Page 4
KISWAH
(Linked through surrogacy)
By
CHUCHUJAY ✍️
Book1⃣
Page 4⃣
"Uhum Hajiya Farry ina jinki kince kina da magana dani"Kiswa ta faɗa tana mai taje sumar kanta mai madaidaicin yalwa,
Tasowa Farry tayi tazo inda Kiswa take ta zaunar da ita kan stool sannan ta karbi comb ɗin hannunta ta cigaba da taje mata kan tana shafa mai a hankali,daga kai tayi ta kalli mudubi wanda ta tarar da idanun Kiswa a ciki suna kallonta irin kallan nan na "nasan wani abu kike so"
Aje comb ɗin tayi tace "Fine i want you to do me a favour dan Allah Kiswa,"zagayowa tayi ta durkusa gaba Kiswa ta kama hannunta tace "Dan Allah Masoyiya taimako na zakiyi dan nasani kina mun soyayyar da bazaki So na faɗa halaka ba,a wannan karan kuma halakar ke kirana,Appa da mother ne ya suka haɗa mun blind date da wani yaran abokinsa wai muje mu sasanta kan mu,kin dai san abunda ya saba mun and i hate it sosai "shiru tayi tana kallan Kiswa wadda tayi mata alamu da hannu tace "uhum So?"dan tasan maganar Farry ɗin bata ƙare ba.
Cije lebe tayi tace"nayi bincike akan sa and bincike na 'ya nuna mun he's not the guy at all dan ba mutumin kirki bane,dan shaye shaye ne sannan clubber dan ance mun har giya yana sha ga neman mata na bala'i"cije lebe farry tayi tana tunanin Ta ina zata fara roƙon Kiswa ,rufe idanunta tayi gam tace"ina son kije a maimakona nasan you can handle Him ta yarda bazai yarda da Alliance din nan ba"
Mikewa zumbur Kiswa tayi tace"na miki sau ɗaya sannan idan na tuna na faɗa miki shine na farko shine na karshe ,solution ɗin is simple,muje mu samu Appa mu faɗa masa dukkan ill halayyarsa da kika lissafo mun in yaso ya sake bincike ,nasan dai babu yarda Appa zaiyyi ya Aura miki miji irinsa"
Ganin fa da gaske yanayin Kiswa yake ya saka farry fashewa da kuka tace"kina tunanin Appa Zai saurareni? Zaice kawai ina san kaucewa Aure ne amma ni ba Haka bane,and worst thing din im not even lying,na kasa zama na fadawa kowa sai ke amma kema da nake tunanin zaki tsamoni daga faɗawa halaka kince a'a ."kuka sosai Ta cigaba dayi wanda yazo ma Kiswa cikin rashin zato da tsammani,da saurinta ta koma ta kamo Farry tace "haba Farry mene hakan?Ban dauka wani abun ba sannan nayi zatan hakan zai zama best solution ne im sorry,when are you guys meeting sannan a ina ne"?.
Da sauri Farry ta ɗago tace "kina nufin zaki je?"
Kada mata kai Kiswa tayi tace "Amma wannan kawai Babu next time dole ne kisan ya zakiyi da rayuwarki sabida you're not getting any younger,dole kiyi Aure kije gida wani no matter abunki,sannan wannan zanje ne saboda na san koda nice a situation ɗinki zakiyi mun Haka,but This should be the last time,no it has To be the last time".
Da sauri Farry ta share hawayen ta tace "thank you sister ina mutuwar sanki,lunch time zamu haɗu a "meet up restaurant. "
And ai kema Haidar bai motsa ba and ke ya kamata ma ayi maganar Auranki bani ba.,kallanta Kiswa tayi tana san kauda duk wani tunani kafun ttace"well gwanda Ni tunda ina ma da wanda nake kulawa sannan kinsan Auren nan is for your own benefit tunda kina san business dinki as a CEO ALIJUA company dole kiyi Aure kinsan dokan Appa and i work under wasu so stop compering ".
********
1:30
MEET UP RESTAURANT ABUJA.
