KHF 10

                       3 Years Later

                      December, 2008

Zaune ya ke a filin da ke tsakar gidan su yana shan shayi kasantuwar lokaci ne na hunturu, Su uku ne da Umar da wani abokin shi Salim, Tare su ke karatu a NDA Kaduna.

"Oh Aliy wai ina little angels ne, tun da muka dawo ban gansu ba" Umar ya tambaya

"Mtswww" tsaki ya ja sannan yace "banda kai wa ke Neman sakarkarun yaran nan"

"That means shima sakaran ne kenan" Salim ya fada yana dariya.

  Dai dai nan ko Ummiy ta turo kofa ta shigo cikin gidan sun tashi daga islamiyya, simi simi ta gaishe su "INA yan'uwanki yau kuma" Umar ya tmby

  "Suna baya"

"Kun daina tafiya tare ne"

"Aa haushi su ka ban na taho na barsu" ta fada tana ya mutsa fuska ta na kuma kar kada jiki alamun fada

Dariya abin ya ba wa Salim "Kai Amma  ko baki kyauta" ya fada yana mata murmushi. "Ya sunanki" ya bukata

"Ummiy" ta bashi amsa tana cigaba da karkadan jikinta game da citson baki

"Real name fa" ya CE

To fah an zo wurin... Sororo tayi tana kallon shi, Umar ne ya cemata "Asalin sunan ki yake nufi"

"Ohh Amina" ta fada tana zaro idanu irin daman tun can shige mata yayi.

Daga Salim in har Umar sai da suka dara ganin draman nata.

"Ke jeki dakina ki dauko min system yana caji kuma sauran ki min shirme, na San halinku" Aliy ne ya fada yana hararan ta.

  Da sauri da sauri ta nufi dakin, sai da ta isa sannan abin da yace ta dauko ya fado mata, ita har ga Allah ba ta San abinda yace ta dauko ba amma ta fada gaban shi wannan abokan nashi masu iyayin tsiya su raina mata wayau.

Newspaper ta hango kan kujera, ta lura yana dan son karanta jarida da yamma kila shi yake nufi daman taji ana kiran shi wani suna da turanci ba mamaki wannan ne.

Da zumudin ta ta dauka ta isa wurin shi. Gashi ta fada tana mika mai, binta yayi da kallo sannan yace "miye wannan"

"Abinda kace na dauko ma"

Rike baki yayi yana kallon ta ya rasa abinda zai ce, Salim da Umar kam me zasu yi inba dariya ba

"Me nace ki dauko"

"Sy sy sy" ta kasa fada

"System?" Umar ya karasa mata

"Yauwa shi" ta fada

Galla mata harara Aliyu yayi "ajiye kije ki kama kunnen ki, zaki Sani"

Kaman daga sama sai ga Zahrau da Maijidda sun shigo suna haki.

"Yauwa kuma Ku zo nan" Aliy ya kwalla musu kira

Tuni jikin su ya dau rawa ganin Ummiy na punishment a gaban su.
"Ku fa ya sunayenku"

A tare su ka amsa "Maijidda, Zahrau"

"Nice name Hauwa'u da Fatima koh"

Daga mishi kai su kayi "amma dai ku kusan miye system ai" Umar ya fada yana musu murmushi

"Maijidda ja daki na ki dauko min system yana chaji" Aliyu ya katse su.

  Da sauri ita ma ta tafi dakin tana dube dube ko za taga abinda za a iya cewa system amma bata ga alama ba.

Can wani tunani ya fado mata Baffah ya taba aiken ta dauko wani Abu mai kama da sunan ta tambayi hamza yace mata maclean ne, da sauri tashiga toilet ta dauko mai close-up.

Wannan karan Salim da Umar tare suka kyal kyace da dariya hadda rike ciki.

