11

💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

  Na

Chuchujay ✍️

Book1⃣

Page1⃣1⃣

  Da mutuƙar mamaki Mother ta juyo tana kallan Appa Wanda ya haɗe rai iya mutuƙar haɗewa,kanta ta nuna da yatsa idanunta sun kawo ruwa tace"ni zaka faɗawa abakin Aurena akan yarinyar da zubaida ta haifa ?"

Cikin nuna mata rashin wasa a maganarsa yace "ƙwarai kuwa idan kuma kina ganin bazan iya ba dan Allah ki ƙara taku daya daga inda kike kiga cikakken mamaki,magana da kika akan yarinyar da zubaida ta haifa Eh ita ɗin sannan ina so ki sani zan iya chanza ki amma bazan taba chanza Zubaida da Kiswa ba"maida hankalinsa yayi ga Kiswa yace"oya fara rama marukanki"Babu musu Kiswa ta matsa ga Farry wadda ke fuzgewa ta fara shatata mata mari har saida tayi mata huɗu masu kyau Kafun ta saka kuka jin yarda Farry ke kuka,har ga Allah rana ta yau ba ƙaramun muni gareta ba a gurinta dan ita mutum ce mai bawa family ɗinta muhimmanci ,bata san abunda zai taba mata su ,yau sai gashi irin sabanin da suka samu bashi da daɗin ji,kallan Farry dake faɗin wallahi bazata yarda ba Appa yayi yace "to dan Allah Faridha ki dauki mataki ni kuma zan baki mamakin da tunda nake matsayin Mahaifinki ban taba baki ba."

Sanin Halin sa idan yayi fushi yasa Mother da tayi tsit cewa"kija bakinki ki yi mana shiru anan Farry"wani irin kallo Appa ya bata yace "better da kina faɗa mata tuntuni da rana irin wannan bata zo ba"'dan shiru yayi yana nazari Kafun yace"Its better ku raba ɗaki, dama ai Faridha ɗin ta nace tun yarinta a haɗa su ,so dole yanzu tunda shashanci ya fara shiga tsakani kowa ya zauna ɗakin sa"

Yana kai karshen maganarsa ya bar ɗakin,kwafa Mother tayi itama ta fita,faɗa sosai Sameer ya fara yi musu inda Sagir yace "Just kallesu akan namiji wanda kilan ma yaudarace a zuciyar sa suke wannan faɗan kamar zasu kashe kan su"tsaki yayi ya fita a ɗakin yayin da Sameer ya yi musu Nasiha wadda Kiswa kawai ke gamsuwa dashi Amma banda Farry.daren Ranar Kiswa guest room ta kwana kafun washe gari tayi aikin parking to koma ɗakinta wanda yake da komai gyarawa kawai zatayi saboda Babu mai kwana cikin sa,washe gari bata iya fita aiki ba saboda ciwan kai dake damunta amma Farry kam karfin hali tayi ta fita dan da zaman gidan gwara ta fita ɗin koda ba office zata ba kuwa,Babu wani breakfast kowa ya kama gaban sa ban da Sameer wanda ya tsaya dan ganin mai Kiswa ke buƙata a saban ɗakinta ya taimaka mata.

              ••••••••••        ••••••••••       ••••••••••

TUKUR BULA'S MANSION

    "Son wait we need to talk like right now"mahaifiyar haidar ta shigo ɗakinsa tana mai zama kan couch kamar an koro ta,

Haidar dake tsaye yana gyara tie ɗin sa ne ya juyo yana mai cewa"Ummi hope im safe dai"kafarta ta ɗora kan ɗaya tace"trust me muddin kana tare da yarinyar nan Kiswa to bazaka taba zama lafiya ba,Ko kasan cewa ba yar ALIJUA bace sannan ɗiyar karuwa ce and bada Aure aka sameta ba,no bazan taba yarda da mace irin wannan ba cikin zuri'a ta".

Cike da confusion ya zauna yace"well rashin zama ƴar sa abune da na sani niece ɗin sa ce da Maman ta dashi uwa ɗaya uba ɗaya and ya ɗauko ta ne daga garin su bauchi bayan rasuwar mahaifinta ,a zallar sanina da kuma gaskiyar magana ita ba wadda aka haifa bace wajen Aure, da mahaifinta dangin sa kuma suna cikin garin Bauchi though sunyi abandoning ɗinsu,yanzu haka mahaifiyarta tana cikin garin Bauchi tayi Aure da yaranta biyu Khalel da Ra'abiatu ,Bansan Wake feeding ɗinki waccan maganar ba amma Ko wanne maƙiyin Kiswa ne and dole zan suing ɗinsa for defamation of character ki bani suna kawai Ummi.