Cikin shiga wadda Kiswa batayi ta ke takawa dan shiga meet up,sanye take cikin body con mai dogon hannu mai kauri wadda ta fitar Da shape ɗin jikinta madaidaici mai kyan gani,boyfriend jacket ta saka a sama sai dan gyalen da kanta kawai ya rufe,fuskarta dauke take da hard Bitch make up wanda kana kallan ta sau ɗaya zakace wannan tab'ata kaji fitsarace yayin da bakin ta ke dauke da chew gum ɗin da take taunawa a hankali,inda Black lips ɗin da ta saka a lebenta dan charas ras yake motsawa cikin wani yanayi mai kyau,
Daga kanta tayi dan ganin table ɗin da Farry ta faɗa mata wanda ke occupied da saurayi wanda ya saka dukkan nutsuwarsa cikin wayarsa da yake faman dannawa ,ta san shine amma dan san clearing doubts ɗinta ya saka tayi dialing numbern sa da Farry ta bata ,tana shiga kuwa wayarsa ta dauki ruri,cikin takun heels ɗinta ta karasa garesa tana making bubbles da cingam din bakin ta,Babu ko sallama a bakita taja kujerar dake kallan tasa ta zauna tana mai yin wani irin ƙas ,
Dago kai saurayin mai daukar hankali yayi ya kalli Kiswa da wani irin yanayi,itama kallan nasa tayi tana mai ƙare masa kallo,haɗadden saurayine wanda ba domin bad halayyarsa Da Farry ta lissafa mata ba Da ta tayata murnar samun hot smokey handsome guy,ya haɗu iya haɗu,farine amma bai kai Haidar ɗinta fari ba,farinsa irin creamy dark ɗin nan ne mai kyau bugu da ƙari ga hutu,yana da idanu masu brown eyeballs Masha Allah waɗanda kallo ɗaya zai maka dasu kayi shakarsu,bazata iya misalta yanayin kyansa ba mai wani irin sirri wanda Ko wacce irin mace idan ya ɗana mata tarkon sa ta kamu,amma banda ita Kiswa Ubaid domin kuwa Babu wani kyau na ɗa namiji da zai ruɗeta bayan na Haidar.
Sanye yake cikin loose baggy riga white da wandonsu shima fari,kansa nada yalwar gashi wanda ke sheƙi Brown wanda ba sai ya faɗa mata ba tasan yayi dying kansa duk da ya fara fading,murmushinn gefen baki tayi tace "exactly like a typical play boy".
Cikin wani irin yanayi ya kalleta yace "excuse me?"
Bell ɗin dake kan table ɗin ta danna wanda yayi mata kira ga waiter wanda babu bata lokaci yazo,kallansa tayi tace "Wine and two plate of steak please".
Kaɗa kai waiter din yayi 'ya juya dan kawo mata abunda tayi order,da kyau saurayin yake kallanta kana yayi wani irin murmushi yace"and what the hell do you think you're doing"?
Ƙafarta tayi crossing kana ta miƙa masa hannunta tace "im sorry ban introducing kaina ba,Sunana Fareedha Aliyu ,ka kirani da Farry i bet We are suppose to be here for blind date ,SB Madugu right?"
Licking lebensa na ƙasa yayi 'ya Faɗaɗa murmushinsa lokacin da 'ya kula da yarda ƙafar Kiswa take rawa out of nervousness , mutum ne Shi mai sharp kai,kallo ɗaya zai maka yasan inda ka dosa, a fannin KIswa ma ya gane cewa tana san ruining date ɗin nasu ne ta bashi wrong impression akanta,abu guda ɗaya ne bata sani ba shima dole mahaifinsa yayi masa yazo yana bata lokacinsa da sunan jiran mace which is not like Him,ganin yana mata wani irin kallo ne yasa ta janye hannunta ta buɗe jakartta ta ciro cigarette ɗin da ta saka Farry siyo mata,guɗa daya ta ciro ta bubbugata kan finger ɗinta yarda taga yan sigari nayi kana ta kalle shi tace "kana da lighter na manta nawa a gida saboda sauri and nasan baza ka rasa ba Cos i know Babu yarda za'ayi ace you don't smoke".
