KHF 1


               11th September, 2016

                 2:30 Am midnight

   Talatainin Dare lokaci ne na hutu da natsuwa. Lokaci ne da Al'umma suke kwanciya bacci domin sauke gajiya. Wadanda ko ba baccin suke ba zaka same su suna Bautar Allah ne ko kuma kallo, karatu ds. Koma dai mai Dan Adam yake a cikin natsuwa ya ke yinta a wannan lokacin in ka cire Shaidanun mutane wadanda suka dauki duniya gidan dadi kaman ba za a mutu ba. Duk abinda suka ga dama yi suke yi musamman sabon Allah da ya hada da shaye shaye da bin gidajen karuwai da na raye raye. Irin wadannan mutanen ne suka maida tsakar dare lokacin yin masha'an su, wasu ma abin nasu a boye ne dan kagansu da rana cikin mutunci da kamala zaka rantse sharri ake musu, Allah ya shirye mu ya kare mana zuri'a Ameen Ameen.

Sulaiman Gidado matashin saurayi ne mai jini a jika. yana da kimanin shekaru Ashirin da shida a duniya. kyakyawa ne burin Ko wata ya mace dake rayuwa a doron kasa. duk da dai ance abinci wani gubar wani amma duk budurwar mai lafiyan da taga Sule wallah sai ta dara. Fari ne tas da ka ganshi kaga dan hutun da naira ta samu zama a wurin. Yana da dogon hanci Sak bafulatanin usuli, idon shi ko manyan ne farare tas mai ruda yan mata masu kwarjini da takama da Kansu, hakan na kara taimaka mishi wurin Yaudaran yan matan kwarai dagaske. Komai na Sule is perfect in ka cire wasu bangaren daga cikin halayenshi, dama ance mutum Tara yake bai cika goma ba... In ko ka ganshi a fili zaka rantse da Allah ba zai aika ta halayen shi daya Zame mai sirrin boye ba amma ina Musa a baki ne Fir'auna a zuci.

Zaune ya ke a Nicon Abuja tare da New catch in da yayi ko kuma ince new target wurin birthday in wata frnd inta. Yayi Nisa a wurin bin clubs, shaye shaye da kuma bin mata. Sai dai ba kowacce mace ya ke bi sai wacce ta amsa sunan ta mace mai ji da kai, zai nuna miki soyayya kaman da gaske yake sai ya samu abinda yake so zai wurgar da kwallon mangaro ya huta da kuda wai in angama shan abun sha wullar da kwalba ake dan bata da amfani.

Rungume yake da budurwar ita kuma sai wani kara narkewa take a jikin shi kaman wata mage. Flash in camera ke ta haske cikin hall in. A daidai wanan lokacin motan polisawa suka wa wurin diran mikiya, ba kanana polisawa bane Aa manya ne masu rank in Inspectors, ASP da DSP.

Cikin Hall in suka karasa da bindigogi a hannun su.

Suna shiga wurin yayi shiru yanda kasan ba wurin kidan ke tashi ba, ganewan da suka yi ba kanana nan polices bane da suka raina ma wayau ya sa su shiga hankalin su.

"Here is him" Wani inspector ne ya fada yana pointing Sulaiman dake rungume da Leelah budurwar tashi.

Wurin shi ko suka nufa hade da mika mai ankwa "You are under arrest"

Sororo ya tsaya yana kallon su domin rashin sanin laifin da ya aika ta musu "I don't Understand Sir"

"Don't argue with us Mr Sulaiman Gidado, You will know Everything after we get to the police Station" Wani DSP ya fada yana mishi shu'umin murmushi

"Okay I will follow you guys, but I think you don't need this thing" Sulaiman in ya fada yana musu kallon sama da kasa

"Fine let's Go"

         
               10:00 Am na safe

                 Birnin Zazzau

  Ahmad deedat ne zaune yana research akan conference in da zai je Abuja kasancewar shi lecturer a jami'ar Ahmadu Bello University dake Zaria.
     
   Wayar shi dake kusa dashi ne ta hau ruri. MUSA ne ya fito baro baro a gaban screen in. wani irin faduwan gaba yaji domin ya San ganin kiran Musa a gare shi ba alheri bane, sai da yayi bismillah sannan ya dauka.

"Ahmad, kayi mamakin ganin kiran na ko?" Musan ya fada yana dariya alamun cikin farin ciki yake.

Gaban Deedat ne ya kara fadi sanin cewa dariyan musan ba alkhairi bane a gun sa "Ina jinka ya akayi?"

"Ka kunna TV, tashar NTA yanzun nan za kaga sakon da nake son isar maka" Kwashewa da dariya yayi Wanda da kaji Kasan na mugunta ne sannan yayi ending call in

Innalilahi wa'inailaihi raji'un Deedat ke ambato a fili, Remote in TV ya dauko ya kunna sannan ya kai Tashar NTA.

Smugglers in cocaine aka kama a Airport, sai dai sunce sako ne su ake basu in suka kawo a biya su kudinsu, Sannan sun tona asirin ogan nasu har ma polices sun kamo shi a club in dare a Nicon Abuja, Wani Dan National Drug Law Enforcement Agency ( NDLEA ) ke bayyanin wa yan jaridan da suka sa shi a gaba.

