16

💥KISWA💥

(Surrogacy was the cause)

Na Chuchujay

Follow my whatsapp channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05

Book1⃣

Page 1⃣6⃣

____________Cike da mamaki Kiswa ke kallan yarda Farry ta gyara zama tana ƙwararo ƙarya harda faɗin ita ke korar mata duk wani saurayi da ke zuwa gurin ta ,bayan ta gama narrating labarin ta bangaren ta Appa ya kalli Kiswa yace"ina san naji daga naki bangaren Kiswa,shin da gaske ne ke kike korar mata samari ko a'a ,sannan wannan magana ta Saleek menene gaskiyar ta domin idan na kama ɗaya daga cikin ku da ƙarya tabbas zan sab'a masa fiye da tunani domin kuwa ba sunanku kaɗai kuka b'ata ba,kun haɗa baki ɗaya da nawa kun lalata wanda bazan lamunta ba".

    Goge hawayen dake fuskarta tayi ta mayar da Kallanta ga Appa tace"Appa magana da Farry tayi na ina korar mata samari ƙaryane domin ni banga menene ribata na son cutar da ita ba ko ganin taci baya,Allah shaida tane,sannan magana da take 'na Saleek bani da shaidar lokacin da abun ya faru tsakanina da ita amma abu guda ɗaya 'na sani wanda Shine Allah na tsakanin mu a lokacin,and ni abunda nayi was out of kindness for my sister domin Farry ta sameni a ranar ta kawo mun maganar date ɗin dan ban ma san da Saleek madugu bane domin bani da masaniyar a lokacin ma yaran ogan mu ne,tace naje a maimakonta saboda bazata iya handling abun da kanta ba ni zan iya saboda na taimaka mata lokacin da wani saurayinta na harrassing ɗin ta,koda ta mun maganar gata nan a zaune sai In taƙi Allah taƙi faɗar gaskiya da ƙyar na yarda dan sai da ta lissafa mun cewa yana shan giya,yana shan sigari,mazinaci ne,wanda babu wahala ya b'ata ka,sai da nace mata zan sameka da maganar But tayi blackmailing ɗina emotionally wanda dole babu yarda na iya haka nan na biye mata wanda na yarda Shine kuskure na,amma a nawa lissafin idan zata fita cikin haɗari hukuncin kuskuren bazai dameni ba alfahari na ɗaya na fitar da ƴar uwata daga mugun hali,sannan duk wani taimako da zanyiwa Faridha bata ƙasa a gwiwa wajen tura mun kuɗi ,cikin wannan satukan da muka fara samun matsala har maganar Saleek ta shiga ciki dan har ta sameshi a office ɗina su sasanta Amma yaƙi,ta faɗa mun akan duk abunda nayi mata a rayuwa ai tana biyana ne ni kuma na maayar mata da duk wani kudi da ta bani akan abun Alheri da nayi mata kimanin Naira miliyan biyu da rabi,ina da alert and im sure itama tana dashi,ban yarda naci kudin nan ba dan gani nake kamar zan cinye zumunci nane,Mother nasan baki sona sannan a yanayi na aikinki kinsan ba karya nake ba ,kiyi mun alƙalanci a matsayina na ƴar Adam ba matsayin Ƴar ƙanwar mijinki da kike ji kamar ki kashe ba.

    Tafi Mother ta saka tace"tabbas Kin girma Kiswa,''na yarda kinyi girman da zaki zauna ki tsara sharri har kike ƙoƙarin faɗa mun maganar banza,to bari kiji wallahi babu wani sharri da ban gani ba kuma ban sani ba"kallanta ta mayar ga Appa tace "kanaji ai ko?kanaji da kunenka ba sai na zauna na faɗa maka wacece kiswa ba,irin ƙaryar dake fita a bakinta kawai kasan zata kashe mutum,yanzu Kai Ina Farry yarinyar da Aka haifa jiya jiya zata aikata hakan?"kana kallo saboda tsabar kuka idanunta har sunyi jawur .

Cike da rashin tsoro Kiswa tace"Mother nima na iya kuka fa dan zan zauna na rerashi koda kuwa banaji amma sanin ina da gaskiya ya saka ban zauna nayi ba sannan maganar nan da nake ba dan dare yayi ba da da na kira Shi Saleek d'in ya faɗa da bakinsa kamar yarda na faɗa muku,shima ai ya san komai kuma nayi imani da Allah itama tasan idan yazo itace zata ji kunya."

"To yazo mana muga ƙarshen gaskiyar ki fitsarariya mara kunya,"Mother ta faɗa tana mai haƙiƙancewa . tashi Farry tayi tana mai rushewa da kuka ta ruga da gudu,Kaɗa Kai sameer yayi yace "kingani ko?"Kina gani kinsan bata da gaskiya,maganace ta fatar baki sai a zauna ayi menene na tashi tana kuka.

