final episode
*KISHIYAR KAƁILA...*
BY SURAYYAHMS
This is For you NOOR EEMAN💞
FINAL EPISODE.
Bayan tafiyar kafayat gidansu bada jimawa ba brother kazim ya soma bullo musu da maganan Auren Ahmed da Adiahar a siyansance,cikin salo yabi dasu har sai bayan daya kwato hanklinsu duka izuwa gareshi snn yabita hanya mai sanyi da hikima cike nitsuwa da kammala tareda sako tausashiyar muryansa ya musu maganganu masu bala'in shigajiiki akan sanin darajar yayansu.
Yace duk wa yann yan mata da suke bibiyar rayuwar Ahmed da aure shikansa yasha sawa ayi bincike akansu snn ya fahimce cewa yawancin su sunada wata manufar su na daban shiyasa bai yarda da zancen fifita burin wata ya mace akan na dan uwansa ba. Yay maganganu masu dumbin ma'ana tare da basu misalai wanda suka shigejikin baban nasu sosai suka sakashi yin nazari da tunani.
Yace musu kowa a duniyan nan is being selfish intakama akan batun auren dansa ,toh Meyasa su bazasu iya tsayawa tare da Ahmed dan susan asalin damuwarsa akan batun aure ba saidai suyita tursashi akan mace daya.
Acikin salo yay amfani da lamarin kafayat ya gaggaya musu laifinsu da sukeyi wa Ahmed na cusa masa damuwar auranta aransa, yace musu alkawari kuka mana cewa bazaku mana auren dole ba amma Sai gashi kuna kan cusawa Ahmed kafaya kmr dan dolenshi ne saiya aureta.
He agree with them da cewa Ahmed ya dade suna tare da kafayat, bayan nan kuma sai ya kawo musu tauhidi yanamai cewa ai ba doka bane yuwar aurensu,xai iya yakasancewa zuciyar Ahmed ya canza with time, ko na kafayat din ya zanca, ko kuma kalamn aure ba qaddara bane atsakaninsu, Saiyake tuhumarsu da cewa inhar ata fannin kafayat ne aka samu jinkiri suna tunanin iyayenta zasu amince su tursasata ta aure Ahmed ne in bata da ra'ayin aurensa ba?..
Sunfi awa biyu tare da brother kazim yana musu magana cikin hikima yanamai kawo musu dalilai daban daban da zai saka su dena saka ra'ayin kowace mace asama dana dansu Ahmed.
Saida ya lura jikinsu yay sanyi sosai snn ya fara kawo musu maganan cewa shikansa yasan sirrikan Ahmed dayawa wanda su basu sani ba. yace Ahmed yakan fadamashi damuwarsa inta masa yawa. Snn ya razanasu cikin salo yace musu Ahmed is going tru anxiety nd depression saboda su,yace yanajin mugun tausayin dan uwansa ga matsi awajen aiki ga pressure agida yace musu Ahmed yanacikin damuwa sosai musmmn akan dalilin family pressure da suke saka masa akansa na batun auren kafaya.
acikin ruwan sanyi brother kazim yamaida maganan ya dawo wani babba snn ya nuna rashin jin dadinsa akai har saida yasaka su acikin tunani da jin fargaba.
Koda suka damu suji damuwar Ahmed din daga bakinsa yace musu shi bazai gaya musu komi ba.
Ranar har karfe goma na dare suna masa bayani akan manufarsu akan Ahmed kowa yana kkrin yayi explaining kanshi, ahakan ya samu daman amfani da nadamarsu yace musu Ahmed yana son kafayat din ai bawai bayasonta ba amma magana ta gaskiya shine akwai wata wacce yake son ya aura.
Bakaramin mamakin jin hakan sukayi awajensa ba, musammn daya fara tsakura musu irin son fitina da yarinyar takeyi ma Ahmed, yace musu idan sukaga yarinyar ma wallh saisun tausaya mata,sai sunce kafayat batayi komi ba wajen nunawa Ahmed kauna, Bai karasa musu labarin ba Yace musu su kwanta haka suyi bacci kawai
Sai gobe da safe zai kirasu dashi da brother hamzat su musu cikakken bayani akan abunda ake ciki.
Duk zakuwarsu da tashin hanklinsu saida suka hakura suka bar zancen izuwa washe gari da safe duk dama aransu basuji dadi da akace Ahmed ya kullace su aransa har yakaiga depression ya kamashi ba. Dake suna son ƴayansu duk sai hakan ya daga musu hankli bana wasa ba, nadaman matsa masa da sukay akan kafayat din sai yafara cinsu akasar ransu sosai.
Hakan ne yasaka har washe gari ranar waliman bude sabon gida dukansu basu wani nemi inda kafayat din take ba dake sun santa da son aiki hala har ta wuce gidansu anty mojushola tayasu shirye shiryen bidiri.
A ta fannin Adiaha kuwa daren gaba daya bata samu runtsawa ba dan duk hanklinta atashe yake da furucin Ahmed akan abunda kakarta tace akansa.
Ta tura masa tex na ban hakuri yafi a kirga baiyi replyn ko daya ba, tana kiran layinsa kuma zataji akashe kusan kwana tay tana cikin damuwa akansa sosai.
Washe gari da kyar ta tashi zatay sallah dake bata wani iya sosai ba saida ta danne zuciyar ta taje sashen hjy hajarat.
A zaune ta sameta akan daddurma tanajan charbi
Kallo daya tay mata ta dauke fuskarta dan bakaramin takaicinta takeji aranta ba.
Ganin yanayin kakar tata ya sakata jin bata kyauta mata ba, dake tana da tausashiyar zuciya hakanan ta zauna kasa kusa da ita tafara bata hakuri akan rashin kunyar datayi mata jiya agaban mijinta.
Hjy hajara taso ta karayi ma Adiaha magana akan Ahmed koda zata shiga hayyacinta a fasa auren nan amma yanayin Adiahan yasaka ta kasa iya ce mata komi.
Cikin sauke nannauayr ajiyar zuciya Tace mata ai komi ya wuce Snn ta amince mata tay aurenta da duk wanda take so tunda Abunda ta zaɓa ma kanta kenan..
Adiaha ta y murmushi tace ta gode,hjy hajara bata karace mata uffan ba harsaida ta kammala guiding dinta tay sallan safiya kafin suka zaune take ce mata Alhaj Aliyu zai kira Ahmed din ya bashi hakuri. Snn za'a daura auren ne da misalin karfe 2 da rabi na rana dan sunce yau zasu koma Abuja tareda ita.
Nasiha na zaman aure ta dinga mata, dana hkrin zama acikin dangin miji da iyayen mijin gabaki daya musmmn ma da dukansu suka kasance kabilu, tanayi tana jefa mata hannunka mai sanda acikin zantukan nata wai koda zata dan fahimceta tay makanta karatun ta nitsu amma ina Adiaha tay mugun nisa a son Ahmed bata gane komi idan ana fadin laifinsa agabanta.
