15

💥KISWA💥

(Surrogacy was the cause)

         Na

CHUCHUJAY ✍️

Ku bi whatsapp channel ɗina domin karatu cikin nutsuwa.

https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05

Book1⃣

Page1⃣5⃣

________Murmushi Shine kawai abunda ke kwance akan fuskar kiswa yayin da a lokaci guda idan ka kalleta zaka gane tana cikin farin ciki ne , hannun ta guda ɗaya riƙe yake da wayarta manne a kunnen ta tana Mai sauraran Haidar yana rera mata waƙar yabonta tare da zayyana mata irin adadin farin cikin da yake ciki,knocking ɗin da ake a ƙofarta ne ya saka tayi excusing kanta da tabbatar masa zasuyi waya anjima kafun sukayi hanging up ta bawa Mai ƙwanƙwasawar izinin shigowa.

Saleek ne hannun sa ɗauke da bunch na flower ,da mamaki ta kallesa tana Mai cewa"Kai ne dama kake knocking?it doesn't sounds like you "

Murmushi Yayi ya samu guri ya zauna yana Mai aje flower ɗin kan table ɗinta yace"Good morning beautiful,ga flower nan Mai kyau na gani a hanya ta 'na siya cos kyawunta a kyakkyawan hannu kamar naki hope you love flowers,and knocking kuma ai abune na wajibi,forget wancan lokacin danake behaving gareki as a jerk ,trust me im one sweet guy that respect women,so tell me naga kamar kina cikin farin ciki share with me".

Ɗaukar flowers ɗin tayi tana Mai kaiwa saitin hancin ta kafun tayi sniffing tace "i love flowers ,and thank you for trying to be a Good guy"aje flowers ɗin tayi tace"dama Ina da empty Vase ina zuwa"tashi tayi ta shiga cikin store room ɗin dake cikin office ɗin ta ɗauko Ƙaramun Vase ɗin ta ɗora masa kan desk a gaban sa tace "oya get to work".ƴar ƙaramar dariya yayi yace "ke bama kya tsoran wani ya shigo yaga kina saka acting chairman aiki ko,i mean the guts for me".

Ƴar karamar dariya tayi kafun tace"well a gaban kowa you're an acting chairman wanda zai zama chairman In two weeks time amma a gabana idan ina tare da kai i only See my friend and i cant help it kai ka bani wannan damar and abun mamakin Shine i like it and Guess what,farin cikin da kaga inayi ba komai yake sani ba face yau Appa yace iyayen Babe su tura a tambaya masa Aure na ,i Just can't help it na kasa boye farin cikina ,i mean it was a rough road ɗin da yanzu nake jin kamar anzo ƙarshe."ƙarshe maganar tayi tana Mai saka fuskar damuwa kaɗan.

Wani irin yanayin Saleek ya tsinci kansa jin wai za'a zo tambayar Auren ta wanda take cikin mutukar farin cikin da ba sai an faɗa maka ba ,Ganin kuma yanayin da ta saka a fuskarta lokacin da takai ƙarshen maganar ya danne san ran sa yace "Wow im very Happy for you,i mean abu ne na ayi murna cos finally Mai sakaki mantawa gaban wani kike zai kaiki gidan sa las las,but What's with the sad face ?hope ba wani matsala ".

Ɗan shiru tayi tana kallan sa tana Mai nazari a akan sa ganin yarda ya nuna mutuƙar damuwarsa ,murmushi tayi tana mai wasa da hannunta tace"kasan its funny yarda wai ni dakai ne muke zaune muke magana a matsayin abokai like har kana nuna damuwarka a kaina,i just hope ba wani fansa kake san ɗauka akai na ba,idan fansa ne just tell me already domin kuwa im getting comfortable around you musamman da yarda kake nuna kulawarka akaina,kaga ni bana da wata ƙawa mace wadda zance maka mun shaƙu sosai,they are all schoolmates waɗanda they are after Farry not me dan yanzu ma duk sune ƙawayenta and idan kaga yarda suke ignoring ɗina sai ka ƙaryata kace ba tare mukayi karatu ba,and ni i dont care cos ni Abunda nake chasing daban yake da wanda suke chasing ,i want to build my self dan ni in ten years ina hangoni da company wanda nice na ƙirƙiresa,Thats how ambitious i am.

