22

💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

By

Chuchu jay ✍️

Book1⃣
22

ADVERT

Assalamu alaikum Habibties Meet AISHA and AMINA , Kai biyu da suka kawo muku "CHAPTER GREEN",💚shin kun san mai chapter ɗin su ya ƙunsaa?

Bari na faɗa muku,chapter ne dake ɗauke da Lover's Chapter ,ma'ana shafin masoya,inda tattaunawa kan abunda ya shafi soyayya zai wakana,akwai Family Chapter,ma'ana shafin iyali inda tattaunawa ta bangaren iyali zata gudana,akwai ISLAM Chapter,wannan sashen shi kuma shafi ne na tattaunawa kan abunda ya shige duhu a musulunci ,akwai Chapter na Rayuwar mu a yau,sannan akwai Matsala da maganinta,kamar yarda Bature yace "two heads are better than one"a wannan Chapter ɗin zaka kawo damuwarka a tattauna matsalar ka a baka solution ,sannan you can also shoot your shot.

Wannan duk zai faru ne da yardar Allah a CHAPTER GREEN.

Mai kuke jira baku kasance da su ba?

Oya join them on Whatsapp via link below

https://chat.whatsapp.com/JVI1jEszfJhHG1kri7xVAb

Follow them on Instagram :Chapter_Green_

On X :Ameenatourh_jay

Page 2⃣2⃣

    Duk da cewa Kiswa na farin ciki da ko yaushe Auren Haidar zai zo mata amma taji abun wani iri,da mamaki ta kalli Mama tace "Mama Aure gobe babu shiri?ni kaina ban sani bafa".murmushi Mama tayi tace"Aure babu shiri?yaran yanzu kenan to mu a shirye muka zo,za'a ɗaura ne inna goggo zata gyara ki na sati biyu,bazaki tare da shi mijin naki ba sai sati biyun 'ya cika ,yarjejeniyar da yaya yayi dasu bisa umarnin Dada,dan haka ki kwantar da hankalin ki zamu haɗaki"wata irin kunyace ta ziyarci Kiswa,cikin san kare kanta tace"nifa Mama ba haka nake nufi ba Allah",shafa kuncin ta Mama tayi tace "koma ya kike nufi kinji tsarin dai, sannan koda baki faɗa mun abunda ya faru ba shima yayan yaƙi faɗa nasan akwai Matsala tunda nazo gidan nan banga juwariyyah ba sannan Yaya ke faɗin sun rabu yaƙi kuma faɗan dalili ga kuma maganar Auren ki nasan akan ki ne ,amma koma mene ki sani babu abunda ta isa tayi miki wanda Allah bai miki ba,sai wanda ya ga dama sannan ni nasan addu'ar uwa bata faɗuwa ƙasa banza ,kullum cikin yi miki nake,insha Allahu bazaki tab'e ba.murmushi Kiswa tayi ta rungume mahafiyarta ta tana kuma mai jin daɗi da ya zamana alfarmar data ruƙa gurin Appa na kar ya faɗa musu abunda ya faru yayi mata,yin hakan kuwa dalili Shine bata so hankalin su ya tashi ,bugu da ƙari kuma bata san mutuncin Sagir ya zube gurin dangin su,mussamman Mamanta dake mutuƙar san shi da girmama shi,haka ta ɗauki girman danginta koda kuwa za'a kirata sakariya,abu guda ɗayane ta sani wanda tsakaninta da sune inda bataji a zuciyarta zata iya yafe musu a yanzu kam

".kafun kace ƙwabo kuwa gidan Appa ya karaɗe da hidindimu,kamar wasa Haka abun ya fara,da yamma Haidar ya kirata a waya,tana ɗagawa yayi wani sassanyan murmushi yace "amarya ta ina ta san na kira ki Ummi ta sakani gaba Ina Boutique ɗinta tana zab'a miki kayan da zaki saka da taro,aƙwatin ki kuwa yana hanya daga Malaysia,Ummi da Draman ta,nace a Boutique ɗinta ma komai daga Chan ne amma taƙi wai ƴarta abu mai kyau ya dace da ita."ƙaramun murmushi Tayi tace "So kasan da maganar Aure baka faɗa mun ba ko?".

