7

💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

   Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page7⃣

Da mamaki Kiswah ke kallan Saleek wanda ya bayyana gaban ta yana tafa hannunsa yayin da fuskarsa ke dauke da wani irin murmushin da take ji kamar ta cire masa Shi da tafin hannunta domin ba sai ya faɗa mata ba labe yayi mata,

Cike haɗe rai tace"na haɗu da maza kala kala amma Ban taba haɗuwa da ill mannared irin ka ba,bana tunanin ka samu tarbiyya sanin menene labe akan maganar wasu take nufi,idan kuma ka samu to a wannan gibar bakayi amfani da ita ba.

Wani irin haɗe rai Saleek yayi domin maganar ta tayi masa zafin da bai tunanin zatayi masa ba,cikin mutuƙar bacin rai yace"Ko Me zaki ce kar ki fara jimamin yama tarbiyya ta take Cos bana tunani Kin fitini ta wani guri Cos Your personality is a mess,kinsan bake nake tausayi ba shi wanchan guy din da ya wuce shine yake mugun bani tausayi saboda he's in a deep shit da yayi getting involved da Gold digging bitch kamar ki,Just imagine baki Ko jin nauyi da tsoran Allah,mata irinki mayaudara maha'inta babu waɗanda Ban gani ba,running from one man's pants to another.....

Marin da ta dauke sa dashi cikin hawaye shine abunda ya katse masa hanzari ,hannun sa ya ɗaga cikin fushi ya daki gefen motarta yana mai faman huci kan ya kama hannunta da karfi yace"This should be the last time da zaki kuma daukan wannan hannun naki mai kama da bulaliyar kara ki taba fuskanta,sannan ki gode ma Allah bana dukan mata da yau sai na fasa miki baki,and for Your information i heard it jiya kece kika je date dina wanda dama na sani i would never be wrong ,ki shirya saboda i will sue you for slender idan ba haka ba ba sunana Saleek ba "

Sakin hannun ta da ya damƙe da karfi yayi ya juya a fusace yana mai fadin"useless girl".

Kuka ta rushe dashi tace"you're the must useless stupid jerk I've ever meet sannan idan ka sake shiga hurumina Zan ci maka mutunci fiye da tunanin ka,wawa kawai"

Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da tafiya zuciyarsa kuma na masa wata irin zafi da ƙuna na tabbatarwa da yayi cewa Kiswa itace taje gurin sa jiya abunda kuma ke sake soya masa zuciya shine rashin sanin dalilin yin hakan,tunanin sa ya fara bashi kilan dan kuɗi tayi,maimakon ya koma ciki sai ya shiga motan sa ya bar harbar gurin zuciyarsa nayi masa wani irin tuya da ba zai iya fasaltawa ba.

   ******

SALEEK BASIL MADUGU babban ɗa a gurin Chairman Basil Madugu da matarsa Hajiya Asiya,asalinsu mutanen cikin Kauyen Gwagwalada ne dake cikin garin Abuja,mahaifinsa Chairman Basil ada talaka ne wanda idan ka kallesa a yanzu da da zaka daɗe kana karyatawa akan bashi bane waninsa ne,rayuwa yayi shida matarsa da yaransu guda ɗaya Habib cikin yan uba wanda suka sakashi gaba cike da tsangwama da takura musamman da 'ya kasance shine bashi da komai ,rashin jituwa da kuma rashin daɗin zama shine ya fito da Chairman Basil daga cikin Gwagwalada inda 'ya tarar da Alherin sa cikin garin na Abuja,Rayuwa da daɗi babu daɗi haka ya dage wajen ganin ya gina rayuwar yaran sa Habib da matarsa Asiya mai hakuri da juriya,lokaci ɗaya ciwan cancer ya kama Habib ta kwakwalwa wadda ke neman maƙuda kuɗin da za'a shawo kanta amma duk yarda ya buga ya buga a kulle ga dukkan wasu samuwarsa ta ta'allake kan ciwan na Habib,ganin abun yaci tura ga habib na buƙatar a fitar dashi kasar yasa ya koma gida domin a siyar da gadonsa a raba a bashi amma abunda ya tarar yafi na da domin kuwa karyata kasan cewarsa jinin mahaifinsa sukayi sannan suka masa korar kare,baƙin ciki goma da ishirin komawarsa gida ya tarar da gawar Habib,yaci kuka iya kuka domin shi daya Allah ya basa ga kuma bakin ciki Na karyata identity ɗin sa da yan uwansa sukayi bugu da ƙari har da manyan garin waɗada suka san tabbas Shi ɗin jin mahaifnsa ne amma suka juya masa baya saboda abun duniya,yayi fushi mutuƙa wanda ya sakashi rantsuwar babu shi babu danginsa har abada,a haka ya rungumi matar sa suka cigaba da rayuwa inda 'ya samu wani uban gidan da yake aiki karkashinsa cikin aminci da amana,a hankali arziƙi ya fara zuwar masa kasancewar 'ya samu uban gida na gari mara mugunta ,yana da nasibi na kasuwanci dan a kome 'ya taba sai albarka ta sauka cikinsa,lokacin da ya samu shago na kansa Asiya ta samu cikin Saleek wanda Chairman Basil ya kwallafa rai akansa ,kulawa ga Asiya kuwa sai tafi ta da a haka har ta sauke cikin Saleek wanda suka dauki san duniya suka ɗora masa,haihuwar Saleek kuwa kamar an ƙara masa arziƙi haka arziƙinsa ya cigaba da habaka,kafun kace mene abun yasha banban Dan shi mutum ne maiyi da gaske,Ko ta ina kasuwanci zuwa masa yake ana damawa dashi,