Sake gyara zamansa yayi yana mai murmusawa Cos yana finding Abunda Ke faruwa gabansa interesting,folding hannunsa yayi 'ya kafeta da idanunsa da suke bata shakka yace"a matsayinki Na Yar sigari wadda bata manta sigari bai kamata ace Kin manta lighter ba,'ya kamata ace itace first priority din ki indai da gaske sigariin zakiyi".
Rolling idanunta tayi ma maganarsa kana tace"ji yarda kake magana kamar you're saint,shan sigari aii ba aibu bane 'dan nasan kaima bazaka rasa sha ba abeg ni da kai kowa yasan harka kar ka fara mun wasu maganganu".
Kafun ya furta wani abu waiter 'ya kawo masu order ɗinsu inda yana kallan sigarin hannun Kiswa yace "im sorry ma''am smoking is not allow here"Dan Murmshi tayima waiter din tace"sadly i left my lighter at home So you see ain't even gonna smoke here ,"murmushi waiter ɗin yayi mata 'ya saka hannu 'ya ciro lighter a aljihunsa 'ya aje mata kan table yace"consider it a gift from me"Murmushi tayi masa kana tace "awwn thank you love".
Yana barin gurin ta Maida hankalinta Kan SB madugu tace"well i got a lighter amma kaji sai Na fita,i would manage amma yanzu ga Alcoholic wine how about We party on it then idan mun gama i will booked a nice hotel i love it on a first date?
Hannunsa 'ya shafa a kansa kana ya tashi ya kama hannunta ya tasar da ita daga kujerar data ke ,take ya fara janta,ganin idanu sun dawo kansu ya saka ta fara ƙokarin kwace hannunta amma yaki sakinta har saida ya gama biyan kuɗin abunda tayi ordering kana ya cigaba da fincikarta,bai sake ta ba har saida suka bar harabar gurin sannan ya kalleta da wani irin kallo wanda ta kasa fassara na menene yace"mai kike So ki nuna mun ,ko kuma mai kike san achieving ".
Mugurɗa baki tayi tace"well abu guda daya nake san nuna maka wanda shine wacece ni,nasan cewa you're not any way better and ni da kai Babu wanda zaiso ya Auri wani Cos dukkan mu muna abunda ɗaya bazai alfahari ace yau ya uwa ko uban yaran sa ba,So Its better muje mu samu masu ɗa'a ba irin mu ba."
Dariya ya saka sosai yana mai nunata da yatsa sannan yace"So ni dake bamu da ɗa'a,?"dariya ya kuma sakawa sannan yace "Kin sanni?tayaya kika san Ban da ɗa'a?"
Haɗe rai tayi ganin yana neman raina mata wayau sannan tace"a kallonka ɗaya ma ai ba sai ka faɗawa mutum kai play boy bane,you look typically like one,nima kuma idan ka kalleni im not anyway better,kai bari 'na fito maka a mutum ,nasan you're a womanizer,clubber,drunkard ,druggie and a smoker So kar kazo nan kana mun acting saint fuck It up, bana san Aurenka sannan kaima na tabbatar ba san Auren kake ba dan haka ka san mai zaka faɗa a gida".
Gefensa ta rabe 'dan ta wuce amma ga mamakinta sai gani tayi 'ya saka hannu 'ya fincikota baya,motar dake bayanta yayi pinning ɗinta da ita sannan yayi mata rumfa da jikinsa,kafun 'ya kai ga furta wani abu ta daukesa da mari wanda yayi mutuƙar shigarsa,hannu tasa ta turesa Tana mai nuna sa da yatsa tace"hungry horny bastard".wucewa tayi har tana mai gurɗewa da takalminta saboda sauri yayin da lokaci guda kuma kirjinta ke dukan uku uku.
