10
*KISHIYAR ƘABILAH...10*
BY SURAYYAHMS.
Saida Adiaha tay nisa sann ta tsaya da gudun datakeyi ajikin jejin tanayi tana dan juyawa baya tana sauke haki.
Mannuwa tay da jikin wani katoton mahagony tree mai wani irin tsayi da duhu idanuwanta a lumshe hannunta dafe da kirjinta tanamai sakin wani irin zazzafan huci..
Wani abu takeji ajikinta na mata yawo zurrrrrrrr tare da sunan Ahmed dake mata amo mai ruri acikin kololuwar zcyarta da kwakwalwar kanta tanajin wani iri irin sassakewar jiki tamkar wanda sihirin soyayya mai karfi ke fuxgarta akanshi wanda bata san daga ina yake fitowa ba.
"Ji take kamar bazata ma iya rayuwa a duniyan nan in batare da Doctor Ahmed bello jimada ba"..
Wani irin bugawa zucyrta yakeyi akansa, kirjinta na sama da kasa cikin hucin tsoron mai tafe da tashin hankli na rashin sanin me zatayi da rayuwarta aynxu.
Kara lumshe idanunwanta tayi tabi tay tsamm ajikin bishiyar jin har an biyota ana kwala mata kira acikin jejin acikin tashin hankli da alaman kowa yafito ne anata nemanta.
ADIAHA...ADIAHA..ADI?
Muryan kawunanta mr akpan da mr udo da na kawayenta duk ya cika koina ajejin,jin muryan
sun a kusa kusa yasa ta sake ballewa aguje ta kara shigewa can cikin jejin taje ta buya akan wani boyayyen tsaunin ciyawa inda tasan ba lallaine suyi tsammanin ta awajen ba.
Banda kuka mai sanyi babu abunda takeyi, ahankli tay ta rakube harta haura can saman tsaunin ta zauna ata inda ba wanda zaiji motsinta koya san tana cikin jejin gabaki daya.
Haka har aka karace nemanta aka dawo gida ba aganta ba. Wani tashin hanklin da ba'a saka masa lokci shiya shiga wanzuwa tsakanin kawunanta, mahaifyarta da kuma bakin da sukazo neman aurenta.
A Daren ranan saida ran kowa ya bala'in baci akan abunda tayi.
Mutane dayawa sunyi Allah wadarar da ita snn babu kalar tsinuwa da ba'a yi akan rashin isashen tarbiya da dattakon gidan nasu da ake cemasa gidan mr bassey ba.
Guduwan da Adiaha tayi saida yazamo wani babban taɓo agare su, harga shi kansa yaron da ake son ahadata dashi, iyakan abunda tay masa ayau kadai ya isa ya zamo masa abun gulma, snn duk inda ya shiga neman aure za'a nunashi ace shine wanda budurwa takishi snn ta gudu masa awajen consent taking dinsu.
Sum ppl now will start seeing him as a cursed ko wanda yake da bakin jini acikin al'umma...
Taruwar dangi elders din yankin sukayi akan familynsu adiaha kowa na fadar albarkaciin bakinsa Musammn ma dayake bayau aka fara samun babban abun kunya acikin wann familyn nasu ba.
Bayan kura ya dan lafa kowa ya watse bakin ciki mai tsanani shine ya rufe fuskokin mrs grace tare da uncles din adiaha wato uncle akpan da uncle udo.
Uncle akpan shine yake bin mahaifinta,shikuma uncle udo twin brother mahaifinta ne sune manyan yaƴa acikin mahafiyarsu mrs chidara
Wanda ahalin yanzu bata tare da su sabida musuluntar dataje tay aure a garin adamawa.
Har wajajen karfe 9 na dare adiaha na zaune ajeji tanamai tunanin rayuwarta wanda yake da yawan rikici da rudani mai yawa aciki.
kokri take ta raba gardama tsakanin soyayyar datakeyi wa familynta da kuma wanda takeyi ma rayuwarta ayanzu.
Dan tabbas idan ta zabi tay rayuwarta yadda take so toh komi zai lalace musu tsakaninta da familynta dan tasan babu abunda zai iya hanata musulunta domin ta aure babban muradin zuciyarta wato dr Ahmed.
Idan kuma ta zaɓi ta hakura da soyayyr Ahmed dan familynta tasan hakan zai kawo martaba wa iyayenta da familynta nata saidai ahalin yanzu batajin aranta kmr zata iyayin rayuwa agidan wani da namiji inba doc Ahmed ba.
This war is btwen her heart desire and her family, abun na damunta sosai dan acikin su duk wanda ta zaɓa dolene tay asara mai girma.
