12
KISHIYAR KABILAH...12.
BY SURAYYAHMS.
Atsakanin Adiaha da mahaifiyarta mrs grace kowa yay hanyarshi ita ta wuce wajen priest dinsu mai jagorantar kungiyar akpo, Adiaha kuma ta shiga yawo agari cikin rasa wajen wanda zataje dan izuwa yanzu kusan kowa baison yay wnai mu'amala da ita sabida abunda tay na guduwa wajen consent taking na aurenta, kowani gida ka leka zaka samu ana Allah wadai da halinta sabida aganinsu rashin tarbiyane kawai yake damun Adiahar shiyasa take kunyatar da iyayenta sosai.
Tafiya take batare da tasan ina ta dosa ba, wajen sosai yay shiru, daidaikon mutane ne awaje suna hada hada dan Yau kusan duk inda ka ratsa shiri akeyi na hidimiman akpo festival wanda shine hidima na karshe da za'ayi kwata kwata a wann shakrar.
hidiman yau din is more of spritual events sabida rana ne da za'a fito domin ayi muamala na musammn tsakanin duniyar rayayyu da na mutattu.
A Al'adansu sun yarda cewa dodonin da zasuyi wasa a filin yau ba ordinary masquerade bane,wasu irin spirit ne da ruhi na iyaye da kuma magabatansu da kuma Allolinsu da suka shude tun zamanin kakanni.
Ko ina shiri akeyi domin tabbatar da yuwar wann hidima cikin nishadi kmr yadda aka saba wanda da misalin karfe sha biyu na rana suke farawa.
Tun fitowar Adiaha daga gidansu take tafiya cikin sanyin jiki da tunanin irin masifa da zagin cin mutuncin da mahaifyarta tay mata wanda hakan ne yasaka bata kara jin sha'awar komawa gidansun ba.
A Wani wajen shan coffe acikin kasuwarsu can inda suka saba haduwa da Ahmed taje ta zauna tay shiru,har sai bayan da ta dan samu nitsuwa aranta snn ta dau wayarta ta tura masa sako akan cewa tana bukatar ganinsa cikin gaggawa..
Daga can Abuja kuwa hanklin mahaifin Ahmed, Alhaj bello jimada yadan samu kwanciya ne musmmn da yake da tabbaci akan inda dansa yake aynzu, Saidai gidan nasane har iyanzu bata masa wani dadi sosai duba da yadda matarsa hjy khadijatu take yawan daure fuska dashi sosai akan batun makircin da yan uwansa suke mata ita da danta ahmed.
duk dama yasan sun zalunce ta amma shi so yake ta mance da komi ta yafe musu kai tsaye batare da sun nuna nadamarsu ko sun bata hkri ba, aganinshi ai anty moju matsayin uwa take awajenshi, snn tunda yana girmamata sosai, babu wani amfanin tuhumarta da dalilin tay musu laifi saidai ayi hkri da ita, hjy khdijatu taki sam ta amince da wann zance nashi na sonkai haka ma taki ta saki jikinta da su sam.
Kwanan biyu Duk saida ta dibi tasharsu ta watsar. Dan a Yanzu damuwarta baifi taga danta Ahmed ya dawo izuwa gareta ba dan ita haryanzu hanklinta bai wani kwanta da shirun san nan ba. Yawancin lokuta, idan tafara jin faduwar gaba mai tsanani akanshi bata jin sakat aranta, tay ta neman layinsa kenan amma haryau saidai tajishi akashe, gashi tunda kafayat ta koma son hira ata sashen baban san sai bata wani fiye wani janta ajikinta sosai ba,yawanci saidai ta zauna a dakinta ta kira babban dadarta hajy maimunatu suyi magana dan itace kawai aynzu take kwantar mata da hanklinta sosai.
Duk wani abunda take ciki agidan saida ta fadawa dadarta dan rashin Ahmed agidan na kwana biyu ya saka ta fahimce cewa itace kadai bare agidan mijinta saboda bambamcin da suke nuna mata na kabilanci.