Sassafe Alhaj aliyu ya danne zuciyarsa ya nemi Ahmed awaya privately ya masa magana man to man akan abunda ake ciki, Abun yadan ba Ahmed mamaki amma dake abokinshi banji ya riga ya bashi hakuri sai ya bawa alhaj aliyun hakuri kawai yace masa ayi masa afuwa lkcin datazo masa da maganan ranshi a bace yake shima badon ransa yaso yagaya mata hakan ba.
Tunda sukadan samu fahimtar juna da Ahmed shikenan kowa hankalin sa ya kwanta aka dawo ana jiran lokacin daurin aure.
Iya bakin kkri alhaj aliyu da hjya hajara sunakan yi wajen hidiman abincin da za'ai awajen daurin aure kominsu dan daidai gwargwado.
Banji ne aka aiko da safe yazo gidan ya kawo ma Adiaha kudi kimanin dubu dari biyu akan ta siya kayayyakin da zata saka da duk wani irin kwalliyar datake so tay na daurin aurenta ayau.
Tun da safen suka shiga kasuwa da kudin ita da kakarta hajya hajarat dan adan kimtsata tay kyau tunda yau ranar aurenta ne.
Bangaren su hajiya khadijatu kuwa tun asubahin fari da suka idar da sallah suka dokawa brother kazim kira atunanin su gara ayi maganan tun yanzu kafin ashiga hidiman waliman komawar sabuwar gida.
Suna kiranshi kuwa ya dauka sai yace musu bari ya fita a office dinshi zai kirasu dan lokacin mun ba daya bane dana can, yace zaiy connecting da brother hamzat sabida maganan babba ne.
Duk hanklinsu a tashe ya barsu yaukam ma sama sama sukayi break fast hanklinsu nakan waya suna jiran kiransa, da safe ne amma sosai gidan yay shiru duk anje gidansu anty mojushola dan anan ne za'ayi duk wata shirin hidima.
8clk dot saiga kirar brother kazim ya shigo.
Suna dauka sai brother hamzat shima yay kira daga yola sai suka hadu akan screen na computern mahaifinsu. Sunkai minti biyar suna gaishe da iyayen nasu cikin nitsuwa da nuna girmamawa sosai.
Kafin nan sufara tattaunawa akan Ahmed a farko ma saida brother kazim ya musu albishir da sabuwar mota jeep high lander ta tayi yar 20 million daya siya musu na gida yace kyautarsa kenan dazai basu na murnan komawa sabon gida, brother hamzat kuma ya dauki nauyin cewa shine zaina ciyar dasu agidan daga yanzu.
Murnan jin hakan yasaka har iyayen nasu har suka mance da damuwarsu akan Ahmed na lkcin sukadinga saka musu albarka suna musu fatan Alheri a rayuwarsu dukansu biyu har suna hawayen murna.
Each time suka shirya kawo maganan auren Ahmed sai sundan yi wasa da emotions dinsu
Koda sukaga sun yi sanyi suna cikin tsananin jin dadi da farinciki anan ne suka dawo a siyasance suka kama kan Maganan rayuwar Ahmed.
Lokaci guda kowa ya nitsu.
Tiryan tiryan Brother hamzat ya fara magana yanamai basu labarin duk wani abunda ake ciki da batun Ahmed da Adiaha yanayi brother kazim din kuma yanamai kara yima abun kwalliya sosai yadda zai saka sunajin tausayin yarinyar sosai.
Abu dayane basu gaya musu ba shine zancen zuwan Ahmed garin calabar akan Adiaha.
Kawai dai sun killace labarin ne ta hnyar nuna musu cewa poor Adiaha ta hadu da Ahmed ne during his reaserch kuma gashi harta sadaukar da komi nata sabida shi, yace "iyayenta, addininta da kabilarta, duk ta aje akan dan uwansu Ahmed kuma tunda Ahmed din yace musu hanklinsa ya kwanta da ita su sun yanke shawarar kawai ayi hakuri kawai abashi ita inyaso daga baya asasanta da kafayat.
Da mamakinsu kuwa Alhaj belllo ne ya fara amincewa da maganan dan bakaramin tausayin Adiahan yaji aransa ba duk dama bawai sun gaya masa asalin labarin ayadda yake azahiri bane.
Saidai jin cewa ta sadaukar da komi nata harta gudo yola domin Ahmed yasan cewa tabbas yarinyar tanason dansa sosai, brother hamzat yace musu yay bincike akanta sosai kuma ya hadu da kakarta a yola sunce in Ahmed din ya shirya zasu bashi auren yarinyar.
Daga hajy kahdijatun har alhaj bellon mamakin yayansun suka dinga sha jin sunyi komi aboye batare da sanninsu ba.
Sun dade suna tattaunawa akan lamarin har dai brother kazim ya fito musu sarari yace yana son aje adaura auren Ahmed din yau domin akawo yarinyar Abuja cos she dont have anyone anymore face Dan uwansu AHMED.
Iyayen sunso suja maganan amma hakanan yayunsa suka cinye su da kalamai masu dadi, duk inda aka bullo saisun toshe.
Brother kazim yace zai turo musu harda files na private investigation akan familyn Adiaha inma suna son suga shaida akan komi domin hanklinsu ya kwanta.
Alhaj bello da hjy khadija still basu amince da zancen auren kai tsaye ba saidai sunce sudai bazasu hana auren ba amma maganan ayishi yau yau sai sunyi shawara atsakaninsu tukuna, Sukace a basu nan da karfe 10 na safe zasu nemesu suji.
Bayan sun kammala wayar suka zauna tsakaninsu suka dan tattauna Akan lamarin Kadan kafin kowa ya koma sashensa domin yin cikakken tunani.
Banda tausayin Adiaha babu abunda ya cikama alhaj bello jimada kai.
Shikansa gani yake kmr tabbas koba dan komi ba iyakar jihadin zanca addini da Yarinyar tayi ta baro iyayenta akan dansa kodan wnn zai bari Ahmed din ya aureta dan su samu ladan shahada dukansu.
Ata fannin hajya khadijatu kuwa kanta sosai ta kulle tsakanin labarin Adiaha da kuma lamarin kafayat da already take zarginta da juya mata baya.
Wani bangaren na zuciyarta na gaya mata cewa idan sukayi hakan basuma kafayat Adalci ba duba da irin jiran Ahmed datay tun tsawon lokcin yaranatar su,awani bangaren kuma inta tuno da labarin adiaha sai taji aranta cewa babu yadda zasuyi su watsa ma yarinyar nan kasa a ido musammn ma data sadaukar da komi nata domin Ahmed.
Jin cewa kamr bata da alqibla yasaka ta kira sister ta hjy maimunatu,
Taci sa'a kuwa dan a aiport take zatazo south africa cikin birnun johannesburg domin tattaunawa da shugaban kasarsu tacan.
Nan ta gaya mata abunda ake ciki dan sosai ta rasa bayan wanda zatabi.
