6
KISWAH
(Surrogacy was the cause)
Na
CHUCHUJAY ✍️
Book 1⃣
Page6⃣
Daga kai Kiswa tayi dan ganin wanda ya shigo,ras gabanta ya fadi lokacin da idanunsu ya sarke cikin na juna,
Nemo murmushi tayi gudun kar ta bada kanta tace "Sir barka come in ,feel free,have a sit"
Wani irin murmushi yayi wanda baya rabo dashi ganin yarda take raina masa hankali,Takowa yayi ya zauna kan kujerar da ya tabbatar tata ce ya wani juya kafun ya dawo direction dinta yana kallanta,Name plate dinta ya ɗaga wanda ke rubuce da KISWAH UBAID a ƙasan sunan kuma an saka Public relation officer 1,shafawa yayi a hankali kafun ya kalle ta yace"idan da za'ace maimakon karatun da kakayi wasan kwaikwayo kika karanta na tabbata zaki ci abinci mai kyau a gurin,im impressed i must say,Kin iya wasa sannan wasan naki ya burgeni,abu guda ɗayane kika yi a cikinsa wanda nake kira ganganci wato wasa dani da shiga hurumin da ba naki ba,ni ba mutum bane mai boye boye ko kwana kwana dan haka zan tambayeki sau ɗaya ki bani amsa ,wacece ke sannan mai kikeyi a Blind date ɗina maimakon wadda ya kamata ace taje?"
Ki fara bani amsa wadda babu karya cikinta domin kuwa idan na kwace bazaki gane ni ba,behind murmushin dake fuska ta akwai wani abun.
Kafafunta taji sun fara rawa gudun faɗuwa ya sakata zaunawa kujerar da tayi masa tayi ta nemo dukkan wani yanayi wanda zai saka ta karyatashi ya yarda tace"Naji daɗin haduwa da kai mutuƙa amma inaso na sanar da kai ,na gamsar da kai akan cewa Bansan maganar da kake yi ba ,blind date or what kake magana bansan anything about it ba ranar ma ina gwagwalada"Haɗe rai tayi lokacin da ta kai karshen maganar ta.
Dariya yasa sosai wadda ta saka ta maida kalllan ta gareshi,sake hade ranta tayi tace"bansan wanne ne abun dariya ba a cikin maganata with all due respect sir,"
Nunata yayi da ɗan yatsa yace"exactly with all due respect my dear,bani da isashen lokacin da zaki zaunar dani anan kina mun karya Cos dana zauna a nan bance miki ga ranar da nake magana akai ba So ya akayi kika san ranar da blind date ɗina yayi taking place?"
Haɗe rai tayi ta saka serious face tace"well abunda baka sani ba you're the talk of the company So bana tunanin da wanda bai san ka dawo an hada maka blind date ba ranar Sunday,any ways you're highly welcome sannan ina fatan bazan baka wani reason da zakayi complaining dani ba a iya kacin aikin da zanyi da kai,its your welcome lunch today if you will excuse me dan ina san zuwa gurin da mukayi reserving dan duba abunda ba'ayi ba domin faranta maka shine first priority ɗin mu a yau"
Tashi tsaye yayi ya kalleta da kyau ya sake darawa Kana ya tako inda take yace"deny it duk yarda kike So amma ina san kisan abu guda daya zan kamaki kuma zan hukuntaki fiye da yarda baki zato,Its a pleasure meeting you Dear KISWAH UBAID"
Yana kai ayar maganarsa ya fita inda ya bar KIswa da wata irin faduwar gaba,wayarta ta jawo ta cigaba da dialing numbern Farry amma still bata dauka ba,cikin gaggawa ta tura mata saƙon "Call Me back Asap".
Jakarta ta dauka ta fita a office din 'dan zuwa duba gurin da aka tanada domin taron,tana fita ta tarar da Saleek 'na magana da wani saurayi wanda bazai wuce shekarunsa ba,ganinsa kawai sai da ya haifar mata da faduwar gaba,tabbas Farry ta saka ta a chakwakiyar da bata san ta inda zata fara tunkarar ta ba,amma abu daya ta sani wanda shine dole tasan yarda zatana avoidinq SALEEK ko yaya ne,saita kanta tayi ta cigaba da takunta 'dan wuce su amma kafun ta ƙara taku ɗaya daga bayan su Saleek ya kira sunanta yana mai cewa "yauwa Kiswah meet Khalifa my best man And PA,Khalifa meet Kiswah pride ɗin Abba cikin company ɗin nan,"cije lebenta na ƙasa tayi tana mai jin kamar ta ruga da gudu,ajiyar zuciya tayi ta juyo tana mai saka fake smile ta kalle su tace"Good morning Its nice meeting you".
