5

KISWAH

(Linked By surrogacy )

                Na

CHUCHUJAY ✍️

Book 1⃣

Page5⃣

  Monday Morning.

Safiyar litinin ya kasance Kiswa bazata fita aiki da wuri ba sai 10 da rabi dan haka bata fito breakfast ba lokacin da dukkan su sunayi sai wurin Tara wanda lokacin kowa na gidan ya fita har da Baraka mai Aiki wadda ta tafi kasuwa domin siyan kayayyakin da Babu 'na amfani.

Fridge ta buɗe domin dauko fresh milk dan ita kawai zata iya sha tunda bata craving wani abinci mai nauyi Cos yau suna da lunch Da chairman Basil ya shirya a kamfanin ta tarbar ɗansa da zai fara zuwa office din yau.,tana kan danna wayarta a yayin da take shan fresh milk din taji kamar ana kallanta,daga kai tayi sabida yarda jikinta ya cigaba da bata Eh tabbas ana kallanta ɗin,kan ya Sageer ta sauke su wanda ke tsaye in a mess Cos daga ganinsa ba sai ya faɗa maka ko wanka baiyyi ba,singlet ce baka a jikinsa sai boxer wanda ke nuna mazantakarsa ta ɗa namiji wadda turawa kewa laƙabi da" morning bone"saurin dauke idanunta tayi cause This is not like Him.

    Ganin abunda tayi ne ya sakashi yin karamun murmushi kafun ya tako yana mai dauko Cup ya karbi kwallin fresh milk ɗin gefenta ya zuba 'ya fara sha yana maiyyi mata wani irin kallo kafun yace"Kiswa baki ganni bane babu ko gaisuwa"?

cup dinta ta kai cikin sink tana mai kunna tap dan wankewa kafun tace"ina Kwana 'ya Sageer baka fita ba ashe ,And Yes you need to get dressed dan you're semi naked,Nasan nima dan baka expecting dina a nan ne ka shigo hakan ,nima yanzu nake san wucewa gurin aiki ,hope you're okay "Murmushi yayi kafun ya tako inda take shedan yana hura masa wata irin sha'awarta wadda ya jima yana faman dannewa,aje nasa cup din yayi cikin sink din sannan ya zauna a gefe yana mai kallanta tana ɗauraye nasa cup din,hannunsa yasa a hankali ya shaafa nata wanda taji zuwan a bazata ,ɗago kai tayi ta kallesa ta ɗaga masa gira ɗaya tace"lafiya dai ya Sageer"?

Cije lebensa guda ɗaya yayi yace "lafiya ba lafiya ba,taimako ne nake san kiyi mun wanda ke kadaice zaki iya yinsa a duk duniyar nan".

Da mamaki ta kallesa sannan ta taka Dan zuwa aje cup din a ma'adanarsu tana mai cewa"Nikam 'ya sageer wanne irin taimako ne da ni Kaɗai zan iya yinsa duk duniyar nan?Just shot it Allah yasa wanda zan iya ne dan bana fatan wani dan uwa na ya nemi abu gurina na kasa masa kar ma ace 'Kai,'ya sameer ko Farry ,sai dai idan yafi karfina ko kuma ya sabawa mahaliccina".

Taune lebensa na ƙasa yayi kafun ya sa hannunsa yana mai rufe gabansa da ke neman fita masa,yana ƙokarin magana muryar Baraka ta katsesa wadda ta shigo kitchen din kai tsaye saboda mantuwan pack ɗin da tayi,a tare suka daga Kai suka kalleta, sallama tayi Kiswa ta amsa tana Mai fadin"baki wuce ba ashe baba baraka"

Kallan Sageer tayi kafun tace"wallahi har naje titi nayi mantuwa na dawo,ashe Alhaji karami ma bai fita ba"wani banzan kallo Sageer ya bata ba tare Da ya tanka ta ba ya  sauko yana Mai kakare gabansa ya rabe ta gefenta yana Mai cewa Kiswa"sis chat you up later"

