6
*KISHIYAR ƘABILAH 6..*
BY SURAYYAHMS.
Tunda kafayat ta dau motarta tahau kan titi tana tuki babu abunda yake dawo mata akanta sai maganan da sukayi da mahaifiyarta, tafiya take amma bakaramin bugawa kirjinta yakeyi ba, ta rasa da wanne xataji tasan dai inhar bata samu Ahmed ba babu Abunda xai hana mamanta yi mata auren dole, atake taji kasala na dirar mata akowani sassa na jikinta,da kyar da wuya ta kaucar da wnn fargaban tafara tunanin yadda xata yi tasamu cikar burinta akn Ahmed, musmmn aynxu data san da cewa xancen ya kwabe mata yaxamo mata tamkar kashin kifi a wuya, tasan dolene komin rintsi komin wuya tasan yadda xatayi su tsaida maganan auren nan nasu da Ahmed damilare kafinan tace xata shiryawa komawa gidansu taje ta gamu da bala'i da masifa irinna mamanta dayake jiranta.
wajajen karfe 1 dai dai na rana kafayat ta iso gaban babban gate na Jimada's family house dake cikin wani hadadden estate dake anguwar gwarimpa.
Duplex ne babban gaske sai parking space gari guda mai dauke da motoci kala kala da basufi guda takwas aciki ba. Kana ganin gidan xa kasan gidane daya kafa dumbin tarihi.
Mai gadinsu bahaushe dan garin yobe yana bude mata gate kai tsaye ta shiga bata tsaya kulawa da gaisuwarsa ba. Tana fita ta wuce babban sashin su anty mojushola, Kayanta ma anan ta bar ma masu aiki su suka ciro a booth suka kai mata cikingidan.
Dan babban falone dake shimfide da turkish carpet brown mai gida gida, ga saitin kujeru manya na daidai rufin asiri masha Allah palon sai kamshin turare yake ko ina tsaf tsaf babu ko digon datti, Anty moju ne a tsakar falo tanakan dadduma tana sallan axhr, kana ganinta kasan tadan kwana biyu a duniya tanada jiki sosai da manyan maxaunai.
After some mints ta sallame sallan cikeda natsuwa sann ta daga kai ta kalli kafayat data kusan kwantawa kasa agabanta sabida tsabar nuna girmamawa.
A mugun ladabce ta shiga Gaishe ta _o dara irọlẹ_ ma..
Anty mojushola dake murmushi sosai tace _irọlẹ mi darling, iyawo wa iwaju_ (Evening my darling our future bride) tana murmushi sosai tace "kafayat hows ur mother? Fatan tana lpya ?..
Wani irin murmushi kafayat tayi kanta na can kasa tace Alhamdulillahi she is fine maaa _o ṣeun_
Anty moju tace its okay.
_ọlọrun bukun fun ọmọ mi_ (God bless u my child) ure welconme
Tace Ameen oo _o ṣeun_
A dede nan Anty temi ta tarar dasu, nan kafayat ta miƙe tana murmushi sosai ta koma gefenta itama ta rusuna har kasa suka gaisa suka danyi hira awajen lunch kadan kafin nan kafayat tayi xcusing dinsu taje quest room in da kayanta yake tayi sallahn axhr tayi wanka ta sake cancanda kwalliya snn ta sauya wani kayan mai kyau ta dawo kasa.
As usual bata xauna acikinsu ba direct kawai ta wuce kitchen ta shiga kkrin shirya musu wani irin hadadden dinner, she planned to cook igbin chops with yam wanda kafin ma ta fara hada girkin saida ta tsaya ta hada musu wani irin tasty mushy butter crumbs na taɓawa snn ta hado musu da cold and refreshing smoothie takawo musu har cikin falo inda suke xaune suna kallo, anan ma babu wanda bai saka mata Albarka ba, hirar lamarinta da Ahmed suketayi suna tabawa ita kuma tanacan kitchen tana shirya musu abincin dare. anty mojushola tayi tayi akan Ahmed yaxo gidan da daddare ayi dinnern tare dashi amma sunkira wayarsa sau babu adadi basu same sa ba,duka line dinsa a kashe suke tun da rana, kai Har gidansu sun kira amma duk ba a sameshi ba.
