9
💥KISWAH💥
(Surrogacy was the cause)
Na
CHUCHUJAY ✍️
Book1⃣
Page 9⃣
AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL.
Cikin Yanayi na nutsuwa Haidar ke takawa domin isa office ɗin sa inda yake mai karban gaisuwar ma'aikatan sa yana miƙa musu cikin girmamawa , yana isa bakin office din sa Ya saka key domin buɗewa amma ga mamakin sa yaji kofar a bude ,turawa yayi yana mai tunanin Ko jiya bai kulle ba Ya wuce,turus yayi lokacin da Ya shiga office ɗin ,roses ya ganin an cicire su an rubuta Good Morning love da kuma tambari na heart,kan desk kuma dauke da food pack wanda ba a bude ba ,dan kalle kalle Ya fara dan ganin Ko zaiga giftawar wani ,a hankali Ya taka dan sake dubawa,kofar shigowa da yaji an buɗe ne Ya sakashi waigawa,Kiswa ce tsaye bakin kofar hannun ta dauke da leda yayin da fuskar ta ke dauke da babban murmushi,dafe fuska Haidar yayi yana mai sauke ajiyaar zuciyar ganinta Kafun Ya ƙarasa gareta hakoran sa washe kamar anma yaro kyautar candy.
Ledan hannunta Ya karba yana mai fadin"Good morning my romantic heartrob to what did i owe this?"
Faɗaɗa murmushinta tayi ta shigo ciki tana mai cewa"to love masoyi,i woke up naji yau ina san ka fara sakani a idanun ka idan kazo office ɗin nan and of course i made you breakfast dan na sanka da rashin san karyawa idan zaka fita office which you will have to work on dan idan mukayi Aure bazan dauka ba,yanzu abunda za'ayi ka zauna nayi serving maka breakfast Then na wuce aiki cos kar ka manta i work for someone and i cant afford being sacked".
Cike da wani irin santa dake faman fuzgarsa ya zauna inda ta masa nuni yana mai binta da ido fuskarsa dauke da wani irin murmushi na farin ciki da ya kasa cirewa ,.
Buɗe food pack din tayi ta ciro Kulan dake dauke da plantain mossa,sannan ta dauko plate ta saka masa guda uku manya a kai Then cutleries Kafun ta aje a kan cinyansa then ta ciro Cup ta buɗe karamun flask ɗin dake dauke da kunun gyaɗa a ciki ta zuba sannan ta dawo Gefensa ta zauna tace "bismillah hero and mind you sai ka cinye mossa ɗinn nan da kunun gyaɗan nan,"rufe idanunsa yayi ya buɗe yana mai shaƙar kamshin abincin dake gaban sa Kafun yace "my favourite,ya akayi kika sani ban taba faɗa miki ba idan Zan tuna"
Haɗa hannayenta tayi guri ɗaya tace "well idan ban san favourite abunda mijin da zan Aura nayi rayuwa ta har abada dashi ba mai ya kamata na sani?,well just eat already"
"What about you?"ya tambaya yana mai zuba mata ido.
Wani fari da ido tayi Kafun tace "well ni a ƙoshe nake burina kawai kai ka ƙoshi,"murmshi yayi yayi bismillah ya fara cin abincin Cikin nashaɗi, bayan ya gama Ya kalleta da soyayya yace"Allah yayi miki albarka Kiswa,Allah ya mallaka mun ke a matsayin matata uwar ƴaƴana wallahi ina sanki da yawa sannan a kullum sake sanki nake sosai ba wai so na wasa ba,dan Allah ki dage da yin Addu'a kema Allah yasa mu mallaki juna kafun mu koma ga mahaliccin mu".
Tashi tayi ta fara haɗa kwanikan kafun tace"na faɗawa Mama maganar ka jiya da mukayi waya and ta ƙosa na kawo ka Bauchi ta ganka,i can tell tun Kafun ta ganka kayi mata already"
Cike da zumuɗi yace"OmG Baby i love you ,dan Allah ki samu free time muje cos ni kaina yakamata na ga macen da ta haifa mun macen da bana da nutsuwa idan akanta ne"dan shiru yayi kafun yace"Yea kafun na manta ina ganin ya kamata ace by this time Mother ta san dani a rayuwarki sabida rashin sanin yasa ta samu Ummi jiya a office tana san haɗani da Farry na Aura and im sure dan bata san muna tare bane ,but i told Ummi jiya about us and tayi farin ciki sosai dan idan da dan ranta ne yanzu ma na kaimata ke ta ganki,ba kiga yarda take murna ba".
