21
💥KISWAH💥
(Surrogacy was the cause)
By
Chuchu jay
Book1⃣
Page 2⃣1⃣
__________Koda suka shiga ma'aikatan gidan ne kawai a falo waɗan da suka gaida su cike da girmamawa,kallan Haidar dake raba ido yana neman inda kiswa zata fito Saleek yayi kafun yace masa"ka zauna bari nayi maka magana da ita ko zata gan ka cos kasan nayi gaban kai na ne babu yardar ta,idan kuma baza ta ganka ba babu abunda zan iya sai dai in na baka hakuri..murmushi Haidar yayi yace "i doubt if she will reject me".kallan sa kawai Saleek yayi ya juya dan zuwa yi mata magana duk da yasan yayi mata laifi tunda ta roƙe sa kar wanda yasan tana nan,but its not his fault Haidar yazo ne using his own method wanda koda Shine a stead ɗin sa shima haka zaiyyi ,Allah kaɗai yasan abunda guy ɗin yayi going through saboda soyayyar sa is Top notch..tsaye Saleek yayi a bakin ƙofarta yana debating da zuciyarsa kafun yayi ta maza ya ƙwanƙwasa mata,Knocking ɗaya yayi tace Wane,amsata yayi yace Shine,jin muryarsa ya saka ta kimtsa kanta tace"Bismillah".
Kamar yayi wa sarki karya haka ya shiga ɗakin ,gaishe shi tayi ya amsa mata yana mai tunanin yarda zata dauki maganar kafun yace "na dawo kawo miki kayan ki ne da Baba Baraka ta kawo mun office so ina tunanin ko zaki buƙaci wani abu shi yasa nazo sannan in the process nayi miki laifi hope za'a yi mun afuwa,ina dawowa na tarar da Haidar bakin gidan nan and i swear bani na faɗa masa kina nan ba,nima i Just saw him ina shirin shigowa and he look Like a mess ,a yarda na ganshi kuma i had no option dole na bar shi ya shigo,but idan kince baza ki ganshi ba bani da matsala dama i told him idan baki yarda ba zai haƙuri ne".. Shiru tayi tana kallan sa kafun tace"yana ina yanzun?"."yana falo"ya bata amsa yana addu'ar Allah yasa kar tace bazata ganshi ba,it shouldn't be Like that,dan Shiru tayi kafin tace"its okay muje na ganshi".
Koda ta fita ya juya baya yana Kallon ta inda zata fito,gyaran murya Saleek yayi yace"oga sir ga Madam ɗin ka fa"juyowa Haidar yayi da sauri take idanunsa suka cika da hawaye lokacin da ya sauke su akanta,bai san lokacin da ya ɗaga kafafun sa ba ya isa gareta kafun tayi Aune ya haɗe ta da jikin sa cikin runguma wadda yake ji kamar za'a ƙwace masa ita,ba tayi zato ba Batayi tsammani ba haka zalika Saleek wanda abun yazowa a bazata,tana ƙokarin kwacewa ya riƙeta yace"please Just a Moment ,"Ajiyar zuciya ya sauke kafun ya raba jikin sa da nata ya kalleta yace "mai yasa kika yi mun haka?,kinsan Wane irin hali na shiga da ban ganki ba,i know kina fushi dani Shine ya saka baki kirani ba,im sorry about abunda na faɗa miki ,sharrin shaiɗan ne and na miki alƙawari bazan ƙara miki zargi irin wannan ba so please kar ki bani wahala irin wannan.kallan sa take wani irin san sa na fizgar ta,ganin yarda baki ɗaya ya rame dare ɗaya kawai ya bata tsoro,ɗan murmushi tayi tace"ka zauna muyi magana"babu musu ya zauna,ganin cewa Haidar da Kiswa sun manta da Saleek ya na Falon ne ya saka shi jejely barin Falon wani Abu nayi masa yawo a ƙirji,sunnan Allah kawai yake kira domin wani irin kishin ta ya tsinci kansa ciki ,ji yake zuciyarsa nayi masa wani irin suka,amma sanin baya da hurumin da zaiyyi wannan kishin a kanta ya lallashi zuciyar sa ya roƙi Allah ya sassauta masa kishi akan abunda ba nasa ba.