Lokacin da Saleek ya shiga shekara goma Asiya ta samu ciki lokacin kuwa arziƙi yafi na da Dan Mijinta mutum ne mara mugunta,cikinta na shiga wata tara ta haifi tsankaɗeɗiya yarinyarta mace wadda taci suna Amatul'islam ,baya ga nan likitoci suka tabbatar wa da chairman Basil haɗarin dake ga sake daukar cikinta saboda wahalar da tasha ga girma Dan haka ya hakura da haihuwa suka rungumi yaransu biyu cikin kauna da tarbiyya dai dai gwargwadon da baza'ayi Allah wadai da iyayensu ba, haka nan suke rayuwa mai inganci inda Suke bawa yaransu kuma karatu mai kyau kar ma ace Saleek dake kan gaba a karatun,cikin kiftawar ido Chairman Basil ya fara planning company dinsa wanda cikin aminci abun 'ya bawa kowa mamaki,a haka ya fara gina kasuwancinsa da haɗaka ta mutanen da baya tsammani,lokacin da Saleek ya isa shiga secondary school mahaifinsa 'ya juya akalar karatunsa ƙasar Australia inda yayi baki ɗayan rayuwar karatunsa har masters,wanda lokacin da ya kammalata ya dawo da akalar rayuwarsa ƙasa Nigeria domin taya mahaifinsa gina legacy ɗinsa,

    Saleek irin mazan nanne haɗaɗu masu san gayu waɗanda Kana kallansu sun san kan gayun,haduwarsa ta saka yake sace zuciyar yan mata wadda Babu inda yake kaisu saboda a nashi yarda da kan"he's not ready for commitment of any sort,ya dauki relationship bata lokaci musamman idan ya kula da san kuɗi irin na matan yanzu,maganar kuwa wani true love or shit bai daukesa da gaske ba,he Just dated have fun in the Name of dating Then ya Kana gabansa ,although dating ɗin da yake is platonic amma 'fa ba Shi yake nufin he's Serious about you ba,lokaci kaɗan zai rabu dake ki ya kama gaban sa,shiyasa lokaci da dama yake daukan hakan bata lokaci ya share yan matan,"

Duk wani kuɗi da suke dashi baya taba mantawa da asalinsa Shi yasa baya daga cikin masu fariya da almubazuranci dan kawai yana dashi,a kallo daya zaka masa kallan marasa ji amma a zahiri kuwa mutum ne Shi mai sanin ya kamata wanda baya wasa da addinin sa,he's a very religious man abunsa guda ɗaya wanda yake fama dashi shine fushi,yanzu zaiyyi losing temper ɗinsa musamman idan abun yazo da an raina masa hankali Ko anyi wasa da tunaninsa kamar dai yarda ta kasance bangarensa da KISWAH.

Dama dai ɗan Adam baya taba cika goma taran nan dai haka yake dole ka sameshi da flows.

                            ***********

    Kiswah bata bari abunda ya shiga tsakaninta da Saleek ya hanata zuwa gama Abunda yake a wuyanta ba,bayan gamawarta kai tsaye reserving inda zatayi having dinner da Haidar tayi saboda she needs to clear up her head ,gidan ta wuce domin freshing up kafun ta je gurin cin abincin,

Tana shiga falo ta tarar da Mother da Appa suna zaune suna hira gwanin Ban sha'awa,duk da girmansu amma akwai wannan shaƙuwar tsakanin su,da far'arta tayi musu sallama inda Suka amsa a tare harda Mother wadda abun yazo ma Kiswa a bazata,

Gaidasu tayi kana tace "sannunku da gida"alamu Appa yayi mata da hannu yace "yauwa Kiswah zo zauna abun kirki ne da Mother take san yi wanda ya sa ni jin daɗi har raina,zo kiga picture ɗin nan "

Babu musu ta taka dan zuwa ganin hoton dake tab ɗin hannun Appa ,namijine wanda kana kallansa kasan yaje ma 40s ɗinsa,kallan Appa da Mother  tayi kafun tace "Wane wannan ɗin Appa im i suppose to know Him?"dafata Mother tayi tace"of course hayatee dan hes Your husband to be sannan Ban zaba miki shi ba sai da na tabbatar da cewa na gamsu dashi da halayyarsa"hes from our firm,sunan sa Barrister Aliyu maitama,very calm young and collected man,recently matarsa ta rasu ,suna da yara biyu so he talked to Me about you nace masa ya bari naji naki dan bazan mikii dole ba duk da Nasan baza ki taba ƙin decision ɗina ba ,trust Me Aliyu is a very nice man,kinga idan waccan yar uwar taki taga Kin motsa she have no option da ya wuce ta motsa itama you guys are hitting 25 and yet still Single.