Hayyayaƙo masa Mother tayi tana mai faɗin"wallahi akan wannan yarinyar Sai na baka mamakin da baza kayi zato ba,dan me kuma bazata tashi ba ta zauna tana gillo ƙarya kuna saurarenta shi shugaban baice komai ba."

Murmushi Appa ya tsinci kansa da yi yace "juwairiyyah kenan,ke kikayi rainon cikin Faridha kika haifeta kike rainta ta girma a gabanki amman ni nafiki sanin abunda zatayi da wanda bazatayi ba,sannan magana da kike Kina wai yiwa sameer hargagi ai gaskiya ce ya faɗa sannan kamar yarda kiswa ta faɗa miki kiyi mata alƙalanci a matsayinki na wadda tasan shari'a ba wadda ta tsaneta to the core ba,wallahi shame on you Juwairiyyah ,shame on you,kunya kike bani sosai idan ina kallan irin wannan halayyar taki mara amfani wadda babu inda zata kaiki sai zauren dana sani,wallahi kisan abunda ke gabanki ki kiyayi kan ki,sannan ke kuma kiswa ba abunda nayi tsammani daga gareki ba Kenan,lokaci da ta nema kiyi mata wannan shashancin da Kin sameni Kai tsaye duk yarda zata biki tana miki daɗin baki,ban ji daɗin abunda kuka yi ba ".

    Ƙasa tayi da kanta cike da dana sani tace"nasan nayi kuskure Appa kayi hakuri insha Allahu hakan ba zai kuma faruwa ba".

Murmushi Appa yayi yace"Allah yayi muku albarka "kafun ya tashi ya Shige ɗakin sa bai kuma cewa komai ba.

Wata uwar ashar da Mother ta durguzo sai da ta bawa kowa tsoro ,tashi Kiswa tayi da sauri ta bar gurin yayin da sameer ya tashi shima yana mai faɗin "Allah ya kyauuta"

Kallan Mother sagir yayi yace "mother kar ki damu ni nan zan miki maganin komai dake neman baki da Faridha Matsala ,ki tashi kije ki ƙwanta".tashi tayi tana mai jin zuciyar ta na yi mata zuga kala kala akan Kiswa .

_____________Washe gari ya kama asabar,duk da yayin da Kiswa ta Ƙwana na rashin jin daɗi bata manta fitar da zatayi da Ummi ba ,bayan gama duk wani abu da zatayi tana ƙwance tana jiran kira Ummi kiran Haidar ya shigo mata,tana ɗagawa yace"Baby na zo ɗaukowa Ummi ke ,im  outside".

Gyalenta da jakarta da wayan ta kawai ta ɗauka ta fita dan zuwa gareshi,har ta ɗauki hanya zata fita ta juya ta nufi sashen mother dan sanar mata zata fita,a falo ta tarar da ita,sallama tayi ba tare da ta damu da rashin Amsawarta ba tace"mother dama zan wuce ne fitar da nace miki zamuyi da Ummi, to ta aiko a ɗaukeni shine nace bari nazo na faɗa miki kar ki jini shiru.

Wani irin tsaki mother ta ja ta juyar da kanta ba tare da tace komai ba amma ji take kamar ta tashi tayi mata shegen duka Ko ta saka hannu ta shaƙeta Haka take ji ,amma tuggun da suka haɗa mata daren yau kawai ya isheta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

Ganin mother ta cigaba da abunda take ya sakata juyawa dan fita tunda ai ta sauke nata nauyin na sanar mata zata fita ,tana ƙoƙarin fita taci karo da Farry wadda taja wani dogon tsaki ta bangaje ta ta shiga ciki tana mai faɗin"uwata abun alfaharina barka da hutawa ".juyawa Kiswa Batayi ba ta fita a ɗakin.

Zama Farry tayi kan kujerar da mother take tace"mother kince na kwantar da hankalina zakiyi maganin kiswa yau mene akwai a ƙasa?murmushi mother tayi tace "Abun bana faɗa bane yanzu amma ki ƙwantar da hankalinki gobe da safe idan Allah ya kaimu zaki karya da labari mai daɗi domin kuwa za'a fasa Auren Haidar da Kiswa."

Ajiyar zuciya Farry tayi tana mai jin kamar ta zuƙo gobe duk da kuwa mother bata faɗa mata ga plan ɗin da ta shirya ba amma tasan koma mene farin cikinta zai fara kaɗawa gobe.