Bugu daya kuwa hjy maimunatu ta zaɓar ma Ahmed auren Adiaha, ta fito fili ta gaya ma hjy kahdijatu cewa yan uwan mijinta sun anty mojushola sunaso suyi amfani da kafayat din ne dansu mallake gidan ta batare da tasani ba,sann tace mata tunda Allah ya kawo mata babban mafita tayi marmaza kawai tay grabbing din shi, wann din wani oppurtunityne babba, tace mata tabi bayan danta Ahmed kawai akan abunda ya zaba makansa karta sake tay sanya akan ra'ayin kowa cos evryone is selfish about his son.
Yau har fada tay mata sosai akan nunawa datakeyi wai tanajin tausayin Kafayat tace mata duk layinsu dayane
Zatazo ne ta mallake mata danta bawai dan tazauna da su lpya ba.
Dake bata da wani lokci sosai maganan a tsaye sukayishi tace inhar ta kammala meeting dinta a south africa da wuri zatazo nigeria sama sama taga me ake ciki dan bazata taɓa kyalewa ayi ma yar uwanta taron dangi ba.
Bayan nan suka kammala wayar.
Ajiyar zuciya hajiy khadijatu ta sauke dan kuwa tabbas tasan babu yadda zatayi face tabi shawarar yar uwarta tabi bayan danta akan abunda yake so din.
Ta tuna jiya jiyan nan ma saida kazim yay musu irin wnn nasiha akan batun cusawa ahmed ra'ayi na daban. Zancen depression din da akace ya shiga ciki akansu sosai ya dameta dan tasan danta yanasonta sosai dolene yasaka abubuwa aranshi muddin zata juya masa bata.
Zama tay tanamai dogon nazari kafin nan ta tashi ta sake yin wanka ta saka wani irin cool royal blue ceibo lace dayaji wani irin aikin stones na alfarma, sosai tay kwalliyarta sama sama mai fidda kwalisa tay kyau ta fetsa turarenta masu qamshi snn ta dawo sashen mijinta ta sameshi yana kan danna wayarsa shikadai
Sau biyu ya kalleta sai yaji yakasa dauke idonsa akanta yafara mata murmushi hartazo ta zauna kusa dashi duk ya rude yana kallonta kmr sabon maye sabida hjy khadijatu kyakkwar bafulatana ce fara sol mai yellowish skin colour tana da tsiririn hanci zar kamr pencil, dirinta na zamani nne irin wanda tsufa baiya nunawa sosai ajikinsu din nan.
Har saida tay murmushi mai sanyi tare da lumshe ido tanamai kwantowa ajikinshi kafin nan ya dawo hayyacinshi sosai yasaka hannunshi slowly ya rungumota jikinshi sosai yanamai shunshuna qamshin turarenta mai dadi da shiga jiki, har wani lullumshe ido yake alaman dadin qamshin yana bugar dashi sosai.
Kaunarta ya dingaji aransa yanamai ratsashi sabida yanason mace irinta yar kwalisa da zata rika waiwayo masa da zamanin kuruciyarsa dan ya dingajin kanshi kamr matashi ba tsoho dan sittin ba.
Kisses masu zafi zafi yake sakar mata akan labbanta da goshinta
Ahankli har abun ya fara yin nisa sukaje dakinshi atare suka biyama junansu bukata cike da shaukin juna kamr ba atare suka kwana jiyan ba.
Bayan kura ya lafa kanta na bisa kan kirjinshi ya rungumota yana shafata kadan suka fara hirar lamarin dansu Ahmed, tunda ta fito fili tace masa itadai inhar Ahmed ya amince itama ta amince dan bata son tayima Ahmed dole a batun rayuwanshi amma zataso idan ya samu nitsuwa yay considering din auren kafayat din itama.
Alhaj bello dake cikin shaukin soyayya yace mata shima ya amince, amma inhar Ahmed baida ra'ayin auren mata biyu kwata kwata bazai sake takura mashi akan aure ba..yace mata duk sakacinsu ne ya jawo Ahmed ya tsallakesu da damuwarsa yakai kukan sa wajen yayunsa.
Haj khadija tace hakane
Sunyi kuskure ahaka amma komi zai gyaru.
Daga nan ta rungume mijinta gam gam ajikinta tanamai yaba mashi sosai akan irin hadin kan yayansa da hallacinsu saijin kanshi yake acan sama yana kara huruwa sama sama tsabar dadi.
Kamar jiki baisha ruwa ba haka ya sake komawa duniyar soyayya da matarsa dake ita kadaice matarsa daya auro mai karancin shekaru snn yayi tarawar aure da ita a matsayinta na budurwa wanda bata taba saduwa da kowani namiji ba saishi shiyasa haryau yake mugun ji da ita a harkan kwnciyar gadon aure.
Saida suka murza junansu akan gadon suka gaji snn suka shirya suka fito cike da shaukin soyayyarsu su mai dadi.
10.30 am suka kira Brother hamzat shikuma yay connecting da brother kazim suka basu go Ahead akan ayi komi daya dace akan batun ahmed din, hjy kahdija ma tace ta amince musu dan tasan hakan datayin ma zai saka dadarta taji dadi sosai
..tsabar alhaj bello ya yadda da yaransa bai wani ja ba da sukace karfe biyu zasu daura auren yace musu suyi komi zai aiko da kudi shima tare da wasu yan uwansu a matsayin magabantan ahmed din daga nan abuja, yace su tabbata bayan an daura auren zasu tura masa file din information familyn Adiaha zai duba izuwa yamma idan an kammala walima zaije ya sanar dasu anty mojushola komi kuma yasan suma bazasuki ba.
Komi ya kammala Alhamdullhi aka watse kowa na farinciki aransa.
Daga nan iyayen nasu suka shiga bidirin walima tare da family members aka fara hidima na komawa sabuwar gida,
hjy khdija da mijinta yau wani sabuwar soyayya suka bude kowa yanata kallonsu yadda suke makale da juna kusan kowani lokaci.
Bakaramin haushin hakan su anty mojushola sukeji aransu ba, kafayat is no where to be found, sai can har an kammala kawo duk wasu nau ikan abinci sann ta kirasu awaya tace musu taje wajen mum dinta for an emergency signature akan wasu document na babanta dayabar mata amma zata dawo sharp sharp kafin yamma dan bazatayi missing wann ranar ba.
Duk basu saka komi aransu game da kafayat ba nan aka cigaba da hidima anata bidiri ana shashewa sabida kaf yan uwan da abokan arziki sun halacci waliman an cika gidansun bana wasa ba dan har ankon leshuna farare saida akayi mata da maza.
A fannin kafayat kuwa tun yau da safe take rikici da mahafiyarta da kuma kawartan da suka kawo mata wani irin maganan banza akan waisuna son ta aure mahaifin Ahmed.
Tsabar takaici Kafayat saida tay kamar zata fasa musu kai da kwalba.
