12
💥KISWAH💥
(Surrogacy was the cause)
Na
CHUCHUJAY ✍️
Book1⃣
Page 1⃣2⃣
__________Washe gari cikin wata irin walwala Kiswa ta tashi,dan haka tayi shirin office ,bata da Niyyar yin wani breakfast dan haka tacewa Baba Baraka idan an tambaye ta inda take tace tana azumi ,ille kuwa Appa ya tambayi Baba Baraka ganin kowa yazo banda ita,Kafun ya rufe baki daga tambayar da yayi Farry ta cabe inda take cewa"Appa we are complete here tunda dai dama ai ba ƴarka bace Ko Mother Why bother?"
Wani irin kallo Appa ya bata Kafun yace"sai dai in ba ƴar maman ki ba amma ni Kiswa tawace domin kuwa yarda nake jinta a raina ma bana jinki sannan idan na sake jin wata maganar banza a bakin ki zaki zauna a gida ki bani kujerar office ɗina dan bana tunanin zaki iya girmama ma'aikatana yarda ya kamata duba da yarda respect ɗinki yake neman ƙarewa ".
Dif kake jin Farry kamar anyi Ruwa an ɗauke,duk da yarda bakin ta ke ƙyaiƙayi akan tayi magana ta ƙwabesa dan tasan halin Appa.
Fitowa Kiswa tayi cikin shirinta tsaf tare da wani vibe Energy da ta samarwa kanta dan tayi Alƙwarin sauke nauyin Saleek dake kanta a yau wanda take ganin Shine best solution,at least bazai kashe ta ba haka zalika bazai daketa ba,ganin yarda suka zauna suna cin abinci zuciyarta taji tana mai bata taje ta zauna musamman yarda taga seat ɗinta empty ,Allah ya sani tana san su tana ƙaunar su saboda sune family ɗin da ta sani sannan ta shaƙu dasu tun yarinta bata fatan ace yau sabani mai girma yana shiga tsakanin su amma Mother is hellbent taga ta b'ata mata abunda take so da sunanta dana mahaifiyarta ,dan haka itama ta ɗaura ɗamarar kare duk wani bullet da zata jefeta da shi,Takawa tayi dan zuwa gaisawa dasu Kafun ta wuce,tana isa gurin Appa ya Faɗaɗa fara'arsa yace "har na fara tunanin fushi Kike damu da yasa ba zakici abinci da mu ba "cike da ƙaunarsa tace "Appa ni ina zan fushi da family na mai kyau,na tashine da azumi ,ina ƙwana"ta faɗa gudun zama taci abincin dasu duk da ba azumin take ba.
Cike da jin dadi ya amsa mata gaisuwarta yayin da ta gaida mother da yayyinta amma su kadai suka amsa banda mother,ba tare da ta damu ba ta tashi tayi musu sallama ta fita..
**********
Ta daɗe cikin motar ta tana tunanin yarda zata fuskanci Saleek kasancewar sa mutum mai murɗaɗen hali,ta iya iyuwa jira yake tazo tayi confessing ya ɗauki wani matakin akanta amma hakan bai dameta ba domin kuwa ta shirya daukar consequences na abunda ta aikata at least ta fito masa da gaskiya kuma zata basa hakuri hukuncin da zai ɗauka ya rage nasa ,wata irin kunyarsa take ji musamman da ya kasance irin sunayen da ta kirasa dasu waɗanda ba hallayarsa bace sharrin Farry ne ,ajiyar zuciya tayi ta dauko Jakarta ta fito a motan ta kulle ta nufi cikin company ɗin,straight office ɗin Saleek ta nufa Kafun kwarin gwiwarta ya ƙare dan a yanzu ta shirya fuskantar sa da karfinta ,koda ta isa bakin ƙofar sa tsaye tayi tana cije baki Kafun tayi karfin hali wajen ƙwanƙwasa masa ,knocking ɗaya tayi ya bata izini da ta shigo kamar barauniya haka ta shiga bakinta ɗauke da sallama,kamar an mitsinesa haka ya ɗago ya kalleta dan baya expecting ɗinta ,jingina bayansa yayi da kujerarsa yana kallanta Kafun ya Amsa mata sallamar ta ya ƙara da cewa"lafiya dai Ko? dan duk wani document, da nake bukata yana kan desk dina sannan duk wani meeting schedule ɗina Khaleefa yayi arranging mini so a yarda nake tunani abu daya ne zai kawoki inda nake wanda Shine ƙarya da rashin kunya domin kuwa idan akwai abunda kika ƙware akai Shine wannan abu guda biyun bayan aikin ki dan haka bismillah nasan duk wata hanya da zanbi dake in dai Nine have a seat ".
Zama tayi tana mai saukar da kanta ƙasaa cike da jin kunyarsa sosai,kula da yayi da kunyarsa da take jine yasaka shi kwashe wa da wata irin dariya har yana mai fito da ƙwalla yace"kaji mun yarinyar nan fa,nine kike jin kunya Ko kuma wani sabon salan munafurcinne kika shiryo da safiyar Allahn nan kika zo ki sauke mun ita dan bana tunanin Ko office ɗinki Kin shiga,Allah yasa ba wani bacin ran kika kullo mun ba domin kuwa Dariyar nan da kikaga inayi akwai wani abu a bayanta idan aka tunzura ni dan haka karki fara.
