2

*KISHIYAR ƘABILAH...*

_BY SURAYYAHMS._

_®Any resembelence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._

Daga cikin Littafan dana rubuta:
#Arne
#samarin shaho
#sakamako
#ajalinso
#Ahumaggah
#tuntuben harshe
#kudi kumbar susa
#takaicin wasu
#shade of rufaida
#fitar rana
#lamarin gobe.

Episode 2️⃣

Wajajen Shida da rabi saura na yamma Dr Ahmed bello jimada yabar headqtr nasu na nigerian disease control ya kama hanyar gidansu dake cikin jerin layin masu kudin anguwar Katampe extenstion dake abuja.

Ahnkli yake tuki yana jan tsaki har ya iso kofar gidan nasu yay horn a bakin gate mai gadinsu ne yazo agurguje ya buɗemai snn ya shigo ciki batare da ya kula shi ba.

Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan kwanciyar hankli da wadata ta zauna.

mahaifinsa Alhaj Bello Ayodeji jimada also knwns as professor Bello jimada(prof BJ) babban manomin shinkafa ne kuma kwararren tsohon professor ne a fannin psychology, wanda ilimi da wayewa yagama ratsashi.

makeken tsakar gidan nasu na dauke da sassa har biyu masu design iri daya,snn ko wani sashe akwai tazara mai dan tsayi tsakaninsa da wani sashen, sashin farko wanda shi zaka ci karo dashi bayan shigowar ka cikin gidan shine mai bungalow dinsa yana da girma sosai don sashin ya fi dayan sashin girma.

Sashen da baida girman ya wuce kai tsaye snn ya haura sama yawuce side dinsa tun anan falonsa ya fara rage kayan dake jikinsa yana yardawa nan kasa while walking like a fierce model cos he have the perfect manly fitted shape and muscular figure.

Ann Cikin part din dake cikin na mahaifiyarsa nasa sashen yake dan kuwa na musamman aka sake gyara yanayin building din tun alokacin da aka haifesa,shiyasa he have his very own parlour da bed room da closet inda ke lode da kayan sawa kala kala masu tsada da kyau. Ya xabi xama a sashen mahaifyrsa ne sabida yafi sakewa sosai da ita. In ka shiga Bangarensa zaka san indeed shi dan gatane awajen mahaifiyarsan..

Bangarensa is well organised kamshi wajen yake kowani lokci sabida kulawa masa dashi datakeyi sosai,dan madaidaicin falonsa mai kyau na dauke da set of expensive and luxury sofas sai madaidacin tv plasma babu wani tarkace ,yana kaiwa tskiyar dakin nasa ya jefar da takalmansa snn ya wuce wajen wanka direct,.

Anan ma Sai da ya kusa hour guda acikin bathroom babu abinda yake sai shafawa kansa ruwa da sabulu ahankali kaman akansa aka fara sauke kalman lalaci da gajiya,sai can daga karshe snn ya fito daure da towel yana goge kansa da wani dan karami,soft palmers cocoa butter oil ya hau shafawa a jikinsa daga sama har zuwa kasa, sai da ya gama yadauko doguwar jallabia kalar toka ya saka ta with small tiny shorts daga ciki. Ya fetsa turare mai sanyi, da Har ya fito zashi masallaci sai ya tuno da mahaifinsa, sai kuma ya fasa ya kulle side din nasa da keys, Sallahn magrib da isha'i yay,snn ya nemi waje ya xauna akan sofa yay zugum harna dan wani lkci.

jin yunwa na neman damunsa yasa ya bude fridge dinsa ransa a harɗe da baiga wani abun kirki anan ba..