Gashinan dai har marinta mijinta yay akan laifin da bata aikata masa ba amma Kwata kwata baiya son ya nuna mata afili cewa yan uwansa ne su kayi kuskure dari bisa dari saidai ya nuna kamr cewa ykmta ita tay hkri ta mance da komi kawai itace din zatay hakurin zama da su.
Har mamakin yadda suke nuna son kansu takeji aranta. They dont even care about her feelings musammn ma da makircinsu ya jawo mata mari da rashin mutunco awajen mijinta, sosai Ta lura da su, kai hatta kafayat tana da wnn dabi'ar tasu na son kansu dan duk sanda aka tashi fadin wani aibun danta Ahmed ko laifin sa sam ita bata tunowa da nata aibun saidai tayi shiru ko tay nadaman zuci.
Tasani sarai da cewa kafayat haryau tanakan zarginta aranta da tunanin hala ko itace take juyawa Ahmed kai ne akanta, kwana biyun nan shiyasa taja jikinta da ita agidan sosai.
Aranta tana zargin cewa son hira da Zama da kafayat takeyi kwana biyu a gefen mijinta bana lafiya bane saidan ta cusa mishi kai donta cimma burinta na tunxira shi domin ya aura mata Ahmed acikin gaggawa.
Ta rasa yadda zatay ta fahimtar da kafayat cewa dukansu basu da masaniya akan dalilin dayasa Ahmed yake kaucewa da yin jinkiri akan batun amsawa aurensun ba.
Sosai kafayat ta zanca mata, wani bin sai taga tana behaving ne kmr bata yarda da ita ba musammn ma dataga ta fara samun cikakken kulawa daga wajen mahaifin Ahmed din shikansa..
Shidin ma tunda yaga kafayat ta fara nuna masa yarda sosai da amincewarta agareshi shikenan saiya fara zargi da tunanin hala hjya khadijatun tana nuna mata bakin hali da warayya ne, aynzu dia kafayat nunawa take yi kamr da shi kawai tafi amincewa, ta fi saka hope dinta akanshi ne sabida aganinta koda za'a mata kabilanc shi ai bazai mata ba.
Sosai kafayat ta dage wajen kyautata ma mahaifin Ahmad, Kwana biyun nan ma tun kafin nan hjya khadijatu ta fito tsakr gida zata zo ta samu har kafayat tay masa komi na girki da arrangin kaya mostly saidai yazo yaci abinci ya tashi ya tafi batare da yanemi kowa ba.
Wani bin intayi nazari akan yanayin halayyar danta Ahmed a lokaci guda take fahimtar cewa ajinin mahaifin shi ya dauko wasu banzayen halayyar sa dayakewa yan mata.
They just love taking advantage of girls dan tunda kafayat ta soma zama ata wajenshi haka nan yake sakata tay masa wann tay masa wann kmr ya samu jaka.
Da abun nasu yabi ya isheta duk ta ibi kashinsu ta watsar agidan duk dama babban dadarta Maimunatu sam bata amince da irin wann dabi'ar na kafayat ba.
Ita tuntuni aranta ba son tarayyar Ahmed da kafayat takeyi ba dan gani take kamar Zata lalata masa rayuwarsa ne kawai dan bata da isashen tarbiya ajikinta.
A tunaninta a al'adance ma bai kamata kafayat din tazo tazauna musu a gida ba, wann dabia na rashin kamiya da wasu kabilu sukeyi sosai yake bata mamaki,saidai ayanzu tasan idan har yar ta turasa yar uwarta tay magana kowa zai juya maganan akanta ko ace ta zalunci kafayat din ko ace tana zargin mijinta wanda zai iyayin sanadiyar zaman aurenta datayi sama da shekara talatin dan tasan kiris yarbawan nan suke jira su tozarta mata yar uwa.
Transcop hotel
Calabar: 10 am.
Da safiyar yau din Ahmed da babban yayansu kazim aremu da kuma brother hamzat dimeji suka hada long video confrence call mai dan tsayi dan su tattauna akan batun auren sa da Adiaha.