Zama Haidar yayi yana mai jin kamar zai buɗe ido yaga mafarki yake,zama itama tayi tana kallan yarda baki ɗayan sa ya kasa nutsuwa,Ajiyar zuciya tayi tace"yarda kazo and da yarda nake kallanka a yanzu nasan kasan komai da ya faru and im sorry ban kira ka ba domin bana fatan ka ganni cikin halin da nake ciki,and ban kira ka ba bayan nan saboda bana san na tada maka hankali"."ai rashin kiran Shine yafi komai tada min hankali baby cos gwanda nasan inda kike da ace Kin boye ban sani ba ,im sorry about komai sannan ina san a Rayuwar nan ace na zama a gefen ki a yanayi mai kyau ko mara kyau domin kuwa Alaƙa na dake is for better and worst ,don't do this to me ever please,nasan kuma abunda na faɗa miki kan Saleek ne yasaka, kar ki ga laifina kece burina ,duk wani ɗa namiji da zan gani a tare dake zuciyata sai tayi skipping beat musamman kuma namiji kamar Saleek,ta ko ina haɗaɗan gaye ne wanda mace zata ji a kallo ɗaya yayi mata Why wont i be scared.ɗan murmushi tayi tace"tsakanina da Saleek Pure relationship ne wanda babu wani tunani mara kyau a cikin sa,yana da kirki he is just very kind to me sannan mutum ne shi wanda na ɗauke sa kamar ɗan uwa haka zalika shima ya ɗauke ni haka,kai ma ka sani i will never be moved By any man When i have you,kai nake so kai na zaba idan kuma za'a sake dawo da hannun agogo baya i will still choose you,you're my muse in love and everything,i will never abandon Your love for another ya kamata ace tuntuni ka san wannan,so please ka daina sakawa kanka insecurity akan abunda ba haka yake ba,sannan da kake cewa kallo ɗaya mace zatayi wa Saleek ya tafi da ita kai kuma fa?ka dai san Saleek ba kyau ya fika ba iya kaci ace ya fika kama da play boys,you're so Handsome My Sugar"ƙarasa maganar tayi tana mai kashe masa ido guda ɗaya.
Haɗe lebensa yayi guri ɗaya kafun ya sake su ya Faɗaɗa fara'arsa yace"dont do that gaban wasu cos you look cute,so yanzu dai kije ki ɗauko belongings ɗin ki mu tafi dan daga nan gidan mu zaki je,ba zaki koma gidan nan ba".ɗan shiru tayi kafun tace "bazan bika gidan ku ba gaskiya ,idan Mama taji ma raina zai b'aci i will be okay here"....kafun ya sake cewa wani abu sukaji ana buga ƙofar falo,tana ƙokarin tashi Saleek ya fito yana mai faɗin"i will get it".
Koda yaje ya buɗe mai gadin gidan ne ya duƙa cike da girmamawa yace"Alhaji kayi baƙine nayi tunanin ma na Alhaji babban ne to amma sai suka ce kai suke nema".da mamaki Saleek yace ni kuma?
"Eh kai kuwa muke nema"muryar Appa da ya kasa hakura ya tako ta karaɗe kunnuwan su,wani irln faɗuwar gaba ne ta ziyarci Kiswa ,tashi tayi daga zaunen da take tace "Appa?"jin tace Appa yasa Saleek cewa "bismillah ku shigo,"babu musu Appa ya shigo bakin sa ɗauke da sallama yayin da yaya sameer ke bayan sa shima yana mai yin sallama ɗin,muzurai Kiswa ta fara da ido tana mai cewa"sannu da zuwa Appa,durƙusa wa tayi domin gaida shi,saurin binta yayi ya ɗagota yana mai kaɗa mata kai yace"No my daughter ina mai mutuƙar jin kunyar abunda ya faru dake amma ina mai jin babu daɗi daya kasance bani kika fara kira kika sanar wa ba duk da ina matsayin mahaifinki".kallan Haidar yayi yace "tana gurin ka kenan,kaima baka kyauta ba domin ni ya kamata ka kira".duƙar da kai Haidar yayi yana mai gaidashi kafun yace"nima Appa zuwa na kenan dan sai da na saka ma a kayi mun tracking ɗin ta,amma wanda ya taimake ta gashi nan,Saleek ogan ta gurin aiki".Gaida Appa Saleek yayi inda Appa ɗin ya bisa da kallo domin yau ne ya fara ganin sa duk da kuwa mahaifinsa abokin sa ne,koda suka so haɗa alaƙa tsakanin yaran su shi baisan Saleek ba amma yana da yaƙi nin duk ɗan da za'ace daga Alhaji Basil yake to mai tarbiyya ne wanda dalilin da yasa yaso su haɗa Auratayya.cike da mutunci Appa ya amsa mishi kafun yace"nagode sosai da abunda kayi wa Kiswa im so glad hannunka ta faɗo thank you Allah yayi maka albarka,muma tracking ɗin nata mukayi,ina gayyatar ka gidan mu for saturday lunch ina fatan kuma baza kaƙi amsa gayyata ta ba".murmushi Saleek yayi yace"insha Allahu Appa ,"kafun ya juya suka gaisa da yaya sameer inda Haidar ma ya miƙa masa hannu suka gaisa.
