9
*KISHIYAR ƘABILAH... 9*
BY SURAYYAHMS..
THANK U ALL FOR THE WONDERFUL LOVE AND MOTIVATIONS. THE VIBE IS TIMELESS FANMILY!!
Tunda suka kwanta bacci a dakin hotel din sautin gurnanin kwartin Adiaha ne kawai yake tashi, kararshi marar dadi mai sauka kamar na sautin engine markade ya kuma bala'in cika atmosphere na ilahirin dakin wanda yasaka Ahmed yin bacci rabi da rabi sai juyi yakeyi akan gadonsa yana jefa tsakin takaici sabida bai saba ba kuma ya mugun tsanar mace mai karfin gurnanin gwarti.
Washe gari da safe Da kyar Ahmed ya farka a baccin daya kwashe sa da kyar, yana bude ido yaga lkcin har wajajen karfe bakwai saura duk jikinshi a muce sabida gajiya da kuma rashin kwantawa da wuri da jiya baiyi ba. Yana miƙewa zaune baiko kalle inda Adiaha take ba ya sauka akan gadon snn ya wuce bathrum direct ya kunna ruwa yay cikakken wanka snn ya fito ya shimfida prayer mat dinsa yahau yin sallah abunshi.
Bayan ya idarne ya juya yadan kalleta a nitse ganin Wani irin baccin datakeyi ta wangale cinyoyinta bakin ta a bude ya dafe kanshi ganin da alaman har wani sabuwar minshari ma takeyi dan ko alaman motsawa batasaka ranan yi ba.
Zama yay a nitse yana mai kafe bango da idanunshi da sukayi sanyi cikin tunanin irin yaudararun kalmomin da zai mata na maganan auren nn nasu dashi dan shikansa baison ya kara kwanaki dayawa anan garin ahaka dan baison wani abu mai suna zina ya shiga tsakaninsu tun yanzu..
So yake ta amince ma qudirinshi ayau din nan if dats possible sabida ya samu ya koma Abuja ga mahaifyarsa dan ya duba halin da take ciki, aransa yasan ynzu halama tay fushi dashi sosai, snn kuma yasan zata damu da rashin jin wayarsa a bude na kwana biyun sosai, wani lumshe idonsa yay kirjinsa na bugawa da tsananin damuwa akan hakan dan yasan baiya mata adalci a matsayinshi na danta datafi kauna a duniyarta.
Tunanin mahaifiyarsan sosai ya ciƙe masa zuciyarsa da kwakwalsa wanda shi yake dada hura masa wutar jin tsananin son samun cikar burinsa akn adia cikin gaggawa kodan yay hanzarin komawa ga mahaifiyarsa.
Yana cikin wann tunanin Adiaha ta farka tana mai kiran sunan jesus acikin yanayin gigin barci da kuma bankararen miƙa..
Idonta a lumshe Tana yar murmushi ta hau tattaba gefe da gefe koda ma zataji shi Jin kanta akan kujerar itakadai shiyay mugun bata mamaki sai kuma tay tunanin hala ko giyar datasha ne jiya ya jefata awajen sai ta kalli kan gadon taga da alaman kmr shikadai ya kwanta awajen batare da ita ba sai tay shiru dai batace komi ba.
Kallo daya yy mata da gefen idonsa yanamai sauke boyayyar ajiyar zuciya cikin sanyin muryansa mai taushi da dadi sosai yace "hey, u re awake? Da kyar ta bude idonta sosai ta kalle shi cikin gigin baccin sosai tace "gud morning babe".
Ya kyabe bakinsa yace
"Yan mata kenan, kin shayu dayawa jiya fa..are u sure bazaki kara komawa baccin nan kidan huta ba kuwa?.. ba acikin hayyacinta sosai ba ta gyada mai kai da can har zata koma ta kwanta sai hannunta ya danna kan wayarta by mistake sai ya kunnu dakanshi sai zutt zuuttt vibrations na shigowar sakonnin ya firgitar da ita.
Lokci guda taji gigin baccin ya watse ta mike zaune tanamai tunowa da cewa mahaifyarta ta nemeta jiya da daddare bata daga ba.
Bude wayar tay da pin taga 15 text messages atake taji zuciyarta ya tsinke rigip,saidai duk ba wann ne yafi damunta ba tana kallon yadda lkci ya tafi saida taji gabanta ya dada tsinkewa, tay kamr a mafarki taga wai har karfe bakwai da rabi ya wuce harma ana neman 8 saura, dafe kirjinta da yake bugawa kamar zai fito ya fado kasa ya tarwaste tay, nan da nan ta hau saka kayanta ajikinta agaggauce.
Yanayin yadda ta daka tsalle ta sauko kasa daga kan kujerar tanamai saka takalminta zata bar dakin agaggauce yasaka Ahmed ya miƙe tsaye yanabinta da kallon mamaki..
Takai hannu zata dau jakarta kenan ya amshe jakar ya rike yana kallon idonta yanamai binta da wani yaudararren harara, fuskansa ba asake ba yace "wait, wai ina zakije haka kike sauri tun bamu gama gaisawa ba and u knw i wnt to talk u about sumting ryt?bana ce miki wajenki nazo ba?