Da har xai rufe sai yaga wani shiny leather acan gefe, budewa yy batare da ya dago ba, Birthday cake din da chilhood friend dinsa kafayat buraimo ta aje masa ya gani a aje, gajiyayyen tsaki ya saki aransa yana jinjinawa kalar xubda aji irin nata,wasu dai haka Allah yayisu basu da aji sam sam, kyabe bakinsa yy tuna yadda yake mugun ja mata aji, birthday din da tayi tayi ya saka kanshi acikin hidiman amma yaki to me na aje mai cake duk da uban walakncin daya mata? Girarsa na sama a adage yasaka hannu ya dauki cake din yafaraci kamar dole, yana taunawa yana tunawa da wagagan lips dinta yana jan tsaki  dan aganinsa halittar labbarta daya danyi kato shine kawai ya ɓata ta, but after that she is clean gata da diri mai daukar hankli. Sede shi sam baisan mace mai katoton baki da girman nono. And kafayat can talk for africa kai kamar ma dan shegen son gulma da shishiginta yasa Allah ya bata kyautar katoton baki. Haka nan dai ya rinka debe mata albarka aransa yanayi yanacin cake din kamr ansaka shi ci dole.

Sai can ya koma kwanta ahankli ya fara resting mind dinshi for a while acikin yanayin lumshe ido iya abubuwan da iyayensa ke yawan gaya masa na batun kawo matar aure sune suka fara dawowa masa akansa daya bayan daya.

Tare da sakin wata shakurarren tsaki yay kasalallen juyi tare da pillown dake manne akan kirjinsa jin kamr cake din ne ya tokarasa akirji.

Shi Duk yan matan dake bibiyarsa haryau bai ga wacce ta masa daya aura ba,tashi zaune yy cikin damuwa, but how comes he does not have feelings for any girl even kafayat dat was his best friend tun na yaranta data san abubuwa dayawa game da rayuwarsa amma bai taɓajin tai masa aransa ba harynxu.

Dada taƙure kanshi yay cikin zurfin tunani tare da tunowa da maganan daya daga cikin babban yayansu wato brother dimeji a.k.a hamzat bello jimada da yake cemai hala shine dai bai nitsu ya gano tashar wacce zuciyarsa take so din ba.

But Ders are so many girls going after him taya ne ma zai gane wacece aciki yake so mtschew! a iya tunanin su ma kawai wani ciwon kai da wahala yake kawo masa,
Ynx bbn matsalar sa shine ya rasa gane  wacce ce special girl din acikin babes din daya taba sani arywrsa, ance dai ur special girl itace wacce tafi fadowa cikin ranka amma sai yay kwana fiye da talatin bai tuna kowace ya mace aransa ba,gara gara ma his childhood friend din kafayat obviously sabida tana yawan kiransa a waya, alwys acting like his wife, bayan ita then there is this innocent yarinyar data dan kula dashi sosai wani lokci dayaje research dinsa a garin cross river calabar wanda yasan dai sai yana cikin wani damuwa ne yake iya tunowa da ita cos she helped me more than anyoda girl can arayuwarsa.

Kuma harga Allah sukadai ne matan dayasan yake iya tunawa dasu aransa involuntary sabida koba komi yana dan iya sake jikinshi dasu sosai, but in his heart kafayat is just a friend and Adiaha was just a helper.

Altho ADIAHA, was just a coincedental friend baxai iya cewa budurwansa bace..

Wanda yasan hala da baije aikin research agarin su ba dabazai ma santa ba, but despite being a typical IGBO/EFIK girl itace dai ta taimakesa sosai,tana da sakin fuska tayi masa hidiman abinci,ga kulawa na musmmn data bashi dayaje aiki a garin calabar during his scientific research programe na lassa fever.

Life was indeed calm with her dan yarinyar sam bata da hayaniya.

Saidai ayanzu baisan ko inya koma wajen zaije ma ya sameta ba dan tun daya kammala damuwar sa a calabar yabar wajen baisake nemanta koda a waya ba. Yasan hakan dayay xai iya bata mata rayuwarta, He is sure hala ynxu har tay fushi ta mance da shi kamar yadda sauran yan matan dayake dumping dinsu a rana tsaka suke yi.