Idan har ta zabi ahmed dolene ta rasa wani babban gurbi acikin zuciyan iyayenta da zuriarta gabaki daya kamar yadda kakarsu mrs chidara ta fuskance tsana, da kyamata snn ta zama tsinanniya a zuriarsu gabaki daya data aure northenr kuma musulmi acan garin adamawa.
Idan kuma ta zabi familyn ta bar soyayyar doctor Ahmed to tabbas tamkar mutuwarta ta zaba dan batajin zata so wani namiji kamr yadda take sonshi. He is evry woman dream, komi na rayuwarshi is perfect to her, kominsa gwanin ban sha'awa ne asaninta doc ahmed baida wani aibu a idanunta haryanzu.
Tay iya tunanin duniyan nan amma at the end kanta kawai take zaba, saidai abu mai matukar wuyane agareta ta yanek hukuncin raba kanta da zuriarta da mahaifiyata kai tsaye shiyasa banda kuka babu wani abunda yake sakata jin dadi aynzu..
Dadin karawa da tasan dukkan wani abunda yake tafe da wanda yake wakana acikin familynsu na auren wani kabila, kabilanma ace moslem.
gaskiyan shine tasaa iyayentq bazasu taba amincewa ta auri wanda ba yarensu ba and worst part ma wai bayarben musulmi.
saidai komi arayuwa lamarine na nuna sonkai da son zuciya shiyasa kowa da yadda yake daukar rayuwarsa
.tadai tasaka aranta cewa Ahmed din kawai zata zaba amma har yanzu bata kammala amincewa da wann tunanin acikin kwakwalrta ba tukuna.
Rabuwa da familynta na har abada wani Babban lamari ne wanda yake da ciwo matuka..
Tana cikin wann yanayin taji an dafata, a firgit ta daga kanta sama suka hade ido da babban kawarta kuma causin sister ta dinta ekaete.
Tana ganin itace ta firgita ta Rungume ta sosai tana sauke sheshhekar kukanta ahankli ajikinta duk sai ekaete ta dada shiga cikin rudani.
Rarrashinta ta kawai ta farayi batare da tasan asalin cikakken matsalar tata ba, har sai can da Adiaha ta dan samu nitsuwa snn Ekaete ta riko hannunta cikin taushin murya snn tace "Sister Adi, meya faru, why did u run away from ur consent taking moment? Kinsan kuwa irin bala'in da hakan jawo ma family?pls Why must u do this to us?
menene ke damunki..tun ranan na fada maki u are behaving weird, nagane kamar baki cikin hayyacinki pls wats wrong with u can talk to me now,..jin Adiaha tay shuru yasa ta dada rikota Cikin lallami sosai tace "ko bakison auren ne?
Are u spritually bound by the spirit??Ko kinyi blood oath da wani ne if not why are u rejecting ur own marriage proposal while ure not getting any younger?
Da kyar Adiaha ta dago ta kalleta da jajayen idanunta da suka kara cikowa da hawaye snn tace" listen Ekaete,nifa inada wani matsala mai girma kuma bana jin zaki iya fahimta ta aynzu.
Hannunta ekaete ta dada rikowa snn tace "just say it" inajinki, kinsan i will alwys support u.
hawayen data suka taru acikin idanunta ne suka sauko zurrrrr snn tace "babban matsalata shine ina mutuwar son shi, i love him soo much i feel like i cant even breath witout him"..
..Da mugun mamaki ekaete tace and who is dat?...i dont get u..
Tsaye Adiaha ta mike ahankli snn ta juya mata baya tana zubda hawaye masu sanyi sosai, cikin dauriya ta soma fada mata labarin yadda ta hadu da dr Ahmed har izuwa abunda suke ciki ayanzu.
Tun kan ta kammala Ekaete ta miƙe tsaye tana kallonta babu shiri dan tabbas ta gane kan labarin tun akan ciwon da adiaha tay daya tafi wancan karon, duk jikin ekaete sai yay la'asar tanajin kamar mafarki takeyi ba gaske ba.
Adiaha na hawaye masu sanyi ta cigaba da cewa "ekaete yace min na aure shi, wai zai tafi dani garinsu, see i love him, i just have to marry him, cos i cant live witout him..