Shiru ummi tayi tana nazari yayin da Abubuwa suka fara dawo mata daga zuwan Mother office ɗinta tayi mata tallan Farry har izuwa kiran da tayi mata jiya da daddare .kallansa Ummi tayi tace "ya zaman takewarta da Barrister juwairiyyah?"

'dan shiru Haidar yayi yana san ya fahimta dan a iya zamansa da Kiswa bata taba nuna masa koda da wasa ba tana fuskantar matsala a gidansu ba ,sannan a iya saninsa tsakaninta da yan gidan Babu wani matsala tana san su suna santa ,dan haka yace"Gaskiya Ummi i dont know about Mother tunda ba hirarta ta cika yi mun ba amma ga dukkan alama tsakaninsu ba matsala duba da yanayi na yarda mu'amalar Kiswa take da yaran gidan".shiru Ummi tayi tana kallan fuskarsa da yarda baya so ace akwai Matsala a rayuwar Kiswan sa,ajiyar zuciya tayi tace"i need to see that girl cos na tabbata akwai wani abu a rayuwarta wanda take boyewa,sannan a wannan gidan na Alijua na tabbata akwai bangaren da bata jin daɗi saboda Barrister juwairiyyah jiya take fada mun maganganun nan da daddare bayan na kirata,but my instinct is telling me otherwise duk da Kafun naji ta bakin ka hankalina ya yarda da maganarta amma da nayi magana da kai yanzu hankali na ya kwanta akan cewa ta haɗa labari ne saboda tana san ƴarta ta Auren ka ba Kiswa ba,koma dai yaya ne zamu san gaskiya Just bring the girl to my Boutique.

Tashi tayi ta fita tabar Haidar da jimami yana san sanin mai yasa tayi ma Ummi ƙarya sannan wacce irin rayuwa ma Kiswa ke yi a gidan ,yakamata yaje ya sameta,wayarsa ya ciro ya fara kiran layinta akashe dan haka kai tsaye da ya fita ya nufi office ɗinta, yana ƙokarin shiga Elevator ɗin da zai sadashi da floor ɗin office ɗinta Saleek ya na ƙokarin shiga,dakata masa Haidar yayi ya shiga kafin yabi bayan sa,kallo ɗaya Saleek yayi masa ya gane sa yayin da Haidar bai ma sanshi ba ,ba tare da Saleek ya kallesa ba yace "You're a doctor right"?

Kallansa Haidar yayi yana mai tabbatar dashi yake magana Ko a'a,murmushi Saleek yayi yace"i hope you made it out of Your relationship Alivee"kafun Haidar yace wani abu  lifter ɗin ya tsaya a Floor ɗin da zasu sauka,Saleek ya Fara fita kafun Haidar yabi bayan sa yana mai Juya maganar da ya faɗa masa Na Allah yasa  ya fita a relationship dinsa a raye wanda baya ce ga mai yake nufi ba,jan kunne ne Ko barazana,ƙaramun tsaki yayi ya nufi hanyar da zata sadaka da ofishin Kiswa , yana isa Amira ta taresa tana mai faɗin "barka da zuwa yallabai ,unfortunately yau Madam Kiswa bata shigo ba and Batayi reporting ba ina ta ƙoƙarin kiranta amma akashe,"dauko wayarsa yayi yana mai sake dialing ɗin wayarsa Kafun ya ɗagawa Amira Hannu ya fita a gurin dan zuwa gidan su Kiswa ,gudu kawai yake a titi dan a yanzu He's worried beyond expectation,koda yaje bakin gidan su cigaba da kiran wayarta yayi amma a kashe ,fitowa yayi a motarsa ya taka zuwa bakin gate ɗin gida ya Fara knocking cikin nutsuwa,yayi wajen knocking uku zaiyi na huɗun Aka buɗe ƙofar gate ɗin,sauke hannunsa da yayi ƙokarin knocking yayi yana kallan wanda 'ya fito,'ya sameer ne tsaye,Takowa yayi fuskarsa babu yabo Babu fallasa ya miƙa masa hannu yana mai faɗin "Assalamu alaikum"

Karba Haidar yayi yana mai amsa masa sallamarsa Kafun kuma yayi shiru bayan sun raba hannun su ,kallan sa ya sameer yayi da Kyau kafun yace "wa kake nema  naga kana knocking hala kazo gurin Sageer ne"murmushi Haidar yayi yace "yaya Sameer right"?

