KHF 12

Kaman da wasa dai gashi su kansu jin dadin ilimin su ke ganin su ma sun fara komawa kaman Nanah sun fara sanin abubuwa, yanzu ba za suji kunya ba in an musu turanci za su iya gane though maidawan tukun dai.

Sosai da sosai su ka sa karatun A gaba sai gashi Ummiyn da ke tunzura su duk ta fisu saurin dauka, tabbas ba ayi karya da aka ce mutum ma ra ji akwai kokari. Yanzu kam Uncle Aliy sai dai ya ma wasu gori ba dai su bah haka suke fadan ma Anty Rukayya ita dai dariya kawai ta ke ta ce musu "shi ma daman ai hakan ya ke so su zama" fir su ka musu don su a ganin su so yake kawai ya ga ya musu tambaya sun kasa ya musu mugunta.

Sun shaku sosai da Nanah da Anty Rukayya har ma khalipha ba karamin saba wa yayi dasu ba, su kan basu ki su dawo Kaduna gaba daya da zama ba don ba karamin dadin hutun su kayi ba.

Some times su kan fita suga gari a biya wurare kala kala ayi shopping sannan cikin unguwa ma suna zuwa masallacin sheikh Ahmad Al-karqawi kallon musabaka da kuma wa'azi hakan ya kara Jan ra'ayin su ga ilimin Addini sosai musamman ganin yanda kananan yara kaman su ke karatun Qur'ani da murya mai sauti ga kuma tajweed abin dai zan ban sha'awa.

Ko da Hutu ya kare Ya Babba ya zo mai dasu da kuka suka rabu da Nanah, Anty Rukayya kanta sai da tayi kewan su balle kuma khalipha da suka shagwaba kaman me, Alkawarin zuwa Kaduna ko wani Hutu suka dauka kaman dai za a barsu.

**********************************

Kwanan su biyu da komawa Zaria Zahrau ta tashi da matsanancin zazzabi sai rawan dari take.

Bayan ta samu ta ci abinci ta sha magani. Su na zaune a falon mami suna kallo gaba dayansu har da hamza da shahida. Amai ta ji tana ji gadan gadan da sauri ta yi yunkurin tashi sai dai me? A bakin kofan falon jiri ya debe ta ta zube a wurin, da sauri su ka nufi kanta, ta yi kokarin tsaida Aman amma hakan bai yiwu ba a wurin ta yi shi gaba daya.

Ummiy ce ta tallafa mata su ka tafi toilet, Hamza maijidda kuma su ka yi yunkurin gyara wurin.

Dai dai lokacin Aliyu ya nufi falon Mami cikin tafiyan shi ta kasaita, a kofan ya cire takalmin shi ya nufi ciki, bai yi aune ba ya jishi cikin Abu mai lami lami, Duba yayi ya ga amai duk ya bata mishi kafa.

Shahida da ke tsaya a wurin ba karamin tsorata da yanayin shi ta yi ba "wa yayi?" Kawai ya ce mata "Zahrau ce bata da..." Bai tsaya jin abinda zata karasa fada ba ya sa kai cikin falon.

Ita da Ummiy ya gani sun fito cikin toilet, bai tsaya wani tunani ba rai bace ya kwasheta da wani wawan mari ai ko a idon Mami da ta shigo corridor din.

Tsabagen rude wa Zahrau zube tayi a kasa ta ka sa motsi hannun ta na tallabe da wurin kukan ma ta kasa sai ma Ummiy ce idon ta ya ciko da hawaye.

Wani irin Kallo mami ta bishi da shi ta na fadin "sannu kaji yarinyar da bata da lafiya ne za ka ma wannan Marin, sa'arka ce? Ko kuma kashe ta kake so kayi?" Dago Zahrau n tayi fuskar ta har shatin hannuwan shi ya fito, idon nan ya kumbura yayi suntum, abinka da farar mace... Daman ya lafiyar kura.