Da wani irin muryan razani ekaate ta taho ta juyo da ita suna fuskantr juna cikin jijjigata a zafafe tace "chimooo, adiaha ,a moslem guy? "A Moslem yorouba, a Moslem u say,..Adiaha kinason ki auri musulumi and a yoruba guy too?chaiiiii , ta rike kanta tana girgiza kan a raunane jin abun adiahan tafadi kamr wani labarin cikin tatsuniya tanamai cewa chaii chaiii _ewoo chi nke, tufi akka machibidoro_
Adiaha batace komi ba tay shiru tana kallon can kasa, ekaete ta dada rikota tace _Adiaha pls tell me,i tufuru ya?_ (kin haukace ne) ta kara jijjigata sosai snn tace..amma kinsan me kike cewa kuwa? _ị bú onye ara?_ Are u insane?..
Da karfi adiiaha ta kwace kanta a hannun ekaeten data birkice mata da masifa atsawace snn tace "i am not mad, "ekaete nasani,nasan menace miki mana, i said i want to marry him cos i love him..what is wrong with that..ko bani da iko da rayuwata ne .ni baiwar su ce?see I am not a slave ohh Inada daman na zabi duk wanda nake so arayuwata snn in aura
Ekaete ta wanka mata mari mai zafi cikin jin tsananin takaicinta hade da wani irin tsananin bakinciki da mamaki jin abunda take cewa...
Tace So you think u know wht ure saying ryt? _ewoooo, Adiaha, ị na-akpọ onwe gị nsogbu_ (ure calling troubling upon urself/kina kiran makanki bala'i) _Iwe nke chi_(wrath of gods upon u/da tsinuwan allolinmu akanki)
Jiki a sanyaye sosai ekaete ta nemi waje ta zauna tana girgiza kai alaman maganan nan ya tabata sosai ta kasa hakuri nan Ta sake kallon Adiaha datake tsaye snn tace ynzu Acikin dukkan mazan dake fadin kasar nigeria baki kalli wanda zaki aura ba sai moslem? Adiah You have really lost it. _Adiaha nke ụmụ nwoke niile nọ na nigeria ị hụghị di, ịchọrọ ịlụ onye alakụba?_ i still cnt believe this chaiii..
Ayanayin damuwa sosai adiaha ta taho ta sameta azaunen snn tace pls pls stop discouraging me ekaete. Nazo nan ne dan nayi tunani akan rayuwata badan in nemi shawarar kowa ba, ina son nasan yadda zanyi in fada ma family nane ni gaskiya zan auri doc ahmed since he propose to me kuma nima ina sonshi..
Da karfi Ekaete ta tureta ajikinta azafafe acikin wani irin yanayin takaici mai mugun shakure wuya snn tace "get out my friend ure totally blind, na rantse da Allah kin haukace..Adiaha kina kallon zaki jefa kanki acikin wata masifa da damuwa amma ba soyayya ba.
Abun na ci ma Ekaete rai tana maganan ta fara kuka mai zafi tana cewa nasha mamakinki adi narasa ke wacce irin yarinya ce, ace Mutimin daya walakanta ki yay treating dinki like a donkey while u worship him, snn ya tafi ya barki kmar zaki mutu da sonshi agadon asibi babu ko sallama ..amma wai daga ya dawo just one night har kinzo kina cewa zaki rabu da kowa naki dan ki aureshi..
please where is ur worth adiaha? Please where is ur worth..ina da darajarki na ya mace yake?
Menene murumin nan yake dashi wanda bazaki samu awajen wasu maza ba. Can u tell me one thing about him thats true and special?..adiaha ko mahaukacine by now yasan kece kikeson mutumin nan amma bashine yake sonki ba but look at u, u just want to secrifice ur family and ur religioun for him, all for what?..
Ido a rufe Adiaha ta mike tsaye jikinta harna rawa tace "All for love, i love him..kinji?And I dont care what u said nidai inason shi kuma shi zan aura..he is my happiness dats all that matters to me..koya walakanta ni ko baiyasona nide kawai shizan zaba sabida shi zuciyata take so.
Cikin girgiza kai ekaete ta share hawayenta snn tace toh shikenan, zakizo wata rana kice na fada maki cewa ure making a big mistake in ur life since kinzabi ki zamo baiwar zuciyarki..
And Rember dis oo,a woman dat chooses to honour her heart desire will suffer, she wll have no self worth, no self respect and dats what u are getting from him adiaha.
Tace eh din, naji, kije kita kishi na, nasan kinajin haushina ne dan na samu saurayi doctor kyakkwa mai kudi, see ehnn..idan har ya aureni I will use my love to win his respect and be worth it awajensa cos i have all it takes to lured him tafada tana rausaya hadadden jikinta dayaji komi da komi.
