page 1

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

KISWAH

(Linked through surrogacy).

Na CHUCHUJAY ✍️

Book 1⃣

Episode 1⃣

A/N

Assalamu Alaikum masoyana abun alfahari na,Fatan na sameku cikin koshin lafiya ,

Ina kaunarku a koda yaushe kuma bazan daina ba domin kuwa Allah ne ya haɗa ni daku wanda ba yine 'na mutum ba,

Ina rubutu kuna kaunarsa sannan kuna bani kwarin gwiwa wajen so da yaba abunda 'na rubuta,😪ni ba kowa bace idan Babu ku ❤.

So yarda Allah ya bani ikon haɗa Littafin AURE UKU da AHALINA ina Addu'ar 'ya ara mana rayuwa da lafiya domin kawo muku wannan littafi nawa Na KISWAH(Surrogacy was the cause ) amma a wannan zagayyen tafiyar ta dabance domin kuwa littafin 'ya kasu kashi biyu ma'ana book 1&2

,book 1 zai zo maku kyauta ne book two kuma na kuɗi,kamar yarda na nishaɗantar daku a series biyu da 'ya gabata ina fatan nima zaku nishaɗantar dani da beautiful sales na wannan littafin Na KISWA,kilan kin taba ko ka taba jin story line ɗin kilan kuma wannan ne na farkon ka,abu guda ɗaya na sani wanda shine ,insha Allahu zai ilimantar,zai nishaɗantar .

Na sake faɗa Book two 'na kuɗi ne kar ki fara karantashi ya katse kiji haushina akan bance 'na kuɗi bane saida mutum ya fara' thats what happpend a Abla Adnan amma insha Allahu zaizo muku akan farashi mai sauki cos biyan zai zo da tsari,iya kudinka iya shagalinka❤

  TSOKACI.

◽Surrogacy Wani method ne da turawa suka kirkira wanda idan ma'aurata biyu na san haihuwa misali idan ɗaya daga cikin ma'auratan bazai iya haihuwa ba ko kuma matar bata san ta haihu ɗin sai su samo wadda za'a sakawa Maniyi na mauratan biyu,da taimakon technology zasuyi developing ciki jikin Matar da wannan halittar samun ciki na Ma'aurata biyu,

Surrogate mother ɗin zata masu rainan cikin ta haife ta basu abunsu wanda shi yasa a kasashen yahudu surrogate mothers suna nan aikinsu ne iyakacin su haifa maka su baka abunka aikinsu 'ya gama kenan,wannan kana ji aikine na nasara domin kuwa Musulunci yayi Allah wadai da wannan tsari,sannan baya da gurbi ko waje ko wata ɗauraya a addinin Islama.

Wannan kenan.

       DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI.

Ko wanne ɗan Adam dake numfashi a rayuwa An haliccesa ne sannan aka rubuta masu ƙaddararsa sai dai yiyuwarta da wanzuwarta a lokacin rayuwa domin kuwa sai tazo kuma sai ta faru jira ne kawai bawa ke yi,

A haka rayuwa da ƙaddarar KISWAH UBAID ke tafiya a rubuce cikin tsari da godiyar Allah domin kuwa duk wani musulmi na ƙawarai yana daga cikin Imaninsa 'ya yarda da ƙaddara wala mai kyau ko kuwa akasinta ,

Iyayen KISWA biyu Malam UBAID da Zubaida ,Mutane yan asalin jihar Bauchi,a rayuwar Aurensu sun jima basu samu rabo ba domin rabon nasu na chan nesa,Zubaida bata samu ciki da mijinta ba har sai da suka shekara huɗu da Aure ,a lokacin kuwa da sanin cikin ya ziyarci Malam UBAID ba ƙaramun mirna yayi ba da farin ciki domin kuwa yana mutuƙar kaunar Ace yau zubaidarsa ta basa Farin cikinsa wanda shine ganin yaronsa ko yarinyarsa a hannunta.

    A lokacin da Ya samu labarin cikin kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha dan murna,idan kuwa ka haɗu dashi a wannan rana To tabbas sai yayi maka ihsani saboda wanda ubangiji yayi masa.

Mutane da dama kan faɗi masa maganganu iri iri akan rashin samun cikin Zubaida dan harda masu ce masa rashin haihuwa Ya saka mijinta na farko sakinta domin bashine Ya fara Aurenta ba a bazawara Ya Aurenta,

Dukkan wata magana Da wani zai faɗa masa zata shiga ta kunne guda ne ta fita ta guda dan Babu wadda ke tasiri akansa,abu guda ɗaya ya sani wanda shine yana san matarsa sannan itama tana sansa sannan mahaifansa basu taba masa ƙorafi akan rashin haihuwar matarsa ba sannan ya sani da samu da rashi duk na ubangijine wanda a lokaci guda ya azurtasa a lokacin da bai tsammani ba,

Lokacin da Matarsa ta isa haihuwa ta zanƙado masa yarinya mace mai kyau wadda yana kallanta yace Allah ya basa KISWAH (Madubi,Rufi na Ka'aba)ya bata sunanne saboda Itace madubinsa na farko gurin sanin menene jininka,yana kuma fatan ta kasance mai tsarki da purity kamar irin na gold and Black lullubi na Ka'aba domin kuwa yan representing unity irin na islama.