Yadda ranta ya mugun baci da suka ambace hakan yasaka sukayi saurince mata wasa suke mata amma har acikin ransu dagske sukeyi domin kuwa plan dinsu kenan sun fada ne dansukaga reaction dinta
Da kyar kafayat tay hakuri tabar maganan ya wuce dan awajen kamar zaginta akayi da akace ta aure tsoho dan shekaru sitttin da wani abu bayan ga Dan autarsa Ahmed nan dan talatin da biyu maijini ajika. Waima Me zatay da tsoho a duniyan nan? Kai ko brother kaxim ne akace ta aura batajin zata aure shi bare kuma babanshi..sosai maganan ta ƙona mata rai duk dama awasa suka mata shi.
Bangaren su Ahmed kuwa shikansa saida yasha mamaki matuka dayaji irin amincewar da iyayensa sukayi afarat daya cikin gaggawa.
Wanda aransa yasan cewa badon brother kazim ya hada musu harda siyasa ba da abunnan bazai taba yuwa acikin sauki ba.
Lokaci guda suka inviting dayan abokinsu bankole
Cos They plan the weding to be secret, shikam bankole akan abun munafurci dama yafi kauri dan ya fara tsanar halin kafayat tun ranar ta taɓa nunamishi cewa batason tarayyarsa da AHMED akan dan yana harka da yan mata.
Dukansu atare suka taso tun suna yara amma banji ne kawai yakeson Ahmed da kafayat, banky baison lamarin aransa ko kadan.
11.am ya iso yola ya same su a hotel, suna da ankonsu na kece raini da sukayi dayawa dan haka samun kayan sakawa baizamo musu tashin hnkli ba. Ahmed ne kawai aka kawo masa sabon kaya daga Abuja.
Brown Shadda ce mai tsada da mahaifinsa ya aiko dashi tare da mutanen da ya aiko su suzo ayi dauren auren dasu.
Basu iso yola basai bayan zuhr prayer,..
Su kusan su bakwai alhaj bello jimada ya turo yolan duk yan uwansane da abokan arziki wanda shekarunsu ya danja sosai. Nan da nan su banji suka taya Ahmed shiryawa, kayan kuwa bakaramin kyau tayi masa ba duk dama baiji aransa kamar aure zaiyi yau ba.
Bangaren adiaha ma sosai aka shiryata awani beauty lounge dake babu lokacin dinka mata kayan aure haka sukayi odering bridal ready made lace flowing gown mai kyau dark green and gold in colour Da duk wani abu na kwalliyar Amarya.
Da kayar da accessories dinta duk saida suka cinye duba dari da sittin dake set biyu ne aka siyo mata harda mayafai da jewries masu kyau da kayan kwalliya.
Kafin 2pm na rana yayi Adiaha was already looking breathlesslessly beautiful irin kyan da bata tabayiwa kanta ba
Koda kakarta da sauran mutanen da suka danzo suka soma yaba kyaun datayi sai kuma taji kuka da damuwa mai tsanani yana gumeta taciki.
She become sooo emotional and weak tayaya ne ma har zatay aure babu iyayenta aganganta?
she tried to call them ta waya amma taji layinsu kaf baya shiga harda na yar uwarta ekaete.
Duk sonta da daurewa bata iyayi ba saida tay kukan jin tsananin kewar familynta ayau din sosai.
She wish and wish suna nan sukagan irin kyan datayi aranar aurenta.
Da kyar aka kwantar mata da hankli da aka nuna mata hoton a
Ahmed awajeb daurin aure taga yadda yay kyau shima tare da friends dinsa hakan yasaka taji sanyi ranta kadan.
2 .30pm na ranar asabar din aka taru a masallacin kofar gidan Alhaj aliyu mutanen Ahmed suka bazama wajen cikin shigarsu ta kece raini da motocinsu masu daukar numfashi.
Batare da wani bata lokaci ba akayi duk wata abunda ya dace snn aka daura auren "Ahmed damilare bello jimada, da matarsa miss Reema bassey.
Bayan ankamala komi cikin mutuntawa akayi pictures Dr banky dayaga Adiaha ta fito saiyaji jininsa ya hadu da ita sosai, haka ya dinga yabonta yana cewa ahmed tafi kafayat tsari da hankli nesa ba kusa ba.
In no time suka dawo tamkar abokanta suna sakata jin dadi aranta sosai musmm ma banji dayasan komi akanta sosai, Adiaha tana bashi tausayi inya tuna cewa Ahmed only married her out of pity and no way out compulsion badon soyayya ba.
Ciwo kan kafayat ya dingayi mai tsanani da kyar ta shirya kanta tsaf taci ado da yamma ta kamo hanyar dawowa Abuja domin tazo a karashe hidiman da ita snn ta zubawa su anty mojushola final drop na maganin acikin abinci suma ta gama da su.
Ciwon kan data dingaji yasaka bata iso Abuja ba sai wajajen karfe shida na yamma saura tazo ta samu angama taro anata daukar hotuna.
Kawai sai ta shiga rubibi akay hotunan tare da ita
Ta zuba drink da magani ta kawo masu anty mojushola ta basu suka sha tasaka su a gaba tana basu labarin tafiyarta na karya.
Ta lura kamr hanklinsu baiya jikinsu dan sama sama suke bata kulawa duk idonsu na waje guda musmmn ma da sukaga kamr alhaj bello da haj khadijatu sun hada kansu yau da alama suna boye musu wani abu.
Harsaida aka daura auren Ahmed kafin nan brother hamzat ya hadasu dashi a video call yay magana da iyayensa suka saka masa albarka sosai. Alhaj aliyu daya kasance kamar shine waliyyin auren ta ln shima saida aka hadasu sukayi magana da alhj bello jimada da hjya khadijatu aka dan gaggaisa.
saida ya dawo cikin gidansa snn yadan fayyace ma hjy hajara yanayin iyayen Ahmed din sai asann tafara jin sanyi sanyi a zcyarta.
Da yamma lis akazo daukar adiaha dan karfe biyar da rabi jirginsu zai tashi izuwa abuja in less than 40 minutes zasu iso Abuja inda za'a kawota family house ta zauna awajensu anty moju shola.
Shiyasa yau din suka daga batun komawa cikin sabon gidan nasu duk dama anyi waliman an kammala
Saukin abun shine brother kazim da brother hamzat duk sun gayawa matayensu dawuri akansu shirya tarban amaryan Ahmed, tare da warning dinsu akan cewa karsu gayawa kowa news din auren sai sun iso da amaryan Abuja.
Anata hidiman waliman nan suna nasu shirin suma agefe duk dama gulman abun na ciccinsu agindinsu musmmn ma anty nuratu.
Duk sunsan masu anty mojushola ake boyewa komi dan ba'ason atada rikici acikin mutane mutuncin familynsu yaje ya zuba. Suna son suyi gulman amma suna mugun jin shakka da tsoron mazajensu
Wajajen karfe biyar na yamma aka kammala shirya Adiaha da wani brown bridal gown na atampa wanda shima siyenshi a dinken sukayi aka rufa mata hadadden mayafi mai kyau akanta golden colour kalar jakarta da hadadden takalminta, duk ta rude ta makale sosai ajikin hajy hajara tanata kuka ayayinda take kan mata nasiha tanamai dada ja mata kunne akan zaman aure.
lokacin har Ahmed ya sauya kayansa na auren izuwa wata simple yadi fari kal dashi yolo yolo datay masa kyau sosai amma baiko saka hula ba acewarsa kayan auren sunmasa nauyi ajiki.
