10
💥KISWAH💥
(Surrogacy was the cause)
By
Chuchujay
Book1⃣
Page 1⃣0⃣
Baki ɗayan ranar haka Kiswa Tayi shi sukuku,tunda Amira ta kawo mata file ɗin da Saleek ya Bata ta sakashi gefe guda ba tare da ta Ko buɗe ba,idan yana tunanin shi baya da hankali to zata nuna masa bai isa ba,bai kai matsayin da zai juyata tayi abunda Batayi niyya ba Just because taje date dashi,da wuri ta wuce saboda yanayin yarda take jinta tana buƙata ta huta domin kuwa yau tana da abunyi a gida wanda tasan ranta zai bacci sosai cos Mother bazata barta haka nan ba amma still yau tayi alkawari ma kanta bazatayi shiru ba ,shirun ya isa haka nan .
Koda ta isa gida babu wanda ya dawo dan haka ta wuce ɗaki kai tsaye ta watsa ruwa Kafun ta fita kitchen dan kamawa Baba baraka aiki,a haka suna hira suka gama dinner ,ɗaki ta koma ta kira Maman ta dan yi mata tambayar da ta daɗe tana so tayi mata,kira ɗaya ta dauka tace"Hello Kiswan Mama"murmusawa tayi kamar tana gabanta tace"Maman Kiswah ina wuni Ya gida ya Khalil da Rabiatu ?"
"Suna nan lafiya ,Khalil yaje makaranta bai kai Ga dawowa ba Rabiatu kuma na aiketa,ya gidan yasu Faridha yarinyar kirki"?
Dan tabe baki Kiswa tayi jin Mama na kiran Farida yarinyar kirki ,gudun kar ta gane sun samu sabani tayi mata faɗa ya saka tace" tana nan lafiya bata kai Ga dawowa aiki bane bama ,yauwa Mama wata tambaya nake san nayi miki amma ina tsoro Ban san ya zaki dauke ta ba,amma kiyi hakuri bana san na bata miki saboda tambayar ".
Mama dake Kwance ta tashi ta zauna tana mai faɗin"ina jinki Kiswa Allah yasa lafiya".
Ajiyar zuciya Kiswa ta sauke Kafun tace "Mama mai kika taba yiwa mother da bata kasa boye tsanarki karara wadda har ta kai Ga ta shafeni ,Babu damar nayi wani abu domin burgeta Ya burgeta ,kullum cikin nuna mun tsana take tana zaginki Nasan dole akwai wani abu da zai saka mutum ya saka gaba,ni dai na duba ,nayi tunani nayi nazari naga Babu Abunda Na taba mata a rayuwa da zai saka tayi ta tsangwamata kamar na kashe mata wani".
Wani irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Mama,cike da kulawa tace "Babu abunda 'na tabawa juwariyyah a rayuwa kawai sai ita halayyar ta kenan sau da dama kalaman bakin ta basu da daɗi,a kullum ita haka take bata so wani na Ya Aliyu Yar rabe ta gani take kamar duk wani abu da Ya tanada zai ƙare kan danginsa ,baki gani ba daga shi sai ita sai yaransu,cikin danginsa babu Wanda yake cin arziƙinsa kamar ke saboda yi na Allah da Ya ɗora masa kaunar ki dan haka wannan Kaɗai 'ya isa Ya zama babba dalilin da zai saka ki shiga idanun juwairiyyah ki zamar mata matsala,roƙona gareki guda ɗaya ne ,kin daɗe dasu ki rabu dasu lafiya kar ki bari a wannan gejin na rayuwarki Juwairiyyah tazamar miki damuwa,Eh tsakanina da Ya Aliyu Babu jituwa shi yasa kika ga Ban taba zuwa ba tunda Ya daukeki,amma tsakanin sa dake da soyayyar da yake miki kuwa fisabilillahi ce daga ubangiji kijini Ko,'dan Allah kada ki bari ta zama sanadin da zaki Bata dukkan wannan abun ".
Dan shiru Kiswa tayi Kafun ta goge yar ƙwallarta tace "Nagode mama sannan matsala indai daga gareni ne bazata taba fitowa ba insha Allah"bayan sun gama waya ta koma ta kwanta tana mai dogon nazari akan tsanar da Mother tayi mata wadda Babu abunda zata iya akai,amma dangane da Haidar akwai abunda zata iya bazata zauna ta nannaɗe hannunta ba.
Lokacin dinner haka dukkan su suka halarci cin abincin Appa na gamawa yana ƙokarin tashi Kiswa ta aje spoon ɗinta tace "Appa ina san magana idan ba damuwa"dan kallanta yayi Ya zauna yana mai goge bakinsa da Napkin yace"Uhum my dota hope ba damuwa,kallan family ɗinsa dake zaune yayi yace"ko muje ciki ne ".?