Tsaye yayi yana binta da kallo inda hannunsa guda ke kuncinsa,he cant blv what happend abunda bai taba faruwa dashi ba yau 'ya sameshi,shi SALEEK mace zata ɗaga hannu ta wankawa mari ba ma wannan kadai ba har da masa ƙazaman ƙazafi,yana tsaye yana wannan jimamin PA ɗinsa Khalifa Adnan wanda ke matsayin abokinsa ,amininsa yazo gurin yana mai faɗin akaramakallu Sir SALEEK 'ya date ɗin and how About Babe ɗin tayi?
Tsintar kansa yayi da murmusawa sannan yace" kai 'dan baka da mutunci kasan ni"womanizer ne,drunkard,smoker, druggie,clubber amma Shine ko da wasa baka taba faɗa mun ba"
Kallansa Khaleefa yayi da mamaki kafun 'ya kwashe da dariya yace"To ni basan kanayi ba amma Ban sani ba ko bayan barina Australia ka faɗa harka tunda dai ni na rigaka tahowa,"Duka SALEEK 'ya kaimasa yace "dan iska ba abun nayi firing ɗinka nasha wahala ba "a tare suka saka dariya Kana suka taka zuwa ga rantsatsiyar Rolls Royce ɗinsu inda SALEEK ke cewa"mutumina kamun bincike kan yarinyarnan ,ina san nasan wacece ita 'dan im sure ta yau ba version ɗin rayuwarta bane"murmushi Khaleefa yayi yace ka shiga ciki kenan?sosa ƙeyarsa yayi yace "Abeg wane ciki ,i Just find her intresting,ina san nasan wacece ita sannan wanene 'ya jera mata wanchan Ƙazamun ɗabiun a matsayin nawa,i have to punish her for that kaga to do that kuma sai na san more about her".a Haka suka garzaya Khalifa nata mai shaƙiyanci.
Koda Kiswa ta isa gida kai tsaye ɗaki ta shiga 'dan tasan a wannan lokaci kowa na ɗakinsa yana hutawa,ille kuwa tana shiga ta tarar da Farry kwance tana bacci,kallanta tayi ganin yarda take bacci peacefully wanda yau da ace ta Auri SALEEK da wannan baccin ma bazata samu damar yinsa ba saboda rashin samun nutsuwa da zatayi da saleek Cos kallo ɗaya zakayi masa kasan ina 'ya dosa,a nata tunanin.
Make up ɗin fuskarta ta cire kafun ta shiga bayi 'danyin wanka ,tunanin kala kala sukayi ta mata zarya a kwanyar kai 'dan ta sani muddin Mother tasan da maganar abunda ya faru yau to ta kaɗe ta lalace har ganyenta,bayan ta fito tana saka kaya Farry ta farka tana mai hamma tace "best sis Kin dawo kenan,"
Wani irin kallo Kiswa ta bata kana tace "Dole kice mun best sis mana ,naje 'na samesa apart from halayyan sa 'na banza da kika lissafa he is a go with Handsome dude i hope Kin samu information a kansa from a good source kar kije ki jamun wahala dan kinsan Mother 'na jin maganar nan sai ta kusa kasheni in bata kashe ni bama kenan"
Dariya farry tasa sosai cikin Dariyar tace "calm down babe Babu mai kashe wani after all gobe ma idan 'ya ganki ba lallai ya tuna ki ba,after all the make up was something And maganar Mother kuwa ko da ta baci ina da plan B And na ma san you can never do something like This wrong Yea And lastly Haidar yazo And We went out together . "
Kallanta Kiswa tayi tace "haidar yazo and bai kira ni ba?
"Uhum,yazo nace masa Kin fita date but ban faɗa masa dawa kika fita ba i was bored and i took that opportunity ta clear up my boredom and i most say he's a nice catch .
Bata kuma cewa komai ba tayi bathroom dan daura Alwala tayi Sallah,bin bayin Kiswa tayi da kallo kafun ta ciro wayarta dan kiran Haidar,kamar zata Kirasa amma sai ta fasa ta aje wayan ta cigaba da abunda yake gabanta.
Share,react and comment.
CHUCHUJAY
08130229878
Follow me on wattpad @chuchujay.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top