    "But im not single mother"Kiswa ta tsinci kanta da faɗa"gyara zama Appa yayi yace "okay this is getting more interesting,so dotana is not single yet bani da koda slightest information akai?"

Saurin tare ta Mother tayi tace"so dama kana rasa su da samari masu hure musu kunne ne my dear?"Ai dama akwaisu amma Na Auren ne babu Wannan kana ganinsa ba sai an fada maka ba wasa yazo ba and na tabbata zai riƙe Kiswa cikin Aminci.

Sake kallan Appa Kiswa tayi a karo na biyu tace "Appa ina da wanda nake tare dashi sannan Ko yau akace ya fito zai fito,nice dai Ban basa dama ba...dukan cinya Mother tayi ganin Kiswa zata baro mata ruwa tace"Its okay take Your time ,and Kije ki sake tunani akai and bazan so ace Appa ya fara jin wanene lucky guy ɗin nan ba,zamuyi magana Then zanwa Appa ɗinki magana"wani irin kallo Kiswa ta bata tana hango tsanarta kiri kiri a cikin idanunta,tashi tayi tace to Mother bari naje na watsa ruwa,jikinta a sabule tabar gurin tana mai jiyo Mother na janye hankalin APpa daga maganar da ta fara,abu guda ɗayane bata sani ba,akan Haidar ta shiya fito na fito,dan bazata bari a tauyeta ba akan rayuwar da zatayi da namiji a matsayin matarsa,

Tana shiga ɗaki ta tarar da wayar Farry na disco daga bathroom kuma tana wanka tana bin waƙar,"ƙaramun tsaki tayi ta shiga walk in closet ɗinsu domin cire kayan jikinta"bayan ta fito ta tarar da Farry tana drying jikinta,kallanta tayi zuciyarta na mata wani irin zafi tace"Amma Farry kinga kiran da na ringa miki earlier amma baki damu da ki biyo ni ba kiji menene ,ba kuma daukar wayarkine bakiyi ba cos yanzu ma waƙar banza kikeyi kina bi kina cikin banɗaki".

Kallanta Farry tayi tace"Kiswah free me abeg,kinsan irin abunda 'ya sha kaina kuwa yau gurin aiki,and i saw kiranki daga baya ban kiraki ba saboda Nasan dole guri ɗaya zamu Ƙwana.

Tsaki Kiswa tayi tace "dont give Me that attitude,kinsan ai ba duniya zaki bani ba dazan ta kiranki adadin wanda na miki tunda ba mahaukaciya bace ni dole akwai dalili,wani kallo Farry ta bata kafun tace"Abeg Kiswa kar mu fara ni da ke kowa yana buƙatar hutu to mu huta mana ".

Kiswa bata kuma cewa komai ba ta shiga bathroom domin yin wanka,bayan ta fito Ko kallan Farry Batayi ba ta shiga closet ta dauko riganta dinkin Bubu ta saka ,tana kan saka pin barimar da ta dauko Farry ta taso tazo inda take lokacin da idanunta suka sauka kan Diamond necklace ɗin da Haidar ya siya mata ,saurin saka hannu Farry tayi tana mai cewa"girl who gave you this"?

Hannunta Kiswa ta buge tace"don't touch my stuffs cos wallahi zan bata miki,tunda ke baki da kirki,kanki kawai kika sani,Kin saka ni a mess wanda danke na shiga amma saboda san kai bazaki ma saurareni ba wato naje nasan abunda zanyi, to ki sani Saleek yaron da Appa yayi fixing miki date dashi naje maimakonki Boss ɗina ne a gurin aiki,sannan he knows cewa bani ya kamata ace naje ba,'ya ganeni so ki shirya yiwa Appa bayani dan zan faɗa masa komai na ɗauki duk wani hukunci da zaimun it doesn't matter any more"

Juyawa tayi ta dauki jakarta tana Mai sake duba wayarta dan bata san tayi dare a waje Shi yasa ma tayi fixing dinner ɗin seven dan ita ke nunawa kanta ba dai dai ba amma indai ta Mother ne to ta kwana waje,bata waiwayi Farry dake tsaye cikin rashin sanin Mai zatace ba ta nufi sashen Baba baraka domin yin sallarn Magreeb Kafun ta fita.

Bayan ta idar ta nufi sashen Mother domin sanar mata da zata fita duk da tasan Ko a jikinta,ille kuwa da ta sanar mata din cewa tayi"ba damuwa ta bace kawai dai ina sake baki shawarar using protection sabida komene kikayi a gari mu za'a zaga,so enjoy it while It last"

Irin maganganun nan na Mother suna shigar mata Zuciya amma ta zabi datayi ignoring domin tasan abu ɗaya da Mother ke so shine lalacewart da yin Abunda Appa zai Allah wadaran da ita wanda tayi ma kanta Alkwarin bazata taba bari ba insha Allahu.

CHUCHUJAY ✍️

08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top