Licking leben sa yayi yace "that sounds interesting ,well wani lokacin aje abokai barkatai ma matsala ne domin sai kiga wanda ka ɗauka naka na jikin ka Shine zai bada babbar gudunmawa wajen ganin ya lalata ka,amma a nawa bangaren what i have towards you is pure ,babu cuta babu cutarwa cos attimes idan na kalleki over hills kan Haidar sai naji a raina mai yasa bani na fara haɗuwa dake ba,cos i mean a fahimtar ki da nayi cikin ƙankanin lokaci na san you're a Good person,tsakanina dake was a bad encounter wadda ta b'ata mun rai sosai bazan boye miki ba,amma daga baya na fahimta you did it for Your sister no matter yarda zakiyi denying nasan you're a family person kuma baki da san kanki wanda yana ɗaya daga cikin abunda yasa naji bai kamata na zama bad guy ba akan ki,i wont lie na fara jin ki a raina ina mai ji dama Nine Haidar ,but idan na kalli yanayin ta wani bangaren sai na bawa kaina haƙuri cos idan ina san na zama right hand buddy ɗinki i have to be like a brother figure,yarda zan so wa Amatul'islam abu mai kyau haka zan so miki and Haidar mutumin kirki ne wanda nasan zai riƙeki da amana fiye da ko wanne ɗa namiji a duniya so Chill girl,komene Kike so a rayuwa Ina san ki sani ina gefenki,Just talk ni kuma zan supporting ɗinki da dukkan karfina i promise,duk damuwar ki zan ɗauke ta tawa,i will be a Good listener indai zaki faɗa mun damuwar ki.

Bata san tana hawaye ba sai da ya ɗiga kan hannun ta,saurin goge wa tayi tana mai yin ƴar dariya kafun tace"you're getting me emotional,nagode sosai,naji daɗi da baka yi complicating abu tsakanina da Kai ba,and naji daɗi da kamun alkwarin Kasancewa a gefena duk lokacin da na buƙace hakan,naji daɗin babu abunda zance maka sai dai nace Allah ya saka maka da Aljanna ya baka mace ta gari and By the way wace Amatul'islam?"

Shafa kansa yayi yace "nasan yanzu nan kina tunanin girlfriend or something ,well im sorry to disappoint you,Amatul'islam sister na ce,shes 19 and yanzu haka tana cyprus' university final year and shes kind of Tough But nice She's low key dan bana tunanin akwai wanda ya taba ganin ta face to face a company ɗin nan sha tana nan dawowa soon "

Ɗan murmushi Tayi tace "and abun mamaki chairman bai taba mun maganar ta ba,bazan manta mata wannan side ɗin labarin ba cos duk labarin sa akan Saleek ɗin sa ne,tho nasan yana da daughter But ban san sunanta ba,sunanta mai daɗi"kallan time tayi tace"well oga Sir aiki muka zo kar anjima kagama hirar nan dani ka aiko mun da sacking letter"murmushi yayi yace "well idan zan sacking ɗinki to tare zamu tafi,mu haɗu lunch time and bills on you".

Dariya kawai tayi masa tana mai kaɗa kai har ya fita yana maimaita mata,bills on you 'fa.koda ya Fita Kai tsaye office ɗinsa ya nufa yana mai jin wani irin nauyi a ƙirjinsa musamman da maganar Auren Kiswa ta ringa dawo masa kamar fitina,zama yayi ya dafe kansa yana mai ambaton Allah,yana wannan yanayin Khalipha ya shigo,ƙokarin saita kansa yayi amma Khalipha ya riga ya gano ,zama Khalipa yayi yace "mutumina menene damuwar ni Nasan Ƙwana biyun nan akwai abunda yake damun ka man talk to me kasan ni da Kai muke sharing damuwar mu kuma kaga mun samawar wa kan mu masalaha,kamun magana mene ke damun ka.

    Ajiyar zuciya Ya sauke yace"Khalipa na gaji da boye maka saboda bazan iya cigaba da boyewa ba,ban san yaushe ya fara ba ban kuma san ya akayi haka ya faru ba,abu guda ɗaya na sani wanda Shine "im madly In love with Kiswa and i cant help it".

Cike da confusion Khalipa yace"wace Kiswa ɗin ?kar dai kace mun babe ɗina?"

Tsaki Saleek yayi yace"abunda yafi babe ɗinka bana san iskanci ina maka maganar da bata wasa ba kana mai da ta wasa,kana tunanin nasan wata Kiswa ne bayan ita?".ɗaga hannu Khalipa yayi yace "naji my buddy is In love,so mene kake jira,Fine boy like you wanda yan mata kewa zarya,ka faɗa mata mana nasan dai bazata rasa sanka ba cos i mean ka kalleka mana".