Ajiyar zuciya tayi ta ɗora hannayen ta dukka kan desk ɗinsa tace "Sir bana zo bane nan domin aiki ba, nazo ne domin confession wanda nake fatan zaka karbi ban haƙurina in the process ,ni mutum ce mai rauni idan abu ta shafi Family na wanda wani lokacin bana tunanin menene zai fito sakamako saboda wannan mistake din nawa,haka akan ka i made a huge mistake wanda ya sakani nake jin mutuƙar kunyar ka a yanzu haka ,kayi hakuri dangane da hallayyata dana nuna maka mara daɗi sannan da ɗabi'un dana danganaka dasu waɗanda ba naka ba,it was all my idea bana Farry ba kar kace zaka ɗauki wani mataki akanta ,ta nuna mun bata san Alliance da iyayen mu ke san haɗawa tsakanin ku ,a yanayin yarda ta nuna mun rashin san abun yasa na kawo idea ɗin wanda na tabbata Babu wadda zai so ya Auri mace kamar wadda na nuna maka a ranar ,nasan ban kyauta ba and it was very stupid of me ,dan Allah dan Annabi ka samu wani guri da gurbi a cikin zuciyarka ka yafe mun ,idan kuma kace zaka dauki wani hukunci ne bazan yi ƙorafi ba ,hakkin kane kuma a shirye nake domin na ɗauki wani hukunci da zaka mun amma ina neman alfarmarka da kayi hakuri kar ka saka Farry Ko mahaifan mu a ciki dan idan Appa yaji maganar nan wallahi bazamuji daɗi ba shi yasa nazo na sameka..
_Ya ɗauki lokaci kaɗan yana kallanta tare da hango tsantsar nadamar abun a tattare da ita sannan a ɗayan bangaren abunda yake hangowa a idanun Kiswa baya tunanin haka yake a bangaren Farry domin shi mutum ne mai gane mutane cikin lokaci mara tsayi sannan selfishness da ya hango tattare da Farry ba wai gizo ne yake masa ba gaskiyar al'amari ne.shafa sumar kansa yayi yace"so idan Babu hannun ita waccan sister taki a wannan babban plan naku mai yasa a office ɗinki ta nemi da nazo mu sasanta bayan ga dama tana da ita tun farko taƙi amfani da ita ,Ko hakan yana nufin ke kina sona ne kuma kina san ki mallakeni a maimakon ta dan haka kika kawo waccan shawarar after all nasan wancan likitan ba fina komai yayi ba and ke kuma you're not bad zan iya maneji dake duk da kuwa you're not my type.
Tsintar kanta tayi da murmusawa kafun tace "Sir with all due respect relationship ɗina bai shafi laifin da nayi maka ba sannan idan zaka mun alfarma bana san ka sakashi cikin maganar da muke yanzu domin kuwa Haidar rayuwa ta ne bana jin kuma a rayuwa zan iya bawa wani ɗa namiji gurbinsa koda da wasa ne shi yasa ban saka hannu akan waccan takardun da ka bani ba na zabi da nazo na faɗa maka gaskiya domin kuwa soyayyata ita ce rayuwa ta babu kuma abunda zan iya trading ɗinta akai,haka ƙarfin ta yake gareni,Farry kuwa akan maganar da tayi maka ta iyu kayi mata ne a yanzu wanda da nasan zaka mata wanchan act ɗin ma bazai samu gurbi ba,and ka yarda dani When i said this Sir Farry yarinyar Kirki ce duk da kuwa ɗan Adam yana da wani guri a gefe guda na rayuwarsa wanda bai cika ba, amma idan kaga Its okay zaku iya sasantawa kamar yarda nace dama abunda iyayenmu ke so kenan,bazan dai daina baka hakuri ba dan Allah kamun afuwa.
Murmushi ne kwance a fuskarsa yana mai yaba wautarta a soyayya Kafun yace"hala wannan soyayyar first love ce,kinsan akanta Babu gangacin da mutum baya aikatawa ,akan maganar ƴar uwarki kuma She's definitely not my type ,sannan ki ƙwantar da hankalin ki kamar yarda kika buƙata bazan saka sister ɗinki a ciki ba sannan maganar nan zata shafe kamar ma ba'a taba yinta ba,kinsa ni family man ne ina mutuƙar san naga mutum na da dedication akan danginsa dan haka zan yafe miki komai ya wuce amma fa cikin sharaɗi guda ɗaya.
Saurin gyara zamanta tayi tana mai san jin menene wannan sharaɗin,ganin yarda ta zama restless tana san jin mai zai faɗa ya saka yayi waving hannun sa yace "calm down ba wani abun tashin hankali bane kike wani zazzare mun ido ,im not a bad person,ba komai kuma ne zai zama hukuncin ki ba face zama abokiya ta sannan mai tayani office work ɗin daya kakare mun ,.wayar sa ya cire a key ya tura mata gaban ta yace idan muna da deal ki saka mun numbern ki cikin wayana daga yanzu kuma Kin zama friend ɗina.
