witching hour

*KISHIYAR ƘABILAH...*

PROLOQUE....

_BY SURAYYAHMS._

_®Any resembelence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._

Daga cikin Littafan dana rubuta:
#Arne
#samarin shaho
#sakamako
#ajalinso
#Ahumaggah
#tuntuben harshe
#kudi kumbar susa
#takaicin wasu
#shade of rufaida
#fitar rana
#lamarin gobe.

#Witching hour

wajajen karfe uku dedei na tsakar Dare wanda lokaci ne da turawa ke kiransa "witching hour" ko "spirituql awakening" inda ratar dake tsakanin spritual world wato Duniyar mutattu dana rayayyu bata da wani nisa, wnn lokci shine lokacin cin kasuwar ko wani irin maita da manyan kungiyoyin asiri, Da shawagin bakaken fatalwowi da kuma bakaken Aljanu da kuma dukkan wani irin launin supernatural spirits dake yawo cikin dare a fadin duniya.

Cikin wata jeji ne mai tsananin duhun gaske wanda ko hasken tafin hannun ka ba lallai ka iya gani ba.

Banda sautin kafafuwa babu abunda yake motsi ajejin adede wann lokaci.

Wata kibabbiyar mata ce mai tudun duwaiwaka gata da tsayi da kuxari ta fito bujum daga cikin wani kurmin ciyawa mai tsananin duhu jikinta sanye da fareren kaya kal mai kama da likkafani.

Wani bijimin bakin akuya ne a hannunta tana kkrin janshi da karfi ayayin da bakinsa yake daure da wani irin jan tsumma da aka masa xane da farin chalk layi layi.

tun daga samanta har kasanta farine babu dison wani kala ajikinta face dan wani jan kyalle data daure tagaban goshinta da shi, kafafuwanta ta babu takalmi amma haka nan take tsagawa cikin duhun jejin da alaman tana cikin gaggawa ne domin ta samu isowa wani tsauni akan lokaci.

Daga bayanta wata matashiyace wancce baxata wuce yar shekaru 28 da haihuwa ba,daga ita sai ita , batasako takalmi ba bare kaya bare kuma dan kwali, saidan farin kyalle na farin xani dake bisa karjinta data dorashi da kyau, bayan babu wani abu a fuskarta face xanen jan fenti a saman goshinta itama.

kanta sunkuye a kasa sai sauri take ayayin da take bibiye da matar dake mata jagora cikin jejin acikin gaggawa..

Tafiyar da baifi na minti goma sukayi ba snn suka billa adede wajen wani katoton fili wanda yake nan tarwal cikinsa babu komi sai shinfidaddyar farin kasa mai kyalli.

Filin shikansa bayyana yy acikin tsakiyar dokar jejin adede wann lkcin domin kuwa koina ajejin wani irin baqin duhu ne amma wann filin shikadansa yana fidda wani irin farin haske mai shiga idanu.

xubewa ƙasa agaban filin sukayi dukansu subiyu ayayinda jikinsu ya hau rawa suna karkarwa kar kar kar kamar wani iskan sanyi nadaban ne yake ratsasu.

Dattijayar matar ce tayi sauri tafito da wani dan karamin kararrawa ta dinga kadawa tana wasu irin maganganu can sai ga wani jibgegen dutsi ya bayyana agaban su mai shape dinsa kaman kujerar sarauta golden colour yanamai fidda farin haske, haske mai tsananin kashe ido ne yay walkiya sann wata bokanya ta bayyana akan dutsen girif tana xaune itama jikinta sanye da fararen kaya. Atake suka xube kasa gabanta atare suna masu mata sujada tamkar itace ubangijin su..

"Almighty Goddess of fire And revenge".

Tsawon lokaci kansu na kasa suna gaishe ta tana kallon can sama sai can snn ta miƙa xara xaran yatsun hannayenta ta shiga shafa bayansu daya bayan daya da shi duk inda taja sai jini ya fito wanda take kaiwa kan harshenta tana lashewa da alaman ta amshe xiyararsu snn xata saurare su.

Hannu ta daga dan ta basu daman yin magana Nan da nan dattijiyar matan tafara mata magana cikin harshen yarensu ta yarbanci acikin wani irin salo na tsananin girmamawa da ladabtawa.

Muryanta na rawa ta xube kasa Tace _"Gbogbo oriṣa yinyin ti ina Ati iku_
Meaning All hail,goddes of fire and revenge, tace naxo neman wani taimakon gaggawa ne awajenki ubangijiya ta,kafadun yarta ta dafa tana layi ma Allansun kamr wance xatayi mata kuka snn tace"All mighty goddess of fire and revenge,tonite i offer my doter to the arrow of your fire and revenge..

