page 3

KISWA

(Linked through Surrogacy)

            Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page3⃣.

ALIYU'HAIDAR TUKUR BULA shine asalin sunan sa matashin saurayi mai shekara ashirin da tara ,haifafen cikin garin Abuja ne amma asalin su mutanen dutse ne dake cikin garin jigawa amma a tashin Haidar Abuja Ya sani gidan dan tunda yake da iyayansa biyu basu taba cewa yau Haidar shirya muje usulin Garin ka ba a yayin da shi ma bai damu ba ganin yan uwan nasu na chan garin suna zuwa inda suke.

Haidar ɗa guda ne tilo wurin iyayen sa Alhaji Tukur Bula da Matarsa Hajiya zainaba Bula dan haka suka dauki soyayya ta duniya suka ɗora masa ,Babu wani abu da Haidar yake nema a rayuwar sa ya rasa tun yarinta indai kuɗi ne zai bada su ,irin girman sangarta da akayi masa kawai ya ishe sa lalacewa a yayin girmansa Amma sai Allah ya rainesa cikin sahun mutane masu nutsuwa da sanin ya kamata,sau da dama mahaifiyar sa kan ɗorasa a abu mara kyau wanda zahiri tasan mara kyau dinne amma saboda dabia ta nasara sai ta danne inda shi kuma idan ya hanga rashin dacewar wannan abun sai yayi kokarin wajen ganin ya dorata a hanya.

Iyayen sa shahararrun masu kuɗi ne domin mahaifiyar sa babbar sananniyar yar kasuwace a garin wadda keda boutiques ɗin da zaka gaji da irgawa a yayin da mahaifinsa yake babban custom,magana ta rashi a gidansu Haidar fa babu ita domin kuwa Allah ya azurta iyayensa wanda dalilin hakan yasaka basu damu da subi danginsu inda suke ba sai dai su su biyosu inda suke su dan lasa.,

Rashin samun wani haihuwar bayan haidar baya damun iyayensa illa shi din da suka samu suka duƙu fa wajen tara masa abunda yake nasu ne ma'ana dukiyarsu,

Sanin iyayen Haidar Nada kudi bai taba kashe masa zuciya ba wajen neman na kansa duk da kuwa yarda mahaifiyarsa ke nacin yaji dadin rayuwarsa kawai domin kudi sun tara masa ba sai ya wahalar da kansa wajen nema ba amma yayi fafur akan cewa su barshi yayi aiki domin career ɗin abunda yake mafarkinsa ne kuma abune wanda yake da sha'awa tun yarinta wato aikin Likitanci,ganin ga abunda yaran nasu yake So shi yasa suka bude bakin jaka wajen ganin sun bashi ilimi isashe wanda ya samu ƙwarewa a harkar inda daga bisani suka tamfatsa masa Asibiti wanda yaci sunasa "AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL "Haidar kwararren likitane wanda ya taba fannika daban daban ,sabida san zaman komai dai dai a asibitin Nasa yasaka yake daukar likitoci wadanda suka san mai suke ,a kalma guda Asibitin Al'Haidar asibitine wanda baza kace likita daya ke duba zuciya ba sannan ya duba hakori ya duba kunne ,ya duba ƙashi  da dai sauransu,asibitine da ke dauke da zuga na komai da ruwanka.

    Da kansa ya samawa kansa ilimin addini duba da iyayensa sunfi bada muhimmanci akan bokonsa cos bai taba zama ajin islamiyya ba sai dai malami yazo gida yayi masa wanda shima bayan fara tasawarsa aka sallamesa acewar Hajiya zainaba 'ya samu 'na sallah ,sanin yana bukatar bunkasa saninsa akan addininsa 'ya saka ya dage wajen sanin littattafai domin duk yarda yake san iyayensa yayi alwashin idan ya haihu bazai taba Bawa yaran sa tarbiyya irin wadda 'ya samu ba,mutum ne shi mai nutsuwa kamili wanda bai damu da sabgar yan mata ba duk da harin da suke kawo masa domin shi din mai kyaune da kyawun kira irin wadda duk wani namiji ke fata,sau da dama idan aka tada ma mahaiffiyasa maganar 'ya kamata yayi Aure sai tace "duka nawa Haidar din yake,abarsa yayi rayuwarsa cos life is too short duk lokacin da ya gama gwara kan yan mata ya samu ta Aure"jin Wannan furucin yasa ƙanwarta mahaifiyar Tasleem ta kawo tasleem gidan da zummar tana daukewa haidar din kewar rashin dan uwa amma a kasan zuciyarta ta kawo tasleem ne domin ta Auri Haidar nan gaba.