Jin maganar mother ta je gurin mahaifiyar Haidar tayi kamar almara,bata taba sunanin san zuciyar Mother ya kai har inda bata zato ba,kallan Haidar tayi da kyau cikin sigar boye abunda ke ranta ta saka wata dariya tace "so mother did that,gaskiya ya kamata yau na shigar da kai gida a samana rana dan yanzu mother taje cikin rashin sani gobe wanine zai je ."
Dariya ya saka sosai yace "ke yarrinyar nan mai kika maida ni,sai kace wani kaya a cikin Boutique din Ummi,well kima saka aranki babu wannan maganar tunda dai duk tallan yan matan da za'a kawowa mother sai na amince zata amince ,and you know my heart beats for only you,zuciyata idan tana bugawa babu abunda take ambato face Kiswy babbyyy".
Dariya ta saka sosai Ganin yarda yayi da fuska kana tace"idan na biye ka anan anjima zan baka labarin An koreni gurin Aiki bari kaga nayi harama.
Dafe saitin zuciyarsa yayi yace "ouch kinga kuwa ni Ai gaba ta kaini sai na daukeki a asibiti na na baki post ɗin Energy plug ɗina ,kawai nayi ta kallanki kullum kina banii Energy".pack ɗinta ta dauka ta kalleshi da kyau tace"get well soon Hayati ni nayi gaba and i love you".dariya yayi ya mara mata baya dan rakata inda ta aje motanta wanda ya jawo manyan Gulma, da yawan ma'aikatansa sunan ta suka sani basu san fuskarta ba,wasu su yabi kyawuntaa wasu su kusheta dama haka rayuwar dan Adam take.
Tunda Kiswa ta baro Asibitin Haidar take tunanin maganar Haidar na zuwan Mother gurin Umminsa dan talata masu Farry bayan ta sani cewa ita ɗin budurwarsa ce,da tunani kala kala ta nufi office inda tasan zata haɗu da sabuwar matsalarta Saleek dan jiya baki ɗaya bai shigo aiki ba Wanda hakan yayi mata daɗi sosai domin kuwa bata san fuskar da zata fara kallansa ita ba dan tagama making up zuciyarta akan faɗa masa gaskiya kafun ya riga nufan Appa ,tun shekaran jiya tsakaninta da Farry kuwa babu wanda yace da kowa komai ,
Tana isa kai tsaye office dinta ta wuce dan bata cikin mood ma na tsayawa doguwar gaisuwa da kowa ,shes so pissed to Spare a kind heart,zama tayi kan kujerarta tana inhaling deep breath a hankali tana san calming kanta,zuuciyarta wani irin zafi take mussamman idan ta duba iya tsawan rayuwar ta taga Babu abunda ta taba yiwa Mother da take kasa boye mata irin adadin tsanar da take mata ,this madness need to stop,din yarda ta kai da kawaici da girmama Mother akan Abunda take so bazatayi shiru ba,lokaci yayi da ya kamata ace ta yiwa Appa magana akan Haidar ya tura iyayansa ayi maganar Aurensu.,tana tsaka da tunani da zuciyarta taji An banko kofar office ɗinta babu excuse, a hankali ta daga idanun ta dan ganin wanene duk da kuwa tasan duk fadin ma'aikatar Babu maiyyi mata haka bayan SALEEK,ille kuwa shike Takowa hannayensa cikin Aljihun wandonsa,binsa tayi da kallo ,sanye yake cikin Suit grey wanda ya cire rigar suit din ya bar long sleeve din dake ciki fara tas,gashin kansa wanda dye ɗinsa brown Ya rage sosai a kwance gwanin burgewa,Takowa yayi ya Zauna kan kujerarta dake facing ɗinta Ya zauna yana Mai faɗin"KISWA UBAID,Niece ɗin Alhaji Aliyu Alijua,Yar asalin garin bauchi 24 years old turning 25 next month,cousin sister din sameer,Sageer da Faridha Aliyu Alijua,Kin karanci Public relationship a Nile university,Kin fara karatu da wuri Kin gama da shekarun haihuwa marasa yawa wanda ya baki damar achieving career ɗinki na yanzu,Kin samu aiki a AYZEL FOUNDATION exactly after service,Kina saurin fahimta da sharp brain a wurin waɗanda suka daukeki mutum,you're in a Serious damn relationship with Haidar Tukur Bula yaro ɗaya tilo gurin Costum Tukur Bula da matarsa Hajiya zainaba Bula a very rich business' woman,a gidansu suna tare da cousin sister ɗinsa Tasleem Haroon ,poor guy bai san macen da ya dauka rayuwa ba miciijiyace mai dafin tsiyarda idan ta kafa maka sai ka mutu. "
