi common entrance in a gani.

Hassan Gwarzo da ke kano aka nema wa Ummiy, Maijidda Islamic training center madallah a local government in Niger da ke gab da Abuja sai Zahrau Ulul Albab Science Secondary School Katsina.

Sunje sunyi common entrance, ba laifi dukkan su sun kai cutt off mark in da ake bukata, Wa'azin da Mami da Ammah su ka musu ne ya sa suka hakura su kayi jarrabawar da kyau amma da plan in su kiyi su kayi.

Da yake dab da bude schools su ka yi jarrabawar hakan ya sa su na koma wa aka fara musu shirye shiryen tafiya.

Tsab an gama musu shopping da komai da komai, washegari ko waccen su zata wuce. Daren ranar in ka gansu sai kace wasu marayu ma rasa gata jikin su duk yayi sanyi sun zama wasu abun tausayi sai kace basu da ke cika gidan da hayaniya don ko dukan su surutun ne dasu sai dai Ummiy ta fisu masifa ne, maijidda kuma ta fi kaifi wurin tsokanar fada Zahrau dai yawanci Tsoro ke Hana ta yin abubuwa don haka ta fi kaifi wurin surutun da kuma wasa.

Sun ci kuka kaman ba gobe a haka suka rabu suna karawa Aliyu Allah ya isa domin kuwa duk shi yaja musu wannan bala'in, Babban Yaya ne ya zo ya dauki Zahrau ya tafi da ita Abujan, Abbah ya kai Ummiy kano Baffah kuma ya tafi da Zahrau katsina.

Katsinan dikko dakin kara

Karfe daya dai dai na rana ya musu a kofar shiga katsina, a haka su ka shiga suna tafiya har su ka kai kan titin da zai kai su lungun da za a shiga makarantar, dai dai wurin wani gini mai kaman torch light da yan makarantar su ka ma lakani da faduwar gaba dalili kuwa da ka fara hango abun kasan ka iso schl din.

Iskar tayar su ce ta sace a wurin hakan ya sa drivern parking a gefen hanya yana Neman inda zai samu mai sa iskan. Zahrau naji iskan garin yana ta busowa sai dai abin mamaki zafi ne ke busowa maimakon sanyi, "ashe da gaske ne da aka ce katsina akwai zafi sosai? Lallai tana da aiki" ta fada a ranta.

Mai sa iskan suka samu ya sa sannan suka cigaba da tafiya, wani lungun gidan mai su ka Shiga su ka sha kwana sannan ta hango makarantar wani irin faduwan gaba ne ya ziyarce ta "shikennan yanzu nan za ta yi ta rayuwa?" Ta tambayi kanta.

Suna parking Almajirai su ka karaso domin taya su kwasan kayan su zuwa wurin bakin gate in shiga makarantar inda ake biyan schl fees da tela sannan a rubuta suna.

Admin block suka nufa wani office, sabbin dalibai ne cike a wurin yawancin yan JSS1 da SS1 ne a wurin.

A nan aka bata Class da Admission no sannan aka bata mattress, Wata malama ce ta hada ta da wata Senior yar SS2 domin ta kai ta hostel in Yan JSS1.

Last corner ta kai ta wurin kanwar ta da ita tazo JSS1 din. "Lah Yaya Safiyya Kawa kika samo min" Yarinyar ta fada tana murnar ganin Zahrau

"Ehm sunan ta Fatima ita ma kinga kin samu bonkiey sai ta zauna a down ki, ko kinfi son Up" ta tambayi Zahrau

Saurin girgiza kai Zahrau tayi "Sunana Fatima Yusuf Danbatta ke fa" ta fada tana mika mata hannu su yi musabaha.

"Fatima Al-ameen Turaki Amma ana ce min Zahrau" itama ta fada bayan ta mika mata hannu sun yi musabahan.

"Friends?" Fatima ta tambayan

"Friends" ita ma ta fada tana mata murmushi.

"Kije kiyi sallama da babanki sai ki dawo ko" Yaya Safiyyan ta fada ma Zahrau.

Can bakin gate in ta koma inda Baffah ke jiranta dake ba a barin maza su shiga girl section in in ba malamai ba

Wa'azi Baffahn ya fara mata akan ta maida hankali tayi karatu banda kawayen banza, wasu irin zafafan hawaye taji ya fara bin kumatun ta, lallashin ta Baffah ya fara yi yana share mata hawayen.

Sheshekar Kukan wata Yarinya da ta kankame babanta ne ya katse su, Baban ne ya karaso wurin Baffah su ka gaisa sannan yace "Yar ta ka ma JSS1 take?" Baffah ya amsa mai da Eh.

Jawo yar tashi yayi yana fadin "to Sumayya tashi kinga ga Kawa ma na miki"

Cikin sheshekar kukan nata ta dago ta kalli Zahrau sai kuma ta saki murmushi, Zahrau inma murmushi ta mata.

Nan dai Baffah da Baban Sumayya su ka musu nasiha sannan suka musu sallama suka wuce, kuka kam da ga ita har Sumayya sai da su ka yi shi sabanin Fatima da ko a jikinta ko dan taga akwai yayarta a schl dinne.

JSS1 Aisha aka ba Zahran ita da Sumayya, Fatima kuma Khadija. Komai banbarakwai ya zamar ma Zahrau kwanan kan bonk, zuwa dinning, bin Layin toilet da sauransu Dan ma Yaya Safiyya da kawayenta na taimaka musu.

Ba ta manta daren ranar da ta zo makarantar ganin sauro ya sa ta fiddo sabon Net inta Fatima ta taya ta suka daura jikin bonk in, a ciki ta kwana da safe ko da ta tashi fuskanta kaman garwashi haka take jin shi dalili kuwa net in sabo ne sai an wanke an shanya.

Da kyar ta gabatar da sallan Asuban, Ruwa ta debo a cup da handkerchief inta, tana sawa cikin ruwan sannan ta goga a fuskan ta unknown to her ruwan kara wa fuskan radadi yake, ta sha wuya ranar.

Da ke itan mutum ce mai saurin sabo ta saba da mutane dayawa ga ta kuma akwai son labari hakan ya karasa wa ta zama mai jama'a ko da yanayin shirin da suke da ita though Fatima da Sumayya daban ne tafi shakuwa dasu hakan ya rage mata kewan gida sosai.

A bangaren karatu kuwa sosai ta mai da hankalin ta musamman ganin kawayen nata masu hazaka ne, gaskiya schl in akwai karatu sosai ga kuma competition da ke both boys and girls ake hadawa a fidda result.

Kasancewar ta mai tsoro ya sa take taka tsan tsan da seniors, ko aike aka bata salin alin za tayi hakan yasa ba ta shiga case insu.

A hankali ta fara sabawa da rayuwan makarantar da duk wani schedules insu, sai karfe goma na dare ake tashi daga Qur'an class Wanda shi ne last activity in rana sannan kuma tun six na safe za a tashi morning prep, wurin karatu kam suna sha sosai.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top