Kafayat kuwa tana kitchen tanakan aikinta happly da Farko ta tafasa doyarta ta xuba a wamer, sauran kuma tayi tuwon sakwara da shi shima tasaka shi a wamer na daban,for igbin dinta bata wani bata lokaci ba ta nemo shelled jumbo snails (dodon ƙodi) da scotch bonnet pper, tattasai da albasa da lemon tsami, bay leaf, manja, shrimp powder da seafood bouillon powder
Nan danan Ta hada igbin chops into 2 difrent ways, daya tayi sauce daya tayi stew. Wanda xa'a iya serving dinsu duka da tuwon sakwarn da tafasashen doya.
Bayan ta kammala hada abincin ta hado musu da drinks masu dadi kala kala ta jera komi akan dinning table snn tahaura sama domin yin wanka.
Kafin kace wani abu gida ya cika da yan uwa da jikoki cos Anty ramatou bata tsaya nan ma saida ta gayyaci surkunayen su wanda suke nan a nigeria suka xo da yayansu yin dinner. Anty Nurat itace matar babban yayansu Ahmed, wato brother kaziim AREMU yana da yaransa uku duk maxa, "shehu", "sulu"da "femi". Saidai shi mijin nata yana kasar waje bai dawo ba tukuna.
Sai Anty Adizatu itace matar Brother Hamzat dimeji, yaranta biyu duka mata, medina bolanle da karimat omolara. Brother hamzat Shine mafi kusanci da Ahmed dan haka komi na shirin da akeyi na bikin Ahmed shine yake saka bakinsa aciki kai tsaye.
Sai sistersu xainab moturayo wanda daga ita sai Ahmed din, itama bata nan taje oshogbo inda gidan mijinta yake ita kuma danta dayane dan karami shine shafi'u dake tadan samu matsalar rashin haihuwa.
Anty nurat taxo da Autarta femi, sai Anty Adizat kuma taxo da duka yan matan nata wato Medina da karimat 10 and 13yrs old.
Around 7:30pm lokcin kowa yaci kwaras an hallaro kan dinning table
Kafayat was really feeling like a bride musammn ma dataga matan yayun Ahmed sunxo da yayansu anacin abincinta anata xuba santi already su medina da su femi da karimat sunata kiranta da sunan iyawon Uncle Dami.
Duk dama rashin halattar Ahmed ixuwa wajen dinnern yaso yadan dameta aranta amma soyayyar da familynsa sukata nuna mata awajen ne yyita sassaita mata xuciya.
Itakanta ta nemei shi awaya sau babu adadi amma duka layukansa a kashe. Around 10pm aka kammala hira kowa ya watse.
Nan Kafayat ta koma makwancinta da tunanin hirar tsokananta da sukayi a tsakanin Anty temi da su anty nurat na cewa yakamata su hada ma kafayat da Ahmed grand surprise engagemnt party a gidan. Acikin wasa da dariya sukayi hirar amma da mamakinta sai taji washe gari da safe Anty temi tana sake dago mata da maganan.
A bangaren Ahmed kuwa aikinsa kawai yake kkrin kammalawa da wuri domin ya samu isasshen daman yin tafiyarsa cikin kwnciyar hankli batare da tashin hankli ba. Jiya monday din da sukata kiran layinsa akashe bai dawo gida ba ne, a office dinsa ya kwana yana aiki shiyasa bai kunna wayarsa ba.
Yau Tuesday morning da Asubah ya dawo gidan batare da sanin kowa ba yy wanka ya shirya kansa ya kara ficewa asibitin Dr hassan don ya kammala da can shima...
Gobe Wednesday by 9.am jirginsa xai tashi ixuwa calabar, and he want to beat it on time ixuwa lokacin daxa aci taron ogoja market festival dan anan ne kawai yasan xai iyacin karo da Adiaha.
Jimada family house
Tuesday morning
wajajen karfe tara saura na safiya kafayat ta fito ta kammala musu komi tana kan Goge goge a kitchen sai ga Anty tem ta shigo,hira suka kamayi suna dan raha a tsakanin su, Anty ramatou tafara gaya mata Yadda suke son komi yayu sabida dama sunkirata ne dan su shirya tarban Ahmed a matsayin angonta na next week.
Anty ramotou ta bata 100% tabbaci na cewa komi xai tafi musu daidai sabida aganinsu sati biyun nan kamar gobe ne so babu amfanin jira shiyasa suka kirata kawai domin taxo afara dan shirye shirye...
Idan ana maganan auren nasu Kafayat will be blushing all the way like jinjirin biri. Sai kaga har tana kasa iya haɗe ido da su anty temi a tunaninta sun riga sun dawo surukunai.