Murmushi Khalifa yayi ya miƙa mata hannunsa yace"the pleasure is mine angel".
Kallan hannun nasa tayi sannan ta kalli fuskar SALEEK wanda ke faman wani irin smirking wanda bata san mai ya kunsa ba,dawo da kallanta tayi kan Khalifa tace"im sorry but i dont do hand shakes"
Wata irin dariyace ta kwacewa SALEEK wadda sai da yasaka hannunsa ya rufe bakinsa kafun yace "says a girl who smoke".
Wani irin kallo ta bashi na takaici kafun tace "excuse me"bata jira mai zaice ba ta wuce su tana mai runtse idanunta ,ta sani ba sai an faɗa mata ba she don fuck up.
Bayan wucewarta Khalifa ya Kalli SALEEK yace "Man that was rude mene nayiwa innocent statement dinta dariya,ni ta burgeni Cos she values abunda addininta ya hana so Ban dauke sa big deal ba 'dan tayi rejecting handshake".
Wata Dariyar Saleek ya saka kafun ya dafa kafaɗarsa yace "calm down man kar kyanta ya ruɗeka ka fara tunanin zura jiki dan nasan halinka da mata wannan yarinyar kuma da kake gani She's not who she seems to be akwai wani abu behind her wanda tabbas zan gano menene shi".
Wucewa yayi shima ya bar Khalifa da sake saken abunda yake nufi.
*****
Kamar yarda chairman baiyi expecting flows ba Haka nan taron da aka ƙirkira domin Saleek ya tafi perfectly kowa yaci to his own satisfaction sannan chairman yayi speech mai karyar da jikin mai sauraro inda yake sake shaidawa kowa a gurin Shi talakane a da wanda abincin da zai saka ma a baki yake wahala ,yarda 'ya gina FOUNDATION ɗinsa from Scratch ,using tears,sweats and blood sannan yake farin ciki Na zuwa ya huta domin bawa magajinsa guda wannan gurin dan tayashi gina legacy ɗinsa,
Tafi gurin ya dauka Kana Saleek yayi nasa speech ɗin inda yake assuring zai bada gudunmawar da mahaifinsa zai alfahari dashi,fatansa guda ɗayane shine hadin kan ma'aikatan domin kuwa sai dasu komai zai zama masa dai dai,
Haka nan welcoming lunch ɗin Saleek ya kasance cikin jin daɗi yayin da yan matan kamfanin ke ta koɗa haduwarsa da humbleness ɗin sa,not like a regular young arrogant And snobbish billionaire.
Bangaren Kiswah kuwa hankalinta ta maida kan abunda ya dameta dan idan zata ɗaga kai sau dubu sai idanunta sunyi arba da Na Saleek ,wayarta ce da tayi ƙara ta bata damar tashi a gurin dan zuwa amsa kiran wanda baki daya yau bataji muryar sa ba,bayan zuwanta inda babu hayaniya ta ɗaga wayar tana mai fadin"ran abun alfaharina ya dade"
Murmushi yayi daga ɗayan bangaren yace"come down stairs "sake maƙala wayar tayi a kunneta ta lumshe idanunta tace"kazo company ɗin mu hala,And muna throwing ma yaran chairman ɗin mu welcoming lunch but give Me a Moment yanzu Zanzo ina sameka don a gaba kake da abunda nake yanzu a rayuwana".
Wata irin ajiyar zuciyar jin daɗi Haidar yayi saki kafun yace"babyyy kina tunanin zan taba mistaking inda kike bayan kina tafiyane da akalar tunanina da alamurana,so get down And see your man"
Kamar yana kallanta ta saki wani irin murmushi mai sanyi kafun ta fara takawa domin sauka ƙasan da ya bata umarni tazo,
Tana barin gurin Saleek dake boye yana sauraran wayar da take ya fito daga gurin boyansa yace "so she even have a man,well muje zuwa a yau sai na san wacece ke And menene dalili ki da hujjarki na aran identity' ɗin wani,Cos dole yasan Kiswah version is her identity not Faridha".
Tana sauka ta fara ɗaga ido tana neman inda zata hango Haidar,har lokacin wayarta na kunneta bata cire ba,taune lebenta na ƙasa tayi tace "Baby just show your self mana ,"murmushi yayi yace kizo inda kikayi parking motan ki,Babu musu ta taka inda ta aje motan ta tana cewa "i hope you're not playing any frank"tana isa figure din sa yayi mata sallama jingine jikin mota irin tata sak komai da komai,maida hankalinta tayi kan tata motan Wadda ke aje inda ta aje ta Kafun ta sake maida kallanta kan HAIDAR wanda ke faman kada key a hannunsa yana mai bata expensive smile ɗinsa mai kasheta,
Cire wayarta tayi a kunnenta tana mai kallansa cikin ido tace"okay now tell Me motan wanene wannan kuma"?