Kallansa sameer yayi musamman da yaga yarda yake sinnewa ga kuma kiransa da yayi yaya wanda a ƙalla zasu iya yin sa'ani,ganin kallan da yake masane ya saka Haidar cewa"sunana Haidar and nazo gurin Kiswa ne dan ina ta kiran wayarta a kashe sannan naje gurin Aikinta an tabbatar mun bata zo ba shine nace bari nazo gida naga Ko lafiya".

Cike da Fara'a Sameer yace "kace mun wanda yayi wuff da zuciyar ƙanwata ya hanata sukuni"ƙasa Haidar yayi da kansa yana mai murmusawa kafun Sameer yayi masa jagora suka shiga yana mai dan jan sa da hira mai kama da tambayoyi har ya ajjesa falon da aka tanada domin baƙi Kafun ya shiga ciki domin yiwa Kiswa magana,ya jima yana ƙwanƙwasa mata ƙofa Kafun ta bashi izini ya shigo,da mamaki ya kalleta yace"har kin bani tsoro danaji baki amsani,ya jikin naki"?

Murmushi tayi tace"jiki da sauki yaya Sameer but my heart is still bleeding na rasa abunda yake Mun daɗi baki ɗaya na".

Murmushi yayi yace"well ina tunanin maganin matsalarki yazo ,kinyi baƙo a kasa,bazan kuma tsaya ja miki rai ba mai kiranki ba kowa bane face Haidar ɗinki,"wani irin daɗi taji ya ziyarce inda lokaci guda ta nemi damuwarta ta rasa, hijab ɗinta da tayi sallah dashi ta ɗauko ta saka taɗan gyara fuskarta kaɗan Kafun ta fita dan zuwa gurinsa ranta fari tas,da sallama a bakinta ta shiga falon tana mai faɗaɗa fara'arta ,tasowa yayi cike da damuwa da kulawa yace"Baby mai ya faru,mai ya same ki?are you sick?mai yasa kika kashe wayarki sannan mai yasa bakije aiki ba?you got me worried".

Ajiyar zuciya ta sauke tana mai sauke idanunta akansa ganin yarda ya wani ruɗe ,murmushi tayi tace "calm down masoyina wannan tambayoyin naka wanne kake so na Amsa,?Nasan duka ne dan haka bari na amsa maka su duka,Bana jin daɗi ne shi yasa ban bar wayata a kunne ba cos i was very sick to talk and bana yanayin da zan iya waya kuma shine dalilin da banje office ba,kaga na amsa tambayoyin ka baki daya.

Cike da damuwar da tafi ta farko yace"baki da lafiya shine baki karani ba ,mene amfanin zamana Likita rayuwata bata da lafiya "?

Takawa tayi dan zuwa ta zauna kafun tace"calm down nawan baka ga na fito gareka ba kasan idan na saka ka cikin idona Ko wacce irin damuwata da ciwo na daukewa suke ,ka kwantar da hankalin ka ciwan Kai ne kuma na warke Alhamdulillah .

Zuwa yayi ya zauna inda take yace"ina fatan ba faɗa kike ba kawai dan naji daɗi,kinsan lafiyarki tafi mun komai a rayuwa"murmushi tayi tace "hayatee calm down im okay wallahi,and maimakon kabari sai ka tashi a aiki kazo amma kabar aikin ka Just to see me".

Kaɗa kan sa yayi yace "yarinya kenan baki san bana tunanin komai ba muddin wani abu akace ya sameki"Serious face yasa yace "yauwa Girl we need to talk idan zaki iya idan kuma You cant talk much just tell me na bari other time.

Kallan sa take cikin ido tana mai san gano maganar da yake san mata amma ta kasa gano komai,murmushinta ta Faɗaɗa tace "na warke fa na faɗa maka Ina sauraran ka.