Biyar na cikawa sukazo gidan domin su dauketa nan ne hjy hajara ta kira Ahmed gefe ta masa nasiha tare da bashi amanan Adiaha harta so ta bashi tausayi duk dama ya lura kamr batason auren aranta itama.
5.30 aka kammala musu nasiha atare snn aka rako adiaha cikin mota tanata kuka Ahmed baice mata uffan ba har suka kai airpot abokansa ne kawai suketa lallashinta hartayi shiru.
Koda suka iso Abuja ana kkrin shiga magrib agidan banji suka sauka tare da ita, after sallahn isha'i ne suka dauko hanya daga ita sai Ahmed din a mota har suka iso family house dinsun kamar yadda iyayensa suka umarcesa.
Tun ahanya yafara fayyace mata cewa wasu daga cikin manya a familynsa basusan da zancen auren ba so she wll have to bear with their first shock and unruly coments.
Akaci sa'a kuwa Lokacin kafayat bata gidan har ta sabule ta wuce gidansu sabida haryanzu maganan brother kazim yana taba mata zuciya sai taji batajin sha'awar kwana agidan kuma.
Karfe 8 na dare daidai Ahmed suka iso kofar gidan aka bude musu gate suka shigo ciki saida ya kashe motarsa snn ya samu nitsuwa ya fara mata bayanin yadda zatay gaisuwa da sauransu.
Duk sai taji ta rude ganin komi ya mata na daban da yadda ta saba gani arayuwarta.
Tun tana cikin motar take karewa gidan kallo ganin gidan babbane ba laifi.
Ahmed yace mata ta zauna acikin motarsan tukuna shi zai je ciki ya dawo kafin azo a dauketa saisu shiga ciki atare. Har ya bar wajen kallonsa takeyi tsabar yadda kirjinta yake bugawa da sauri da sauri.
Daga ta cikin gidan kuwa
Babu wani mahalukin da ba'a kirashi a falon yau ba.
Duk wani mai amsa sunan jimada ya hallara su anty moju kansu ya bala'in daurewa tunda sukaga an kirawo meeting din gaggawa nabazata.
Yaransu ne kawai basa wajen amma tunda ga kan brother hamzat da aunty nurat, aunty adizat da any zainab da su manyan gidan kowa ya halacci taron, sai brother kazim daya kira a video call dan ayi komi dashi.
Tun kafin zuwan su Ahmed gidan anty mojushola ta matsa sai dai agaya mata dalilin taron nan dan ta matsu taji meyene, nan alhaj bello jimada ya nitsu bai boye mata komi ba ya fara musu da bayanin yadda aka ciki da batun Adiaha snn yace musu dansa Ahmed ne suka yiwa aure yaudin zasuyi introducing matarsa wa duka family.
Anty moju tay ihu tace karya suke yi batasan da wann zancen ba, tun tunin nan wa ita kawai akeyiwa bayani amma shock din data shiga ciki najin cewa har anma Ahmed aure yasaka ta dawo musu tamkar wacce bata fahimtar mesuke cewa harsanda akace ga Ahmed din ya iso da matar da ya aura.
Kowa awajen jikinshi yay sanyi dasukaji ance ga labarin Adiaha amma banda su anty moju
Babban damuwarsu shine da ba'anemi shawarsu tun farko ba akayi komi da hjy khadijatu. Gani suke an raina musu wayo snn dan uwansu ya kaskantar dasu sosai, ya dora matarsa a sama da matsayin dayake basu na respect aransa.
Brother hamzat yace ma su aunty nurat akan da suje waje ita da anty adizat su shigo ciki da Adiahan kowa ma ya ganta, caraf anty ramatou ta tashi tabi bayansu cos she just cant wait for this bomb blast gani take kamar karya ake musu.
Lkcin Ahmed yana sauri dan ya shigo ciki sai gasunan suna fitowa suma, a kofa suka hadu ya tsaya cak dan gani yay kowa na kallonsa kamar basu taba ganinsa a rayuwarsu ba, ko ajikinsa ya tsime snn ya wuce ciki dan ko gaishe su baiyi ba ya haɗe ransa sosai.
Anty ramatou ce ta tsaya dagata kofa bata karasa can din ba ta zuba ido tanata kallonsu, kirjin Adiaha bakaramin bugawa yakeyi ba musammn dataga manyan mata subiyu sun doso ta inda take, da wuri ta ja mayafi ta rufe fuskanta da mayafin mai gabaki daya.
Anty nurat ce ta bude kofar motar tsabar gulma saida ta yaye fuskan adiahar duka suka kunna hasken bulb din motar suka mata kallon tsaf tsaf dasukaga bata da aufi nan suka buga wata shewa tareda rangwada mata guda a kunne.
_Iyawo wa_
"Ure welcome our bride"
Lokcin Kirjin Adiaha kamar zai fito wajen dan tsabar bugu,take sai taji hawaye masu dumi na neman kufce mata a idanunta jin yadda suketa yaren yorubanci atsakaninsu suna mata dariya kadan kadan.
Calmy and politely anty adizat ta cirota a mota sunata mata sannu da zuwa jikin adiahar sai rawa yakeyi batace musu komi ba har suka fara tahowa da ita cikin gida.
Ahmed ya shiga cikin familynsa yay gaisuwa ya zauna acikinsu kenan
Suka fara jin karar gudu anty ramatou ne ta dawo cikin gidan tana ihu da yare bayan ta tabbatar da cewa dagaske ne batun auren nasa.
Gaban anty moju ta tsuguna hartana haki muryanta kasa kasa tana cewa _Ahhhhhhh Anty moju jẹ otitọ ooo, jẹ otitọ. Is truee oo is true_
Zumbur anty moju ta mike game da maida hanklinta bakin kofar tana jiran ganin shigowarsu.
Ahankli suke tahowa da ita har suka iso ciki.
Brother kazim yafara magana da yare yanamai ce masu anty moju suyi controlling emotions dinsu su kama kansu dan kar yarinyar tazo ta rainasu a matsayinsu manya, maganganun daya dingayi ne cikin mita yasaka suka dan daure suka zauna atsomare anty moju tana ta karkada kafarta kmr wacce aka mata mutuwa.
Daidai bakin kofa suka saka Adiaha tacire takalmi tay bisimillah aka mata adduoin sann aka shigo da ita cikinsu cikin nitsuwa.
Tafiya take kirjinta na tsananta bugawa dan Tsabar kallon da ake mata a palon yasaka tafara jin kafafunta na harhadewa sai wani jiri jiri dataji yana debarta.