Ekaete ta girgiza kai tace
"Yarinya Ki tashi a barci, dan ni danayi soyayyr hauka irin taki aigara na sha poison na mutu
,..alredy bakida mutunci ko daraja wajenshi Allah kadai yasan meyasa ma yazo har garin nan yace miki zai aureki..babu bincike babu komi..and u just accept him, kinsan familynshine? Kinsan ya behvrs dinsu yake? Zasu karbe ki acikin familyn su?..will dat bloody ahmed of a guy also live his family and religion for u? chaiiiii, Adiaha oooo . bantaba ganin jaka irinki ba, mmmm na today i see the height of desperacy in you, toh wani namijine ma zai soki tsakani da Allah ahakan bayan baki san darajan kanki ba.
Rai abace adiaha tace
"Toh Ya isa haka, Dat Is none of ur business tunda bazaki supporting dina ba..
Nan Ekaete ta miƙe tsaye tanacewa yes please say it again...i wont support u akan abunda zai cutar da rayuwanki dan haka kinga tafiyata, Inkin ga dama kiyi tunani akan abunda nafada maki inkinga dama kibari tarihi ya memeta kansa akanki...shey u see how ur grand mother ends up?
Tace yes, i saw it. Kije north kiganta she is happier than us. Tana da mijinta, tana da addinin ta, tana kuma da good business and she dont even need anyone
Ekaete tace karya kikeyi,
She might have evrything amma bazaki taɓa sanin bakinciki da ciwon dake cikin zuciyarta ba ayanzu musmmn inta tuna cewa duka yayanta na cikinta sun tsaneta snn dukkan zuriarta sun juya mata baya.
Adiaha tace oho dai Wann ai damuwarsu ce
Dama menene suke kara ma rayuwarta? Nide i want to be like grand ma..kuma zan shiga moslemi badan Ahmed ba, i have admire them since..they are peaceful they cover and..
Ekaete tace Abeg abeg Shut ur mouth idiot girl...u dont knw them..suma sunayin dukan abunda mukeyi so cut the crap..
Tace eh, Amma ai bakamar namu ba, we do illicit sex and taking bear is almost part of us gashi bama covering kanmu kamrsu.
Ekaete tace Thank god u said part of us, but not path of christianity, dan addinin christa baice ay adultery ko fornication ko shan giya ko atafi tsirara ba, those things are sins too, mother mary also cover and she did not fornicate u rmbr?
..all thos bad things are inventions of our selfs not our religion, ke kije kawai kiyi addininki in zakiyi but stop tryng to find reason againt us.
Adiaha tace naji, zanje.
Ekaete ta karkada kafarta tace gudluck and please count me out of ur way ooo babu ruwana da lamarinki gaskiya.
Adiaha batace komi ba har ekaete ta sauka ta bar wajen sai kuma taji wani irin bakin ciki mai yawa ya mamayeta jikinta a rwgwabe ta sulale kasa ta kara fashewa da wani irin kuka mai tafe da rudani..
Saida tay mai isarta snn ta nitsu ta zauna shiruuu dan tsabar damuwa datake ciki ko yunwa yau bataji ba haka nan takai tsawon lokci tana tunani akan rayuwarta harsaida ta yanke makanta hukuncin auren Ahmed mai kankat.
Ahmed ya kammala yin waya da yayan sa kenan sai yay wanka ya fito waje domin cin abinci, yana isowa nan saiga wata hadaddiyar yarinya irin kyakkywawan yan matan calabar runs girl din nan fara doguwa kamr mami water saidai wann din mai aji ce, tun tahowarsa ta lura da cewa shikadai ne namijin daya zo ta wuce ta amma ko kallo na biyu bai mata awajen ba, tana ganin shi zai zauna itama tazo tayashi zama nan tafara dan janshi cikin hira suna cin abincin a tare.
Tayi sa'a kuwa ya bata fuska sabida alkcin He is feeling quite disturbed sabida rashin sanin halin da mahaifyrsa take ciki yana neman abunda zai dan dauke hanklinshi daga tunanin gida daya addabeshi.
Hira sukey sama sama amma sosai yagane cewa babe din sha'awar shi takejii dai yanata jajja mata aji baison nuna kamr yagane manufarta aknshi danko sunanta bai gama rikewa ba.
Tana cikin masa hira mai dadi wayarsa tay kara baiko yi excusing dinta ba ya daga wayarsa confidently yanamai katseta unexcused ayanayinsa na tsinannen jan aji da rainin hankli, nan ya saka wayar akunnen shi yafara magana da friend dinsa bankole dayay kwana biyu bai gansa awajen aiki ba.