"Nima Baba ya faɗa mun, amma labari ne da ban taba jin Mai daɗin irin sa ba,ina cikin wata irin murna da bazan iya misaltawa ba,nasan kema kina cikin farin ciki,,i mean mene yafi wannan farin ciki? "Murmushi tayi tace"babu fa,kawai dai an shammaceni ne ,but either ways Allah yasa haka shine mafi alheri." Ehen now you're talking"a haka suka cigaba da bawa junan su kalamai masu daɗi da sharing ma junan su irin burikansu na zama ma'aurata.

    ******

    "Ban fahimci abunda kike faɗi ba Faridha,ki sake faɗa mun daga farko,kina nufin kice mun Aliyu Aure zai ɗaurawa Kiswa da Haidar gobe?"Mother da maganar ta daketa kamar saukar guduma ta faɗa zuciyarta nayi mata wani irin tafasa.

Sagir dake zaune ne shima maganar ta shige sa yace"wallahi Mother bazai iyu ba,ai ko Kiswa zatayi Aure ni ɗin nan da ta nakasa ni zata Aura , kawai Mother kiyi wani abu".shiru Farry tayi kafun tace"ni dai a ganina Mother kinga dai inda abun nan ya kawo mu, akan ta Appa ya sake ki ya kore ki da Ya Sagir daga gida mai zai hanna mubar bala'in nan tayi bacci, yanzu yarda Dada tazo ɗin nan wallahi ƙiris Abu za'ayi ya zama babba,duk da na bigi cikinta kamar bata san mai ya haɗaki da Appa ba dan har tana tambayar inda Yaya Sagir yake nace mata baya ƙasar"."mitsiyaciya ,Algunguma kanwa uwar gami ai Dada tana ɗaya daga cikin masu zuga Appan ku,sannan idan bataji ba sai mene?idan yana ganin gwaninta ce yayi da zai boye abunda ya faru bai faɗa musu ba ,babban bala'in da zan jefesu dashi bazaiyyi tunani ba zai faɗa musu,na yarda a yanzu bana da wani abu da zanyi na katse Auren nan amma tabbas sai na lalatashi"Mother ta faɗa tana mai tashi ta ɗauki jakar ta da Car key ɗinta tana mai cewa"bari naje na samu Hajiya zee ɗin ma ku gani".tashi Farry ma tayi tace"nima dai bari na wuce gida dan nasan yanzu Dada zata fara nema na".

Tare suka fita daga gidan wanda yake mallakin Mother ne ,Farry ta kama hanyar gida dan bata san matsala inda Mother kuma tayi hanyar kaiwa Ummi ziyara,kamar kuwa yarda ta ayyana tana Boutique ɗin ta,koda taje babu wata wahala ta samu ganin ummi ,tana shiga ta washe haƙora yayin da Ummi ta ɗaure fuska tace "fatan lafiya dai".kujera Mother taja zata zauna Ummi ta dakatar da ita hanyar faɗin"ban baki wanna izinin ba,sannan ina san ki faɗi kai tsaye abunda ya kawoki duk da nasan san zuciya ne amma still na baki damar ganina,i know how wicked and heartless you can be so dan Allah ki tafi mun kai tsaye ki kama gaban ki".

Da mamaki Mother tace"ban san yaushe Alheri Ya zama sharri ba,mene laifina dan ina san cire ɗanki daga ƙangin fitina da yake neman zira kansa ?dan fa ina san taimakon ki bashine zai saka na zauna kina faɗa mun magana mara daɗi ba.".dariya Ummi tasa kafun tace"taimakona kikace ko?to Allah ya tsinewa halinki da taimakon ki,Kin bani mamaki sosai,ki kalleni nan da kyau,zan iya zuwa ko Wane extent domin na samu Farin Cikina dana iyalina ,amma Allah ya kiyaye naje level ɗin ki,sannan ina san ki sani zuwa gobe idan Allah ya kaimu,zamu bawa Kiswa legal right na zama dangin mu,wallahi ko ciwan kai tayi ta sanadin ki zaki sha mamaki,zan nuna miki baki da komai a bangaren power da kuɗi,get out now next kuma idan kika sake nuna minn ugly face ɗin ki ni kaina ban gama haddace abunda zan miki ba wallahi. "Da mamaki Mother ke Kallanta kafun tace"ba laifin ki bane"sannan ta juya ta fita a office ɗin gwiwarta a sage,tsaki Ummi tayi bayan fitar ta tana mai jin haushin Mother da rashin kame girmanta da darajarta ta uwa.