Murmusawa yayi har haƙoransa na fitowa kafun yace "tawa of course,na siya mota ne irin taki dan na nuna miki zan iya zuwa ko wanne level akan ki muddin nan kike san muje,i dont mind na ringa hawa okada indai kema Shi zaki hau ,so daga yau bazan sake hawa wani luxurious car ba sai wadda kika hau ,so daga yau ga motan Haidar nan masoyin Kiswa".
Cike da kulawa ta matsa kusa dashi tace"habibi this is not necessary and i told you wasa kawai nake maka ,you dont have to stood to this so abunda ya hanaka nemana koda jiya kenan ka fita da Farry".
Kashe mata ido guda ɗaya yayi yace"Well ina san baki surprise ne so Farry ta rakani siyan mota irin naki And We went for lunch after that,she was teasing Me wai na fara tunani irin naki ,kinsan Shi soyayya babu abunda bata sakawa,a nawa bangaren kuma soyayyata takice komai kuma zan iya domin zama dai dai dake so tell Me Farry tace mun you went on a date ,who was it with,it doesn't matter idan ex boyfriend ne,stalker Ko crusher cos duk zanji dasu dan yanzu you're mine i just cant wait to mark you kowa ya gani ya fahimta"
Dariya ta saka ganin yarda ya kare maganar tasa Kafun ta jiingina ita ma da mota tace"business date ne naje so calm down kar ka fasa ma mutum baki cos Ba sai kayi marking dina ba duniya zata san ni takace And only yours,juyo da fuskarta tayi tana kallansa tace'i really do love you habibi ,bana ganin Ko wanne namiji a matsayin kallan da nake maka,i can give up my everything for you idan da bukatar hakan,my identity,my work ,my life and everything indai iyuwar hakan ta kama,but kamar yarda kasan sirrin zuciyata da irin raunin da take akan ka ina roƙonka kar ka karya ta,Ban san soyayyar wani da namiji ba bayan kai bama mahaifina ba cos ban ma rayu dashi ba ballantana Nasan dadin soyyyarsa".
Dan shiru Haidar yayi yana kallanta,da ace tasan yarda zuciyarsa ke fitinar santa da bazata taba kawowa zai karya tata zuciyar ba wata rana,kallan sa itama take inda ta hango moist na ƙwalla a gefen idanun sa, nuna sa tayi da ɗan yatsa tace"habibi mene a idanunka kamar hawaye?"
Saurin gogewa yayi yana mai cewa"Na sanki ne kafun ya saka dariya yace"how wish nayi recording confession ɗin nan na bazaki iya rayuwa Babu ni ba for future use.
Dariya suka saka a tare Cos sai a karshe dukkan su suka bama juna dariya,juyawa yayi ya buɗe motan yana mai fadin"kar na manta da kyautar ki,"
Dan shagwabe fuska tayi tace "kai kam baka gajiya da batani da kyauta kullum idan zaka zo gurina"
Ciro dan box yayi daga motan yana mai cewa"well ba hakarum bane idan nayi spending ma matata kuɗi after all ina dasu kuma dan na kashe miki nake nema,"miƙa mata box ɗin yayi da ƙaramar package bag ɗin da yake ciki yace ba yawa.
Ƙarba tayi tana cewa"awnn you're such a durlyn,tana buɗe wa idanunta suka ci mata karo da diamond necklace dake ta faman sheƙi"saurin kulle box ɗin tayi tana mai kallansa tace "no no Baby i cant take this"
Motansa ya buɗe ya shiga ya mata key kafun ya kalleta ya kashe mata ido daya yace"you're welcome and i love you to the Moon and back,kiss yayi blowing mata da hannu kafun yace "na samu charge dina ta hanyar ganinki ,kinga yanzu Zan iya aiki cikin walwala Babu kasala,
Ɗaga mata hannu yayi ya kunna motan yana mai bata murmushin nan nasa mai kyau,itama murmusawar tayi tana mai ɗaga masa hannu kafun ta ciro wayarta ta tura masa saƙon"lets have dinner ,Its on me".kallanta yayi yayi saluting dinta bayan ya kashe mata ido daya kafun yaja motarsa ya bar harabar gurin.
Tsaye tayi tana sake duba sarkar da ya bata tana murmusawa cike da shaukina inda a zuciyarta take addu'ar Allah ya sa hutunta yazo mata da wuri shekararnan taje Bauchi ta fara bawa Mamanta labarin Haidar ,ya kamata tasan da labarin wanda ke kaunar ƴarta fiye da yarda yake san kansa its high time,tafin da taji anayi a bayanta shine abunda ya katse mata hazari ta juya...
TBC
CHUCHUJAY ✍️
08130229878.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top