Ahankli Ta lumshe ido ahankli snn tace yes i knw, im sorry doctor i have to rush home, my mumy..tun bata karasa ba ya wani harde ransa ya miƙa mata jakarta a fusace ya dangwala mata ahannun ta yace "just take ur bag,ya isa haka i dont want to hear it"..
yadda yay maganan da wani irin arrogant and dissapointing attitude yasa jikinta yay mugun sanyi sai kuma taji wani iri sosai...
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe snn ta matso kusa dashi zata rungumosa ta fara lallaba shi nn ya tsime ya dan tureta ajikinshi ya matsa gefe ayanayin fushi.
Binshi tay cikin lagwame masa wuya da saukar ta kuma muryanta kasa kasa, Muryanta kmr na wanda zatai masa kuka tace "doc Ahmed pls now, karkay fushi mana kayi hkri, i was just carried away, ina sone na isa gida cikin gaggawa yanzu..my mum is angry with me am sure, wai jiya baka na kalla ta kikkirani awaya ba?im sure she is mad at me..dats why i hv to rush home now
Yy rolling idanunshi yana mata wni irin kallo da daurarren fuska, murya ciki ciki yace "toh shikenan, jeki mana. Nagode da kika nuna min cewa fushin mamakin yafi fushin nawa maman.
..did U knw dat my mum is also not happy with me dat i left her just to come over here and see you.? fushin mum dinki is more importnt than mine ko? Wowwww, Okay thnks..nima bari na koma Abuja wajen mahaifyta kawai.
Yana fadin hakan sai kuma taji gabaki daya ta rude musmmn ma dataga harya isa gaban wardrobe yana kkrin jawo trolly dinshi jikinta har na rawa ta rikoshi ajikiinta tafara bashi hkri with all her might sai shan qamshi da basar da ita yakeyi ya harde ransa sosai yanamai dada daga mata hanklinta sosai.
Lallamin duniyan nan tay masa amma duk ya basar ta rasa meke mata dadi gashi tana cikin matsatsin sauri, karfe shida da rabi na safyar yau din yakamata za'a shiryata dan karfe bakwai ne suitor dinta zai zo gashi har karfe takwas ya wuce bata ma je gidan ba tana nan tana fama da rokon ahmed daya mugun bata ransa.
He alwys love taking advantage of her weakness na mugun son shi datakeyi shiyasa ya zamo soo comfortable wajen aikata mata duk wani abunda yaga dama dan yasan dolene zata bishi snn ta lallameshi.
Saida tay kmr zata masa kuka kafin nan Da kyar ya kyaleta ta wuce gida tare da masa alkwarin zasu hadu awajen next event suyi magana anjima da yamma.
Tafiyarta keda wuya ya kimtsa kansa ya fita yaje yaci abinci ya koshi snn ya samu wajen shan iska mai sanyi inda babu wani hayaniyan surutu ya kira abokinsa oyebanji suka fara shirya maganan da zaije ya gayawa brother hamzat dimeji a office ayau game da zancen auren ahmd da adiaha.
Ahmed yana son lallai yayanshi hamzat dimeji shine zai shige masa gaba akan auren nan dan yasan da wuyane ya shawo kan mahaifinsa acikin sauki musmmn ma da ba kafayat din tasu zai aura ba.
A fannin hajya khadijatu kuwa yau haka ta kwana tana kuka bata samu wani runtsawa ba sabida bakincikin marinta da mijinta yyi. Tunanin duniyan nan tay amma bata samu wani mafita ba. Duk danta Ahmed ya gama daureta da jijiyan jikinta, aynzu dai tasan babu ta inda zata iya bullo ma mijinta ya fahimceta cikin sauki musmmn ma data lura da cewa kamr zugin da su anty moju suka masa wnn karon yay mummunan tasiri a brain dinshi.
Ranta a mugun bace yake da danta Ahmed danta nemesa a waya sau babu adadi amma kirar baije ba, dacan har taci alwashi bazata kara nemansa ba,aranta tace ko ya dawo ma bazata kulashi ba, amma wani bangaren zcyarta kuma acike yake da damuwar son tasan inda Ahmed din yake takuma ji lpyarsa.
Da kyar tay sallah tay wanka snn ta dan samu nitsuwa ajikinta, coffe kawai tasha tana zaune saita soma tunowa da shawarwarin da mahafiyarsu take yawan basu tun dacan kafin Allah ya amshi ranta na cewa idan ransu ya baci kar su sake su bari hanklinsu yana gushewa.
Dacan taso ta fita aharkan mijinta kodan ya wahala ya gane kuskusren dayay na marinta akan maganan da baizamo gaskiya ba.
Daga baya kuma sai taga kmr sharesa da yin shirun shine zai iya sakawa munafukai irinsu anty moju su karacin galaba akan aurenta da salon makircnsu.
Zama tay tana tunanin yadda zata bullowa sha'anin mijinta da yan uwansa. Tasan dai kishinta sukeyi tuntuni.
Amma batay tsammanin zasu riƙe abun har sukaishi wann matsayin ba. She have lived with them for more than 30 yrs, amma sai taga kamr kullum kabilancinsu sai dada huruwa yakeyi akanta.