    Kowa yana saka da warwararsa a yayin da Haidar yayi gamo da tauraruwar da ta sace masa dukkan nutsuwarsa da tunaninsa a lokaci guda wata rana da tazo  asibitinsa,yana kokarin fita daga Asibitin tana shiga a motarta wanda ta shige da zuciyarsa at first sight,bai wata wata ba 'ya koma Asibitin 'ya jirata har ta fito 'ya bita, babu kasa a gwiwa 'ya fallasa mata asirin zuciyarsa,ya dan sha wahala kafun 'ya samu hadin kanta cos a ranar bata kulasa ba sai da yayi ta bincike 'ya gano inda take aiki ya sarrafi addabarta wanda a hankali ta bude masa tata kofa zuciyar da ta gama karantarsa,yarda bai taba budurwa in a Serious way ba Haka nan Kiswa dan haka suke ma juna mayyar soyayya cos akan juna suka san daɗin ta.

                             ******

Duk weekend rana ne da Kiswa da Haidar suka ware domin kasance da juna ta hanyar zaga duk wani gurin shaƙatawa domin ranar ne suke free baki ɗayansu,yau ma kamar kullum 'ya sameta gurin Spa 'dan su wuce classic restaurant ɗin da aka buɗe sabo aka bashi gayyata,chan 'ya tsaya bakin motanta yana jiran fitowarta inda bata wani bata masa lokaci ba ta fito garesa,tun daga nesa take kallansa tana yaban kyan da yayi mata a zuciya cos a ko wanne sutura takan tsinci Haidar dinta cikin kyawawan maza da komai ke fitting,sanye yake cikin royal blue button up riga mai sleeves gajere da dark Pants,sosai yayi mata kyau,cikin takunta mai daukar hankali ta ƙaraso garesa ,snapping 'yatsunta tayi a fuskarsa ganin yarda ya zama lost a kallonta,murmushi yayi lokacin da ta jingina da motan kamar yarda yayi tace"'na sake kama hala?"

Juyowa yayi yana kallanta yace"dan Allah kiyi wuff dani Girlfriend ,husband me cos kina kasheni da yawa ,i just cant wait naga kin zama mallakina,What are we waiting for?

Licking life dinta 'na ƙasa tayi tana mai tambayar kanta a zuciya "What is she waiting for?"'ya kamata ace yarda ta yarda da Haidar zuciyarta kuma ta gamsu dashi magana ɗaya 'ya kamata ace a yanzu anayi tsakaninsu which is maganar Aure,shekarar su guda kenan tare da juna amma bayan Farry Babu wanda yasan labarinsa a gidansu,itama Farry din kamata tayi suna waya ta dinga bin kwakwafi sai da ta gano wanene shi,lokacin da tasan kuwa Mai Al'Haidar hospital ne kamar tayi hauka tana mai ingiza Kiswa akan kar ta sakesa cos shi ɗin catch ne babba.

Tana san maganar Haidar ga Appa amma tana tsoran Outcome 'na Mother wanda tasan Babu daɗi domin duk cigabanta idan mother zata sanshi to zatayi yarda zatayi ta koresa 'dan haka ta sama ranta maganar Haidar sai ta shirya,kamar yarda  take faɗa masa a kullum yauma shine dai wato"Babe ka bani time kaɗan na dan Sake gina career ta kaɗan ,i assure you indai ina rayuwa kaima kanayi to da yarda Allaah da ikonsa nida kai mallakin juna ne".

    Daɗi maganar tata tayi masa 'dan haka ya tsincii kansa da washe mata baki,ganin yarda ya washe hakoransa 'ya sakata darawa tace"baka da dama baby baki ɗayanka,"tana ƙokarin buɗe motarta 'ya wani marairaice yace "baby muje motana mana"daga gira guda daya tayi tace "Aw kaima ka fara looking down on my car kamar kowa ko, kana jin kunya muje high class restaurant na aje motana ace ga motan budurwar Mai Al'Haidar ko? "

Okay good ka wuce nima bari na tafi gida kar na kunyata ka.

Saurin rike bakinsa yayi yace "Auzubillah Girlfriend mene hakan kuma,kisan dai i would never look down on you,beside motanki yafi Rolls royce Phantom ɗina cos ni Daddy ya siya mun ke kuma you bought This with your hard earn,im sorry idan na baki wrong impression"

Ganin yarda ya wani marairaice ya sakata saka dariya sosai tana mai kallansa kafun tace"oga park well i was joking ka wani saka Serious face kana bani jamb answer go hop in your car ina bayanka,"

Shafa kansa yayi yana mai kallanta kana yace "kinsan wani Abu?"