Okay kawai tace masa tana Mai binsa da kallo saboda ba Haka ta san ya SAGIR ba,tabbas wani abun ba dai dai bane ba,shigowa Baraka tayi itama tana Mai binsa da kallo kafun ta dawo da kallanta kan Kiswa tace "kiswatu Anya sagiru kalau yake"?'dan tabe baki Kiswa tayi tace nima dai Bansan Mai ke damun sa ba Cos ko niyar fita aiki banga yana da ita ba kilan dai yana da uzuri ne,dauko pack din nan rage miki hanya Cos nima yanzu zan fita,

"To" kawai baba Baraka tace amma yanayin sagir da yarda ta shigo taga yaana kallan Kiswa abu ne da a matsayinta na babba tasan akwai wani abu a ƙasa,har suka bar gidan ita da Kiswa abun yana ranta tana tunanin ta yarda zata fara fadarsa,kasa hakuri tayi domin tana ganin Kiswa ne matsayin diya a gurinta 'dan haka bazata iya ganin abu zai cutar da ita ba ko ba dai dai ba tayi shiru dan Haka cikin hikima irin ta babba tace"Nikam kiswatu ina san faɗar wani abu ina tsoro Ban san ya zaki dauki magana ta ba"

Kallanta Kiswa tayi kafun ta mayar da hankalinta kan tukin da take ta 'dan murmusa tace "Baba Baraka ai ke uwace ko me zaki faɗa mun bazan taba jin haushi ba dan Nasan duk abunda zaki fada gyara ne".'dan gyara zama Baba Baraka tayi tace"nasan ke da yaran Alhaji babu bambanci sannan ku din yan uwan juna ne wanda nake fatan kar wani ya cutar da wani,a gaskiya yau yanayin da naje na riskeki da sagir da yanayin da yake da kuma kallan da yake miki bai gamsar dani ba,bakiga yarda mazantakarsa ke neman fasa wando ba dan banza suyi Aure sun Kai munzali sunƙiyi,ba wai ina san hadaki dashi bane saboda nasan shakuwar ku ta yaran gidan nan amma ina So a kullum ki ringa sakawa a ranki ke dasu ba muharramai bane tunda zasu Aureki basu Auri Farida ba,idan magana ta bata miki dadi ba kiyi hakuri amma wai dama nayi gyarane".

    Murmushi Kiswa tayi tana Mai packing bakin super market ɗin da Baba Baraka zataje Kafun tace"Baba Baraka ki daina bani hakuri sannan ai maganarki gaskiya ce ba ƙarya ba nasan cewa ba muharramai na bane ,amma abu guda daya wanda na yarda dashi shine na yarda dasu da rayuwata,irin yardar da nayi musu yarda nasan Babu wanda zai kalleni da wani tunani mara kyau a zuciyarsa insha Allah,yarda kuma kika tunatar dani ,insha Allahu zanyi ƙokari wajen ganin na kula"

"Allah ya duba yardarki dasu Ƴar nan"shine abunda Baba baraka tace kafun ta fita tayi wa Kiswa sallama ta wuce,bin ta Kiswa tayi da kallo tana nazari a yayin da guri guda kuma take ƙaryata duk wata wasiwasi da ke ɗarsuwa a zuciyarta,take kuma maganar Ya Sageer na taimakon da zatayi masa ya fara mata yawo a ƙwanyar ki,"shin wanne irin taimako yake bukata gareta har yake ikirarin ita kaɗai zata iya yi masa shi?"sanin baya nan da zai bata amsa 'ya saka ta ja motarta dan tafiya Aiki Cos tasan koma menene zai nemeta .