"lasar leben sa na ƙasa yayi Kafun yace "ban san ta ina zan fara ba and i wish baza kiyi fushi dani ba,im Just curious ina san nasan ya yanayin zaman ki yake da Mother cos im not understanding it ,bana san na boye miki saboda tsakanina dake bana fatan boye boye ya shiga tsakanina dake ,ummina ta kira Mother akan maganar mu so Mother take faɗa mata cewa ke ɗin ba da Aure aka sameki ba sannan mama zaman kanta take which im sure ba haka bane ,na kasa haɗa maganar guri ɗaya sannan im confuse akan mai yasa Mother zatayi hakan ,hope banyi mata ko Kin mata wani laifi ba cos im sure akwai wani abun a ƙasa."

Cikin wani irin siga da yanayi Kiswa ta tsinci maganar wadda tayi mutuƙar bata mamaki ,yar dariya Tayi tace "for real ?Mother tace ni bada Aure aka haifeni ba sannan idan na fahimta tana nufin mama ma karuwa ce,wata Dariyar ta kuma sakawa Kafun kuka ya kwace mata,bata san lokacin da ta kama hanunsa ba ta saka kuka sosai tana mai faɗin"Baby i swear To God wallahi Mama ba karuwa bace koda kuwa a baya bata taba karuwanci ba sannan ni ba yar zina bace idan Ummi bata yarda ba kuma ta saka ayi mata bincike,mahaifiyata da Aure ta Haifeni sannan bayan rasuwar Mahaifina bata zauna haka nan ba sai da ta sake wani Auren inda ta haifi Khalel da Rabiatu wallahi ba ƙarya nake maka ba ,idan ma baka yarda ba bari na kira maka yaya sameer kaji a abakinsa ,zumbur ta tashi dan zuwa kiran Yaya sameer,da hanzari ya saka hannunsa ya jawota ta zauna,tana zama ta fashe da wani irin Kuka mai ban tausayi tana mai faɗin"ban san mai na tabawa Mother a rayuwa ba da take san kushe Asalina ta lalata mun soyayya,idan ban Aure ka ba zan iya mutuwa saboda dukkan wata soyayyata na dauka na baka,bazan boye maka ba ,a soyayyarka baki ɗaya na zira jikina saboda na gama yarda da cewa naje destination ɗin karshe ,Babu wani gurbi dana ajewa wani ɗa namiji a wannan rayuwar,dan Allah Haidar kar ka rabu dani duk runtsi duk wahala".

A wannan gejin ji yake kamar ya jawota 'ya rungumeta jikinsa har sai hawayen dake zuba a idanunta sun daina zuba ,jin dumi a kuncinsa ya saka shi ɗora hannunsa inda ya tabo hawaye,kokarin gogewa yayi domin kuwa baya san ya zama mai rauni a lokacin da Abar kaunarsa ta kasance a raunace,dolene ya nemo dukkan wani ƙwarin gwiwarsa ya bata karfin gwiwa,saita kansa yayi yace "Baby its okay ki daina wannan kukan cos idan kina yinsa jina nake kamar zuciyata zatayi bindiga ta fashe ,Bansan mai nan gaba zai haifa mana a rayuwa ba saboda ban san abunda Zai faru gaba ba sanin wannan sai Allah amma koma mene ina san ki sani,Ina miki san da bana kallan komai da kowa face ke,ina maki soyyayar da bana iya gane dai dai da kuma abunda ba dai dai ba,ina sanki to the extent that zan iya sadaukar da dukkan wani abu da na mallaka domin na mallakeki,Baby i love you to the very last extent that i don't give a shaking damn about how you were born,abu guda ɗaya na sani an halliceki an Haifekii sannan Allah ya haɗani dake,nasan waccan maganar ba gaskiya bace cos bayan kowa maganarki ce gaskiya,a rayuwata Babu wanda zai faɗa mun abu mara kyau akanki na dauka,koda ace maganar ma gaskiya ce Babu abunda zai sauya yarda kike a zuciyata so calm down ki kwantar da hankali Haidar naki ne da yardar Allah koma mene ke faruwa it will get over saboda insha Allah cikin satin nan Baba zai zo suyi magana da Appa ,magana ce ta bincike ko wanne side yayi then bayan nan cikin wata jikina ya ma gama bani Zanzo na daukeki na maidake gidana karkashin kulawata ,'dan haka ki goge wannan hawayen naki mai tsada kinji yar tsana ta"