    Ranar sunan KISWAH kuwa ba ƙaramun bajinta yayi ba dan idan ka gani zakayi tunanin dukkan wata dukiyarsa yake ƙoƙarin ƙararwa a wannan rana,

Yana samu domin ɗan kasuwa ne wanda Allah ya bawa nasibi a kasuwancin nasa,

A lokacin da Zubaida tayi Arbain ya biya masu saudiyya domin kai KISWAH ya shafa hannunta akan KISWAH.

Lokacin da KISWAH ta shiga shekaru huɗu a  Duniya Allah ya jarabci Malam UBAID da larura wadda tazo da ajali,bayan Kiswa basu sake samun wani rabon ba ashe ita ɗin ita kaɗaice rabo tsakaninsu.

Sosai Lalurar ta far masa wadda likitoci suka kasa gano bakin zarenta yayin da a bangare guda kuma ciwan ya ringa tafiya da dukkan arziƙinsa da tanadinsa wajen nema masa lafiya inda daga bisani Allah yayi masa cikawa ,

Bayan rasuwarsa a hankali Zubaida ta fara shiga chakwakiya ta rayuwa domin kuwa komai nasa ya kare sai gida wanda suke ciki inda shima ya shiga cikin gado,iyayensa da basu nuna masa san zuciya a fili ba lokacin rayuwarsa sai suka Nunawa Zubaida da ɗiyarsa KISWA domin kuwa ana saida gida suka karbi gadonsu suka sallama mata KISWA,itama iyayenta ba masu ƙarfi ba amma a haka ta cigaba da rayuwa da daɗi ba daɗi karkashinsu inda daga bisani lokacin da KISWA ta isa shiga makaranta Yayan zubaida ,Aliyu dake da Hali ya ɗauketa ya kaita gidansa domin sakata makaranta wanda ya shaida mata shine kawai abunda zai iya mata domin ba wani shiri suke ba amma sai Allah ya ɗora masa san Kiswa ,daga bisani kuma miji ya fito mata mai mace biyu ta Aura a nan cikin bauchin inda a gefe guda ta kama sana'ar abinci.

                         ***

24 YEARS LATER

ABUJA NIGERIA!

    Zaune ƙyakƙyawar budurwa take  kan gado a wani ɗaki dake ihun Naira,komai na cikinsa princess like ne cikin color na pink and white,ɗakin na ɗauke da gado guda biyu wanda zai ɗauki mutum biyu each,a hankali take taba tab ɗin dake hannunta cike da siga ta mayar da hankali,ba fara bace irin matan nan ne da ake ma ikirari da black beauty wadda a kalo ɗaya idan kayiwa fatarta tabbas kasan ta samu kulawa,tana wannan zaman aka turo kofar ɗakin ,wata budurwarce da bazata wuce tsarar ta ba,Babu sallama a bakinta ta shigo ta na mai jefar da jakar hannunta kan gado na biyun a yayin da ta zauna tana mai cire takalminta wanda Ya gaji da tsini,

    Kallo ɗaya budurwa farkon tayi mata ta dauke kanta,ƙaramun tsaki ta biyun tayi tace"Wallahi KISWA kina da matsala ba kaɗan ba ,kina jina na shigo Ai ko sannu ne kya faɗa mun amma dan tsabar bakin nukuburci kinyi kamar bama kisan na shigo ba,tsaki ta kumayi tace "today was beyond stressful ".

  Murmushi kawai KISWA tayi sanin halin mai magana,tana so a koda yaushe kasan da ita  ka bata attention,

FARIDHA ALIYU kenan wadda ake wa laƙani da FARRY ɗiya mace tilo a gurin ALHAJI ALIYU yayan zubaida mahafiyyar KISWA da Matarsa Barrister JUWAIRIYYAH ,yarinya wadda a kayiwa rainon gata da sangarta,yarinya wadda aka raina kamar ɗiyar sarki,Yarinya mai taƙama da ita ɗin yar gatace gurin Yayyunta guda biyu maza SAMEER da SAGIR wadanda basu san laifinta,

Bata da kara bata kuma gudun nuna maka kaiɗin ba komai Bane,duk da Halinta a bangare guda tana mutuwar san Kiswa duk da kuwa yarda mahaifiyarta ke mutukar nuna tsanar Kiswa ɗin tsantsa 'dan a cewarta tana neman kwacewa yayanta gida ne duba da yarda mai gidanta ke nuna kulawa ga Kiswa ɗin bugu da kari kuma yaranta maza dake faman mata shishshigi ,tsoranta guda kar wani cikinsu yace yana so,

Sau da dama Kiswa ke bin mess ɗin Farry tana gyarawa 'dan ita ɗin bata ji a yayin da gefe guda kuma Kiswa tasan ta duk wata hanya da zata bi ta kare Farry ɗiin.  