Hakanan daita daure har saida aka zaunar da ita snn aka dan yaye mata mayafin fuskarta tare da kammala zagawa da ita kan manyan gidan tana tsugunawa kasa tanamai gaishe su snn aka dawo da ita wajen zamanta danta samu nitsuwa.
Babu wanda zai iya kushe halittar Adiaha dan kuwa itadin ma Allah ya bata kyaun fuska bazaka dai ce mata tana da muni ba kuma ba ramammiya bace.
Tanajin akayi introducing dinta wa family members Din Ahmed daya bayan daya.
Anty moju taki sam ta kulasu sosai. Sai jefa musu bakaken maganganu take cikin jimami wanda inba kana jin yarensu bazaka fahimce cewa masifa da bala'in take sauke musu.
Acikin salo take kada kafarta tana maganan tanayi tana share hawaye dan gani take hjy khadijatune ta jawo musu wann abun
_Emi ko le gbagbọ eyi._
I dont belive dis. _bawo ni o ṣe le ṣe Bello?_
_haaaaaa nitori obinrin ti o yi ẹhin rẹ pada si mi?_
(Haaa, akan mace yau ka juyamin baya?)
Kowa sai hkri yake bata ana dada mata bayani akan yanayin situation din amma takijinsu sam sai maganganu take tun Adiaha bata fahimta harta soma ganewa.
Anty ramatou ta rirrike ta
_bawo ni o ṣe le ṣe itiju mi bi eyi? kini mo ti ṣe lati tọsi eyi lati ọdọ rẹ_ _brother bello, how can u disgrace me like dis? what ive done to dersve dis from u._
_Emi ko ni iye ninu igbesi aye rẹ, Bello_ (baka daukeni da daraja a rayuwarka ba bello).
Awajen kusan kowa ya amshi batun auren Ahmed hannu bibbiyu sabida tausayin Adiaha amma bandasu anty mojushola da suke kan kukan cewa dan uwansu bai darajasu ba.
Hakanan dai aka yanke hukuncin cewa Adiaha zata zauna agidan tare da hjya khadijatu zuwa gobe da safe idan komi ya lafa su anty moju shola sun sauko sai a saka ranar da za'ay mata waliman kaita sabuwar gida.
A dalilin rikicinsu yasaka aka daga tarewar Adiaha da mijinta acikin dakin daya akan harsai sun koma sabuwar gida nan da sati guda.
Yau kusan kwana su anty mojushola sukayi suna tsinewa hajy khadijatu a dakin su.
Sam kwanansu a gidan nayau tare da Adiahan bai wani musu dadi ba sabida yadda anty moju take daukar komi da zafi zafi.
Tunda aka yanke maganan cewa sai bayan kwana bakwai su tare Ahmed yay hamdala aransa dan dama bai shirya tarawa da mace acikin waynn yanayin tashin hanklin ba.
Brother hamzat ya miƙa ragamar komi a hannun su anty adizat na batun koyawa Adiaha wasu abubuwan kafin akaita sabon gida.
Washe gari da safe aka sake taruwa a falo anata bawa su anty mojushola hakuri Sabida cewa datakeyi an raina ta a matsayinta na babba an dauki matsayin ta an bawa hjy khadijatu.
Sosai ta tuma ta dawo da maganan ya dawo wani babba ta daura laifin komi akan hjy khadijatu, tun safe ta tarasu tana ta surutu ran Ahmed saida ya sosu sosai idonshi yy jaaaa jin yadda suke fassara masa uwansa agaban idonsa suna ce mata babbar munafuka.
Taruwar dangin suka so suyi mata subiyun sai ga hjy maimunatu tay sallama acikin gidan.
Wani sabuwar rikicin ne aka bude dan kuwa nan ne itama tabude musu wuta tace musu bata yadda da rainin wayon nan ba. Haka sukata jefawa junansu baqaqen magana harsuka rusuna sukayi shiru sabida hjya maimunatun babbar mace ce mai izza da kudi gata da matsayi kowa na jin shakkarta awajen sosai.
Zuwarta gidan da safen sosai yay amfani wa kowa dan kuwa itace kadai ta tsaya agabansu anty mojushola ta wankesu snn ta ajesu a matsayinsu ta musu tass tass ta rufe musu baki.
Tunda tay musu gori akan rashin kulawa da suka nuna akan lamarin Adiaha data baro komi nata tazo cikinsu zaman aure sai basu kara kushe zancen auren ba.
Dramar da akeyi aciki har waje ana jinshi dan haka kafayat datayi isowar safiya tazo ta samu ana kan baje kolin maganan auren Ahmed wanda ya doki kahon zuciyar a bazata.
Bari jikinta yakeyi sabida babu abunda bataji ba.
Harda warware maganan da akayi akace anty ramatou da anty adizat sune zasu shirya Adiaha kafin ranar tarewarta a sashen Ahmed na sabon gida.
Adiaha was so down to earth sam batada hayaniya duk kiciniyar da akeyi dinnan saidai tay hawaye tashare wasu abun ma baji takeyi ba.
Saiyau da safe da hjy maimunatu tazo ta saita kan kowa snn Adiaha taji dan dama daman zama acikinsu ganin har anty ramatou ta sauko da fushinta tadan amsa gaisuwarta ta fara kulata kadan kadan.
Lokcin Kafayat tana daga waje ta jikin windownsu tana jeka ka dawo tanakan jiran wanda zaizo ya gaya mata gaskiyan abunda taji dan she is in shock irin daukewar brain dinan batama san mezatay ba.
Tana cikin hakan sai ta hango motar banji yay parking a tsakar gidan.
Ta Hanyar baya taga yay ta wawuro cikin sauri tabi ta wajen da niyyar zataje ta tsaresa, ko ina ajikinta rawa yakeyi har ta isa wajen bata cikin hayyacinta.
Banji yana dosowa ta wajen saiga Ahmed nan ya fito daga cikin gidan nan ya biyosa ta baya inda babu hayaniya da waya a hannunsa.
Cak kafayat ta tsaya tanata kallonsu daga dan nesa.
Daga cikin gidan kuwa tunda aka kammala magana sai Kowa ya watse ababbn falonsu aka bar Adiaha da su hjy khadijatu suna masu kare mata kallon tsaf din suma. Har yanzu Adiaha ta kasa sakewa acikinsu dan tsoro takeji aranta sosai.
Hjy maimunatu ne tacewa Adiahar akan da taje ta kirawo musu Ahmed suzo tare zata musu magana.
Babu musu ta mike tabar wajen suka bita da kallo cikin kyabe baki Hajy maimunatu tacewa yar uwartata " Da dan juma ne da dan jummai, saiki saka mata ido itama karko kyaleta tazo dana nata salon kabilancin dan duk layin iri dayane ya kwasosu.