Kaɗa kai tayi 'a'a ganin yarda ya saka Serious face tana tunanin wani Abu ne ,

"I LOVE YOU"

Shine abunda ya faɗa 'ya shiga motan nata yana mai faɗin a motanki zani nima,

Haka nan ta jasu duk yarda tayi dashi akan yaje 'ya shiga motansa amma Yaki dole ta. Jasu suka tafi,she love teasing  Him alot.

    After long day na soyyayya da suka sha Tayi dropping ɗinsa 'ya dauki motansa kana ya rakata gida,sun jima nan ɗin ma kafun su rabu kana daga bisani sukayi sallama shima calls din Mother da ta ringa gani yana shigowa wayanta ne wanda bazata ce Ga dalili ba 'dan sabon abu ne,ile kuwa tana shiga gidan suka ci karo da mother wadda ke faman safa da marwa a falon cike da damuwa,cikin kulawa Kiswa ta ƙarasa bakinta dauke da sallama tace "Mother naga kiranki ina hanyar shigowa shine yasa ban dauka ba hope lafiya"?

Marin da Mother ta dauke ta dashine yafi komai daure mata kai,da mamaki take bin mothern da kallo wadda ke faman kumbura kamar wata mesa kana ta nunata da ɗan yatsa tace"duk wani abu mai kyau bai dace dake ba,baki chan chanci duk wani abu da yake da kyau a rayuwa ba sannan kisan da sanin cewa i cursed you,bazaki taba samun cigaba a rayuwarki ba 'dan Haka tun muna mu biyu kuma mu biyu muka san maganar nan kiyi saurin rabuwa da Al'Haidar domin jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa,ba sa'anki bane ba tsaranki bane,Haidar irin mazan daya kamata suyima Farry rububine bake ba stinky orphan ,saboda Kin tsotsi munafurcin Kin iya boye relation ɗinki har na shekara babu wanda ya sani,yanzu ba dan an ganku tare an faɗa mun ba Haka zaki maida kowa dan iska,to Allah ya tona miki asiri."

Tana kai aya ta juya 'dan barin falon,cikin karfin hali Kiswa tace"kiyi hakuri Mother amma bazan iya rabuwa da Haidar ba,abu guda daya ne zai raba mu wanda shine mutuwa ,sannan ba dan na bata miki ba ko na miki rashin kunya ba amma kowa da kika gani yana rayuwa marayane a tafe ,maganar kuma bazan nasara a rayuwa ba wannan ba sani na ban ba naki bane ba,na Ubangiji ne".

Kafun Mother ta furta wani abu Kiswa tabar gurin dan nufa dakinta,Sameer dake sama yana kallan komai ne 'ya sakko 'dan fita ya kalli Mother yace "Thats embarrassing Mother stop it already mana ,ni banga mai yarinyar nan ta tsare miki ba duk kinbi Kin saka ta a gaba ,'dan Allah Mother ki daina mana kar ta rainaki"

Cike da bala'in da bata saukewa Kiswa ba tace"to 'dan ubanka sameer ka hanani magana sannan tunda Zubaida tace bazan rintsa ba wallahi ko gyangyadi baza tayi ba,idan ba balaii ba an kawo yarinya an aje mun Ban haifa ba na raina ,to ta Auri mai kuɗin na gani ,wannan toilet din data fito nan zata koma ta Auro amma ba'a abuja ba"wani dogon tsaki taja ta haura sama zuciyarta na mata wani irin zafi 'dan har ga Allah bata san dangin Mijinta karma ace Kiswa data rabe su.

Kaɗa kai sameer yayi ya nufi ɗakinsu Kiswa,sau biyu yana kwankwasa kafun ta bashi izinin shiga bayan ta gama dai daita kanta,yana shigowa ta washe masa haƙoranta tace "Yaya Sameer?"

Murmushi Yayi yace "yes"yana mai jan stool 'ya zauna kana yace "dont fake it i saw everything"murmushin yake tayi tace"Kayi hakuri Ya Sameer Nasan nayiwa Mother magana out of tone,na kasa rike kaina ne".

    Hannunsa 'ya saka ya kama nata 'yace"ki daina yawan bada hakurin nan Kiswa akan abunda baki da laifi bana san shi,trust me idan da Nine a maimakonki i would have acted worst,kiyi hakuri nasan babu abbunda zan fada yayi justifying hallayyar mother gareki ,ki kara hakuri wata ranaa sai labari,ehn kafun na manta wanene Al'_Haidar"

Dan kasa tayi da Kai tace "He's your in law to be"Rike baki yayi yace"kaji yarinya babu ko kunyaa"Dariya tasa tana mai yin kasa da kanta inda shima ya tayata yana mai fadin "kima daina jin kunya aii" a haka cikin hirarsu ya kawar mata da dakuwar Mother inda suka kafa hirar Haidar.

TBC

CHUCHUJAY✍️

08130229878

Wattpad:Chuchujay

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top