Shi kam tsaya wa yayi ya kasa gaba balle baya har ga Allah zuciya ce ta debe shi ba wai da gan gan ba, maganar mami ce ta katse shi daga dana sanin da ya ke "ni wuce ka bar min bakin kofan daki, in ba so kake ka karasa min ya'ya' ba.

Maijidda da Ummiy da suka yi zuru suna shirin kuka ya wulla wa harara sannan ya shigo toilet ya wanko kafan shi. Ko kallon su bai kara yi ba ya fita ya bar side in gaba daya. Halin ko in kula da ya nuna ba karamin haushi ya ba wasu Ummiy ba dan gani suke duk cikin kiyayyan ne.

Marin da yayi mata ya taimaka wurin zafafa zazzabin Wanda har ya kai ta da kwanciya asibiti, akwai Mami ta sa shi a gaba dashi aka yi jinyan gaba daya, duk wani aike daga gida zuwa asibitin a kanshi ya kare gashi ba kusa bane. Saukin shi ma ta boye wa su Abbah abinda ya faru ko da suka tambaya me ya sami fuskanta kawai cewa tayi ta bige ne.

Satin ta daya sannan aka sallamota, ta warke garas sai da har yanzu akwai tabon hannun shi a fuskanta Dan ma wani cream aka bata tana shafawa.

***********************************

Lesson Gadan gadan Baffah ya sa Aliyu ya dinga musu, musamman suka zauna su kayi meeting akan ko sun iya kar su bashi amsa saboda kiyayyar daya ke musu.

Ai ko sun hada kai Dan taurin kai sosai suka nuna mishi, yayi dukan, punishment in amma duk a banza shi kanshi ba karamin wahala yayi ba akan hakan.

Sosai Ranar ya tsaya yana musu explaining, yanda su ka dage suna kallonshi ya sa yayi tunanin suna ganewa amma me? Duk cikin su ba wacce ta amsa mishi question daya.

Ba karamin harzuka yayi, ba kallan punishment in da bai basu ba a ranar suna yi suna kuka amma ko kallo basu ishe shi ba, wani abinda ya ke matukar bata mishi rai duk wuyan da zasu sha basu taba bashi hakuri.

Mami ce taji shiru ta fita domin ta duba su, samun su tayi duk sun jigata suna ta haki ba hawaye sai ambaliya yake, kasa cewa komai tayi ta tsaya tana kallon shi, kara hade fuska tayi yana hararan su. "Ehm dole ka daure fuska, wannan wani irin zalunci ne? An fada su ma makarantar sojojin suke ne, yaran ma duka duka nawa suke?" Shiru yayi dan ya San bai da abin cewa.

Tattara su tayi suka tafi tana fadin "daga yau ma na kashe lesson in inga karshen zalunci"

Washegari da sassafe yayi Sallama falon Baffah, da fara'a ya tarbe shi yana fadin "maraba da Sojanmu mazan fama"

Sai da ya gaida Baffahn sannan ya fara sanar dashi abinda ya kawo shi. "Baffah daman batun yaran nan ne, Allah ya gani nayi iya kokari na amma ba su dauka kuma in na basu punishment mami tayi ta fada"

Girgiza kai Abbahn yayi yana jimamin irin hali nasu Zahrau, sannan ya ce "Shikenan Aliyu hakan ma mun gode zan San yanda zan bullo wa lamarin"

"Baffah ni kam ga shawara, me zai hana a kai su boarding school amma daban daban" ya fada yana Sosa kai

"Shawaranka abun dubawa ne Aliy, zanyi magana da Abbah "

Abbahn ma daya ji shawaran yayi Na'am dashi sai dai Ammah da Mami ne suka so su hana, convincing in su suka yi da alkawarin cire su in suka yi first term basu canja ba.

A bangaren little angels kuwa abin ba karamin kidima su yayi ba sai dai ko shakka babu sun San aikin Uncle Aliy ne domin ko gar da gar ya fada  musu.

Allah ya is a ko kwando kwando  ya sha.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top