          **

Kamar kullum yarda ta saba gaisawa da abokan aikinta yau ma hakan ta shiga Building ɗin cike da fara'a yayin da take gaisawa da duk wanda taci Arba dashi a hanyarta ,tana ƙokarin shiga office dinta sakatriyarta Amira ta tareta tana mai faɗin "Ina kwana ma ,barka da shigowa yanzu chairman ke nemanki na faɗa masa baki shigo ba da wuri cos yau 10 zaki zo",cike da girmama Amira ɗin tace"hope im safe ,sannan kinyi forwarding documents ɗin nan zuwa ga office ɗin chairman."?

Ƙaɗa kai Amira tayi tace"Nayi Ma'am and as the gossip is going on and on kamar yaran chairman yazo office yau zai fara aiki kafun chairman yayi masa handing over,"ƙarasa maganar tayi cikin ƙasa ƙasa da murya tana mai faɗin"And guess what rumours said he's dead Handsome".

Dariya Kiswa tasa tace "kai jama'a Amira,hala yan department ɗin ƙasa suna sa bata mun ke da gulma"dariya itama Amira ɗin ta saka tana mai faɗin"kinsan halin ma'aikata ta gaji Haka 'this,them and that".

Kaɗa kai Kiswa tayi tace "And las las na work We go do,bari na aje jakana naje gurin chairman din cos nasan yanzu yana sanin zuwana zai fara nema na."

    Bayan fitowarta kai tsaye office ɗin chairman ta nufa tana tunanin New headache ɗinta da zai fara kawo mata ziyara 'dan koda ba'a faɗa mata ba tasan yaran chairman Saleek zai bata wahala adduarta kawai Allah yasa wanda baya wasa da Aiki ne,bayan kallo na banza da PA ɗin chairman da fake gaisuwa da ta karba ta nufi office din bisa jagorancin Pa ɗin wadda ta sanar dashi zuwanta,

Bakin ta dauke da sallama ta shiga office ɗin yayin da take Faɗaɗa fara'arta,lokaci guda kuma chak sai fara'ar ta tsaya a yayin da idanunta suka dira kan  SALEEK wanda ke zaune calmly cikin ash Sweatpants da black polo shirt ,wani irin ras gabanta ya bata inda lokaci ɗaya nutsuwarta ke neman daukewa domin kuwa fuskarsa ba fuska bace da zata manta a dare ɗaya.

KISWAH??

Muryar chairman ta fito da ita daga trance ɗinta ,cikin yanayin in ina tace,yeesss.sir Good morning,cike da kulawa 'ya kalleta yace"Good morning but bana tunanin taki safiyar mai kyauce hope lafiya dai"

Saurin taresa tayi tace "Lafiya lau sir something skipped my mind ne ,im sorry"

Murmuushi yayi yace 'bismillah zauna,And proudly zanyi introducing ɗinki ga SALEEK babban yarona wanda zai gaji kujerata,

Kallan SALEEK yayi wanda ya kafe Kiswah  da ido yace "my boy meet my lovely beautiful And smart PR officer ,KISWAH UBAID"

Murmushin gefen baki SALEEK yayi yace "KISWA UBAID,ga sunanta ma mai daɗi 'dan yarda kaketa koɗata ma Abba ai tafi Haka,bai daina kallanta ba wanda kallan ke watsa mata Chill ta ko wanne sashe na jikinta,"wani irin smirk Saleek yayi da 'ya fahimci halin da ya jefata Kana yace "Anya bamu taba haɗuwa ba"?

Cikin dakiya tace"gaskiya ba dai dani ba 'dan Ban taba zuwa Australia ba kaga kai kuma chan kai rabin rayuwarka,maybe dai wata mai kama dani ce"murmushi SALEEK ya kumayi yace"gaskiya to wannan kama ta baci"

Baki chairman ya saka masu cikin maganar taso inda yake fadin"kasan Allah yana Haka ,sai kaga wani kuna mugun kama kuma baku ma sa juna ba,And kamar yarda ta faɗa maka bata taba zuwa Australia ba So ba ita ka sani ba amma soon ina sa ran zuwanku tare saboda akwai wani business opportunity da nake So kayi mana grabbing sannan my dear Pr would be of help that i can promise".