Sukuwa abunda suke so kenan suga sun same total submission and biyayya daga wajenta, ta inda koda anyi Auren sune xasuyi controlling Rayuwar Ahmed tunda Hajy khadijatu uwarsa itace take juya musu kan dan uwansu Bello, But with kafayat by their side sunsan xasu same nasu daman suma ata wajen Ahmed.
Haka suka nitsar da kafayat suka nuna mata cewa babu wani abun kunya wajen ya mace idan tayi proposing ma namijin datake so dan ba haramun bane.
Tunda Ahmed yaki ya furta mata yana son ta kuma yana son suyi aure sukace toh ita saita shirya furta masa dakanta inhar Ahmed ya amsata toh basai ma anjira 2 weeeks din nn ba xa'a fara shirin aure .
Hakanan su anty nurat da anty najat suka taru suka cikama kafayat kasa aciki, aka fara shirya grand suprise proposal party wa Ahmed. Kasuwa suka baxama na musammn aka sissiyo kayan ado wanda xai saka Ahmed ya kasa iya rufe bakinsa inyagani. Wani hadadden backless red flowing gown kafayat ta siya mai tsada na dubu arba'in da biyar da takalmi mai tsini da head crown da flowers da rings dinta masu kyau.
Har dare sunakan yawon siyayya agari suna shiri ma suprise engagement party kafayat kuwa tasha hadadden gyaran gashi da attachement cos batada dogon suma sai tayi manicure da pedicure tasaka nails dinta masu shegen kyau da tsada she is ready shining like a bride kowa sai yabonta yakeyi ranar
Shiyana can yanata aiki baima san me sukeyi anan ba, Tun safiyan ranan tuesday din anty ramatou taxo gidansu ta same hajy khadijatu ta gaya mata abunda suke shiryawa, itama batayi kasa agwiwa ba tasaka albarka akan lamarin dan aganinta kafayat will make a good wife to her son ahmed inhar yana son auren ita bata da matsala sam.
Sunyita nemansa awaya still yauma tuesday din amma basu same shi ba,sai can da yamma lis kafin nan yabaro asibiti ya taho gidan agajiye da niyyar shiryawa tafiyarsa na gobe da sassafe.
Samu yy hanklin maman sa duk ya tashi dan ta nemesa awaya har ta gaji,tun bai Xauna ba tafara bashi labarin tafyar, haka tayi tayi dashi akan cewa ya shirya kawai gobe da safe karfe takwas suje gidan su anty mojushola tare amma haka nan yaki mata sam yace baxaije ba dan yasan baida wann lokcin domin kuwa karfe tara jirginsa xai tashi ixuwa garin calabar, toh gashi abun nasu suprise ne ba ason agaya masa harse yaje ya gani hjya khadija ta rasa ta yadda xata soma shawo kansa.
8:30 am na safiyar wednesday aka shirya masa suprise party din.
Kafayat is already feeling sooo excited dan gani take ko ba dan Allah ba idan Ahmed yaxo yaga idanun manya awajen kamar irinsu anty moju da mahaifyarsa da su Anty temi hala xai hkra ya amsa batun aurensun kawai even if its out of compulsion. Sosai ta saka ranta akan wann lamari shiyasa ko wani baccin arxiki bata samu tayi ba.
Batasan da cewa shawo kansa dan yace xaixo wajen ma saida akata drama da shi agidansu sosai ba...
Karshenta ma Anty mojushola ne ta kirashi dakanta awaya ta dinga kuka tana kora masa ashariya ahakan ma saida ta hadashi da babansa kafin nan yace musu xaixo tare da mum dinsa Cos he is already very annoyed da yadda suka matsa masa akan saiyaje wajen musammn ma da basu gaya masa dalilin xuwan ba.
Cikin dare adakinsa yau ko runtsawa baiyi ba yahau kimtsa trolley na kayansa na yin tafiyarsa ixuwa calabar,sassafe karfe shida ya farka a bacci bayan yy sallah yy wanka yaxauna yana shiri at same time suna waya da abokinsa banji.
Bayan sun kammala maganan Adiaha Ahmed yafara bashi labarin irin matsa masa da akayi jiya akan wai yaje family house dinsu yau da safe, lokci guda banji ya soma dago kan xancen a mind dinsa. Ahmed yana kan mita banji ya datsi numfashinsa da cewa
Guy wait..amma kayi magana da kafayat awaya jiya kuwa?
Ahmed yace no, akan me ita uwata ce daxan mata magana..naga dai tulin miscalls dinta jiya ban bita kanta ba..
Banji yace hmm to mesa baka kirata ba.