Tashi tay ta shirya cikin wata milk colour lace mai ratsin fararen duwatsu masu kyalli ta gyara fuskarta yay kyau ta fito rass kamr ba itace take cikin damuwa jiyan sosai ba. Yadda ta fito cikin gidan ta tanamai zuba qamshin turarruka masu tsananin qamshi iri kala kala zaka rantse babu wani abinda yake damunta aranta bacin damuwar danta Ahmed ma kawai ya isheta taciki shikadai..
Falon mijinta ta dosa kai tsaye inda qamshin turarenta ya soma musu sallama kafin nanma ta iso, a cikin takunta na nitsuwa ta shugo ciki bakinta dauke da sallama fuskarta ba awani sake ba ganin har sun farka suna shan shayi atare. Ido ya zuba mata azauce ganin yadda tay kyau sosai tana zuba uban qamshi masu tsananin dadi.
Nn kafayat dake sanye da nite gown riga da wando tay saurin rusunawa tafara gaisheta,a cikin sakin fuska hjy khadjatu ra amsa mata tanamai tambayarta ya jikinta yake.
Har suka kammala gaisuwarsu baice mata uffab ba, Shiru yay yana jinsu dan bai sauko daga fushin dayake kanyi da ita ba msm ma na marin anty moju da akace anyi danshine yafi komi cin masa rai danji yake kmr mahafyarsa aka mara.
Ta juya ta kallesa ba yabo ba fallasa ta gaishe sa ya amsa da sakin fuska badon ya so ba saidan kyan datayi, snn tace "Alhaj ina son magana dakai..tun kan ya amsa kafayat ta miƙe respectfully zata fice ta basu waje, muryansa ciki ciki yace mata my doter ki dawo ki zauna..im enjoying ur company.
"Jiki a sanyaye kafayat din ta koma ta zauna sai kuma tay saurin maida hnkli izuwa kallon tv, hjy khadija sai kallonsa take tana kan shan mamkin sauyawarsa akanta.
kyabe bakinta tay batace mishi uffan ba ya daga ido ya kalleta sama sama snn yace iya dami, ure joking with me ryt? Nagaya miki bazan tsaya yin wani bayani dake ba hatta saikin umarce danki Ahmed ya dawo gidan nan..cikin dagon murya yace "im tired of all this nonsense, tunda kece kika daure masa gindi ya gudu just comand him to come back here and face me like a man, ai makanku kuka rainawa hankli bani ba..
Da kyar ta shanye maganan snn tace alhaj Amma nagaya maka ban san inda Ahmed yaje ba..kuma sakon daya turo kowa yaji shi..how isit my fault?
Hararata yy snn Yace "wani sako?Ahmed ya turo sako ne?.. Zatay magana cikin katseta yace "ohhhh ohh, wato har Kin taho min da wani salon sabuwar makricin yau kuma ko? See erhnn ki bace min anan wajen _oya jade.._ duk sanda danki ya dawo kika kawomin shinan zan saurareki..
Shiru tay nadan wani lokci tanamai sassaita zuciyarta ta ciki, duk ba dan Ahmed ne ya jawo mata wann walakncin ba tasan da wallh ba'a isa ayi mata hakan asha ba, aranta tace amma ai bakomi akwai ranar kin dillanci, daga nan Batace uffan ba ta juya jikinta a sanyaye zata bar wajen kenan sai ga sautin live broadcaster daga can calabar international trade fair center. Kafayat ne ta fara hango Ahmed agaba tare da sauran likitoci adan gaggauce ta wara idonta snn tace "Dady Watch!!! Isnt dat dami?
Kusan a lokci guda iyayen nasa suka maida idonsa kan tv hjy khadj nadaga tsaye kafayat ta dauki remote ta kara sautin tvn.
News report aketayi akan HIV/AIDs confernce/walk din da akayi a calabar jiya Ahmed na gaba gaba dan haka kusan dashi jounarlist din yay hira yna dan tambyarsa yana amsawa.
Shiru falon ya dauka suka zuba ido suna kallon sa harya kammala magana akan progrm din which is alwys cool nd impressive. Alhaj bello sai yaji wani iri aransa sosai dan duk cikin zugin nan da aka masa babu wanda yace masa dansa ahmed ya turo ma family sako ajiyan bare ma suce masa wani abu na aiki yajeyi awani waje, sude kawai ce masa sukayi uwarsa ta daure masa gindi ya gudu dan karya engaging din kafayat, snn dansa ya kunyarta dasu ya jawo musu cin mutunci harda mari daga wajen hjy fatihat.
Kafayat kuwa sai bayani taketayi, tace "mammy kin ganshi ashe har can calabar yaje..sounding proud of him tace i knew Ahmed will neva joke with his work i shhud have known dat..
Murmushi kawai hjy khadija ta mayar mata data furta hakan wanda yasata jin nauyin hakan sosai sabida tasan dukansu biyune basu mata adalci. Ahmed ya tafi ya jawo mata abun magana, itama ta daga hanklinta ta jawo mata baqar magana awajen dangin mijinta da mijinta.