Jin maganar tayi kamar wasa dan ba abunda take tsammani daga tare shi ba kenan,haɗe hannayen ta tayi guri biyu tace "Sir im sorry ban gane ba".
Ƴar dariya yayi yace "na faɗa miki ni ba mutumin banza bane sannan bana nufinki da cutarwa ina sone kawai mu ƙulla abota wanda Shine hukuncin ki so zabi ya rage naki sannan na baki assurance bazaki samu aboki kamar Saleek ba and yauwa bana san Kina kirana Sir ɗin nan sunana Saleek kuma dashi nake san ki kirani ba wani Sir ba"
Kallan sa take cike da mamakin juyin halayyar sa inda shi kuma yayi mata alamu da ido akan ta ɗauki wayar ta saka number ta.cikin nutsuwa ta ɗauki wayar tasa ta rubuta number ta ta miƙa masa,faɗaɗa fara'arsa yayi sannan yayi dialing ,ringing wayar ta tafara cikin Jakar ta ,daukowa tayi ta kalle shi,shima ɗin ita yake kallo Kafun yace"oya save my number sannan ina mai tayaki murnar zama abokiyar Saleek ina kuma san na tabbatar miki kamar yarda kike loyal a soyayyar ki,haka nake a abotata so lunch during lunch time and Its on me".
Murmushi kawai tayi tace "thank you"still awkwardly domin kuwa abun baki ɗaya sabo ta tsincesa,ta kasa yarda wannan arrogant man ɗin ne a gabanta haka,koma dai mene tasan she will need to be very careful,sallama tayi masa ta tashi dan fita,tana ƙoƙarin fita Khalipha yana shigowa,matsa mata yayi ta wuce tana mai gaida sa inda ya amsa cike da fara'a da sakin fuska,binta yayi da ido har saida ta b'ace Kafun ya kulle ƙofar ya shigo ciki yana mai faɗin"mutumina ka ƙyaleni na gwada sa'ata kan Kiswa dan Allah alaji,babyn nan ta kashe ni so nake koda ba Serious abu ba a ɗan wana".
Haɗe rai sosai Saleek yayi yace "a wana mene?bana san iskanci fa Khalipha,ba tun yau ba nake faɗa maka Kiswa ba Ko wacce irin mace bace kaje dai Chan ka nemo yan matan ka marasa nutsuwa amma banda wannan sannan idan baka sani ba na sanar da kai cewa She's in a Serious relationship sannan She's so loyal about it dan Ko kaje kace kana santa a banza dan haka ka riƙe sauran mutuncinka da take gani mu zauna lafiya.
Zama khalipa yayi kan desk ɗin sa yace "ita da take Serious relationship sai kayi yaya?"
"Nayi yaya kuwa?dame fa?"dariya Khaleepa ya saka sosai yace "mutumina kenan nasan dai akwai wata a ƙasa kuma idan tayi tsami zamuji "ƴar waƙa ya fara masa ta zolaya,jifan sa Saleek ya fara da files ɗin sa yana mai faɗa masa he's fired!
Dariya khalipa ya fita yanayi yana mai faɗin"mutu ka raba ɗan nan Koma bazan daina faɗa maka you're in love ba"
Hannu Saleek ya saka a baki yayi ƴar dariya yana mai shafa kansa yana maida maganar Khalipha a kansa,Kaɗa kai yayi a fili yace "No Babu ma yarda za'ayi haka ya faru no",files ɗin da ya jefi khalipa da ya kwashe ya fara duba su da kawar da tunaninsa.
Kamar yarda ya nemi suje lunch hakan ya faru inda baki ɗaya cikin rashin sabo dashi taci abincin yayin da shi kuma yake mata hira cikin san ta saki Jiki dashi,wayarta da tayi ringing ne ta saka ta dakatawa tana mai faɗin "excuse me "kafun ta kara wayar a kunne tace"Assalamu alaikum hayatee"
Take bite ɗin da Saleek ya saka a bakin sa yana tauna ya dakata,wata irin shagwababiyar murya da tayi magana da ita ce ta dake shi,he Just cant blv a gaban sa dan yarda ta cigaba da wayar kamar ma baya gabanta,cigaba yayi da cin abincinsa a hankali yana sauraran yarda take jefawa Haidar kalaman soyayya,ya kasa yarda wai Kiswa ce.
Sai bayan ta gama wayar ne tayi realizing wai a gaban Saleek take,take wata kunya ta lullube ta ta fara kame kame,murmushi yayi yace"yanzu ne kike jin kunya ta bayan Kin gama narkewa a waya,dole nayi jotting down friend ɗina idan babe ɗinta ya kira ta mantawa take da kowa a gabanta"
Sosai taji kunyarsa ta kamata dan kamar yarda ya faɗa indai akan Haidar ne ta wuce nan,haka suka gama cin abinci suka koma office a tare yana ta janta da hira wanda bata taba expecting yama iya ba.
Chuchujay
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top