Presently ogan na hannu Polices sannan EFFC sun fara bincike akan shi, sunan shi Sulaiman Gidado. Wani Dan jarida ke magana sannan karan hade da nuno hoton Sulaiman in.

Dafe kai Deedat yayi gami da kiran sunan Allah, "Sulaiman cocaine? Sannan club in dare? Anya ba sharri aka mai ba? kodai Musa ne? Kai ba zai yuwu ba karya ne" ya fada hade da girgiza kai

Hayaniyan da ya ji yana tashi daga cikin gidan su ne ya katse mai tunanin abin ban alajabin da ya ke ciki. Da sauri ya nufa cikin gidan.

A tsaitsaye ya iske su wasu na sallalalami wasu kam kuka ma suke, abin ka da mata hamza ne kadai Babban Namiji a gun.

Zahra ce a tsaye jikinta sai karkarwa yake basu ankara ba sai gani suka yi ta zube a kasa, A rude su kayi kanta dan daman jimamin ita suke tayawa.

Hamza ne yayi karfin halin dauko ruwa Deedat ya shafa mata sannan aka samu ta farfado amman ba natsuwa a jikinta, ko ina  na jikinta rawa yake, a hankali Deedat ke mata addu'oi tana amsawa sannan fa ta Dan samu natsuwa.  Bacci su ka samu tayi Wanda daga gani kasan ba na lafiya bane.

"Ni Gsky abin nan ya daure min kai anya Ya Deedat ba sharri bane?" Hamza ya tambaya

"Ni ma ban Sani amma Sulaiman in da na Sani hakan ba halin shi bane ko kadan" Deedat ya fada cikin tsantsan mamaki

"Ya Deedat ba abokin ka bane, Gsky a ganina kawai sharri aka mai" Wannan karan Ummi ce tayi maganan

Mai Jidda da Nanah kam har yanzu sheshekar kuka su ke. "Dan Allah Ku bar kukan ya isa haka, kukan Ku ba zai fidda shi ba" Ammah ta fada cike da  lallashi.

Mami kam mamakine ya hana ta magana Suleiman in da ta sanni natsatse, mai addini ga hankali da tarbiyya. Ba dai kama ko kadan, Allah ya sa ba da gaskr bane. Nima dai nace Ameen...

                  12th September, 2016

                Birnin Tarayya Abuja

    4:00 pm na maraice Deedat su ka tashi daga taron da ya je a cikin Abujan, Hotel in daya sauka ya koma, wanka yayi bayan yayi Sallah, ko ta kan Abinci bai yi ba ya dauki keyn mota ya fita.

  Abatcha Barrack dake Asokoro ya nufa kai tsaye Wurin dan'uwan shi Captain Aliyu Wanda ya sanar wa zuwan shi tun da safe.

Cikin Girmama juna suka gaisa, in kaga yanda Deedat ke wa Aliyu za ka rantse shekaru daywa kawai ya bashi amma shekara Uku kawai ya bashi, Aliyun mutum ne mai kwarjini da kima a idon mutane. Aliy kenan mazan fama.

House boy in shi ya kira Daniel, kallo daya ya mi shi ya dauke kai hade da fadin "I have a guest, attend to him"

Abinci kusan kala uku, Fruits da drinks Daniel ya cika wa Deedat gaban shi dashi domin ko Aliyun Mutum ne da bai wasa da cikin shi ko kadan.

"Bismillah Malaman jami'a, gidana ai ba bakonka bane ai ka Sani"

Murmushi Deedat in yayi sannan ya fara cin Abincin.

"Ashe kuma abinda ya faru da abokinka kenan?"

"Ehmm wlh ni har yanzu abin daure min kai yake, gani nake sharri ne"

"Ko daya, ba sharri a ciki dagaske ne, kawai dai baka San halin shi bane"

"Kai Ya Aliyu? Sulaiman din gaskiya da mamaki"

Murmushi Aliyun yayi sannan yace "Shiyasa nace maka baka San halin shi ba, Abokantakan naku a Zaria da Kaduna kadai ya tsaya, hasalima zaka dauka mutum daban ne na can da kuma na cikin Abujan, Nasan waye Sulaiman shi yake ganin ban San shi ba. Na kyale shi ne kawai domin yayi nisa ba zai taba jin kira ba Rana irin na yau ya bayyana wa duniya waye shi, dazu na je na gan shi and yana kokarin Denying kuma shi ne the worst abinda zai yi, Wlh mutanen nan sunfi shi taurin Kai."

"Tabdijam, Gaskiya abin akwai daure kai a ciki, Yanzu ya Aliy miye abin yi?

" Ba abin yi Deedat sai jiran hukuncin Ubangiji, Wlh kaf Naija banga me amso Sulaiman ba, can akwai business insu daya hada su ya sa su kayi kulla kullan da suka tona mai asiri."

Me zai faru gaba?

Me ya sa hankalin  Deedat ya tashi sanin boyayyen halin Sulaiman?

Miye Alakarsu?

Ku biyo ni...

  Vote, comments and share

 

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top