Tsaki Ahmed yaja yanakan daura igiyan booth dinsa yana cewa
"I cant oo,ina maka maganan family na meya kawo maganan kafayat anan kuma, dat one na normal thing now..ai dama ta saba min irin waynn miscalls din sabida bata da aikin yi a rayuwanta sai bina.
Banji yace hmm ba haka nake nufi ba,i just smell sumting fishy abt her cos she called me yestade tana tambaya na wasu abubuwa game dakai dana tambayeta tacemin wai gift take son siya maka, kuma naji surutun su Anty adizat anan gefenta sai nayi tunanin me sukeyi atare ahaka?
Da mamaki Ahmed yace kafayat din ne take tare da sun anty adixat??
Banji yace yea i am sure naji muryansu sosai lkcin she was shouting at her doter medina, surutu awajen dai kmr suna kasuwa nace kodai wani abu suke shiryawa ne baka sani ba.
Ahmed ya kyabe bakinsa a yanayin ko inkula snn yace "Oho nide sunki sufada min komi kawai cemin akayi wai muje family house before 8 amma karka damu koma miyene ni nasan mexanyi dasu.
Banji yace toh shikenan dai inka sauka lpya dai ka kira take care bro.
Ahaka suka kammala wayar kowa ya cigaba da abunda ke gabansa.
After some few minutes saida ya lura kamr babu motsin kowa snn ya fito acikin sanda ya yaje ya bude bayan booth dinsa ya aje trolley dinsa aciki ya kulle snn ya dawo ciki
tsaye agaban mirror yy lkcin harya kammala shiri yana fetsa turare yanata tunanin abunda xai gayawa mum dinsa idan yaje mata sallama qamshin jikinshi gabaki daya ya gama cika dakin yanamai dada gyara gashin kansa da brush. 8 o clck na bugawa aka fara buga masa kofa akan ya fito, Baiyi wata wata ba ya sauko kasa dan ya nufi dakin mum dinsa dan shikansa yana son ya isa airpot by 8.30 kuma baifi saura 30 min ne 8:30 din yy ba.
Qamshin turaren jikinshi dayasaba sakawa ne ya dinga baxa ilahirin gidan ayayin daya sauko yana doka sallama a dakin mum dinsan ta juya tanamai tsaresa da idanuwanta da sukayi luhu luhu sabida kukan dataci. tun dagacan mahaifiyrsan ta xuba mai ido tana sauke sanyayyar murmushi datake fiddawa da kyar ganin irin mugun kyaun da yyi yau yasaka All black casuals ne na marks and spencer mai 3 qtr jacket, yasha booth dinsa ubansu da agogonsa na new police irin matte black din nan snn ya shafa mayukan gyaran gashi sai kyalli kansa yakeyi..
Yanayinta dayagani ne na ragwabewr jiki da jimami yaso yadan dagamai hankli nan take ya taho wajenta a gaggauce cikin tashin hankli, tambyarta yake amma bata amsashi ba har saida ya karaso ta wajenta tukuna ya lura da cewa video call takeyi da babban dadarta wato Anty hajiya maimunatu mohd gidado.
Su biyunsu mahaifinsu ya haifa amma suna da wata kanwarsu yar kanwar mahaifinsu da aka rainesu tare.
hjya maimunatu din itace Babbar yayansu, sai mahaifyrsa Hajiya Khadijatu,snn hajiya Aminatu wanda itace yar kawunsun snn itace karamarsu wanda bata wani jima da yin aure sosai ba ta rasu awajen haihuwa.
Yau shekara 18 kenan da rasuwarta amma haryau sunajin mutuwartan kamr sabuwa domin kuwa wann mutuwarta yar uwartasu aminatu ya musu ciwo musammn ma da hjya maimunatu take da tabbacin cewa *Kishiyar kabila* ce ta kashe musu yar uwansu aminatu akan batun haihuwa.
Mijin yar uwansu Aminatu Alhaj Amadu hussaini yy aure yakai sau goma amma bai taba samun haihuwa ba sai akan yar uwarsu aminatu wanda shiya jawo kishiyarta datake *kabila* ta hade baki da likitoci aka kasheta awajen haihuwa.