Sunzo suji dalilinsa na aje batun aurensa da kafayat shikuma yay iya bakin kkrinsa wajen nuna musu cewa hanklinsa ne kawai bai gama kwantawa akanta ba amma bawai don baisonta aransa ba.
bai dai wani bude musu dalilansa sosai ba sai ya gaya musu cewa adiahan ma tafi sonshi dan har kashe kanta takeso tay dayace ya hakura kuma baison yay sanadiyar mutuwar yar mutane.
Duk da hakan Hanklin Brother Kazim aremu bai wani kwanta sosai da yaji cewa da akwai jinin inyamuranci ajikin Adiaha ba, cos normally they are this little skeptical particularly da igbo ppl sabida dukansu yare ne wanda basu wani yarda da junansu sosai ba.
Aransa yaso ace da duka iyayentan mutanen garin cross river, calabar ne. da hala bayanin nasu zaizo masa da sauki, shi duk tunanin shi yadda su aunty mojushola zasu dauki maganan ne, dan yasan basa kaunar hada jininsu da inyamurai sam sam.
Sosai suka tattauna akan hakan atsakaninsu Brother hamzat dimeji ne ya dan kwantar masa da hankli dayace masa ai mahaifin Adiaha wato mr bassey ba inyamuri bane asalin dan calabar din ne dan shi yaren calabar din yakeyi dake yaren mahafinsa ne.
Saidai uwarsace mrs chidara data kasance inyamura gaba da baya take inyamuranci, dan haka yana ganin kamr yaren adiaha bazai zame musu wani matsala ba Cos technically,duk yaren uba ake bi so za'a iya cewa Adiaha calabar girl ce not an igbo girl duk dama ansan yes tana da jininsun ajikinta sosai ta wajen kakannin ta mata.
Ahmed Bai wani bude musu abunda ake ciki da rikicin dangin Adiaha ba amma ya gaya musu cewa da akwai babban matsala wajen iyayenta sabida basu son yarsu ta canza Addini ko tay aure anan arewa. Snn ya gaya musu yadda sukayi da grand mum dinta hjy hajara da iya abinda tace mishi na cewa inhar da gaske yakeyi zai aure jikarta adiaha ita zata yi musu komi na batun auren nasu.
Ahmed ne dan autarsu snn Dukansu Sunason dan uwan nasu sosai dan haka suka masa alkwarin tsaya masa akan batun auren nasa dik rintsi duk wuya.
Brother kazim aremu yana kasar waje dan haka suka bar komi na formalities din auren a hannun brother hamzat dimeji, shikuma brther kazim din yay musu alkwarin cewa shi zai fayyace ma mahafinsu komi da komi dan sunada fahimtar juna tsakaninsu sosai.
Brother kazim yasan cewa abu mai wuya ne duka familynsu su aje maganan aurensa da kafayat a lkci guda amma dake yana da shirinsa na musammn dayake musu duk sai abun bai wani damesa ba.
Shidin yana da arziki sosai dan har kamfanin kanshi ya gina inda ake processing din kayan abinci ana kaiwa kasar waje. Yanzu haka ya siya
ma iyayensun wani irin makaken gida family house size irin hadadden luxury bunglow din nan nagani na fada mai sashe sashe wanda kowane acikinsu zai iya zama da familynsa aciki anan A Abuja cikin anguwar garki.
Yana so ne ya kammala furnishing din gidan kafin yace musu su duka su koma can tare da matar sa wato aunty adizat da yaransa uku maza, Da shikansa brother hamzat din da matarsa aunty nurat da yayansu, Da Shi Ahmed din duk dai yace zasu iya zama a kusa da iyayensu acikin gida daya in har suna son hakan.
Yay hakan ne sabida babban burin mahaifinsa kenan yaga kan yayansa duka ahade kuma familynsa su rayu a waje guda cikin hadin kai da taimakawa juna.
Already brother hamzat baida matsala da wnn plan din dan dama gidan dayake zaune aciki mortgaging dinsa yay da bank,hakama anty adizat tana son duk adawo waje guda dan tasamu daman bada hankli akan aikinta, hakan zai iya yuwa ne idan yaranta suna gida agaban idanun kakanin su ana kula mata da su. Saidai haryau basu san ra'ayin Ahmed akan hakan ba tukuna.