Wani gullutun Tsaki ya ja tare da sauke pillon daya rungumar akirjinshi yanamai jin haushi kansa a karo na farko dan baisan meyasa ya kasa neman yarinyar kodam yy mata godiya ba.She was nothing but good to him, innocent and care free, sau tarin yawa tayi ta kkri wajen nuna mai irin kaunarsa datake mutuwar yi aranta saidai bai taba nunawa cewa yasan da cewa tanayi ba cos dats was his habits alwys. Yana son yaga mace tana son shi yana nunawa kamr baisan tanayi ba. He love to ignore ppls feelings cos he is self obsessed kuma yana mugun ji dakansa bana wasa ba.

Ko aynxu Ya tabbata dan acikin matsi xcyrsa take da ko kadan baxai tuno da ita ba,Sassanya kuma nitsutsyar murmushin ta ya soma tunawa yanamai jin sauyin yanayi mai tafe da bugun zuciya atattare dashi. yasan dai yay kuskuren rashin yi ma zuciyarta adalci msmn daya guje mata batare da cemata komi ba,she is faultless saidai shi ba mutum bane mai son tunowa da kuskurensa dan haka sauri yay wajen kawar da wann feeling din aransa na jin cewa yay mata rashin adalci dan kar ya karaya sosai,Ransa a dan hargitse ya sauƙo kasa daga kan gadon kamr ana ingiza shi, yarasa meke masa dadi, ruwan sanyi yaso daukawa a fridge dinsa sai yaga babu mai sanyi sosai dan haka acan gefen gadonsa ya tsuguna tare da buɗe bedside drawer nashi da key,ya ciro wata kwali aciki ya fidda wata kwalban wine mai tsada dayazo da ita daga UK.

Ya dade da dena shan giya amma ji yake yana bukatar sha sabida  yadan ciremai tunanin komi musmmn ma na auren nan dayake dagula mai kwakwalwa, nan ya buɗe kwalban yafara sha ahankli after a while ya yarda kwalban akasa ya kwanta batare da yin tunanin komi ba daga nan sai bacci.


Washe gari da safe
Farakal din Agogon dake manne jikin bango ne yayi ticking dot 6:30am dai dai na safiyar ranar friday tare da yin sautin alarm mai karar water ascent wanda tuni ya gauraye wajen da wani irin kara mai cikka kunne,

tashi yayi firgit tare da miƙewa daga kan lallausan katafaren gadon da yake kwance akai,yana mai dafe kansa datake mai nauyi.

Dagowa yayi sann ya juya ya kalli agogon da ya farkar dashi daga bacci yaga har 6:35am tayi, da dan hanzari ya diro kasa daga nan baijira ba ya fada toilet din dake cikin dakin shi cikin hanzari ya saka toothpaste ajikin brush dinsa wanda yake fari kal da sauri da sauri yayi brushing teeth dinsa ya kunna warm shower yay wanka sannan ya fito daga toilet din daure da hadadden white body towel da kuma wani dan karamin towel din a hannunshi yana famar goge fuskarshi da ita har ya karaso gaban wani babban mirror da mutum kan iya kallon kanshi tun daga kai har kafa yana mai kare ma hadadden dirinsa takaitacen kallo tare da sakin nannauyr ajiyan zuciya, sake tunowa da lamarin Adiaha daya karayi aransa yasashi lumshe idanunsa tare da buɗewa ahankli cikin rasa dalilin dayasa ya fara sakata aranshi.

Dagata cikin mirror ya hango empty wine bottle dinsa akasa dayasha jiya yaja tsaki bai kara kallon wajen ba yafara goge kanshi cikin saiɓi.
Aransa yana mita yana cewa Inba irin wann damuwar auren ba maixai saka shi yasha giya dan ya samu nitsuwa?

yana cikin karasa goge kanshin kenan zai shafa mai yaji karar wayarshi na ringing,Dan daga girarsa sama yy da har yayi kaman bazai dauka ba sai kuma ya juya ya karasa inda wayar take yana ganin mai kiran da sauri yayi maza ya dauki kirar tare da neman wajen zama cikin risina kai mai nuna alamar tsantsar girmamawa tamkar mai Kiran na gabanshi zama yayi kamin ya kara wayar a kunnanshi tare da cewa

"mamy na kin tashi lpya?