Muryanta a sanyaye cikin nadaman zuci tace "Its all my fault for over reacting duk dama ahmed ya tura mana sako ya sanar damu amma na kasa kwantar da hanklina.
Maganan takeyi acikin aranta amma ya fito fili bata sani ba duk suna jinta..
Da ta farayin bayani akan sakon alhaj bello kuma sai ya soma dawowa cikin hayyacin shi, he was like so Ahmed really send them a messge to even apologise for his absence amma toh meyasa basu gaya masa hakan ba? Nan ya juya zai kalli idon matarsa da yanayin sanyin jiki da rudani lokcin kuma hjy khadiya tana tsaye tana kallon danta a tv batace musu uffan ba ta kuma mugun daure fuskarta.
Budan baki yy zai mata magana sai caraf suka hade ido da hajy fatihat adetunji balogun datake kkrim shigowa ciki.
Babu sallama karar taunar cingam dinta ne ya saka dukansu suka maida hankli su kanta.
Hjya khadijatu ta daure fuskarta sosai uffan basuce ma juna ba.
"Excuse me"
Hjy fatihat ta fada tana kada duwaiwaka ta wuce ciki har gaban yarta kafayat data mike tsaye tana kallonta da bacin rai ayanayinta.
Hjy fatihat ta kare musu kallo dukansu snn tay wani shuumin murmushi
Kafin ta budi baki cikin tsareta kafayat tace Stop mumy, What are u doing here?
Kafin ta amsa alhaj bello jimada ya miƙe tsaye cikin harshen yarensu yafara mata magana yanamai ce mata bata da hankline Da Zata shigo musu gida gatsau ba gaisuwa ba komi.
Da harshen yaren itama ta maida masa martani a fusace tana cewa
"How dare u question me When u took my child custody by fire by force?ku kuka haifamin ita ne?Alhaj bello im warning u ooo, ka rike wa'azinka makanka,ni badan nazo duba yata bama mezai kawoni gidan ka? U can rant all u wnt but No matter waht u say kafayat is my child kuma babu wanda ya isa ya hanani duba lpyarta musmmn ma da danka yake wasa da feeling din yata sabida baisan darajar ya mace ba.
Hakan data fada yasaka shima ya maida mata martani akan marin da akace tay wa anty moju.
Ya zaxxageta irin zagin huce takaici innan.
Saidai da mamakinsa wani Dariyar mugunta tayi masa dan Abun ya mugun bata mamaki dataga alaman baisan komi ba sai tafara kallonsa a matsayin wawa soko musammn jin irin zagin dayay mata na cewa bata da respect da tarbiya..
A masife ta dunkula masa baqar magana da yarensu akansu anty moju snn ta yaɓa masa.
Tace duk rashin tarbiyata dai bazan yi karya da tsufan shekaruna ba,so i dint slap her, i just ask what hppen to my doter is dat a crime?..yy shiru baice mata komi ba, tace " toh shikenan tunda sun iya hadamin hada munafrci i promise u next time muka hadu da anty mojushola saina wanka mata mari dagske dan ni ba tsoranku nakeji ba, Ransa a bace ya tashi zai mata tsawa ta tsaresa.
Masifa da Borin datayi masa awajen ayayin da take warware masa asalin abunda ya faru jiyan yasakashi kara shiga cikin rudani cos abunda take cewan its totally difrnt da abunda su anty moju suka gaggaya masa akan matarsa da dansa.
Hjy fatihat Tana kammala sauke masa buhun masifa ta jawo hannun yarta tace mata suje waje da niyyar mata magana privately tana yi tana nanata musu cewa zata zame musu kashin kfi a wuya akan batun yarta muddin dansu ya cigaba da walaknta ta.
Duk dahaka bata hkra ba ta dinga jefe masa baqar magana a iska tana tafiya tana cewa ce ai yan uwansan dayake ganin girmansu sune asalin gagaruman munafukan gidan tunda sune suka fara shirya komi snn ta gaya masa yadda suke damun kafayat da waya da fake promises tace zata kaisu court kwanan nan akan yarta,and she wll sue them for emotional damage and mental torture.
Tay ta bambami tana masiifa akan yarda ake juya kan yarta agidan.
Basuji sakat ba harsaida taja kafayat din suka tafi can waje..
Wani Sororo alhaj bello yy jikinshi duk yy sanyi yanajin kanshi yana juyi da magangnun hjy fatihat da kuma abunda yagani a tv dazu...
Tunda aka fara maganan hjy khadijtu ta tsime tay kyamm ta hade rai bata ce musu cikanku ba ta kuma mugun daure fuskarta kamar wacce bata taɓa dariya a duniyan nan ba...
Ganin maganan hjy fatihat ya shigesa ya dawo dashi hayyacin shi yasa hjy khdij taji dadi aranta amma ko nuna hakan batay ayanayinta ba ta kada kai itama ta dubeshi snn ta yaɓa masa baqar magana mai zafi akan marinta dayay jiya, snn taja tsaki ciki ciki ta kama gabanta.
Juyawarsa ke da wuya da niyyar bata hkri su sasanta saiyaga wai harta bar wajen jin karar rufewar kofan ta kawai yay.