Har Waje Adiaha ta zaga dan batasan inda zata sameshi ba,ahnkli take tafiya tana juye juye har tabiyo wani hanyar daya kawota waje
Lkcin Magana Ahmed sukeyi shida abokinsa banji wanda bama jinsu kafayat takeyi ba, sai data matso kurkusa takejin yadda banji yake tambayarsa lpyar matarsa da yadda family suka amsheta, tun bai amsa Banji ba, kafayat ta katsesu, a mugun haukace ta karaso wajensu tanamai shigewa tsakiyarsu kamr wata tababbiya wanda ta rasa hanklinta shekaru tamanin da suka shude.
Awargaje ta tsaya tana kallon cikin idanun Ahmed, nan take hawaye masu dumi suka wanke mata fuskarta then She decided to confront him akan abunda takeji akan zancen aurensa, muryanta na rawa zosai tace Ahmed wai dagaske ne kayi aure?...daidai fitowar Adiaha kenan sai ta tsaya agefe tanata kallonsu ...kafayat ta memeta masa tambayar ajere yakai sau biyar..
sosai Banji yaji tsoron yadda kafayat din take ɓari kar kar kar idanunta suka jujjuya sukayi jajir duk yadda taso tay control kanta ta kasa tafara masa tambayar acikin ihu da kuka mai ragwabarwa.
Yadda kasan baisan me takeyi ba hakanan ya kalleta a kiyasce cikin bata wani irin cold attitudes mai bala'in kufularwa zaka rantse da Allah Ahmed baida imani ne acikin zuciyarsa.
Wani irrin balamin gurnani kafayat taja wanda yasaka Banji ya sulale sidif sidif ya barsu wajen.
Tafara masa raki cikin birkicewa tanakan tambayarsa akan meyasa zai yaudareta har yaje yay aure? Wacece ya aura? Yar waye a kasar nan?snn Dame ta fita?
Yace mata ra'ayinshi ne yasaka yay aure, and he wont explain himself to her.
Kafayat tafarajin kamr ta shakureshi awajen ta kaishi har lahira, inzai wuce saita birkita tasha gabansa, ran Adiaha sosai ya sosu datagan su a hakan,dan ba laifi ta fahimce cewa da alaman wnn din budurwan Ahmed ne koda ba agaya mata ba, yadda suke hargagin rikicin zaka gane cewa sun dade suna tare, a birkice kafayat take tambayarsa ko sonta ne bayayi yaje ya auro wata ba ita ba.
"Tafara tuna masa irin dadewar datay tana dakon sonshi, da irin burikan data daura akansu.
Rikici mai yawa ta balle masa dashi Har saida ta hatsala shi yace mata "baice mata baisonta ,
haryau yana sonta,She is his first love, kawai Allah ne baiyi ita zai aura ba.
Numfashinta taji yana shirin daukewa cak dahar zata fadi kasa yay sauri ya tarota ya rungumota jikinshi, tafara masa bori sosai,sai kuka kawai takeyi ajikinshin ta wani tantameshi tammm jikinta na rawa rawa anashi jikin sosai, cikin yanayin tallafota jikinshi yace mata ta fahimce shi snn tay hakuri shima ba hakan ya tsara ba amma hakan Allah yay auransa da yarinyar qaddararsu ce ya jawo.
Adiaha sai taji kishi mai yawa ya dabaibayeta musmmn ma dataji ahmed yace auransu na qaddara ne kuma yana son kafayat
Hawayen da ya soma gangaro mata ne tashare da sauri taje ta buya awani bayan pillar dan kar aganta awajen.
Ahmed yana barin wajen kafayat ta juya itama zata bi bayanshi,tana sauri zata wuce suka hade ido da adiaha nan suka tsaya jefawa juna kallon kallon batareda sunsan junansu ba.
Duk jikinsu ya basu matsayinsu amma basucewa juna uffan ba kowa ya kama gabansa.
Bayan yar nasihar da hajy maimunatu tay musu da Ahmed sai tay musu sallama akan cewa zataje gidanta dake katsina tay sati biyu kafin nan ta koma turkey dan su shirya dawowarsu nigeria gabaki daya nan da wasu kwanaki
Tay musu nasihan zaman aure snn Tasaka musu albarka amma hanklin Adiaha baiyaji jikinta sabida tunowa da maganganu da kuma rungumar da kafayat din datagani sunayi tare da Ahmed dazu ya tsaya mata a wuyanta sosai.
Hjy khadijatu tay musu sallama agidan itama nan suka fito tare ta raka yar uwanta har cikin mota, ta fito zata shige nata motar kenan sai ta hango Kafayat atacan baya tana tahowa a tsandare tana bari bari kamar wancce ruwa ya kwashota.
Kallo daya tay mata ta fahimce cewa she is in shock na jin batun labarin auren Ahmed.
Bakinta dauke da salati tazo ta rukota tana tabata kuwa ta sume mata a hannu.
A motarta ta sakata suka bar gidan takaita asibiti saida ta farfado snn ta dawo da ita gidanta inda babu hayaniyar kowa.
Haka ta dinga rarrashin kafayat tanamai bata hakuri, kafayat tay kuka harta dena, hjy khadija babu abunda bata gaya mata dan zucyarta yay sanyi ba. Itace ta bata labarin Adiaha da dalilin daya saka suka amince suka bar Ahmed din ya aureta, Karshe dai kafayat tace mata ta fahimce qaddara ne ya kawo Adiaha rayuwar Ahmed tace zata bukaci lokcin da zatay tunani akai domin ta samu nitsuwa akan hakan sosai.
Har gida hjy khadijatu ta rako kafayat har cikin gidansu snn tazauna da ita nadan wani lokci ta dinga lallashinta tamkar yadda uwa zatay wa yarta na cikinta harsaida kafayat din dankanta ta fara nuna mata babu komi ta fahimce komi.
In 7 days time za'a koma sabuwar gida tare da sabuwar amaryan Ahmed kowa na shiryawa wann ranar.
Ahmed tuni ya koma bakin aikinsa..
Anan family house aka aje Adiaha,kowa yasan kan labarinta shiyasa daga ta zauna su anty mojushola saisuyita zaginta da yarensu suna kiranta matsayaciya yar ciranin arziki. Idan suna son cimata fuska sai suyi ta mata tambaya akan gayan gara ko akwatin aure ko suta zakwalo mata zancen iyayenta wanda azahiri yana sakata jin wani iri aranta sosai.
Ga ahmed ya fara focusing akan aikinsa sosai sai baida lokacin zuwa dubata wani binma saida dare zaizo gidan inyazo ma baiya dadewa saiya koma gidan iyayensa dan bayason gulman su anty moju.
Kafayat was going tru a mental depression duk dama kowa yana kkri akanta amma mahafiyarta taki bari suna zuwa ko suna kiran yarta awaya.
Ahakan ta samu babban damar cusawa yarta ra'ayin plan dinsu.
Ana saura kwana biyar a koma sabuwar gida jikin kafayat din haryau babu kanta, sosai hjy khadijatu ta damu, kusan kowani lokci takan mata aika dan taji lpyarta a boye,
acikin daren kwana na biyar din ne hajy fatihat ta tasheta a barci takaita cikin jeji da tsakar dare suka yi wani ritual na musamman akan Adiaha( refer to prologue to read this part in detail)
Bayan dawowarsu ne washe gari anty moju shola da anty ramatou suka fara fita suna yawo ixuwa wajajen da babu wanda yasan inda suke zuwa sai Allahnsu.