"Nan matsalar take my guy,ina mutuƙar san Babe ɗin nan amma ina yi mata san da bazan so kaina ba domin shi ba domin maganar da nake maka yanzu haka maganar Aurenta ake sannan yaran da zata Aura mutuwar sanshi take ,babu abunda wani Zaice ta rabu dashi,and i respect that saboda bangaren sa ma haka take,ni dai Just pray for me Allah ya yaye mun cos bazan so ace nan gaba ina san matar Aure ba ,domin kuwa ina san na zama kamar ɗan uwa a gareka domin idan na kalli cikin idon ta  yana faɗa mun wani saƙo daban bayan wanda take nunawa a zahiri,i can feel it that tana zagaye da maƙiyanta kawai bata san magana akai ne".Saleek ya faɗa yana mai jin wani irin nauyi a ƙirjinsa.

Tasowa Khalipa yayi ya dawo inda yake ya zauna kan desk ɗinsa ya dafasa yace"mutumina this is deep amma kasan shawarar da zan baka cikin wannan tafiyar? Ba komai bace face ka fara dating,Just Try Elham yarinyar nan tana sanka tana binka ,tana da kyau ga kuɗi ga aji malam,ni zan iya cewa tafi Kiswa ma.

Wani wawan tsaki Saleek yaja yace"wannan fiƙaƙƙiyar yarinyar ce tafi Kiswa?"you're mad,ka kalli Kiswa da kyau ,black beauty ga aji ga nutsuwa ga sanin ya kamata,amma Elham 'fa kasan idan magana ake ta tarbiyya bata da ita ko kaɗan,tayi ta wani tab'a mutum da sunan relationship abeg Who does that,yarinya mai nutsuwa da kamun Kai bazatayi abunda Elham take yi ba.

"Naji naji SBM amma ka sani Elham na maka soyayyar da zaka iya juyata zuwa yarda kake so,amma kaje kayi tunani,yanzu dai bari naje nayi aikin gabana kafun ka fara maganar kora ta".

Dariya Saleek ya saka yana mai bin Khalipa da kallo yana wata tafiya da rangwaɗa,juya maganar Khalipa ya ringa yi akan sa yana tunanin iyuwar hakan dan Elham bad news ce .

                    ***********

    Zaune Farry take a office ɗin Haidar tana sipping coffee tana jiran ya gama ganin patient tukunna,wurin awarta guda a zaune tana jiran sa dan coffee ɗin da take sha Cup na biyu kenan,ta riga ta saka a ranta bazata bar office ɗin sa ba yau sai ta gansa,tana wannan zaman Ya shigo fuskarsa cike da kulawa yace"im sorry Farry na barki ke ɗaya anan wallahi patients ne sai godiyar Allah yau ɗin,and its Like a charity thing muke yi yau dole ni zan duba su a basu magani,But i will make it up for you".

    Murmushi tayi tace"how will you make it up for me?ko ni zan zab'a cos ina buƙatar abu a gurinka".zama yayi yace "Uhum ina saurarenkii,ki faɗa ko mene zan miki indai zan iya"gyara zaman ta tayi tace"zaka iya ma dan ba abune wanda yafi ƙarfin ka ba,nasan kasan maganar da Mother sukayi da ummi akan mu Sannan Nasan dan bakaji ta bakina bane amma Haidar ina san ka sani nice na dace da Kai ba Kiswa ba,zan so ka fiye da Yarda Kiswa zata so ka,aso mene ma take maka bayan kuna tare ma tayi samari biyar,yanzu ma ana maganar Auren ku soyayya take da Saleek yaran chairman ɗin company ɗinsu, kalleni da kyau Haidar ni ce na dace da Kai ba Kiswa ba,kasan dai nice nake zaune da ita gida ɗaya, i know her best ,babu wani abu da zata ƙareka dashi amma ni fa?nike kula da dukkan wani aiki a kamfanin Alijua,karfin signature  yana hannuna,bazan maka bani bani ba saboda im loaded amma Kiswa fa?shes Just a rat hiding behind Ayzel foundation nothing more,babu wani abu da Kiswa zata tsinana maka dashi sai dai ta zamar maka liability,please Haidar marry me. "