Nan Ya rasa me zaiyi gabaki daya.
Adan gurguje yabiyo bayan matarsan yanamai kiran sunanta waidan ya tambayeta sauran wasu abubuwan tanajinshi amma ko kulashi batay ba bare ta amsashi.
Wucewarsa a kidime yana bibiyar matarsa hjy fatihat da kafayat suka gani lokcin sukuma sun kammala fadarsu kenan harsun shirya kansu.
wani file ne a hannun hjya fatihat datazo dashi tanamai nuna ma yarta kafayat na wani boyayyr kudin mahaifinta data kwaco mata shi a hannun accountant dinshi.
Kafayat naganin kudi ta fara washe baki nan da nan ta canza tafara bin mahafyartan sau da kafa kmr ba ita ba.
Daure fuska hjy fatihat tay tamau tafara mata gori akan yarda take treating dinta agaban mutane witou respect.
Cikin magiya sosai Kafayat tace mummy sorry now. Kinsan fa bacin raine but u know i respect u alot ure the only one i have in my life.
Da harara mai mugun zafi ta tsareta tana cewa "lie lie ooo, i no hear dat one..kafayat, kafayat sau nawa zamuyi haka dake?kedai saidai namiki abu dan Ni na haifeki amma badan halinki ba, kece yau kin tuba kinyi hnkli gobe damilare na dawowa zaki dawo kmr wata shegiya yar iska.. Akan damilare U have calld me a witch,ko jiya ma sanda kika ce min munafuka agaban kowa da kowa kamr banice na haifeki ba,sam baki san darajana ba kwata kwata kafayat kina sani kunya agaban enemies dina
..bazan ma iya kirga sau nawa kika cemin banida kirki dan kawai ina fada miki gaskya akan damilare ba dat boy is just using u.,me, I only care about ur life amma sam baki gani, Wayene zaiki jininshi ehn? Nina sukuna na haifeki, babu abunda nake so a duniyan nan face rayuwarki yay kyau but ure alwys againts me.
Kan Kafayat akasa krm wacca taji magana a cikin sigar nadama sosai tace e pele maaa, am sorry mum pls am sorry
Tace "Saboda kinga kudi ba? Kafayat ure just like ur father very deceptive human beings..
Tace aaahhh no maa, badan ina jiran ahmed ya dawo ba da tuni nazo na baki hakri, my consience do judge me anytime i misbehave with u,ure not a witch ma, nasan ke kika haife ni..blive me mum i love u soo much..
Hjy fatihat taja numfashi mai dan nauyi Ayanayin rashin amincewa da zancentan snn ta basar cikin cewa its okay..
Nazo ne zan duba zamanki anan din domin zanyi tafiya for some few days i want to make sure ure fine kafin na wuce
..murmushi kafayat tayi ta rungume mahaifyartan tanamai cewa "Dont worry maaa im fine..they are both taking care of me _o seun_ .
cikin kyabe baki matar Tace ehhhn..dats good to hear, Inde akwai wani problem just call me zanzo da gaggawa cos i dont trust dis ppl amfani dake kawai sukeyi..and rember what i said,inhar damilare ya dawo abuja baizo ya yanke decision akan aurenki da shi ba,belive me nine zan dauki nawa matakin akanki and u must obey me.
Kafayat ta gyada mata kai tanacewa hakan ma bazai faru ba, cos his dad is angry with him banajin idan ya daawo zasu barshi yay kwana biyu batare da an daura mana aure ba..
Hjya fatihat tay shiru bata amsa taba ganin yadda gulma yake ciccin yartan duk ta kasa tsayawa waje guda..
Harta budi baki zata tambayeta kenan sai tace mum kinsan meya faru agidan nan jiya kuwa?
Da mamki hjy fatihat tace meyafaru oya gist me..
Gefe da gefe kafayar ta kalla kmr barauniya danta tabbatar da cewa bamai zuwa tawajen sabida ta kwarance a iya zuba zancen gulma.
Nan ta fara warware ma mahafyartan duk abunda ya faru tsakanin alhaj bello da hjya khadijat tiryan tiryan batare tsallake ko digon aya ba.
Murya kasa kasa tanayi tana tsarguwa tace mumy jiya ina barci kawai naji suna musu can u belive it matar nan kishi na takeji? When thy left my room sai nabisu abaya, Har naji tana ce masa wai yen yen inba halin kabila ba wazai kai budurwan dansa a side dinshi da dare kiji fa mamy? Hmmm hehehe..he even slaped her..Allah yaso dai basu ganni ba nayi gudu gudu na koma room dina naje na kwanta nayi kamr ina bacci.
Shiru hjy fatihat tay tana mamaki tana kuma jinta kamar mai nazari akan wasu abubuwan..
Dan dai koda kafayat din bata mata gulman ba alama ya nuna cewa suna rikici tun daga ganin yadda alhaji bello yake bibiyar matarsa dazu yana kwala mata kira tana basar dashi.
Kafadun kafayat din ta dafa tace just stay close to them babu ruwanki acikin fadarsu..kedai idan wani abu ya shafeki dont hesitate to call me okay? Tace yess maaa.
I wish u Safe journey.