Hkama aka kasa ganewa kan alhj bello jimada agidan kwana biyu sam baya walwala sosai sabida yawan kiranshi meeting da sukeyi a boye suna tattaunawa da shi
Kwana biyu akaji sakat gidan yay shiru dasu anty moju suka dawo basa zama agida sosai,
Nan kuwa Adiaha harta fara sabawa da zama da su anty adizat dake suna koya mata sallah da dabiarsu na al'adansu sosai musammn ma gaisuwa ladabi da yadda suke girki idan hidima ya taso ko idan akayi baki.
Ranar da aka cika kwana bakwai ranar komawarsu new jimada mansion ranarne kowa acikinsu ya cancada ado aka ma Adiaha rufi mai kyau da kayan amare na alfarma da hjy maimunatu ta aiko mata da su kyauta,yau kowa saida yamugun shan mamakin irin gayun da sun anty mojushola sukayi.
Da yamma lisss bayan duk an hallara, aka nemi alhaj bello aka rasa kwata kwata. Haka nan har aka debi motoci daga gida aka fara sako amaryan ahmed agaba za'a koma sabon gida da ita.
Sun shiga gidan kenan har anyi addu'oi kowa ya wuce sabuwar sashen jim kadan saiga hayaniya da gangamin mata ana kida ana rawada yaren yorubanci, na musammn aka debo mawakar shela mata na yarobawa suka rako sabuwar amarya cikin sabuwar gidan jimada.
Su anty mojushola ne agaba sun riko hannayen kafayat dayaji lalle an bata tsamiya da goro tanaci tana kumsa yawun abakinta tana tofarwa ana binta da kida ana mata wakoki masu dauke da habaice habaice masu zafi sosai.
Wakokin da suke yi a tsakar gidan suna rawa suna shewa saida yasaka Kowa ya fito a sashensa acikin gaggawa kowa ya tsaya yana kallonsu.
Tun hajiya khadijatu bata kammala isowa filin ba tafarajin rade raden cewa mijinta ne ya kara aure.
Tana kuwa fitowa sarari tazo ta samu su anty moju da anty ramoutu tare da hajy fatihat da kawayenta na kasuwanci suna wani irin rawa suna karkada duwaiwakansu kafayat na tsakiyarsu tana taunar goro da tsamiya tana zubda yawu wanda hakan wani alamane na habaici da cin fuska da akewa uwargida na nuna mata cewa ita ta tsufa, dan haka ankawo fertile young woman wanda zatazo ta haihu da mijinta agidan.
Haka suka cika mata gaban site dinta har ta inda take tsaye kafayat na tsakiyarsu idanunta a bushe tana rawar itama.
Daukewar cak hjy khadijatu tay tanamai kallon ikon Allah.
Wani doguwar capert suka shimfida akasa inda kafayat zata bi ta shiga gidan mijinta wato alhaj bello jimada kowani step tay sai anzuba wani irin ruwa a gora anyi habaici tare da addua kafin nan ta karaso.
Hjy khadijatu data tabbata da cewa wai kafayat ne ta aure mata mijinta sai tay na maza ta juya abunta zata koma ciki saidai shock din ya riga dayay mata yawa ko wani nisa batayi ba jiri ya kwasheta tafadi ajikin danta Ahmed dayay sauri wajen rikota jikinshi.
Agurguje ya karasa shiga da ita ciki dan shima shigowarsa gidan kenan jikinshi a ragwabe Bayan sunji labari awaje cewa mahaifinsu ne ya auri budurwan dansa kafayat yau a masallaci.
Nan brother hamzat da su anty adizat suka yo kansu suka tayashi rike mahaifiyarsan jin har ta dena numfashi sukayi sauri suka sakata a mota hankli tashe suka wuce asibiti da ita batare da sun kula kowa ba.
Hanklin Brother kazim ya mugun tashi sabida kukan da matarsa anty adizat takeyi data kirawoshi awaya abirkice tana gaya masa abunda yake faruwa musu agida, tun daga nan yay dialing lambar mahaifinsu yanata kirar wayarsa danya tabbatar amma baya daukar kiran.
Jininshi har tafasa yakeyi yana diri shikadai Ji yake kamar ya bace yaga kansa a nigeria acikin dare Dayaji wai kafayat ce mahaifinsu ya aura...
A rikice Anty nurat da Adiaha suka fito zasu bi bayansu,lokcin anty nurat taje dauko key din motar ta kenan Adiaha taji an riko hannunta an wani matseta da karfin tsiya.
juyawarta keda wuya suka hade ido da kafayat da tay wani irin mugun hade rai tanai mata irin shakurarren kallo mai cike da baqar kishi da tsananin tsana.
Sanda tay mata zagin kare dangi da yarensu snn ta zungureta tace mata "su zuba su gani, "yau tay maganin Ahmed saura ita, ynzu ne wasan zai fara atsakaninsu dan ita ba zaman aurene ya kawo ta ba"..tazo ne dan ta kwace Ahmed dinta kmr yadda taje ta kwace mata shi agarinsu, Tace tay mata alkwarin cewa saita kwaceshi agaban idonta tana kallon komi babu yadda ta iyayi..
Da wani irin kallon mamaki Adiahan take binta dashi taja tsaki mai zafi aranta tace mata "ga fili ga doki.
Itama kallonta take ranta sai cewa takey Indai har bata samu Ahmed ba alkwari tay cewa babu wata ƴa macen da zata zauna lpya tare dashi hr Abada......
Galala Adiaha ta tsaya tanata kallonta harta juya cikin sauri bar wajen ta koma cikin yan kawo amarya ganin anty nurat tana dawowa kallonsu takeyi har suka bar gidan.
Tun ahanyar asibitin Adiaha ta buga tagumi tay shiru kmr wacce akamata mutuwa dan babu abunda yake nanatuwa a kwakwlarta face maganganun kafayat na cewa zata kwace mata Ahmed dinta...
ALHAMDULLHI...
DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA ACIKIN LABARIN AHMED BELLO JIMADA DA MATARSA ADIAHA DA KUMA MATAR UBANSA KAFAYAT.
DA KUMA YAR UWARSA YASRA HUSSAIN YARINYA YAR SHEKARU SHA TAKWAS DA ZATA ZO TA KASANCE WATA SABUWA ACIKIN SHAFIN QADDARAR RAYUWARSU DASHI DA MATARSA ADIAHA..
KISHIYAR KABILA IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF HATE TURN INTO ROMANCE
KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
*VIA 0152983148*
*MOHD SULE SURAYYA GTB*
EVIDENCE TO *08060712446*
MTN CARD SEND ONLY PIN OR PICTURE TO *080607124476*
OR TRANSFER VTU TRU *09132352275*
©SURAYYAHMS2023.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top