Tsintar kanta tayi da yin dariya tana mai faɗin Wane ƴar tsana,murmushinsa mai kyau yayi yace "ke mana abar kauna,you look like a barbie doll bakiga ba da kikayi Dariyar nan kamar na saceki mu gudu,"

Hannu ta saka ta rufe idanunta,tabe baki yayi yace "aw kunya come on jo yanzun nan ko tashi ba'ayi ba kika gama fallasamun sirrin zuciyarki Shine kike mun wani kunya yanzu ,im very sure baki ci komai ba so yanzu ki tashi na kaiki wani sabon gurin cin abinci mai kyau "

Binsa tayi da kallo tana mai jin daɗin idea ɗin Kafun daga bisani tace"Aikin naka fa i mean bana san kayi late"ɗaga gira yayi yace "well im the Ceo ,d king and the founder Babu mai bani query,shall we?"

Tashi tayi tana mai nuna masa farin cikinta tsantsa tace "bari naje na chanza kaya"

Kafun ta kai ga takawa yace "Why?,kinyi mun kyau a haka so muje kawai sai dai in zaki dauki wani abu ne kuma".

Kallan kanta tayi Kafun tayi murmushi tace "okay bari na ɗauko wayata Just a moment"bayan mintina Kaɗan ta fito bayan ta sanarwa da baba Baraka cos yaya sameer ma ya fita.

*******

________________"Sageer magana mai muhimmanci nake san nayi da kai matsayina na mahaifiyar ka "Mother ta faɗa tana mai bin Sagir da kallo wanda ke zaune kan stool a bedroom ɗinta.

Nutsuwar sa ya bata yana mai faɗin"Ina sauraran ki Mother"

Gyara zamanta tayi tace"well a matsayina na mahaifiyar ka kasan cewa Babu wani abu da zakayi yayi skipping ɗina sannan babu wani abu da zaka so na gagara ganewa ,after all i gave birth to You,lokuta da dama idan iyaye suka fuskanci abunda ɗan su yake so sai su zauna su duba suga yanayin kyan sa da rashin kyan sa,a wannan zagayen ni dana duba kyansa na gani sabida zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya,ni mahaifyarka ce dan haka ba sai wai an faɗa mun kana sha'awar Kiswa ba"..

Da saurin sa ya zabura yace "Mother ni kuma,wallahi..…"saurin katse tayi da hannu tace "uhm uhm kar Kafara mun rantse rantse Ina sane da irin yarda kake kallan waɗan nan manyan mazaunan nata da kallo, so cut it ni ba wani abu zanyi maka ba ,im fighting for Your sister sannan nasan ko wanne abune zaka iya yi Muddin Faridha zata samu fari ciki dan haka wannan karan zumuntar ka da tausayin ka zaka bada 'na ɗa wani lokaci,so nake kayi wa Kiswa fyaɗe sannan Ina san ka ɗauko mun ita wasu hotuna na Nudes ɗinta,zan baka dukan goyan baya daga baya Babu wani abu da zai faru "

    Wani iri sagir ya tsinci maganar musammman da ya kasance da mahaifiyarsa yake wannan maganar,sosa keyar sa yayi yace"Mother kin san Idan Appa ya kamani na mutu sannan this is a sin in the other hand"

Tsaki ta buga tace"amma lokacin da gabanka ke tashi idan ka ganta baka taba tunani sin ne ba ko,kalli nan Sagir Allah gafurur rahim ne Mai yafiya ne zamu nemi gafara daga baya"shiru yayi yana nazari yayin da a lokaci guda shedan ya cigaba da assasa mishi sha'awar Kiswa wanda a lokaci guda ya amince,daɗi kuwa a gurin Mother ba'a cewa komai domin kuwa ta kai wani guri da ake cewa ba gudu ba ja da baya musamman da ya zamana a ranar farko saboda Kiswa mijin ta mai kaunar ta yayi mata barazanar saki gaban yaranta,wannan abune wanda bazata taba yafewa ba har sai taga ta lalata wa Kiswa rayuwa ta yarda Appa zai ƙwashe ta ya mayar da ita inda ya ɗaukota.

TBC

I miss you guys,

Do you miss me?

Chuchujay ✍️

08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top