Anyi case sosai bayan mutuwar aminatu saidai Kafin lkcin basu da wani kudi snn iyayensu kaf sun rigamu gidan gaskiya dan haka basu samu mai tsaya musu akan gaskiyarsu ba,snn alkcin shikansa mijin yar uwartasu yay gamone da wani irin kaddara na shanyewar rabin jiki sanadiyar hawan jinin daya turnukesa ayayin dayaji cewa matarsa Aminatou ta rasu awajen haihuwa dan bakaramin sonta yakeyi ba.
hjy maimunatu itace tamkr uwa kuma uba agare su dukansu dan haka lamarin sosai yay mata ciwo fiye da kowa wanda shine sanadiyar dayasata shiga harkan siyasa da neman kudi har Allah ya daukakata. Sosai take son taga ta raya xuriarta da kuma jininta, Shiyasa haryau take kaffa kaffa da rayuwar yar uwarta hajya Khadijatu agidan yarbawan nan dan yanxu ita kadaice ta rage mata a duniya bayan mutuwar aminatu, Basu da kowa a duniya sai yayansu, wato yarta nafisa da kaninta sadik,da shi Ahmed din da kuma yarinyar da aminatun ta haifa kafin rasu ta bar musu mai suna YASRAH AHMED HUSSAINI wanda a hannun hjya maimunatun ta girma.
Yau yasra take cika shekara 18 takwas a duniya wanda yy dede da ranar mutuwar mahaifyarta aminatu shiyasa duk suka taru sunata kuka suna masu tunawa da ita atare.
Ahmed yana isowa wajen ya fahimce abinda suke ciki, jikinshi a mugun sanyaye ya xauna akasa yanajin conversation dinsu mai saka tausayi da jimami dan mahaifyr sa tasha bashi labarin rayuwar hajy aminatu da yadda kishiyarta ta bala'in axabtr da ita dan ance har hauka saida tayi da ciki ajikinta.
Shidai yasan shi bamai son xumunta bane dan haka baxai iya kirga sau nawa ma yajeshi katsina wajen hajy maimunatun ba dayake karami, xai dai iya tuna lkcin da akayi sharia a kotu aka kwato custodyn yasra daga hannun dangin ubanta da suke son riketa na dole dan sabida sunacin arzikin mahaifinta tunda shi baida lpya,da asirin su ya tonu kotu sai tabawa hjy maimunatu amananta na har izuwa lkcin da mahaifin nata zai samo sauki, amma bayan nan bai san komi ba saidai duk da haka yasan dacewa antynsan tana son famlynta sosai.
Xamansu A turkey na tsawon lkci a matsayin ambassada na kasa shiya dada sakawa xumuncinsu yyi nisa sosai wanda shiyasa ma kwata kwata bai taba sanin kamannin yan uwansa nacan turkey ba.
yasan dai da akwai adda nafisa wanda take babban ƴa ga hajya maimunatu, dake ta girmeshi a shekaru ita a U.K ma take da aure, sai sadik wanda kusan ya girmesa da shekara guda ne,amma yasran kam baida tabbacin xai iya ganeta ynxu dan rabuwarsa da ganinta ido da ido tun tana yar shekara bakwai lokcin ma tana fama da ciwo sosai.
Saida suka dan samu nitsuwa snn ya rusuna kai ya gaishe da anty maimunatu wanda ganinsan ne yadada sanyaya mata xucyrta taji dama dama, albarka ta rika saka masa tanamai masa adduar samun lpya da kuma tsari tanamai nuna alfaharinta dashi dan tana son jininta sosai.
Lokacin kan yasra na kallon kasa sama sama takejin su suna gaisawa saidai sam bata iya dagowa sama ta kalleshi ba duk dama tasha jin labarinshi awajen hjya maimunatu itama tana son taga kamannin dan uwantan amma sabida kukan tuna mahaifyrta dataci sai bata iyayin hakan ba.
Ahmed Yanata satar kallonta ashe itama satar kallonsan takeyi da shanyayyun idanunta da suka gama canxa kala bai sani ba,a cikin wani irin bakon yanayi ya tsinci kanshi mai tafe da rashin samun nitsuwa, sai can data tamaida idonta ta rufe ruf snn ta dago akayi akayi ta gaishe sa amma sam taki cemai komi, shima sharr yy da ido yanabin ta da kallo kamar bai taba ganin kyakwar mace irinta ba musmmn ma dan karamin bakinta mai kyau irin wanda bai taba ganin irinsa ba .
Saida iyayen sukadan lallabeta snn Ahankli ta budi baki muryanta can kasa kasa kamr xatay magana, suka hade ido yarasa me xaiyi sai ya hade rai ya watsa mata harara, ta sake budan bakin ahankli suna kara hada ido taji wani irin kasala na dirar mata da yanayin irin kallon da yake jefo mata nan da nan ta girgixa kai yanayin ta cike da shan qamshi da shagwaba tayi masa shiru batace mai uffan ba sai shima ya basar. Cikinsu babu wanda yacema wani uffan.