Wani kallo ya bita dashi sannan yace "ajiye kiyi joining yar'uwar ki"

Kan Zharau ya koma "Sauran ke, je ki dauko min System ina a daki yana caji"

Itan ma jikin ta na kyarma ta nufi dakin, a hankali ta fara binciken ko ina na dakin amma ba ta ga abinda take nema, tunowan da tayi yace a caji ya sata murmushi, Dan tsale tayi tana fadin woo ni yau zan tsira a gun Uncle Aliy.

Jikin socket ta isa ta cire tana wani murmushin jin dadi.

Da karfin guiwa ta karasa ta mika mai. "Ya akayi kika dade" Umar ya tmby

"Ya Umar na tsaya nema ne da kyar ma nagani"

  Habawa wani dariya ya saki gami da ba Salim hannu su ka tafa suna rike ciki, har kasa suke kaiwa Dan mugunta.

Bangaren Aliyu ko rechargeable lantern in dake hannun ta ya amsa ya buga mata a kai. "Dalla wuce ki yi abinda kika ga sunayi.

Shahida ce ta fito dauke da Yusrah tana mata wasa " Zo nan shahida" Aliyu ya kwalla Mata kira

Karasa tayi sannan ta gaishe su, amsan Yusrah Salim yayi yana Fadin "cutie ya sunan babyn taki"

"Yusy" ta amsa mai

  "Oh Yusrah ke fa toh"

   "Shahida"

"Seriously Salim ina ga Sunan mutane ya kama ta kayi specializing a kai ba Army ba" Aliyu ya fada yana mishi dariya

  "Na sha fada mai ai, da ya ga bakon fuska to burin shi kawai ya San sunan ko yaro ko babba kuwa" Umar ke maganan yana kallon Salim

"Allah kun San da naga Mutum karantar face in shi nake inga zai yi matching da sunan shi to sai in tambaya in ji"

"Shahida je ki daki na ki dauko min System yana caji kinji"

"Tohm" ta fada

Da gudun ta taje dakin sai gata da da jakan mini laptop a hannun ta.

"Yauwa Good girl amshi Yusrah Ku shiga ciki kinji"

  "Dukkanku Ku tashi Ku zo"

A hankali su ka matso gaban shi suna turo baki sun kumbura kaman za su fashe, Zahrau kan hawaye ke zuba a idanun ta shabe shabe saboda lantern in da ya buga mata a kai kanta ya fara ciwo.

"Shekarunku nawa" ya bukata

  "Goma" Ummiy ta amsa

"Class fa?"

"Primary four"

"Ta ya ake muku promotion, Ku kunya ma ba kuji"

Duk dai shiru su kayi suna kallon shi sai sheshekan kukan Zahrau da ke tashi.

Amma abinda ke kular da Aliyu duk abinda zai musu ba zasu taba iya buden baki su bashi hakuri ba sai dai in ya gaji ya barsu dan kanshi.

"Zaku sani, tunda ba za kuyi karatu ba aiki zan dinga baku shine maganin Ku"

Tun daga ranar ya sa su a gaba, Saharan tsakar gida da wanke wanke kiri kiri zai hana masu aiki yana zaune yana kallo dole suyi, saukin ta ba su da kiwiyar aiki.

Tun a lokacin su ka sa wa ransu tsana ce kawai ya sa Uncle Aliy ke musu haka don ko abincin shi ne aka ba daya daga cikin su ta kai mai ya dinga mita kenan kuma ba zai ci Abincin ba

   Anyi bikin Anty zainab da yaya Muhammad (Babban yaya). Kano aka kaita can ta ke karatu daman a can suka hadu da mijin nata.

Yaya Babba kuma Kaduna ya tare da matarsa Anty Rukayya Itan ma yar kadunan ce, yana aiki da NNPC

Su  Zahrau yan mata an sha biki har da gayyata aka yi kawaye gasu nan dai barkatai wasu ma sun girme su babu dai na arziki duk tarkace ne.

 

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top