Cikin datsar numfashinta da muryanta dake fitowa acikin amo mai tsananin kuwwa da ban tsoro goddess din tace "My child, what do you want?

Matar Ta dada rusuna kai har kasa snn tace "i want Justice for my doter, goddesss..we demand justice.

Goddesss din tasu sai tay shiru batace komi ba,
Sai can sanda ta kalle akuyar da suka kawo snn tay mata alama akan taja shi tsakiyar filin sann ta yanka shi ta xuba jinin sa awajen..

Yartan kuma ta umarce ta akan data ja katoton round circles a filin snn ta xagaye su dashi snn ta kunna wuta a kan layin shima wutan ya xagaye su.

Wani bakin kwarya ne ya bayyana ta mika musu suka amsa, nan da nan dattijayar matar ta janyo baqin akuyan ixuwa tsakiyar filin ayayin da yarta ta xagaye su cikin katoton circle data xana shi da kasa snn ta cinna ma circles din wuta suka tsaya daga ciki.

Akuyar suka danne a tsakiya fuskar akuyan na kallon gabar kamr yadda goddess din ta umarce su,a dede inda jinin yankan xai xuba matashiyar ta aje bakin kwaryan jinin akuyan na xuba aciki, sauran da ya rage suka bari ya kwalala akasa acikin wajen

dattijayar matan ce ta yanka wuyar akuyan amma bata sake shi ba harsanda jinin nasa ya cika kwaryan dake hannun yarta sosai.

Bayan sun kammala hakan nan suka kawo jinin dake cikin kwaryan har ixuwa gaban goddess dinsu suka mika mata cike da ladabi da biyayya, amsa tayi ta miƙa kwaryan jinin can sama, wani haske mai yawa yabi ta kai snn ta saukar Da shi ta hura iskan bakinta akai wani farin haske ya fito daga bakinta ya shiga cikin ruwan jinin gabaki dayansa snn ta saukar ta basu dukan su sukayi kurbi daya, bayan nqn tawatsa ma matashiyar budurwn sauran jinin ajiki Wanda atake ta fadi kasa ta suma sabida spritual electric shock din daya kwasheta.

Bayan hakan ya faru ta juyo ahankli ta dube dattijiyar matar dake tsaye kanta a kasa tanamai jiran hukunci dq harshen yaren su tay mata magana snn tace mata menene sunan yaron..

Kan dattijar matar na kallon can kasa tace sunan shi "AHMED DAMILARE BELLO son of BELLO Ayodeji JIMADA.

Goddess ta jinjina kai tace and the girl in question?

Tace "Efik girl, born by an igbo woman.

Goddess ta kalli can sama snn tayi wasu maganganu da yare sosai tanayi tanamai bushewa da dariya mai kara.

Can ta tsaya cak da dariyar snn ta juyo tana kallon matar ido da ido

tace "you can go now my child. ur work of revenge is done (ki je, aikin ki ya kammala)..

Ni Allahn ki inamai baki tabbacin cewa Ahmed, son of bello jimada and his wife doter of effiong will never bear a child
..NEVER.

Acikin harshen yaren su tace"rashin haihuwar nan shine xai xamo silar rashin farincikin auren su ta har Abada. Snn yarki ce xata kasance musu kashin kifi a wuyarsu dan haka na baki ixinin kaita cikinsu.

Goddess Tana kammala fadar hakan ta bushe da wata iriyar dariya ayayin da dattijar matar ta xube kasa tanamai mata godiya sosai

...sai can ta bace musu bat tare Da filin duka da kuma wutar da komi ma sai wajen ya dawo kamar ba wajen ba,dan ganin kansu kawai sukayi agindin wani katoton bishiyar mangwaro mqi tsinannen duhu suna tsaye, wani katoton duji mai manyan idanu na gabansu ya xuba musu ido yanata kallonsu.

jan yarta dake layi tayi suka fice ajejin acikin gaggawa dan wajene mai hatsarin gaske. After like 20min suna gudu suka kai bakin hanya suka shiga cikin motarsu acikin sauri nan ne kowacce acikinsu tamaida abayarta ajikinta snn suka kama hanyar xuwa gida.

Koda suka isa gidan nasu dattijiyar matarce ce ta rirriko yarta dake layi ixuwa dakinta cikin kulawa sosai ta kwantar da ita tanamai rarrashinta dan ta samu tayi bacci..

Sai kuka yarinyar take dan Da sunan Ahmed din abakinta baccin ya kwasheta.

dattijyr matar ta jima axaune tanamai kallon yarta dats looking helpless and heart broken ,atsaye ta miƙe tanamai sauke huci mai xafi Aranta tanamai cewa Familyn Bello jimada saiku shirya cos i fatihat adetunji balogun am coming for u......

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top