Tunda suka kammala maganan auren brother kazim ya soma bada oder wa client dinsa dan asamu agaggauta kammala furnishing din babban gidan nasu dan yasan da hakan ne kawai zai iya rufewa mahaifin su da su anty moju shola bakinsu akan maganan auren Ahamed da Adiaha acikin gaggawa.
He believe dat Komi arayuwa yana bukatar nitsuwa da kuma siyasa, dan haka bai damu dayin komi ba musmmn in hakan zai samar ma dan uwansa Ahmed damilare kwanciyar hankli.
Ata fannin mahaifyar Adiaha kuwa tana isa wajen chief priest dinsu da fushi da takaici ta zauna gaya masa iya bukatun ta akan yarta adiaha,saidai bai wani bata goyon baya tay ma yarta auren sadaka ba sabida al'adansu yana daraja kimar mace sosai musmmn ma akan batun aure, shawara ya bata yace mata tay hakuri tabi yarinyarta ahankli
council of elders zasu taru suyi mata fada snn aja kunnenta ahankli zasuyi komi domin a aurar da ita ayadda al'adansu yace.
Badon ranta yaso ba tay hakuri ta koma gida da tunanin abunda ya gaya mata na cewa taje ta jawo yarta ajiki ta lallame ta snn ta fara jin damuwarta tukuna.
Tun dawowarta gidan ta aika anemo mata adiaha amma ba'a ganta ba, duk kuma sai taji ta damu sosai da taji shirun yartan yay yawa,nemanta takeyi agari taje duk gidajen kawayen ta, sai can data gamu da wani crier ahanya zashi kasuwa snn ta lallabeshi ta bashi kudi snn tace masa yaje ko ina lungu da sako dayasan adiaha tana zuwa ya nemota ta dawo gida acikin gaggawa.
Ahmed yana kammala magana da yayunsa yaga sakon Adiaha almost 30 minutes ago, ya gaji sosai da fitinanta amma haka yay Refreshing kansa ya saka wata black dubai jallabiya mai laushi da kyau snn ya fito domin yaje ya dubata.
Lokacin ita kuwa harta gaji sosai da jiransa ta siye abinci tanaci kenan sai gashi nan ya taho awani motar haya.
Miƙewa tay ta koma ta can ta inda babu wani hayaniyar mutane sosai snn ta tsaya tana ta kallonshi ayayinda yake karasowa ta wajenta.
Wani iri ta dingaji a ranta dataga irin azaban kyan dayayi dayasaka simple sutura ajikinshi,yanayin shi mai cike da aji da kasaita take kallo ayayin da yake zuba nitsatuyar takunshi mai tafe da kamiya da wata iriyar nitsuwa,tsikar jikinta duk saida suka motsa ganin ya zuba idanunshi shima tun daga can yana kallon ta,ahankli ta lumshe idonta snn ta bude cos she feel soo very lucky to have him, atake wasu irin zafafan feelings masu wuyar fassarawa suka fara shigarta tundaga tsakar kanta zarensa yabiyo harta kololuwar sawayen kafafunta yanamata tsitta mai saka ragwabewar jiki.
Tun kafin ya iso taji duk wani damuwarta ya kawar tafara masa murmushi, dan abunda tazo gaya masan ma gabaki daya sai taji yay escaping mind dinta sabida farincikin datake tsintar kanra acikin inta kallesa, yana isowa daf suka hade idonsu waje guda yanamai kashe mata jikinta da kyakkwar murmushin sa mai taushi wanda ya tarbeta dashi snn suka gaisa tq riko hannunshi cikin nata sauya fara tambayarta halinda ake ciki.
Hannunshin ta dada rikowa cikin nata tana sauke ajiyan zucya sann ta fada masa cewa "tsoro takeji" Da mamaki Yace mata tsoron me takeji ko wani abu ya farune agidan nasu?
Tace masa a'a, tana tsoron dai kar ya watsa mata kasa a idonta ne dan ta riga da ta fara fahimtar cewa kamr iyayenta bazasu amshi batun auren nan nasu ba.
Tace masa" dolene itace zata hkra ta sadaukar da komi nata dan tay fighting ma soyayyarta .