Anty maimunatu tana Dan murmushi tace Ahmed pls understand her kaji?, duk ranar birthdaynta haka take rigima sam bata son yin magana bare murmushi.
Ta sake kallonta cikin lallami tace yasra, Ahmed fa babban yayanki ne kisaki jikin ki dashi kinji? Dan yauko da bana duniya sune jagora agareki da shi da sadeek, shine yau kuma baxaki iya cemai koda sannu ba?
Batace komi ba ta dada sauke kanta kasa alaman dai baxata cemai komi ba
Babu yabo ba fallasa Ahmed ya kyabe bakinsa snn yace its okay bakomi momy, ahnkli yana satar kallonta yace atleast muma ai baxamu ce mata happy birthday ba.
Tashi tayi tabar gaban screen din tana tura baki ko irin murmushin nan batayi ba, atake sai yaji attitude dinta ya kuma shakesa a wuyarsa amma saiya ya basar cikin murmushi suka dan gaggaisa yanaji suna maganan shirye shiryen graduation party da xasuyi na gama scndry school din yasra idan suka dawo nigeria in few months time.
Bayan sun kammala wayar hjya khadijatu ta sauke nannauyar ajiyar xuciya tana cewa Oh Allah ka nunamin ranan dawowarsun nan lpya,sounding sooo happy tace i just cant wait..dan kuwa katsina xan koma wajen adda maimu nayi hutuna ko kunaso ko bakwaso.
Murmushi ahmed yy sigar tsokana yace Wann ai ma dad knan kike tura wnn sakon, nidai saidai na xama muku dan aika dan nasan shine baxai iya jure xama babu ke agidan nan ba..
Kunnensa taja tana dariya tace marar kunya kawai kaci kaniyarka kenan wato kai lkcin har kayi aurenka ko?
Kansa ya girgiya yace no binki can xanyi ai dama rabona daganinsu na dade kafarki kafata,..
Dariya kawai tayi yace
a babban gidanta na katsina xata xauna ko?
Tace eh, kasan tunda tenure dinta ya kare acan turkey, already har president yay signing mata wani new political appointment anan senate house of assembly Abuja. Kaga ko da ban tare a katsina ba still xatana xuwa abuja akai akai sabida aikinta Yanxu haka ma maganan karatun yasra ne yake damunta tanata tunanin a nema mata university anan ne ko acan turkey ne xaifi, but i dont think xata iya kyaleta a wani kasa da karancin shkaruntan nan u knw sumtimes she can be soo protective. Inde anan din yasra xatayi karatu i think nice xan dauki ragamarta kawai sai anemo mata spot a nile ko base university tafara karatun anan Abuja kusa dani tunda kaikam ma aurenka xakayi.
Baice komi ba yay murmushi sai can snn yace toh Allah dai ya dawo da su din lpya.
Tace Ameen
Agogonsa ya kalla ganin 8.15, yace mamy lets go mana akwai inda nake son xuwa and Its very important daman tun jiya naso na fada maki sai bansamu dama ba.
Tace 'a a ,abar wann maganan kawai tashi muje dan tun asubahi anty temi take min waya akan na make sure naxo tare dakai. Inyaso idan munje saika fadamin inda xakaje din
Yace mammy what is it dat ure not telling me?
Wai meyasa akace dolene sai munje family house by this time
Sharesa tayi ta dauki hadadden golden veil dinta ta yafa snn tace meet me outside my friend da already ma munyi latti..
Baice komi ba ya miƙe yabita abaya suka fita kusan atare, tunda suka dau hanya yake takurata yyi yyi ta gaya masa menene amma sam haka taki har suka isa kofar mansion din jimada.
Ana bude musu gate yy ma mai gadi ido akan karya kulle kofa alaman yanxu xai juyo..
Lpya lpya ya sauke mamansa har kusan bakin main door,snn yace mata ta shiga daga ciki shi xai gyara parking din motarsa acan parking lot xai biyota abaya .
Batasaka komi aranta ba ta shige cikin gidan kai tsaye, ko minti biyu batayi da rufe kofar gidan ba yay kwana snn yaja motarsa cikin gaggawa ya bar gidan aguje ya wuce hanyar airpot abunsa....
COMENT AND SHARE FISABILLAH.
SURAYYAHMS WHATSAP ONLY 08060712446.
SAVE AND CHAT❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top