    Koda Kiswa ta fita Landcruiser prado ce ta fara yi mata sallama cikin compound ɗin gidansu wadda tasan ba ta gidan bace sannan bata san haidar da ita ba,sanin Shine ciki ya saka ta taka cike da tafiyarta da ke mutuƙar burge Haidar wanda yake daga cikin tinted motor ɗin sa yana kallo,kafun ta ƙaraso ya fito ya buɗe mata motan fuskarsa cike da fara'a,murmushi tayi masa kafun ta shiga tana mai cewa "thank you"bayan ta shiga shima ya zagaya ya shiga nashi seat ɗin yana mai faɗin"you're welcome abar ƙauna,sannan kinyi mun kyawun da nake ji kamar kar kifita da Ummi instead ni na ɗaukeki mu tafi on a date kwana biyu bamu fita ba".

Gyara zaman ta tayi ta juyo tana mai facing ɗin sa kafun tace "nima ina jin hakan a raina amma duk yarda nake san yin hakan Ummi first dan kasan yau idan nayi disappointing Ummi mun bani"

Dariya yayi yana mai tashin motan yace "duk abunda kika ce haka za'ayi"Kashe mata ido guda yayi yana mai tashin motan ,hira suka ringa yi ta soyayya har suka isa "QUEENS PARLOUR "guri mai kyau ya samu ya faka motarsa ya maido da kallansa gareta yace"ko dai nazo na rakaki ciki?"tana ƙokarin bashi Amsa wayarta ta hau ruri ɗauke da sunan Saleek a jiki,idanun Haidar akan wayar tata kafun ya mayar kanta yana mai Kallanta,ita ma ɗin shi take kallo kafun ta mayar da idanunta kan wayar Har ta yanke bata ɗauka ba sai da ya sake kira ya kalleta yace "ki ɗauka mana"murmushi tayi masa kafun ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta tana mai faɗin"Hello sir"

Daga ɗayan bangaren Saleek dake ƙwance kan makeken gadon sa yace "Sir ?,girl kar ki manta its weekend a wajen office muke and da friend ɗinki Saleek kike magana ba Sir ba,so are you free,i want to take you out for a frndly date".kallan Haidar tayi wanda Shima ita yake kallo,murmushi tayi tace "well zanyi disappointing ɗinka domin yanzu haka ina tare da Haidar ya kawo ni gurin Ummi cos muna da appointment "

Sauke ajiyar zuciya na disappointment yayi yace "well have a nice day sai munyi magana ,and send my regards".

Bayan ta kashe wayar ta kalli Haidar wanda ya ɗauke kansa yana mai kallan gefe,"babe shall we"?ba tare da ya juyo ba yace "you shall"a yanayin da yayi maganar ya tabbatar mata da cewa wani abun ba dai dai ba,gabanta taji ya faɗi cos tabbas fushi yayi da ita wanda bata san akan mene ba,

Babe?ta faɗa tana mai saka fuskar damuwa,juyowa yayi yace"Haidar ,Just call me Haidar tunda Yanzu ai abunda kika kirani kenan tunda baki san asan wanene ni a gurin ki,and this Saleek of a guy dama ni already i hate his guts"he is asking you out ko?zaki iya cancelling appointment ɗin Ummi kije ai,dama ai i was warned akan sa ,i was told kuna soyayya.

Shiru tayi tana kallansa domin abunda take gani na kishi a idanunsa bata taba gani ba,bangare guda kuwa maganarshi ta karshe ce ta dake ta na cewa wai dama an gargaɗesa sannan he was told suna soyayya,bata ce masa komai ba ta buɗe motar ta fita,kai tsaye ta shiga QUEENS PARLOUR ɗin bayan ta nuna ID ɗin da Ummi ta tura mata ranta yana mata babu daɗi sosai .

    Koda Kiswa ta fita a motar dafe fuskarsa yayi yana mai dana sanin abunda ya furta,bai so ya dawo da maganar Farry ba amma tunani da yake Shine guy ɗin da suka haɗu dashi a company ɗin su ya saka zuciya ta jashi ya faɗin abunda ya faɗa,sanin bazata tsaya ba ya saka baiyi yunƙarin binta ba amma shi kansa yasan ya taro match ɗin da baida players'.