Ahmed sam baison jin tana furta hakan sabida yasan abunda yakeji aransa akanta baikai haka ba. Aransa yasan Inda ace adiaha bata zafafa mgn aurensun ba,hala da tuni shikam ya hakra ya bar garin ya koma Abuja abunsa sai dai gani yake kmr a zauce take da giyar soyayyrshi ayansu da wuyane ta iya rabuwa dashi tacikin sauki
ynzu kawai tabbaci take nema daga wajenshi na cewa bazai guje mata ba duk rintsi duk wuya zai kasnce yana tare da ita harsai sun cimma burin su na aure.
Cikin rashin wata mafita Ahmed Yace mata karta damu babu inda zaije snn har yay magana da brothers dinsa shi ata fanninshi kusan ma a shiryesuke ita kawai suke jira.
Sosai wann maganan ya faranta mata rai snn ya kara mata karfun gwiwa gani take a brain dinta kamr dagaske ne Ahmed yana mutuwar sonta aranshi.
Nan ta soma masa bayanin abubuwan da zai iya faruwa yau izuwa gobe Dake duk abababen daya shafi a'aldarsu ta dabbaka bautar Allolinsu ne tun na kaka da kakkani, nan Tafara gaya masa yadda akeyin wnn festival din, suna cikin maganan sai tafara ji ajikinta kamar wani ya labe yanata kallonsu saidai kodata juya baya tana dubawa bata ga kowa awajenba.
Tay murnushi snn Tace masa dodonin Allolinsu zasu bayyana yau asarari da siffofi mafi muni da kuma ban tsoro Dan haka bazaiyu yau tazo wajenshi ba harsai an kammala komi sabida wann festival nayau din is very spritual for all the tribes din dake wann yankin nasu basu kadai ba.
Yanzu haka dodonin nasu suna kiillace ne a makewayensu inda ake ginashi da fresh palm tree leaves mai tsawon dayakai 15fts sabida ba a bukatar kowa yay ido biyu dasu harsai lokcin fitowarsu sarari yay.
Suna cikin wann hirar tasu cikin nishadi sai ganan motsin kafafu ata bayansu da alaman mutane suna tahowa ta wajensu agaggauce.
Dukan tara tara kirjin adiaha yay tay saurin kwace hannunta ana Ahmed snn ta leƙa ta bayanta agurguje kafin nan ta dawo da baya jikinta yanamai barkewa da wani irin rawa mai tattare da rudewa.
Mahaifiyarta tagani tare da wani crier sun tattaro kattin maza har su guda uku masu jini ajika sun runtumo manyan sandu na a hannayensu suna tahowa ta inda suke dashi. Gabanta ne yay mummunan fadi dan sai yanzu ta gane cewa dagaskene dazu da jikinta ya bata ashe tuntuni da akwai wanda yake lekensu da alaman shine yaje yakai gulma.
Tsabar bugawar da kirjinta yakeyi sama sama numfashinta yake hawa, ta juyo a rikice ta kamo hannun Ahmed tace masa dolene ya boye kansa anan wajen inda suke kar mahaifyarta tazo ta ganshi su tada wata fitina harsu jawo ace za'a kashe shi.
Yace mata shi bazai buya ba saidai in ya tafi
Ta dada lekawa taga sun riga sun iso kusa dasu inhar Ahmed ya juya ya tafi toh tabbas zasu bishi sumasa illa awajen dan asananinta da fushi da fada suka rabu da mahafiyarta dazu agida dan haka koda tazo nan hala ma bazata tsaya ta fahimceta anan din ba.
Jawo hannunshi tay cikin gaggawa da narkakken magiya idanunta cike da tsananin tsoro tanace masa karyay mata taurin kai, duk yabi ya gaji da lamarinsu, amma hakann take janshi, nn ta bude wani old sac tace masa ya daure ya shiga ciki ta rufeshi, da taurin kanshi da komi da kyar dai ya shiga ciki ta rufeshi acikin wani katoton buhu snn taja ta tsaya awajen abunta.
Tana kammala rufe bakin buhun saigasunan sun fantsamo cikin wajen a hargitse, "wher is he?tambayar da kowaa ya jefo mata kenan aka barta da zare ido tana kallonsu.