Duk yarda zuciyar Kiswa ke assasa mata ƙin komawa gida kasa nuna wa Appa tayi lokacin da ya mata izinin ta ƙwaso kayanta su wuce,kula da Appa yayi da rashin jin daɗin komawa gidan ya saka shi cewa"ki ƙwantar da hankali ki ,Mother da kika gani bata gida dan Aure na da ita ya ƙare,shima babban shaɗanin yaran na sallama mata shi dan haka ki saki jikin ki,gida na mahaifin ki ne kuma zanyi waje da duk wani wanda zai wasa da ƴata muddin ina raye.wata irin kwanciyar hankali ce ta ziyarci Kiswa domin dama tsoran ta su.
Koda suka isa gidan kai tsaye ɗakinta ta nufa,tana shiga Baba Baraka tazo tana mai tambayarta abunda zata kawo mata.kallan ta Kiswa tayi kafun ta tashi ya rungume ta ta fashe da wani irin kuka,shafa bayanta Baba Baraka ta fara a hankali kafun tace"kiyi haƙuri Kiswatu,komai kika ga ya faru ga bawa ƙaddararsa ce,ke taki kenan,kuma Allah ya kawo miki da sauƙi,".cikin kukan Kiswa tace"banji daɗi ba Baba baraka da ya kasance hasashen ki ya zamo gaskiya,ji nake dama ace mafarki ne,nayi dana sani da ban bawa maganar ki muhimmanci ba inajin da ba'akai yanzu ba dan zanyi wa tufar hanci,gashi yau na zama silar da gidan nan yake neman tarwatsewa".cike da lallashi Baba Baraka tace"baki zama silar lalacewar komai ba cikin gidan nan kiswatu sai ma ke da akaso a lalata Allah ya tsaya miki dan haka ki daina wannan maganar,ba tun yau ba nasan Hajiya bata ƙaunarki ,dan haka hukuncin da Alhaji ya ɗauka akan ta yayi dai dai dan ni bana ko tausayin ta"haka nan tayi ta lallashin ta har ta ɗan samu nutsuwa.
Bayan sati da faruwar al'amarin komai ya lafa domin bama sa jin Mother yayin da babu wata maganar arziƙi da ta shiga tsakanin Kiswa da Farry,Kamar yarda Kiswa ta nema kuwa hutun sati biyu Saleek ya bata na aiki,ranar Monday tana zaune tana aikin office ɗin ta a ta gida taji buruntun mutane a waje,rufe system ɗinta tayi ta tashi ta fita dan ganin meke faruwa,tana fita idanunta suka sauka kan na Maman ta ,gefe guda kuma kakar ta ,wani irin tsalle tayi ta rungume kakar tata tana mai faɗin"Dada"ɗan karamin ƙara Dada tayi tace"Ke kar ki karyawa mijina ni ki cucesa,jaira yaushe rabon da kije inda nake sai anyi magana kice aiki aiki"ƴar dariya Kiswa tayi tace"nima ina ƙewar ki abar ƙauna"Kallanta ta mayar kan Mama kafun itama ta rugumeta tana mai cewa "Mama na".kafun Mama tace wani abu Rabia Ta shigo tana mai faɗin"Didi"da gudu tayi kan Kiswa ta ɗane ta inda itama ta chab'eta tana mai jin wata irin murnar da ta rasa ina zata saka kanta,kallan ƙofa ta fara tayi tae"ina khaleel?"."yana boarding ai basuyi hutu ba".suna wannan ihun murnar yan uwansu Na bauchi suka fara shigowa ,mamaki ne sosai ya kama Kiswa wadda ta fara musu maraba tana gaidasu.tambayoyine fal zuciyar Kiswa tana san sanin abunda ya kawo su gidan wanda ita dai tasan ba taro ne ake yi ba,bayan kowa ya samu masaukin sa ne Kiswa ta nufi ɗakin Dada,chan ta tarar da Farry ,ƙin shiga tayi kawai ta koma gurin Mamanta,nan ne take ji wai Gobe za'a ɗaura Aurenta da Haidar.
CHUCHUJAY ✍️
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top