Nan Ta rungumeta kadan sukayi sallama saita juya ta tafi..
*******
A bangaren Adiaha kuwa ba ita da isa gidan su ba sai wajen karfe 9am saura lkcin kowa yanata aikin gabansa, tafiya take kirjinta na tsananta bugawa har ta iso bkin gate din gidansu.
Babban gidane irin family house bungalow compound din nan mai Zagaye da jan gate wanda yadan tsufa amma ba sosai ba ahankli ta tura gate din ta shigo ciki cikin sanda luckly enougg bataga kowa a tsakar gidan ba.
Da Wani irin sauri ta fizgi kanta da gudu zatay sashen su taji an damko kafadunta tana juyi taci karo da jajayen idanun mahaifyarta dayakenan cike da baqar masifa.
Jawota tay waje tsakar gida ta wullata tsakiya dede inda aka jera wasu kujeru na tarban baki.
Kamr adiaha zata saki fitsari ajikinta haka nan ta tsaya cak tana sose sose gefen kunne tsabar tasan bata da gaskiya.
A mugun masife matar tace "mrs carnival From Where are u coming from? adiaha ta bude baki zatay magana kenan mahaifiyarta ta ta rufe ta da fada ta inda take shiga batanan take fitowa ba.
Tun safe suitor dinta sukazo da elders karban consent dinta amma basu same ba sabida bata nan, duk iya kkrin boye musu cewa adiahar bata kwana agidan ba duk yaci tura dan saida suka fahimce cewa adiaha kam bata kwana agidansu ba on such an important ocassion..
Hakan bakaramin abun magana da kunya ya zamo ma mahafiyarta da sauran kawunan ta da sukazo karban bakin ba sabida rashin zuwan ta wajen kadai zai saka a dinga kallon familynsu a matsayin wanda basu da cultural values.
Sosai Adiaha tasha masifa amma batace komi ba saidai ta basu hakri..
Duk sun dauka taje irin yawon nan nasu na matasa ne inda suke zuwa sudan sha giya su kwana da maza..
Ita kanta mahaifyartata a matse take Adiaha tay tay aure sabida duk sanda taje tay cikin shege dakyar cikin yake fita ajikinta sabida jininta yana da mugun karfi....
A gidansu Ahmed kuwa tsakanin hjy kahdijatu da alhaj bello jimada haka akay ta drama agidan yau dan sosai tay fushi itama tafara jan masa aji saidai ita acikin sauki take nata ramokan bata fada amma cikin ruwan sanyi take ramawa haka sam taki ta saurare shi musmmn ma dataga ya fahimce gaskiyan yasan cewa babu hnnunta acikin tafyar da ahmed yay, tunda safe yake ziriya a sashenta yanata son ta zauna ya bata hkri ya lallameta amma haki fir taki. Duk sai yaji bai kyauta mata ba.
Tanajinshi ya harzuka ya kira anty ramotou dake itace take kasa dashi ya titsiyeta snn ya bata rai ya zazzageta yay mata warning akan gulman da suka kawo masa wrongfully akan matarsa.
Duk wani abunda akeyi kafayat tana tare da shi tanajinsu itadai bata cewa kowa komi sai ido sai ciye ciyen abinci dake yanzu sosai hanklinta ya dan dawo jikinta data gane cewa Ahmed yana calabar duk ta dauka aikine yakaishi can.
Wajajen karfe biyu na rana Banji yaje ya same brother hamzat dimeji a office dinsa cikin nitsuwa sukayi magana akan batun Ahmed kafin nan ya kirashi awajen suka kara tattaunawa.
Da kyar ma brother hamzat din ya fahimce shi akan batun auren amma still dai ya bashi cikakken goyon baya yace masa duk abunda macen dayagani yake so a duniya shi yana tare dashi.
Sunyi akan indan har Adiahar zata aureshi kuma iyayenta sun amince zai kirashi ya sanar masa, snn shi saiya fadawa babban yayansu dake kasar waje wato brother kasim aremu sai su san yadda zasu bullowa maganan kafin sukaiwa mahaifinsu for approval.
Sosai Ahmed ya ji dadin yadda brther hamzat ya fahimce shi snn bashi cikakken goyon baya, abunda ya rage masa ayanzu shine kawai ya samu yardan Adiaha dana iyayenta snn ya nemeshin kmr yadda yace masa
2:30 na rana za'ayi hidiman festival dinsu nayau wanda shima a filin kasuwa ne za'a gabatar, toh daga wnn ranar sai ranar karshe na fitowar spirits na ekpo wanda shine rana na karshe kuma ranar da ake saka ran saka ranar auren yan mata dayawa wanda suka dan girma suka wuce 25yr kamr irinsu adiaha.
Tsabar takaici da fushin abunda tay musu yau yasaka ko magana ta fatar baki mahafyarta bata son yi mata agidan sabida kaf yan matan da ake jiran suitors dinsu suzo da safe kowa taga nata suitorn dn harma sun zaɓa, yarsu adiaha ce kawai batanan batama gana da nata suitor din bama bare ta zabeshi a matsayin tsayayye.
Abun haryana son ya dawo wani abun gori wa mahaifyarta mrs grace udofia.