Da kyar Taja taci fuska jin yadda mahaifyarta ita kanta take cika ta da tambayoyi akan mutumin da akace anganta dashi saidai batace mata uffan ba
Matasan nan kuwa atake suka fara bincika wajen suna hargagi kusan dik inda suka taba sai sun buga ma wajen sanda dansu razanar da su sosai, aganinsu inma boyeshi tay ai zaiji tsoron rasa ransa ya fito amma ko motsi Ahmed baiyi awajen ba
Duk borin da Adiaha tay musu na cewa ita kadai ce awajen bai hanasu komi ba har jikin sac din suka bubbuga wanda yay sanadiyar jima Ahmed ciwo agefen kunnenshi.
Da kyar dai suka hakura suka kyaleta musammn ma da adiaha taki ta amsa tambayoyin su.
Crier kuwa yace musu tabbas yaganta anan tare da wani hausa man yasaka jallabiya snn da dukkan alamu sun saba da junansu sosai.
Hade da mahaifiyarta da wayann matasan duk suka taru suka mata barazanar cewa indan ta yarda har suka ganta da irin wayann mutanen da crier ya fada toh zasu mata abunda bazataji dadinshi aranta ba.
Inhar yarinya budurwa fara biye biyen strangers irin haka She will be question by the gods.
Sanin hakan yasaka mahaifyarta tamata jan karfi ta tasota agaba har suka kai gidansun atare.
Tun ahanya take turawa Ahmed tex duk ta damu da yadda ta barshi awajen shikadai, ta tura masa sako ajere yafi sau takwas tana tambayarsa koyana lpya, ciwo kansa ya dingayi sabida buga sac din nan da suka dingayi da karfi. Tsabar baison wani fitinan kawai sai ya rubuta mata cewa he is fine, hakan ma ai bakomi bane. Sosai hnklinta ya kwanta daya rubuta mata hakan.
Daga isarsu gidansun kuwa wani sabuwar cece kuce ne ya kaure a tsakaninta da mahaifyarta.
Mrs grace ta matsa daa cewa lallai sai Adiaha ta fito fili ta gaya mata wayene mutumin da aka gansu tare da shi.
Tun Adiaha tanajin shakka da nauyin fada harta soma fayyace abun ahankli ahankli, matsalar shine sudin suna bala'in mutunta iyayensu dan haka bata iya fitowa fili gatsau ta fayyace mata komi dake wakana a tsakaninta da Ahmed ba
Kawai ce mata tay aynzu tana da wanda take so, shiyasa gaskiya bazata iya auran zabin da aka mata ba.
Wann bai dame mrs grace sosai ba dan ta riga tasan halayyar yaran zamani da canze canzen ra'ayi na banza.
Babban Damuwarta shine ta tabbatar da cewa ba wani hausa man din bane kamr yadda labari yazo mata dazu
Da kyar ta samu nitsuwa aranta akan hakan, sann ta tutsiye yarta adiaha akan data gaya mata wanene wann masoyin nata,daga in ya fito, snn waye shi? tsoro da fargaba saiya hana Adiaha iya furta komi, tin mahaifyar tata nabinta cikin lallami harta soma fahimtar cewa da akwai abunda yarta adiaha take boye musu. Gashi dai crier din nan ya riga daya fayyace mata siffar yaron ya tabbatar mata da komi, amma sam batason ma ta fara amincewa da hakan aranta dan aganinta inhar hakan ne toh kwakwalrta ma bazai iya daukawa ba bare ajega ta furtashi da bakinta wani yaji.
Duk wani wayo da uwa takeyi domin ta samo bayani awajen yarta saida tay ma Adiaha saidai the more tana tursasata ta fada the more tana fahintar cewa da akwai babban lamarin da adiaha take son gaya musu mai girgizawa da kuma nauyi sosai wanda shine take boye musu ayanzu.
Tun ba'aje ga bayyana komi a fili ba jikin mrs grace ya soma mutuwa, jiknta a sanyaye tace "Adiaha, ki rantse da ubangiji cewa baki da wata alaka da wani bako
Dayazo garin nan..