    Koda Kiswa ta shiga a VIP tayi locating mother da ƙawayenta yan trillion dollars club ko waccensu ta manyanta amma sun gagara yarda da hakan,koda ta isa gurin Ummi kamar ta mayar da ita ciki,kamar yarda ko wannensu ke ɗauke da bathrobe hakan nan Itama taje ta chanza bisa umarnin Ummi,haka nan take finding abun weird ita kaɗai cikin iyayenta da sunan sunzo beauty parlour ,kafun kace mene ya faru Ummi ta fara bragging da Kiswa,mutum ɗaya da Kiswa ta kula ba wani shiri suke da Ummi bace tace"nayi zatan zanganta kamar tsada saboda haske"ƙarasa maganar tayi tana mai tab'e baki yayin da Ummi tayi ƙaramun murmushi tace"well idan kika kalleta da kyau ba sai  an faɗa miki tafi sirikanki ɗin nan guda uku ba kar ma ace matar babban yaranki abun sai godiyar Allah,kamar da daddare suka haɗu amma kinga Kiswa kuwa,She's a spec ,real definition of melanin,Black beauty,hanci har baka,ga class,Ga hutu sannan gata san kowa ƙin wanda ya rasa"kamar jira yan koran bayanta suka cigaba da ƙoda Kiswa wadda take jin kamar ta tashi ta gudu,haka nan Aka masu massage sannan ,then gyaran da yake necessary,a wannan zaman Kiswa ta fahimci Ummi ce biggest influencer a gurin,idan da za'a tambayeta zata ce wannan Group ɗin is not healthy,dan toxicity ɗin dake cikin sa is In another level,kasan cewar Ummi mai kuɗin ciki sai abunda tace koda baiyyi sitting da sauran ba,saboda wani ƙwaɗayi sai kaga sun mata mubaya'a a bayan idanunta kuma su zageta. haka nan bayan sun gama Ummi ta dauke ta zuwa ɗaya daga cikin Boutique ɗinta tayi maa shopping na gani na faɗa duk kuwa yarda Kiswa ke nuna ta bari hakan amma kamar tana sake zugata dan a cewarta wadda haidar yake so ta wuce hakan a gurin ta.

Har ƙofar gida Aka mayar  da ita bayan dinner cos yawo sosai Ummi tayi da ita kafun sukaje 5star sukaci abinci,it was kind of hella girls out ,kamar yarda Ummi take faɗa girls out amma a gurin Kiswa it was hell,koda ta shiga gida ya sameer ta tarar a Falon farko yana sintiri,tana shiga da ledoji niƙi niƙi ya kafe ta da ido yace"daga ina kike Kiswa karfe takwas na dare?"

Ɗan murmushi Tayi tace "yaya ina tare da Ummin Haidar ne"ɗaga Kai yayi ya kalli agogon dake Falon yace"amma dai sense is common mene ya saka baza ki faɗa mata dare yayi ki dawo gida haka nan ba,Eh iyayen wanda zaki Aura ne amma a matsayin tarbiyya bai kamata ki bisu kuyi wannan daren da kikaje kikayi ba,you got me worried musamman da na tambayi Mother tace mun bata san ina kikaje ba,koda mene ke tsakaninku Atleast idan zaki fita ki sanar mata ko kuma ni ki sanar dani."

    Batayi mamakin cewa mother tace bata san inda taje ba,rashin san ta ƙaryata mahaifiyarsa a gaban sa ya saka ta kama kunnuwanta guda biyu tayi narai narai da ido tace"kayi haƙuri yaya samir insha Allahu bazaka kuma samuna da laifi kamar wannan ba,kayi kun hakuri nayi kuskure ".

Ganin yarda ta marairaice kamar zatayi kuka ne ya saka shi ɗan ƙaramun murmushi yace"ya isa ni kar kiyi mun kuka amma ina so wannan ya zama na karshe,sannan ba domin na takura miki bane ina dubawa ne saboda ke,"kallan ledojin hannun yayi yace "kawo nan na taimaka miki dasu"babu musu ta bashi tana mai binsa a baya tanaji a ranta kamar shine ya rage mata bayan Appa a gidan sannan tana fatan hakan kar ya zama hasashe.

Koda ya aje mata sallama yayi mata yana mai sake sanar da ita ta kiyaye.

Bayan ya wuce ta fara duba kayan tana ji a ranta sunyi tsada da yawa sannan sunyi yawa ,amma hannayenta a ɗaure suke dan muddin tana san zama da Ummi lafiya wajibine tayi shiru,zubasu tayi kan couch da zummar idan ta kintsa ta kaisu closet,key ta sakawa ɗakinta kafun ta rage kayan jikinta ta ɗauko bathrobe ɗinta daga Cikin kayan wankin ta da aka kawo ta saka,

Kai tsaye bayi ta nufa dan wankan take so kawai taji tayi ,tana ƙokarin buɗe kofar taga ta buɗe kamar tsafi,Yaya sagir ne ya bayyana daga cikin bathroom ɗin yana mai faɗin"tadaaa,Good evening delicious".

Topa.

Bakina da goro.

TBC

Muhaɗu gobe idan Allah ya kaimu dan jin ya zata kaya.

Nice taku

CHUCHUJAY🥱

08130229878

Message me kofar amsar ƙorafi a buɗe takee❤

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top