Da yare suka fara hirar su sam baiyi tsammanin babe din gabanshi tana fahimtar meyake fada ba cos she is a typical calabar girl amma mum dinta yoruba ce,sai tay tsuru tsuru tanata kallonshi jin yadda yake magana full of i dont care attitude har yana refering dinta da sunanta na karuwa and he even mention dat ko sunanta ma bai kama ba.
Bankole kuwa sai zugashi yake akan cewa ya tafi da ita room dinsa kawai yaje ya kwashe rabonsa ajikinta tun da ita ta kawo masa kanta
ahmed yanata dariyar karfin hali yanamai ce masa ajinshi yafi karfin yay zina da yar mutunci bare kuma da katuwar karuwa irin wnn babe din.
Yadda suke maganan cikin kadadi da raha bazaka taba tsammanin abunda suke fada ba kenan.
Ahmed yazauna ya kushe mata masu saurin bibiyar maza iya kushewa baisan duk tanajin duk abunda yake cewa
Aganinsa inda shi mace ce da komin muninshi da tsiyarshi wallh bazaibi namiji bare har yana cusa masa kansa..
yace shiyasa sam baiya ganin matan da suke bibiyarshi da daraja sabida aganinsa basu da aji da mutuncin da zai sosu aransa.
Yace daga mace ta fito fili ta nuna tanason shi tun baice yana sonta ba toh tamkar wata shara yake kallonta dan shi yafi daraja mace mai kare kimarta, koda ace tana sonshin ma kardai ta nuna cewa ita yar araha yar sauki ce dan harga Allah shikam ya tsani yay wata muamala da duk wani abu mai araha.
Yace koda shi a karuwa ya fito wallh da bazai zubda mutuncin sa yana bibiyar opposite gender karara ba saidai in karyay kasuwa har abada
Sunata hirar duk ya shagala suna dan toshewa da dariya da abokinsa bankole.
Ganin babe dib ta kafe sa da ido kmr na wance zatay kuka yasa yay mata yar murmushin yake itama ta maida masa da kyar dan sai yanzu tasan da dan rainin hankli take zaune..
Da can har zata ja tsaki ta bar masa wajen sai kuma taga ya katse wayar sai kawai ta wayance ta zauna tana kallonshi.
Tex messges ne suke shigo masa akai kai wanda rabonsa dayaga ana turo masa sako haka tun rabuwarsa da kafayat a Abuja. Tsaki yaja aranshi Yana budewa yaga lambar adiaha ne
Cewar harta zo hotel din wajenshi gata nan tana waje.
Ya daga kai zai kalli ta bakin kofar shigowa kenan sai gatanan harta shigo ciki, wani irin kallon sa takeyi tun daga can nesa ganin datayi masa da kyakkwan budurwa suna zaune sai taji ranta ya sosu sosai bana wasa ba.
Idonta a rufe da tsananin kishinsa ta iso waje tana zuwa ta shiga watsa ma yarinyar wani irin kallon banza shidai yanata kallonsu baice musu uffan ba,nan yarinyar ta miƙe sikinini tana jan tsaki, da har zata bar wajen snn ta juyo ta kalli Ahmed cikin harshen yorubanci tayi masa sallama dan ya san taji duk abunda yace akanta wanda yasakashi kyabe bakinsa sabida mamakinta dayaji.
She looked very annoyed as she left.. aransa yace can miki .
Nan Adiaha ta zauna cikin yanayin fushi da huci snn tace masa Doctor and who is she?
..kuma meyasa tazo nan harkuke cin abinci tare?
Jin yanayin yadda ta fadi magana with anger and comand saiya shareta yay kamr baisan dashi takeyi ba.
Hakan sosai ya kular da ita rai abace tace hey i am asking u?
Cikin basarwa sosai yana danna wayarsa a tsime Yace "repeat ur self "..
Tace nace wancan yarinyar..
Tun bata karasa ba ya hade rai snn ya katseta da cewa Adi bana son yarinta fa, kawai daga na baki ring dazu kinsaka a ytsunki shine har zaki fara rainani ko?
Tace "what? Ahmed mani kake ce ma haka,me kake nufi?. Ya shareta baice mata uffan ba.
Ajiyan zcya ta sauke snn tace see is not just like that..kasan damuwar danake ciki kuwa akanka kake cemin haka? I cant even go home..banda inda zan kwana fa yau.
Bai amsata ba, yay shiru saida ya gama latsa wayarsa snn yace lest go to my room toh sai muyi maganan acan ko?...
08060712446 SURAYYAHMS:*Wanda ba su yi saving number ta ba su yi sai su mini magana ni ma zan saving ta su* Reply with "saved" is enough.👍🏻
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top