Ajiyar zuciya Kiswa Tayi tace"Saleek menene point ɗinka anan,baka tunanin bincike da kayi haka akaina ya shiga personal privacy ɗina,i mean you have no damn right"murmushi yayi yace "calm down baby girl kar kizo nan kice zaki ɗaga mun jijiyoyin wuya When you wronged me sannann shine worst abunda kikayi a rayuwarki da zai barki da dana sani".
Wani irin kallo tamasa Kafun tace "na dauki wannan threat Ko mene cos it sounds like one,"Kaɗa kansa yayi yace well bani da ikon hana ƙaramar ƙwaƙwalwarki yin tunanin da taga dama ,imma ki daukesa threat' Ko warning na abunda kika saka kanki Ko akasin haka matsalar kice Abu guda ɗaya na sani wanda shine Kin debo ruwan dafa kanki da kanki "kafun Kiswa tace wani abu an turo kofarta a hankali,kallan kofar tayi dan ganin mai shigowa yayin da Saleek Ko alamar kallan kofar ma baiyyi ba,cikin sanyin murya Kiswa ta furta "Farry?"
Takowa ciki Farry tayi tana mai cewa "look here babe banzo nan muyi faɗa ba,i came to apologise and..."kasa karasawa tayi lokacin da ta sauke idanunta Kan Saleek wanda shima ita ɗin yake kallo wadda a kallo ɗaya ya gane ta,haɗe rai yayi yace "im very pleased and glad you came here kinga sai ayi a gabanki afer all you're the mastermind "dan kallan Kiswa Farry tayi Kafun ta zauna kujerar dake facing ɗinsa Ta danyi murmushi tace "you must be Saleek right"haɗe rai yayi sosai yace"bai kama ta ace kina tamabaaya ta ba "
Cikin rashin nutsuwar ganin haɗuwarsa Farry tace"Nasan definitely abunda nayi bai kyautu ba sannan bazan boye maka ba nayi dana sanin abunda ya faru musamman da ya zama nayi involving innocent sister na ,i was not fair sannan banyi tunanin abunda zai faru ba,i was wrong so ina mai neman afuwarka da yafiyarka and domin gyarawa zamu iya magana da iyayenmu mu sasanta kan mu a shirye nake domin zama matar ka,a shirye nake domin gyara abunda na bata but please ina sake roƙonka da ka yafewa Kiswa We are Adults zamu iya gyara abunnan ba tare da kowa yaji ba.
Kafe Farry Kawai yayi da ido yana mai observing ɗinta da wani kanannaɗa da take kamar wata crayfish ajiyar zuciya yayi yace "kinsan wani abu,koda ace ke kikaje gurina ba ita ba bazan taba approving ɗinki ba domin you're not my spec ,You are not in my lane,you're not my type i mean ki kalli kanki a mudubi mana ,so Just shut the fuck up and get out of my issue, ita kuma sister ɗin naki da taje ta raina mun wayau zata biya da kanta dan haka idan kinsan abunda yake damunki ki cire kanki daga shirgina cos next time abunda zan miki bazaki so shi ba kar kice Ban faɗa miki ba and mark it bazan taba sanki ba ballanta na Aureki ,bana san mata masu tura kansu shamelessly ga namiji"kallansa Ya mayar kan Kiswa wadda take binsa da idanun takaici yace "ke kuma punishment dinki guda ɗayane ,zaki rabu da wancan likitan da kike faman yaudara sannan zakiyi dating ɗina har sai lokacin da domin kaina na koreki daga rayuwata ,zan bawa PA ɗinki ta kawo miki contract paper kiyi signing wannan shine hukuncinki nayi mun katsalandan a rayuwa idan kuma ba haka ba da kaina zan kai ƙararku gurin mahaifinku kunsan kuma mai zai biyo baya"
Yana kai ayar maganarsa ya tashi a kujerar da yake zaune yana mai bin Farry da wani irin disgusting kallo kafun ya saka kai ya fice.