Uncles dinta kuwa banda masifeta babu abunda sukeyi. Wucewa goma in zatayi sai sun mata tuni sau dari na cewa itace kadai ta rage musu su aurar a danginsu kuma dataki dataso sai an aurar da ita wnn karon sabida kowa ma ya huta
Ko ajikinta maganan nasu bai wani dameta sabida tunanin yadda suka rabu da ahmed dayake mind dinta, sun rabu yana fushi fushi hakan shi kawai ta sako agaba, Allah Allah take lokci yay taje ta same sa awajen festival suyi maganan dayace yanason suyi dan ta kagu taji menene zai gaya mata.
A tunaninta tagama sakawa aranta cewa zai ce mata yana sonta ne dan tun da taganshi sai taji duk wani sha'awar yin aure agarinsun ya fice mata aranta gabaki daya she just want to be with ahmed right now koda ma ba auranta zaiyi ba.
Karfe biyu daidai filin taron traditional music festival din ya cika da tsala tsalan yan mata dake musical ceremony ne kida, da raye raye da wakokin yararukkan garin daban daban ya cike koina anata rawa masu daukar hankli.
Tsala tsalan Yan matan kyawawa masu jini ajika sun sako wani hadadden colourful Traditional attires dinsu wanda sukan daura zani ne snn su saka white shirt sai su kara dora wani colourful wrapper akan waist dinsu.
Wuyansu kuma sukan saka abun wuya ne mai suna okpomokpom da beautiful beaded shoes da hula shima da akayi shi da colourful beads.
Rawa mai kyau sukeyi ayayin da suke tahowa filin wajen dan kuwa bakaramin kyau yay ba sabida high theme na difrnt colourful cultural displays daga yaruka daban daban dasuke ta tururuwan tahowa.
Hankli kwance Adiaha ta saka one of best cultural attires, multi color wrper ne mai wani irin azaban kyau da dauke ido kowa sai sha'awarta yakeyi aransa maza da mata.
Yau kwalliyarta ma na daban ne, dan sosai tay kyau daga kaganta zaka san wa wani na musamman tay wann adon.
She look like a queen kowa sai son hada hanya da ita yakei, koda ta fito filin rawa tana rawa tare da sauran yammata acikin kwarewa lkci guda potential suitors dinta suka rude wanda aka zaɓar matan kuwa nan da na ya fara tunanin sake komawa gidansun da yamma domin asake yin sabuwar consent taking tunda dazu ba asameta agida ba.
Duk kwalliyarta da fara'arta yau tanayi ne domin aranta tanajin cewa hala Ahmed zaice mata yana sonta. She just cant wait ya furta mata hakan Dan sosai tay makanta alkwarin bashi dukkan zucyarta da imaninta inhar zai kasance nata.
Ahmed yana hotel yana kammala wasu yan ayyukansa a computer yanata kallon kirarta a wayarsa baiko kula ba dan yau bayason yaje wajen sun da wuri yafison daga yaje ya samu attention dinta zai gaya mata abunda ya kawoshi cos he cant keep wasting his time here hanklinshi gabaki daya yakoma gida.
Tun karfe biyu aka soma taron har wajajen karfe 3.30 ahmed baizo ba duk sai hanklinta ya soma tashi tafara dube dube amma bata gansa ba.
Dacan harta cire ranta tay fushi ta koma can gefe tanata rubuta masa tex messg har ana daf za'a fara shirin rufe taron sai gashi nan ya taho.
Sanye yake da wani irin red t shirt mai tsada da kuma bakin wando ya saka sneakers data mugun dacewa da kayan sai ya rufe fuskarsa da facing cap da hadadden clean eye glasses mai dan fadi. Fadin irin kyan da simple dressing din yay masa ba a magana dan duk inda ya ratsa sai anyi yuuu ana kallonsa.
Bata ganshi ba harsaida ya taho daf kusa data inda take snn ta taso tana dube dube har saida taga babu wani mai kallonta sann ta wuce wajensa da gudu taje ta rungumesa sosai tanamai jin tsananin dadi da sabuwar kaunarsaa dake neman mata yawa aranta.
Dressing din datay yay mata kyau shiya saukaka masa wajen fidda zancen sa acikin hikima ta inda yasan bazai zurfafa maganan soyayya tsakaninsu ba.
Sai ya tsaya kawai akan yaba kyaun datayi baije da nisa ba.
Wani irin yaba kyaun datayin yakeyi acikin raha mai kama da gaske yana ce mata tafi dukkan yan matan garinsu kyau da iya wanka shiyasa yake kulata sosai..
Tunda adiaha take arayuwarta namiji irinsa kyakkwan mai aji mai kudi kmr ahmed bai taba kodata kamar na yau ba...
Wani iri nadaban tadinga ji aranta tana jin sonshi na cizonta a kwakaltrta.
Itakam ta furta masa tana sonshi alokcin yafi sau goma amma bai iya amsata koda sau daya ba saidai ya wayance da wani zance na daban daya shafi na yabon surar jikinta ko kwallyarta.
Tsakaninta da Allah take sonshi har ranta shikuwa sauri kawai yake ya cika burinsa akanta ya samu ya koma gidansu akan lokci.