Gyara zama SALEEK yayi yace "zanji daɗin Haka Abba dan nima ina so ace naje na karbo maka business' ɗin nan yarda bazakace mai yasa ka bani Matsayin nan ba ,and nima ina so ace kana praising ɗina kamar yarda kake praising dear Kiswah ".

Dariya chairman yasa yana mai faɗi"i smell jealousy,to naji make me proud my boy"Kallansa ya maida kan Kiswa yace So my dear ga SALEEK nan ƙarkashin kulawarki,guide Him da abubuwan da bai sani ba na cikin company ɗin mu,but mind you he knows business Cos masters ɗinsa gareshi at 29.

Faɗaɗa murmushinta tayi nervously tace "insha Allahu sir and nasan dama yaranka koda bai kwaso komai naka ba zai kwaso kwakwalwarka da smartness ɗinka that im sure of.wani irin murmushi SALEEK yayi yana hango girman gut ɗinta domin kowa idan duka makeup ɗin duniya zata saka Babu yarda za'ayi ya manta macen da ta ɗaga masa hannu ta sauke a fuskarsa ,abu guda kuma dake masa zarya yake neman tarwatsa masa tunaninsa shine rashin sanin wacece ita ,Yasan dai da ita Abban sa ya haɗa masu blind tare zai faɗa masa sannan bazai bashi wrong suna ba which he is Sure ba Fareedha sunanta ba Kiswa ne dai dai,to amma wacece wannan Fareedha ɗin and how are they related ?

Cos babu yarda za'ayi ace basu da kusanci ,

Bayan komawarsa gurin mahaifinsa da ya tambayesa blind date ɗinsa Haka nan yace masa yana san ya sake saninta more sannan ya duba yanayi na samuwa da Auren nata zai bashi da amfana inda mahaifin nasa bai masa jayayya ba ya amince masa,dama yaso ace ne daga baya ya kawo masa wasu excuses masu karfi wanda yasan dole ya rabu dashi da labarinta amma a yanzu kuwa wani tunani daban yake domin labarin yazo masa da wani twist da ya ɗauki hankalinsa wanda bazai iya bari ya wuce haka nan ba.

    Har lokacin da tawa mahaifinsa sallama ta fita yana binta da kallo sannan bai masa doguwar tambaya ba dan ya lura Abban sa naji da ita bangare guda kuma bai san wace ita ba,wannan Aikin nasa ne kuma zaiyyisa da kansa.

Wata irin Ajiyar zuciya Kiswa ta sauke lokacin da ta fita daga cikin office ɗin yayin da zuciyarta ke wani irin lugude domin kuwa bata taba tunanin date ɗin Farry heir ɗin Chairman Basil bane which makes him her Boss,da ace ta sani babu ma yarda za'ayi taje date ɗin nan har tayi tarnishing ma kanta image,Babu ma yarda za'ayi hakan ya faru,nervously take cinye farcenta har ta isa office ɗinta inda lokaci guda kuma take dialling number ɗin Farry wadda Batayi picking ba,aje wayar tata tayi kan desk ɗinta tana mai kwantarwa da kanta hankali akan Babu yarda za'ayi ace 'ya ganeta Cos the make up was hard and da ace ya ganota to tabbas zai iya maganarta gaban chairman,sannan a yarda bata disclosing identity ɗinta ko chairman bai san tana da dangantaka da ALIJUA company ba yana ganinta ne kawai as a girl wadda kesan aikinta and take ƙokarin kaiwa wani mataki na nasara a rayuwa inda yake bata goyan baya,abu guda ɗayane bazata dauka ba wanda shine Saleek ya shiga rayuwar aikinta ya lalata mata,dole tayi wani abu.

To amma mai zatayi?

Tana wannan zagaye da saƙe saƙen taji an buɗe kofar office ɗinta anshigo babu neman izini kai tsaye.

CHUCHUJAY ✍️

08130229878.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top