System Kiswa ta jawo ta cigaba da aikin da take ba tare da tace Ko uffan ba,juyi Farry Tayi akan kujerar da take tana nazarin Saleek Kafun ta kalli Kiswa wadda tayi kamar ma ba mutum a office ɗin tace"Kiswah naga kamar maganar Saleek bata dameki ba ,yana san kiyi breaking up da Haidar ne fa,and to date Him is one stupid method of thinking a bangare guda,and God kinji abunda ya faɗa mun he is so mean and full of him self,to hell with him after all baya da abun bani he is Just a rat and chewgum sticking beside his father sakarai kawai,in kyau yake taƙama dashi nima ina dashi sannan yaje Ya tambaya irin mazan dake bina basa samu"A hasale ta kai karsheen maganar ta tana Kaɗa kafa guda.
Kallan ta Kiswa tayi kamar bazata ce komai ba da farko amma sai taga rashin amfanin yi mata shirun dan haka tace"i thought Kin tsani relationships sannan baki shirya sadaukarwa dake cikin sa ba,bai kamata ki cusa masa kanki ba daga ganin ya haɗu baki san halin mutum ba,to wannan baya da mutunci ba sai na faɗa miki ba saboda kunnuwanki Ai sunji irin cin mutuncin da yayi miki anan,had It been kinsan zakiji ya kwanta miki ai bai kamata ki tura ni ba in the first place wanda a yanzu nake mutuƙar dana sanin biye ki,and maganar na rabu da Haidar kuwa Allah ne yake da wannan ikon ba mutum ba duk girmansa duk surkullensa,idan kika ga kuwa mutum yayi sanadin rabuwata da Haidar to Allah ya basa wannan karfin amma ba yin kansa ba".
Cike da jin zafin maganarta Farry tace"kinga Kiswah bafa daureki nayi Ko na zare miki ido Ko na miki dole ba akan zuwa gurin Saleek ,i Just asked for a favor duk nacina idan baki je ba Ai bazan kashe ki ba,so kema kina da equal laifi da kin ƙi da dole zanje and im sure da wata maganar ake yanzu ba wannan ba".
Da mutuƙar mamaki Kiswah ke bin Farry da kallo tana san gasgata maganar daga bakinta take fitowa,ƙaramun murmushi Kiswah tayi tace "ba laifin ki bane Faridha laifi nane,da ace nayi refusing dinki da hakan bazai faru ba har ki zauna a gabana kina kallan tsabar idona saboda baki da kunya kina faɗin wai ina da laifi,Its okay ina da laifi da banje na kai ƙararki gurin Appa ba lokacin da kika nemi na taimake ki,laifi nane da banyi hangen nesa ba saboda rauni na akanki naje na miki abunda kike so dan haka kar ki damu zan gyara abunda na bata ,now get out of my office kafun nayi losing cool ɗina akanki".
Wani irin dogon tsaki Farry tayi tana mai karewa office ɗin kallo kafun tace "wannan abun kike kira office har kike wani faɗa mun na tashi na fita?ba sai kin koreni ba cos kinsan na wuce nan dama this place is suffocating me already and yes na me fuck up".tana kai karshen maganarta ta dauki Jakarta ta fita a office ɗin yayin da ta bar Kiswah da bin kofar da kallo cos jin abunda ya faru yanzu tsakaninta da Farry tayi kamar almara Ko mafarki mara daɗi.
TBC
CHUCHUJAY ✍️
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top