Gefe suka koma inda bamai ganinsu ya mannata akan kirjinsa yanadan shafata suna shan hirar soyayyarsu kamar na dagaske, Saida ya tabbata ya zurma zucyarta sosai da yaudararrun kalamai masu kama zucya snn ya fara gaya mata abunda ya kawosa garin nasu.
Bawani boye boye yace mata "indai harta tabbata tana sonshi, shi yana sone ya aureta. Suyi aure kawai tabishi garinsu a matsayin matarsa.
Da can adiaha ta dauka giyar soyayyace ta debe sa ya furta mata wnn maganan bata yarda ba harsaida ya fidda zoben gold mai kyau acikin aljihunsu ya tambayeta ko zata aureshi.
Tunda taga wai dagske yake jikinta ya mutu dan har wani Suman tsaye tayi nan hawaye suka fara sauka daga cikin idanuwanta jin kamar mafarki takeyi amma ba gaske ba.
She tried her best to wake up daga mafarkin amma ta kasa, saida ya saka mata zoben a ytsarta snn ta dawo hayayyacinta ta rungume sa tana kukan murna sunfi minti 10 ahaka manne da jikin juna.
Gabaki daya ta rasa amsar da zata bashi sabida rudewar datayi
Tafi kowa sanin kalar jan aji da iya walakancin ahmed sai yau rana daya kwasam yazo yace mata zai aureta ai abun daban mamaki kwarai dagaske
Dan duk a burinta data saka akanshi bata taɓa kawowa dacewa hakan zai taba iya fitowa daga bakinsa ba.
Jikinta har rawa yake taciki Hawayenta ya ki tsayawa sai kallon zoben takeyi jin kmr haryanzu a wani duniyan take.
Ganin ta shiga shock dayawa yasaka yace mata taje tay tunani akai xuwa gobe, shi kam a shirye yake zai aureta amma inta amince, snn yace mata zai iya jurar duk wani abunda hakan zai jawo muddin dai zata aureshi shikoyanzu ne zai iya auranta, snn basai ta canja addininta ba, indai bata so is fine with him..he just want her to marry him and dats all.
Yau dukkan wani kalamai da Ahmed ya furta mata bakaramin narkan da zuciyarta yay ba..
Tana son ta amsashi snn tay masa bayanin halin da ake ciki da yadda rikicin familynta yake amma ina lokaci ya riga ya kure musu yamma yafarayi snn itakanta tasan batada nitsuwar da zata iya gaya masa wani abu mai muhimmanci ayanzu.
She is just overwhelmed har suka rabu bata dena share hawayen murna ba gashi ya bata kudi har dubu hamsin kyauta.
Wajajen karfe shida ta dawo gidansu tazo ta samu an gama shiri ita kawai ake jira tazo taga suitor dinta ta amsa ma elders tana sonshi sai akai maganan aurensu wajen ekpo sprits gobe asamusu rana.
Duk wani abubuwan daya dace na al'aada suitor din nan nata ya kawo dake daga gidan sarauta yake bakaramin bajinta sukayi ba.
Kawayenta dayan uwa duk an taru ana jiranta tazo ta badaa consennt dinta agaban elders by offering her suitor a cup of pure palm wine and share of kolanut to the elders and few visitors.
Sharp sharp akaje aka shiryata aka saka mata typical igbo dress wani white blouse da double wrpper da head.
Cousin sis dinta Ekaete da wasu kawayenta sune agewaye da ita sai iyayen ta abaya har aka kawota cikin fili..
Rawa ake ana waka ana murna yau adiaha is finally going to make a decison once nd for all
Saidai tunda ta shigo filin basu gane mata ba dan babu abunda ke yawo a kwakwlarta face maganganun ahmed na zancen aurensu..
Binsu a filin takey kawai amma haklinta baya jikinta sam dan Bataji bata gani muryansa ne kawai yake mata yawo acikin zuciyarta bana wasa ba.....
Kawayenta ne suka rakata ta rabawa elders kolanut kowa ya dauka yana saka mata albarka.
Bayan nan aka rakota har gaban suitor din tare da cup of fresh palm wine akace tay kneeling akasa ta miƙa masa inya karba yasha toh shikenan saidai gobe ajira jin ranar bikin aurensu daga bakin chief priest.
Har adiaha tay kneeling kasa Maganganun Ahmed bai dena yawo a kwakwarta ba, rawa rawa hannunta da jikinta yafarayi ta soma jin wani irin kasala da jiri jiri.
Kowa jira yake yaga ta miƙa cup din tana kuwa dagawa ta kwara shi akasa...nan kowa ya miƙe tsaye cikin mamaki.
Ganin duk an mike ana kallon abunda tay yasa ta yaye rufin kanta ta watsar akasa ta fice a filin da gudu bata tsaya ko ina ba sai cikin jeji tana huci tana furta cewa bazata iya auran wani namiji a duniyan nan inba Doctor Ahmed ba..Surayyahms chat *08060712446*
*Wanda ba su yi saving number ta ba su yi sai su mini magana ni ma zan saving ta su* 👍🏻
Reply with "saved" is enough😍
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top