Cikin haɗe baki Mother da Farry suka furta a'a,a tare dukka suka kallesu,Ita Farry na tunanin Maganar Saleek zata tona Mother kuma nasan dole taji menene,kallansu Appa yayi a tare yace"so ina tunanin babbar magana ce da kuka sani yarda kuka haɗa bakin nan wajen faɗin A'a.haɗe rai Mother tayi tace "ba wani babbar magana Amma ai we are family Babu wata magana da zamu boyewa juna"
Dan murmushi Appa yayi yace "my Barrister akwai maganar da take bukatar privacy tsakanina da dota na,so please calm down idan ta sani ce zaku sani"aje cukali Kiswa tayi tana mai Kallan Appa tace "Appa ba magana ce ta boyewa ba ina ɗan jin kunya ne amma tunda Mother na san sani its okay nasan ita ma zatayi farin ciki da maganar da zan faɗa,dan cije lebenta na kasa tayi tana debating da zuciyarta kafun tayi mustering courage tace "Appa ina tare da wani in a relationship na almost shekara ɗaya da rabi and Appa yana so ne Ya saka iyayensa a maganar ayi magana dasu,Shine nace bari na faɗa maka"
Cikin rashin tsammanin maganar Mother ta ɗago da sauri tace "Wane irin shashanci ne wannan sannan mai kuke san zama yan matan yanzu,tsabar baki da kunya kike zaune nan kike faɗan saurayinki zai turo"
Kallan Mother Sameer yayi yace"Ah ah,Mother mene abun kunya a ciki ?"cike da masifa tace "idan baka mun shiru ba sai na watsa maka plate ɗin nan tunda kai wannan yarinyar bata isa tayi ba dai dai ba a nuna mata kayi shiru"kallan Kiswah wadda ta mayar da kai cikin Plate ɗinta Appa yayi yace"yar Albarka who is the guy,a ina yake sannan ɗan wanene kinsan dole nayi bincike Akansa ".
Cike da wutar balai Mother ta sake cewa"au mahaukaciya ka mayar dani ko,?dama wa kake tunanin zata kula idan ba yan iska ba abunda yar Zubaida zata iya kenan"wata irin tsawa Appa ya buga mata yace "keep quit you damn woman,mene yake damunki,sau dubu nawa zance ki cire zubaida a bakinki amma baki ji,bari fa kiji na faɗa miki duk wani maltreatment da kike yiwa Kiswah ina sane,Nasan you never wish good on her amma ina dauke miki kaina,idan Batayi Aure ba mai kike so tayi,kina so tayi ta zama kamar wannan Silly yarinyar taki da bata san Aure,nan blind date na haɗa mata da yaran kirki amma me tayi sai da taje tayi abunda yasa yaran yaje ya faɗawa mahaifinsa Batayi masa ba,gata nan ki tambeyata ita Kaɗai tasan abunda tayi"
Wani irin faɗuwa gaba ne ya riski Farry lokacin da ya sako wannan maganar,Kallan bakin Kiswa ta fara tana adduar Allah yasa kar ta tona mata asiri.cikin fushi da saurin tare Kiswa Mother tace "bata sanshi ne amma yanzu da take san Haidar Mai asibitin Al'Haidar ai gashi tana kokarin settling down faɗa maka ne Ban ba"
Da mamaki dukka yaran suka kalli Mother 'dan basuyi tsamanni ba karma sameer yaji labari Wanda takaicin zubar da girmanta yake ƙona masa rai fiye da tunani,ƙaramun murmushi Kiswa tayi Kafun Appa yace wani abu tace"but Mother kisan Its not true Babu komai tsakanin Farry da Haidar Ban san mai yasa kike san kwace mun farin ciki na ba ,"da wani zafin Nama Mother ta taso tana mai cewa "naci ubanki dan uwarki,kike ƙokarin kwace mata saurayi dai shegiya mai gadon witchcraft to Aureshi mugani yar dangin kwaɗayayyu".plate ɗin da Appa yayi jifa dashine ya saka kowa maida hankalinsa a razane,cikin wani irin fushi da yake san daidaitawa gaban yaransa yace "Juwairiyyah rashin mutuncinki yana nema ya wuce gona da iri Wanda bazan dauka ba,wallahi idan bakiyi wasa ba gaban yaran nan zan baki mamaki".cike da rashin kunya tace "to dake ni mana Aliyu Shine kaɗai mamakin da zaka bani,kar ka manta im a lawyer that knows her right wallahi duk ranar da ka saka hannunka jikina sai na baka mamaki mara misaltuwa,nuna Kiswa tayi da hannu tace"akan wanna ɗiyar karuwar zaka nemi ka raina mun wayau"Kafun yace wani abu ta bar gurin Farry ma ta tashi tana kuka ta mara mata baya,aje spoon Sageer yayi yace "Allah ya kyauta "yayin da Kiswa ta fashe da wani iri kuka mai cin rai,lallashinta Sameer ya fara yayin da Appa ya zauna ya ɗora hannunsa a fuskarsa yana mai jin wani irin yanayi na baccin rai a tattare dashi,tashi yayi bai ce musu komai ba ya bar gurin,kuka sosai Kiswa ta cigaba da yi tana mai jin kirjinta kamar zai faɗi Yayin da sameer ya cigaba da lallashinta yana mai bata hakuri har sai da tayi shiru kafun yayi mata magana masu kwatar da hankali Kafun ya rakata ɗakinsu.