Adiaha tay shiru kanta na can kasa harsaida hakrin mrs grace ya kare ta daka mata tsawa snn tay motsi ta dago kai tana kallonta awani irin yanayi na rashin sanin inda zata fara furta wann maganan
Nasu da ahmed a fili.
Ahankli Tace mum, its true ina da wani saurayi, he is not from here...
..amma ina sonshi,..ina son Doctor Ahmed
..shinake son na aura..
A rikice mahaifyartan take kallonta ayanayin shock ta kunce zani ta yar akasa snn ta daka wani rikitaccen tsalle snn tace "Doctor who?kikace A..Ahmed,ewoooo a Hausa man?.Adiaha a hausa man, cikin girgiza kai tace _mba nu_ banji ki da kyau ba..zoki min bayani i dint get u..
Adiaha bata iya cewa uffan ba tafara ja da baya baya sabida tsananin tsoro, acikin bambami ta karashe cewa mumy im serious ooo, ni dai shi kawai zan aura. .
Mrs grace ta harzuka ta na shirin cafkota ta firgita ra ruga aguje ta shiga dakinta ta kulle kofarta da key jikinta na tsananta rawa jin inda mahaifyartan take dada kwala mata ihu cikin tambayarta daga waje.
"Adiaha you must come out and explain urself ooo..
Shiru tay ayayinda ta jingina bayanta da jikin kofar tana jinta tana ta rusa mata buhun masifa
mrs grace sosai ta fara fahimtar inda yarta adiaha ta dosa, duk sai taji jikinta ya mutu, After a while adiaha sai taji shiru bata karajin motsinta a bakin kofar ba.
Da kyar ma ta leko ta windo taga ko ina shiru da alaman babu kowa agidan nasu ji take hala duk anje ne ayi shirin festival dan haka ahnkli ta bude kofar ta fito tana mamakin inda mahaifyarta zata kasance ayanzu.
Wayar Ahmed ta kira bai dauka ba ta tura masa text messg ta gaya masa cewa mahaifyarta ta soma fahimtar komi game dasu tunma bata fayyace mata ba.
Ficewar mrs grace agidanta yau sam bai mata kyau ba dan kuwa koda taje tay kyakkwan bincike abakin mutane saiji take ana ce mata lallai ana ganin adiaha da wani bakon mutumi wanda basu taba ganinshi ba.
Kanta duk ya daure, Wani tunani tay snn ta wuce gidan dan uwan mijinta uncle uno,tana isa direct ta aika aka kirawa mata yarsa ekaete.
Agaba ta sakota har gaban iyayenta inda tasan bazata iya boye musu komi dake tafe da yarta adiaha ba.
Haka suka saka ekaete agaba ta tambayoyi har saida tay musu bayanin komi batare da son ranta ba..
Ita kanta ekaete din sai data jibgu sosai awajen iyayenta data kammala fayyace musu kan lamarin..
Tsabar rudewa da mugun gudu mrs grace tay hanyar jeji tana kuka tana mai kiran sunan mahaifin adiaha, tunma kafin ta isa gareshi muryanta harya soma dishewa..
A gigice ta isa gaban bukkan da mijintan ya gina Lokacin yana kan bishiya yana hutawa.
Da asalin yarensa na calabar ta soma gaya masa cewa ya sauko kasa kawai yaje yagani da idonshi Tarihi zai memeta kanshi agidansu
Tace masa Yarsu adiaha ta kawo namiji dan hausa tace lallai sai shi zata aura kuma hartana zuwa wajen shi batare da sannunsu ba, Kafin ma ta kammala fada masa sauran bayanin na cewa yarsa na cikinsa harta yanke hukuncin cewa zata sauya addini tuni zuciyarsa tay fat fat ta buga garin saukowa kasa cikin gaggawa nan ya rikito ya fado kasa sumamme.
Daga nan asibiti kawai aka wuce dashi inda atake yan uwansa suka kewayeshi,koda ya samu ya dan farfado tun akan gadon yake famar tsine ma yarsa adiaha, yanamai cin alwashin cewa zai kasheta ya huta da bakincikin datake so ta gundura masa anata daddaneshi ana bashi hakri. Ekaete ne tay kkri wajen sanar da adiaha halin da ake ciki batare da kowa ya sani ba, dan ko kadan bata son ta rasa aminiyarta akan namijin da tasan hala basonta yakei ba.