Daga daya bangaren aka amsa da murya kasa kasa da cewa lpya lau Alhamdulillah ,sannan ta sake ce mishi Ahamad harka shirya ka fita ne?

Fuska ba yabo ba fallasa yace à ah mamy Amma saura kadan yanzu zan shirya in fito ina dan sauri ne yaudin..

Ajiyar zuciya ta sauke snn tace ok toh kadai sauko din, na shirya maka breakfast inajiranka akasa inason magana dakai. Take yaji walwalar fuskarsa ta dauke tuna cewa basuda wani maganan da suke masa a kullu yaumin face na AURE ita da mahaifinsa, da can dai yadauka wa yan mata kawai ake irin wnn takuwarar akan suyi aure subar gidan iyayen su amma sai gashi shima baida katabus agidansu sabida duk sauran yayunshi suna da aurensu shine kawai ya rage baiyi ba, adan gaggauce yace "toh" Yana fadan Hakan ya katse wayarsa batare daya jira Wani furucinta ba, da alamar ranshi bai wani so amsawar dayay ba.

Tsaye ya mike cikin sauke huci tare da yin wani ball da empty wine bottle din yanamai turasa cikin karkashin gadonsa.

Closet din kayanshi ya bude sannan ya dauko wani true blue men suit mai laushi da tsada ya saka ajikinshi,ya bude wata madaidaicyr transparent safe ya dauko nordstrom neck tie dinshi marching colour mai azaban kyau na kamfanin steve sannan ya sanya ya masa das,agogon shi na rolex submariner ya makala a hannunshi na dama sannan ya dauki
Turaren paco rabane  dake gaban mirror dinshin yafesa a jikinshi Duk Inda ya juya kansa qamshin ne ke binshi.

gaban wata small coffee table ya Mika hannu ya dauki car key din motar sa dake ajiye akai da kuma wayarsa daya jefata acikin aljihun sa sannan ya jawo takalmin shi baqin cover shoes mai sheqi yasaka a kafarsa snn ya fito daga dakin yana saukowa yana dan kallon agogon hannun shi yaga wai har bakwai da rabi tayi.

Saukowa yake daga kan benen cikin kwanciyar hankali da natsuwa har ya karasa sauka ya isa katafaren parlourn su.

karasowa yayi cikin parlourn ya isa wajen mahaifyrsan dake tana da dan haske tasanya wani babban atamfa purple colour an mata dinkina alfarma sanye take da farin gilashi à idonta Gabanta kuma 10 inches dinning table ne dauke da hadadden royal flask din tea tazuba Kadan a dan karamin transparent kofi na shayi tana zuƙa ahankli, Nan ya karasa gaban ta tare da zama dab yana kalle kalle can snn yace mamy yana ganki ke kadai anan, DAD fa, kodai bai farka bane?

Sauke cup tay agabansa ayayin da tadaga idanun ta sama tadan kallesa kadan tace badai bakaje sallahn asubah yau ba?

Fuska ba yabo ba fallasa yace na makara, tace hmmm shiyasa, Baban ka tun a lokcin ya fita, Jiya ya tura da saƙo wajen ka an sanar maka?

Dauke kanshi yy kmr Bai amsa ta ba ya girgiza kai. Bata kulashi ba tace malam liman yace min wai jiya ka dawo da wuri amma kuma ka rufe kofa kuma wayoyin ka ma duk a kashe. a kasale cikin rashin son jin maganan Yace mamy nagaji ne shiyasa nay bacci da wuri. Cup din data aje mishi ya dauke ya kai baki badon yay niyya ba
Ya kurbi kadan snn ya sace kallonta yace Mamy Pls lest have our breakfast now in mungama mayi maganan later, batace mai uffan ba ta zauna tafara serving dinsa beans cake da wainar panke, har ya deba yafara kaiwa bakinsa kenan yana taunawa sai ya dago kansa sama caraf idanunsa suka fada kanta ganin yadda ta rabza wani irin tagumi tabi ta zubamai ido tanata kallon sa cikin yanayin matsanancin damuwa da zurfin tunani.
#surayyahms
08060712446
Follow wattpad @surayyahms.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top