Bangaren Mother kuwa tana shiga ɗaki kiran Mahaifiyar Haidar ya shigo mata,cikin zumuɗi kuwa ta dauka ta samu guri ta zauna tana mai saita kanta tace"Assalamu alaikum future sirikata barka da warhaka,daga ɗayan bangaren Ummi tace"barka dai dama ina ta san na kira ki amma Ban samu dama ba saboda jiya naga dare yayi,na kiraki ne da albishir mai daɗi,jiya na zauna da Haidar nayi masa magana kan diƴarki Faridha,so ya faɗa mun yana dating ,amma abunda yayi mun daɗi sosai yar uwar Faridha ɗin yake so daya yarinyar ki Kiswa,im Just happy da ya zamana either way zamu zama sirikai na bada dukkan goyan bayana musamman da ya zamana Haidar na mutuƙar san ita Kiswa ɗin Ko ya kikace? Ajiyar zuciya Mother ta sauke Kafun tayi wata ƴar dariya tace"Hajiya kenan,kicce sharriin Kiswa ya ziyarci Haidar kenan,kyau Babu kyan hali ake faɗa miki,to ni Kiswa ba yarinyata bace domin kuwa ina Allah wadai ace na dauki ciki kamar na Kiswa a jikina ban zubar ba wada da haihuwarta gwanda barinta,koda yake ai ba abun mamaki bane idan tazo duniya Ta hanyar uwarta domin kowa ita kanta uwar tata karuwace wadda ta samu cikinta ba da Aure ba kasancewar Mahafiyarta kanwar mijina ce ta saka ya daukota domin bata rayuwa mai kyau amma duk da haka bata bar komai ba a halayyar uwarta,kinga hajiya ba wai san zuciya ba Ko wani abun ba amma Kiswa bata dace da shiga zuriar ku ba domin kuwa Kiswa Wake ɗaya ce mai bata miya.
Shiru Ummi tayi tana mai jin maganar kamar dukan guduma,sai da Mother ta sake cewa "Hello Hajiya"Kafun Ummi ta dawo daga shock ɗin da ta shiga,ajiyar zuuciya tayi tace"zan nemeki Hajiya i need to digest this".tana kashe waya Mother ta saka dariya tana mai faɗin"indai nice wallahi muzuba mu gani domin kuwa nafi karfin bataliya guda",zama Farry da mamaki Ya kusa kashewa tayi tace "mother mai yasa kike yin haka wai don't you think Bai kamata ba sannan ni dake munsan Kiswa is decent kuma da Aure aka sameta mai yasa zakice yar karuwa ce,beside ni mai yasa kike san haɗa ni da Haidar?.
Wani irin Kallo mother ta bita dashi kafun ta kamo hannun Farry tace "kalli Nan Faridha,kowa da kike gani kansa ya sani sannan a maganar da na faɗa ai ba duka ne karya ba cos Zubaida Na da reputation ,but ba wannan ba ,ki saurareni da kyau,duk duniya babu mai sanku sama dani ,ina san ki sani Kiswah ba sanki take ba,da zataga abunda zai cutar dake bazata taba faɗa miki ba ,iyakaci ma ta tura ki,ni Na tabbata idan kika kuskura kina gidan nan ta Auri mai kuɗi kamar Haidar to kisa a ranki wulakanci da sharri a gurinta sai ya baki mutukar mamaki,She's Just using you a gidannan domin zuwa wani matsayi mai girma,and gradually zata kai dan tunda Appanku ya fara wannan Abun wata rana zakiji ya tsigeki daga Kujerar ki ya bata.