Tunda Adiaha taji abunda yake faruwa da mahaifinta a asibiti take bari kar kar dan atake ta fara jin wani irin fargaba da tsananin tsoro mai rudarwa yanamai nakasa mata gabobin jiki
Tasan tabbas sukayi ido hudu da mahaifinta yau kasheta zaiyi har lahira dan haka dolene ta san abunda zatayi, tunanin
Duniyan nn tay amma da kyar ta samu wani mafita kwara daya wanda bata da kwakwaran tabbaci akansa amma tasan shine iya hanyar tsirar wanda zai iya kubutar da ita daga mutuwa awajen mahaifinta ayau.
Sako take shirin rubutawa wa Ahmed sai kuma taga kamar sakon bazai iya fayyace masa muhimmacin plan din nata ba.
Acikin sanda ta sudade jiki ta wuce hotel din taje ta sameshi, yau ko zama batay ba ta hau gaggaya masa abubuwan da takeson yay acikin gaggawa kafin yamma yay. Nan ta aje masa phone number da home adress na kakarta tace masa duk yadda za'ayi dai yanemeta ya gaya mata halinda takeciiki.
Tana kammala masa bayanin komi tay masa sallama cikin yanayin gaggawa ta barshi ta komo gidansu adan gaggauce dan batason wani ya biyota abaya bare har asan inda Ahmed yake bare ajega zancen cutar dashi.
Dan aynzu ji take kamar Ahmed din nan shine kawai rayuwarta ..
Tana isowa compound din gidansu ta samu daf lkcin an dawo da mahaifinta daga asibiti ganan yan uwan da elders na zuriarsu duk an taru a tsakar gida ana jiran aga kalar hukuncinn da iyayenta zasu dauka akanta kai tsaye.
Da kyakkwar shirinta tazo dan haka ta zube kasa tafara birgima tun daga gate tafara kuka mai yawa tanamai nuna nadamarta akan abunda yake faruwa.
A farko duk sun dauka tsorone ya sakata ta rikice amma daga bisani da sukaga cewa ta kama kafafun mahaifinta tana kukan fitar rai tana cewa ta tuba duk sai jikinsu kuma yay sanyi.
Tay kneeling agaban kowa tana kukan makirci harda majina ta shiga gaya musu yadda ta hadu da ahmed da irin son datake mishi, sai kuma ta wayence tace musu aynzu tay nadamar abunda tay na cewa zata aureshi bayan tasan irin baqin cikin da hakan zai jawo ma iyayenta.
Atakaice dai Adiaha ta nuna musu cewa ta yanke alakarta da Ahmed
Yau Snn ta tuba hardace musu ta amince ayi mata auren kawai da duk wanda sprit of the ancesstors dinsu ya zaba mata ayau awajen festival.
Yadda ta dinga neman gafararsu da zuciyarta har Saida ta bawa kowa tausayi kowa jikinshi yay sanyi aka fara tausayinta sosai..
Duk da haka saida aka dan yiyyi mata masifa aka kara ja mata kunne
Nn mahaifinta ya yanke hukuncin cewa daga an zabi mijin adiaha awajen apeasing gods dinsu yau, gobe da sassafe za'a fara shiryata domin bikin aurenta.
Ahaka suka tsaya da maganan kowa yaje ya hau shirin fita wajen festival hnkli kwance dan adiaha sam taki ta nunawa kowa cewa badagaske takeyin dukkn wayann biyayyar ba hatta ekeate ma saida ta boye mata wnn shirin nata.
A bangaren Ahmed kuwa iya abunda tacemai yay shidin yayi, ya tura ma kakar tata sako, snn sukayi waya sai tace masa zata biyo jigi tazo calabar daganan zasu taho yola tare da jikarta adiaha, amma kafin nan tana da bukatar shima ya je gida yataho da nasa magabantan domin ayi maganan aurensu a lokci guda komi ya wuce musu.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top