    Idan da wani zai zaunar da Haidar ya faɗa masa wai Farry ke zaune gaban sa tana faɗa masa waɗannan maganganun sai ya ƙaryata,Kallanta yayi still mamaki yaƙi sakin sa yace"da ace mafarki nake na wannan scenario ɗin tsakanina dake zan ta addua ne na farka nayi Kuma fatan ban maimaita ba,wallahi Faridha im very disappointment In you,Kin bani kunya fiye da yarda bana tunani,wallahi Faridha ke ba yar uwa bace ta gari domin da ace ke yar uwace ta arziki bazaki taba zuwa mun da wannan maganar ba bayan kinsan da ace Kiswa ce a matsayin ki bazata tab'a yi miki abunda kike ƙoƙarin yi mata ba amma ina san ki san wani abu,Kiswa bazataji wannan maganar ba saboda ban san yardarta  ta ƙare,abu guda ɗaya kuma da nake so ki sani Shine Allah kaɗai zai iya raba tsakanin da Kiswa ba mutum ba,ina kuma so ki sani idan ni dake muka kasance a duniya bazan taba Aurenki ba na miki alkwari,abu guda ɗaya yasa bazan faɗa miki magana mara daɗi ba wanda Shine Kiswa,bazan so a ce wanda suka haɗa jini dashi ba ya ji maganaa mara daɗi daga bakina ,hakan kamar na zagi soyayyata ne ,ki tashi ki fita mun a office kuma kar na sake ganin ƙafarki a inda nake .  "

    Sosai zuciyar Faridha take mata tafasa kamar zata ƙone,tashi tayi ta ɗauki hand bag ɗinta da wayarta ta nuna sa da hannu tace"Kai nawa ne Haidar ,tunda na saka idona da zuciyata kuwa akanka babu abunda zai hanani samun ka musmman da kowa ke nuna mun bazan samu ba,kajira zuwana"binta yayi da kallo har ta fice a office ɗin tana maiyyin wata irin tafiya kamar zata karye,tausayin Halin da Kiswa zata tsinci kanta muddin ta samu wannan labarin yaji,he cant blv tana undergoing irin wannan trial ɗin, dan koda bata faɗa masa ba yasan tunda aka fara maganar su tana fuskantar ƙalubale wanda yake sakashi jin dama a dai dai lokacin ta zama matar sa ya ɗauketa daga dukkan wani yanayi mara daɗi na rayuwa ,wayar sa ya ciro sanin a dai dai lokacin tana aiki ya tura mata text na"i love you and i will forever do".

Murmushi yayi lokacin da yaga ta maido masa babu bata lokaci da"i love you back Baby,no one But you".idan yace bai san Kiswa fiye da kansa to tabbas babbar Ƙarya yayi,domin kuwa yarda yake jinta a zuciyarsa abune da idan yafara faɗa za'ace yayi shiru haka nan,fatansa guda ɗayane wanda Shine kar ya mutu bai mayar da ita matar sa ba ,koda kuwa ana ɗaura musu Aure Allah ya ɗauki ransa ya gode masa domin kuwa ya biya masa buƙatarsa na mayar da ita matarsa and babu wani mahaluƙi da ya isa ya chanza iyuwar hakan.

________kamar yarda Appa Ya bukaci ganawa da Mahaifin Haidar hakkan ne ya kasance domin kuwa washe garin ranar suka zo dan ayi maganar ,kawun ta Halilu da taso a saka a ciki surprise Appa ya bata dan kuwa jirgi ya biya masa yazo Abuja,zama ɗaya sukayi Aka saka Aure watan da zai kama,Kawu Halilu yaso a ɗaura a ranar dan acewarsa mene amfanin jinkinrin tunda sun riga sun fuskanci junansu,Appa ne ya bada shawara akan a bari zuwa watan dai a ganinsa zaifi dan haka suka samu masalaha da juna aka tsayar da magana guda,a ranar idan ka kalli Haidar da Kiswa abun ba'a magana dan sun taka wani mataki ne na zama tare wanda lokaci ƙalilan ne ya rage su Kai matakin da suke mafarkin kaiwa a rayuwa.

    Tunda akayi maganar tsayar da ranar Kiswa da Haidar mutane uku suka shiga cikin mutuƙar tashin hankali,meeting suka zauna na musamman Farry na ta cin uban kuka,lallashinta kawai Mother take ita kanta ta rasa abunda yake mata daɗi,cikin kuka Farry tace"Mother ya ake so nayi?lokaci guda na nuna ga abunda nake so Amma Appa ya kulle ido zai bawa Kiswa bayan kuma Shine mutum na farko da yake fara faɗa mun na kasa samo miji nayi Aure ,yanzu kuma ga wanda nake so kuma. Idan da ace za'ayi adalci dani ya dace bada Kiswa ba,ba wai maganar san Kai ba,itace ta lalata blind date ɗin da Appa ya haɗa mun da Saleek and yanzu gashi tana tare da Saleek ɗin to tabar mun Haidar mana indai ba san Kai ba.