da sauri Farry tace"God forbid Mother kar ki mun baki mana"ajiyar zuciya mother tayi tace "abunda nake nufi kenan kuma zai faru idan baki bani Haɗin kai ba zaki sha mamaki dan haka dole ki kwace Haidar a hannunta,a hankali cikin karfin Zancen uwa ga ɗanta Mother ta wankewa Farry kwakwalwarta tass inda ta fara disgusting tunanin marasa kyau kan Kiswa ,
Kai tsaye bayan ta gama da Mother ta nufi ɗakinsu da zummar korar Kiswa daga dakin ,tana shiga ta tarar da Kiswa kwance ta rumtse idanunta Ta lullube da bargo, kanta tayi kai tsaye ta yaye bargon wanda yasa Kiswa buɗe idanunta amma bata tashi ba,fahimtar idanunta biyu ya saka Farry cewa"bai dameni ba ki tashi Ko kar ki tashi amma Nasan kunnuwanki suna saurarena,to kiji nan you're selfish,san kanki yayi miki yawa ,idan ba haka ba mai zakiyi da maza biyu indai ba zalama ba tunda kinsan mutum ɗaya zaki Aura and maganar Saleek kuma ai kinsan i appreciate Handsome guys idan da na ganshi bazan taba cewa bana sanshi ba sannan bazan taba kirkirar masa halayyar banza da na lissafa ba,da Kin bani hint bayan dawowarki yarda yake da yanzu komai ya dai dai ta tsakanin mu"
Tashi zaune Kiswa tayi tace "madam Hold on ,kina nufin duk abunda kika faɗa mun kan Saleek karya kike?"murguɗa baki Farry tayi tace and so?after all kuɗi kike yiwa cos ina baki baki taba so mun abu mai kyau ba a rayuwa,you're always this greedy ga san nuna ke mai gaskiya ce bayan cewa mamanki ma dake bauchi reputation gareta...wani irin tashi Kiswa tayi inda Kafun Farry ta ankara a dauke mata fuska da mari mai kyau Kafun tace"wallahi tallahi idan kina haukanki da aka doraki akai kika zo inda nake kina ƙokarin faɗan abu mara kyau kan mamana to baki ɗaya garin nan yamana kaɗan,sannan magana da kike akn kuɗi ko mene ke kinsani abunda nake dashi baya mun kaɗan sannan a kullum ina godewa Allah da abunda ya bani and kuɗinki idan har ba daƙiƙiyace ke ba kinsan ban taba roƙonki ba sannan in faɗa miki idan baki sani ba duk da ban taba kawowa zaki mun gori ba amma ban taba kashe su ba suna nan a account and i will send Your fucking shit back,sannan maganar Saleek da kika hada kika saka nayi making fool of myself shima zan baki mamaki ,sha sha sha kawai wadda bata san inda yake mata ciwo ba".
Cike da fitina Farry ke riƙe da kuncinta hawaye na mata reto a fuska,cije lebe tayi tace "ni kika mara Kiswah?"kaɗa kai Kiswah tayi tace ki rama mana sai naga adadin haukanki,ai Kafun kace ƙwabo faɗa ya kece a tsakaninsu ,hayaniyarsu Mother ta fara ji,dakin tayi kai tsaye dan ganin maike faruwa,ganin yarda suka chakume gashin Juna ya saka Mother shiga da gudu tana fadin"wanne irin hauka kenan"ganin yarda Kiswa ke neman fin karfin Farry yasa Mother shiga ta kama Kiswa a rike kam tace ma Farry "oya zo ki yamutsa mun fuskarta da mari,aikuwa kamar Farry na jira ta fara haɗawa fuskar Kiswa mari,tana ƙokarin yin na huɗu Appa ya Sameer da sagir suka shigo,cikin zafin Nama samer ya shiga ya dauke Farry da wani irin mari da saida ta tuntsura,kafin ya farga Mother ta rama mata tana mai faɗin"'dan baka da hankali kasan mai tayi mata da zaka rama mata."wani irin fushi ke daukar Appa dangane da Mother wadda idan ya biye ta yau bazata kwana gidan sa ba ,a hankali ya saita kansa yace kai Sageer je ka riƙeta kamar yarda Mother ta riƙe Kiswa,Babu musu sageer ya riƙeta ba tare da ya saurari mai Mother ke faɗi ba,kallan Kiswa da fuskarta ya tashi yayi yace"idan har na isa dake ina so yanzu ki rama adadin Marin da tayi miki "aikuwa ba abune mai sabuwa ba"mother ta faɗa hannunta a kugu".
"Idan kuwa kika kuskura kika matsa daga inda kike da zummar hanata to a bakin Aurenki,na miki alƙawari".
TBC
Chuchujay
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top