    Komai da Kiswa zata buƙata Ya hallarta ,kama da wadda zatayi mata gyaran jiki,kai,lalle da komai da amarya zata ɗauka wanda hakan nauyine da Ummi ta ɗora a wuyan ta domin kuwa irin mutuwar san da Ummi ke yi wa Kiswa abun ba'a cewa komai,gidan babu abunda kuwa ke tofawa sai irin sa'a da Kiswa tayi na samun mace ta gari a matsayin mahaifiyar miji dan soyayyar da Ummin ke nuna mata kana gani ba wai soyayya bace ta ƙarya musamman idan ka duba daga bangaren irin soyayyar da takewa Haidar wadda itace ta shafi Kiswa ɗin,kafun kace mene amarya ta fito ɗas kamar za ka saceta ka gudu,Fitowarta daga wanka turaren da Dada ta saka tayi taji wayarta na ƙasa,ɗauka tayi ganin sunan wanda ke jin wayar,da sallama a bakin ta tace"Boss Saleek good evening".karamin murmushi yayi kafun yace"kin san dai baki da kirki ko?,bai kamata ace bikinki a media zan gani ba,Kinsan koma mene im Your well wisher mai yasa zaki boye mun,abune na farin ciki fa".zama tayi kamar yana kallanta tace"im sorry, Like im very sorry kayi haƙuri nasan bazaka yarda ba idan nace maka nima yau nake sanin za'a ɗaura min Aure gobe iswear,kaima kasan kana na gaba cikin masu sanin Aure na bazan taba boye maka ba,abun kaji da yarda yazo"..ɗan shiru yayi kafun ya sauke ajiyan zuciya yace "its okay na yafe miki Just this one time nasa Abba ma ba mamaki ya rigani sani 'dan ina maganar Ɗazu ya katseni yana mai sabanta murnarsa ,but any ways im very happy for you naji miki daɗi sosai,sannan ina miki fatan shi ɗin abokin Alherin ki ne,and bazan boye miki ba,duk da yau ne last day amma ya kamata ki sani,'ina mutuƙar sanki Kiswa amma duk yarda naso da san kaina bai kai yarda nake sanki ba,dan haka ina miki fatan Alheri a sabuwar rayuwarki,sannan kamar yarda na faɗa ni dake mun zama family dan haka just a call idan kina da wani damuwan and i wil be right away,sannan kafun na manta,company ya baki month honey Moon leave,kiji daɗin ki"..tsintar kanta tayi da share ɗan hawayen da bata san taya ya fara fitowa ba,ta yarda tayi sa'ar samun mutum kamar Saleek a rayuwarta,goge hawayenta tayi tace"nagode Saleek im blessed to have you in my life ,sannan ina fatan Allah ubangiji ya baka mace wadda ta fini komai da komai ,inayi maka fatan Alheri,and im looking forward to meeting you as Mrs HAIDAR BULA."..bayan sunyi sallama ya kashe wayan Khalifa dake gefensa ya kallesa yace "mutumina kana da ƙarfin Hali da imani,wannan Babe ɗin fa you dey do her ne kana santa kaƙi kula kowa akanta amma gashi magana ake ta Aurenta fa Har kana da ƙarfin kiranta kayi mata fatan Alheri,omo nagode ƙanin Mother teressa.".Kallansa Saleek yayi kafun yace "abu guda ɗaya na yarda dashi wanda Shine babu wanda ya isa 'ya Auri matar wani sannan ga dukkan alamu ya bayyana cewa Kiswa ta Haidar ce so mene kake so nayi,kana san na halaka ne saboda ina santa?abeg idan zakayi mun Addua Allah ya kawo min sassauci kayi mun idan baza kamun ba ka zuba mun ido,kuma kar ka Sake kiranta babe".tabe baki Kalipha yayi yace"kaji dashi ni bari kaga tafiyata ma kafun yanzu saboda nasan akan Kiswa za ka nemi ka zageni."Bai ce masa komai ba har ya fita,komawa yayi ya ƙwanta ya rufe idanun sa abun duniya na mutuƙar damun sa ,ya kasa yarda da cewa wai Kiswa zata zama matar wani gobe da safe sannan yana addu'ar Allah ya bashi ikon Hallarta ,he Just can't bear it.

💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥

    __Kamar yarda komai ake saka masa rana ya tabbata cikin yardar Allah haka nan ranar da aka saka domin Kiswa da Haidar tazo,Babban Masallacin na central mosque a cike yake da manya mutane domin amsa gayyata Ɗaurin Auren da yazo babu zato babu tsammani,bikine na kuɗi wanda cikin rana ɗaya suka tsinci Ɗaurin Auren amma kasancewar lahadi ne yasaka duk wanda ya samu gayya yayi ƙokari wajen ganin Ya amsa ta, taro yayi taro inda da albarkar jama'ar gurin Waliyin Haidar ya karba masa Auren Kiswa akan sadaki naira dubu ɗari biyar daga hannun Waliyinta,inda shi kuma waliyyin nata ya bada Aurenta bisa shedun mutanen da suka hallarci wannan Ɗaurin Aure mai Albarka,wani irin yanayi na farin ciki da Haidar ya tsinci kansa abun ba'a magana yayin da Saleek wanda yazo a daddafe yaji Abun ya saukar masa kamar Aradu,a haka dai ya ke ta faman washe baki gefen Abban sa wanda Shima nasa bakin ya kasa rufewa .

    Ana ɗaura Aure maganar ta isarwa mutanen gida inda take masu hancin guɗa suka kama,Kiswa dake zaune bakin gado cikin wani irin sassanyan ado kuwa ji tayi kirjinta yayi wani irin mugun bugawa,Kallan ta Dada tayi tana mai shafa mata baya tace"Alhamdulillah,maza kiyi sujjada ki godewa Allah da ya kaiki wannan matakin da kowacce mace take san ta ganta Akai."babu musu Kiswa tayi abunda Dada ta umarceta tana mai nunawa ubangiji godiyar ta da ya nuna mata wannan ranar da ta daɗe tana dako,guɗar da aka ɗauka sabuwa ce daga waje ta ja hankalin su,Baba Baraka ce ta shigo tana mai cewa "gafa mahaifiyar Haidar nan da tawagarta sun kawo akwatin Kiswa"Tashi Dada tayi tana mai cewa ,akaisu ɗakin masaukin baƙi za'a zo a tarbesu,hakan kuwa akayi inda sukayi musu tarb'a cikin mutunci da karramawa,kaya kuwa kamar za'a buɗe shago,Ummi ce ta nemi ganin Maman Kiswa domin gaisawa da ita sannan tayi mata godiya na haifan ɗiya kamar Kiswa wadda ta tafi da dukkan wata soyayyar Haidar,sanarwa da Mama akayi inda ta kimtsa tace a rakota dan itama tana san ganin Mahaifiyar Haidar domin tayi mata godiya da bata amanar ɗiyarta.    Sallama Ummi tayi inda sallamarta ta katse sakamakon ganin Mama yayin da amsar Mama da farin cikinta ya katse ganin Wadda tayi sallamar a matsayin sirikarta .

Tashi Mama tayi tace"wa nake gani kamar Hajiya zainab?"da mamaki Ummi tace nice Zubaida ba dai kece mahaifiyar Kiswa ba,

Ƙaramun murmushi Mama tayi kafun tace"yanzu na fahimta sannan kema nasan Kin fahimta,wannan Auren dake tsakanin Kiswa da Haidar shi da zuba ruwa a rariya Ya tsiyaye haka yake ,dan Wallahi babu shi bama zai taba iyuwa ba".da sauri Ummi ta shigo ciki tana cewa"kar kice haka mana Zubaida,farin cikin ƴa ƴan mu ne kar mu bata da hannun mu"ƙarasawa tayi ta kama hannun Mama idanunta sun fara kawo ruwa..ƙwace hannu Mama tayi tace"tun ran gini tun ran zane wallahi indai nice na Haifi Kiswa wannan Auren babu shi ba zai taba zama da Akwai ba har abada".

Dan dan dan dan dan dan

Shin meke shirin faruwa ne?

Muhaɗu a littafi na biyu domin jin Mai ke shirin faruwa mene zai faru,kamar kuma yarda na sanar a book 1 book 2 na kuɗi ne kan 300N kacal.

0264267657

Gt bank

Amina jamil Adam

Shaidar biya

08130229878.

Ku zo maza ku biya kudin ku domin a cigaban da tafiyar daku❤

Nice Take a kullum

CHUCHUJAY ✍️

(Amina jamil Adam)

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top