Cike da wani irin yanayi Mother tace"kika ce mene?Kina nufin ita ta b'ata miki blind date Shine kikayi shiru baki faɗa mun ba?"cikin kuka Farry tace"wallahi Mother baki ga yarda ta b'atani agurin sa ba,a irin shigar da tayi kanta In dai namijin kirikine yana ganinka zai fasa Auren ka sannan maganganun da ta faɗa masa kansu bazan iya maimaitawa ba".

Tashi Mother tayi tana mai cewa"jar bura ubancan,ai kuwa wallahi bazata sab'u ba,taci ƙarya ta tarwatsa miki farin cikin ki ita ta samu,wallahi idan a tafe take ni Chan na ƙwana bari naje na samu Appan naku".

Cike da fitina Mother ta nufi ɗakin Appa,Kai tsaye ta faɗa tana mai cewa"wallahi an daɗe ana ruwa ƙasa na shanye wa,wannan karan kuma ta gaji,billahillazi idan baka ɗauki mataki ba ni zan ɗauka da kaina".

Appa dake zaune yana danna wayarsa ne ya ɗago ya kalleta yace"wai ke a rayuwar ki ba ki san a zauna lafiya ne?tunda aka fara maganar Auren Kiswa kullum Kina da damuwa ,a yanzu mene damuwarki mata?"

"Nice nake da damuwa ma kuwa,ai a idanunka Kiswa bata laifi to a yanzu bazan taba yarda ba sai an Ƙwatarwa Faridha yancinta ,wannan yarinyar Kiswa da kake gani muguwa ce wadda bata san cigaban wani,to date ɗin da Ka haɗawa Farry da yaron mai AYZEL FOUNDATION itace ta lalata domin ita taje maimakon Farry sannan bata tsaya nan ba sai da ta b'atawa Farry suna a gurin sa ,dama ni dai ince ta yaya namiji zai ƙi yarinya kamar Farry? "

Aje wayar Appa yayi yana mai kallan Mother yace"daga ina kika samo wannan maganar kuma?"

"Ka fito kaji ai Kiswa ɗin na gida itama haka Faridha ɗin babu wanda ya isa yayi ma wani ƙarya"fita tayi inda Appa baya da wani zab'i da ya wuce ya bita.

Koda Mother ta fita Kai tsaye ɗakin Kiswa ta nufa wadda already ta kulle ta kwanta dan bata barin ɗakinta a buɗe tun haɗuwarta da Sagir,irin ƙwanƙwasawar da Mother take kamar tashin hankali Shine ya tashi kiswa daga ɗan baccin da ta fara,cikin muryar bacci tace "Wane?"

"Uwarkii ce Zubaida "Mother ta bata amsa,hijab ɗin da tayi sallah dashi ta dauko ta saka kafun ta buɗe ƙofar,kamar tashin hankali haka Mother ta Jawo ta waje ta ɗauke ta da mari.

Gafe guda Farry ce wadda taƙi daina kuka inda sagir ke gefenta yana bata haƙuri Appa kuma yana mai kamo Mother dake shirin yiwa Kiswa luguden masu,ihun da Mother take ne ya jawo hankali Sameer wanda already shima ya kwanta dan a lokacin ƙarfe Goma na dare.cike da mamakin halin da ya same su yace "lafiya ??"

Cike da bala'i Mother tace" inafa lafiya,gata nan ka tambayeta mene tayiwa Farry,.ganin abun na neman wuce gona da irin ne ya saka Appa cewa "kowa ya sameni a falo na."

    Zaune baki ɗayan su suke Falon Appa inda Farry taƙi daina kuka,sameer ne kalleta yace"to ke idan baki daina kuka ba tayaya za asan mene matsalar har ayii maganinta,dama ai kuka alamune na mara gaskiya".

Cikin bacin rai mother tace"ka kuma faɗa mata mara gaskiya kaga abunda zai faru sakarai mara kishin yan uwansa"saka bakin da Appa yayi ne ya saka kowa ya nutsu kafun ya saka Faridha ta fara bayanin abunda ya faru.



*su hajiya Farry kuma da karyaa ake tunanin za'aci yaƙi,Allah ya kyauta,

Shin zata ci wannan yaƙin ko kuwa A'a?

Ko kun san mai yasa ake wa wannan littafin laƙani da Surrogacy was the cause?

Ku cigaba da bibiyar littafin Kiswa domin jin yaya zata kasance.

Mu haɗu a update na gama.

TBC

CHUCHUJAY ✍️

08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top