    Aje tab din nata tayi ta kalli Farry wadda ke ƙokarin Ɗaura towel tace "last da na tuna lokacin da zaki shigo bakinki babu sallama so mene zai dameni akan kulaki,and Yes maganar guy ɗin chan dake stalking ɗinki is all done and Abeg Farry ki barni haka nan na huta i have a life too"

    Da sauri Farry ta dawo inda Kiswa ke zaune ta kama hannunta tace"God ina mutuwar sanki yar uwata ,na gode and anjima kaɗa zakiji alert na 500k "

Kallanta da kyau Kiswa tayi tace "you must be Nuts,wai sau nawa zance miki idan abu haka ya faru tsakanina dake ki daina ƙokarin biyana bana so abeg ,idan kina san ana miki aiki ne kina biya ki samu masu aikin a waje wanda irin aikinsu kenan mana."

Saurin kama hannunta Farry tayi tace"Chill girl calm down ba ina nufin wani abu haka ba wallahi,kawai ihsani ne and Yes nasan you're doing Okay financially amma aibu ne dan na maki kyauta?"

Kinsan im off better financially ki kalla fa ina hawa Landcruiser kina hawa 306 so girl i mean no harm,Tashi tayi tana mai gyara towel ɗinta ta nufi bathroom ɗinsu,har zata shiga ta juyo ta kalli Kiswa dake kallanta tace "500k im sending it idan kinga dama ki kyautar"Tana kai aya ta faɗa.

'dan murmushi Kiswa tayi a fili tace "im also doing well cos ina da savings na wajen 5 million and ban raina ba cos i earned it and motana i bought it my self"

Daga cikin bayin Farry tace "'dan kina da 5 million doesn't mean zaki saka kanki cikin millionaires ,you have alot way To go,so idan zakiyi quiting wannan kamfinin da kike ma aiki ki dawo na Daddy kiyi cos chan zaki samu kuɗi ba inda wani zai biyaki ba trust Me zan biyaki da kyau,yes im enjoying daddys money wanda kema ke kika hana kanki,cos motar nan Ya siyan miki kika ƙi karba.

    Tashi Kiswa tayi tana mai sake gyara gadonta tace "nasan dai kinyi karatun addini sannan a cikinsa kinsan surutu a bayi haramun ne ,so ki bari idan kin fito sai ki bani wannan lecture ɗin."

    Haka nan Farry take,idan magana tazo bakinta bata tunanin saka mata filter idan zata faɗe ta sannan duk abunda tayi niyyar faɗa shi take faɗa bata damuwa da abunda kai zakaji as far as ita ta futar da ta cikinta,haka nan take koda kuwa da Kiswa ne amma idan abu ta bangaren Kiswa ne bata wasa dashi komai ƙanƙantarsa,koda zuwan Kiswa gidan afafur ta ki yarda da a raba masu ɗaki duk da wadatar hakan ,duk nacin mahaifiyarta dole ta barsu.

Dauke takalman da ta watsar Kiswa tayi tana mai jadadda mitar ta daina aje masu takalmii a ko ina,

Kafun Farry ta fito ta gama gyara ko ina tana mai haɗama kanta cornflakes ɗin da tasa akawo mata,tana cikin ci Farry ta fito Babu wani tambaya ta kwace cup ɗin Ta fara ci tana mai cewa"ki haɗa wani"

Tsaki Kiswa tasa tace "wata rana sai kinci abu mai guba".

Zama gefenta tayi tace"indai a gurinki ne sis nasan bazan taba cin guba ba,kinsan dai kin bani wata ɗaya dole ne kina Cin girman,yauwa ina ma san tambayarki Ina Haidar ɗinki,

Ɗan ƙaramun tsaki Kiswa tayi tace "rabu da wannan yana tunanin bazan iya rayuwa babu shi ba shine yake faman shan ƙamshi a faɗan da ba laifina ba,well muje zuwa wanda Ya fasa gajiya."

Yar dariya Farry tayi tace "ke dai faɗanki da Haidar ɗinkin nan bamu shiga muji kunya,ina,ni 'fa shi yasa da kika ganni Babu ruwan da wani relationship' kuɗin dai da power ɗin tukunna .

A tare suka saka dariya 'dan a kullum furucin ta kenan a yayin da Kiswa kan faɗa mata bai zo Bane shi yasa.

Share fisabililahi

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

CHUCHUJAY ✍️
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Join my Whatsapp channel

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top