Chapter 27
"Wannan karon jikin khushi sanyaye ta kalli aneesa dake tsaye tana jiran answer din da zata bata,ganin khushi bata da niyyar yin magana yasa aneesa sake kallonta tace can't you say anything khushi?da kyar khushi ta bude bakinta tace anee i am busy right now kije idan na gama abinda nakeyi zanzo,jikin anee a sanyaye tace promise?murmushi tayi kadan tace yeah don ita yanzu lamarin aneesa har ya fara bata dariya.....bayan ta gama hadawa mum kunun gyada dinne ta kai mata bangarenta tareda bakinta sannan ta koma dakinta ta zauna,wayarta ta janyo abinda ya bata mamaki shine yau throughout najeeb be kira wayarta ba bayan kuma ko kafin ta fita sai data yi masa missed call tare da ajiye mishi offline message a whatsapp amma still be dubaba,jefar da wayar tayi akan gado bayan ta tuna da kiran aneesa wanda tayi mata alkawarin zataje wajenta,kallon agogo tayi taga har lokacin sallar magrib yayi ta mike tayi alwala bayan ta iddar da sallah ne ta dauki wayarta ta saka slippers dinta ta nufi dakin anee,a bude ta tarar da dakin tura kanta tayi ciki bayan tayi sallama,wannan karon akan sallaya ta tarar da aneesa zaune ta iddar da sallah,ganin khushi yasa ta mikewa ta ajiye daddumar a gefen gadon sannan ta zauna kusa da khushi,shiru sukayi gaba daya har na kusan 50 seconds kafin anee tace why are you ignoring me khushi?lumshe kyakkyawan idonta tayi tace i am not ignoring you anee kawai dai nafiso ki gane wannan game din namu ya kamata ace yazo karshe,da sauri anee ta dakatar da khushi muryarta na rawa tace this is not a game khushi,ban fara sonki saboda na denaba,dora hannunta tayi akanta cikin damuwa tace anee you have to stop thinking anything negative about us kinsan aure zanyi nan da 2 days ya kamata ace kin gane halin da nake ciki na rokeki don Allah ki barni nayi rayuwata kamar yanda kowa yake yin rayuwarsa mu cire komai da ya faru akanmu gaskiya i,m tired of this relationship na gaji banaso sam ta karasa maganar tana kuka,murmushi aneesa tayi hakan ya bawa khushi matukar mamaki sannan ta kalleta cikin rashin fahimta,murmushi aneesa ta sakeyi tace you made a mistake wlhy bazan taba barinki ba ko kinasona ko bakya sona ya zama dole in shiga rayuwarki sannan dole kiyi rayuwa dani kuma a matsayin da nakeso,tsaki khushi tayi cikin zuciyarta tace wannan wanne irin masifa ne haka,ganin aneesa ta kasa fahimtarta ya sata fita daga dakin ta koma nata dakin zuciyarta sam babu dadi......tunda ta shiga bata sake fitowa ba,da wuri tayi bacci jin yanda kanta yakeyi mata ciwo gaba daya ta kashe wayarta saboda batason takura
"Bata tashi da wuri ba har karfe 10 tukunna ta shiga tayi wanka sai data gama shiryawa tukunna ta karasa palour don gaishedasu mum da baqinta,kamar ana zaman makoki ta kalli fuskokinsu banda jimami babu abinda kowa yakeyi a cikinsu,jikinta sanyaye ta tsuguna ta gaishesu a tare suka amsa mata tana shirin juyawa ta fita mum ta kira sunanta,gabantane yayi mugun faduwa a hankali ta juyo ta sake tsugunawa gaban mum tace na,am,itama mum shiru tayi jin bakinta yayi mata nauyi,matar dake kusa da mum ce wacce suke kira aunty salamatu tace meenal,gaban khushi ne ya sake faduwa muryarta na rawa tace naam....itama shiru tayi sannan tace magana nakeso na fada miki amma yanada kyau kiyiwa maganar kyakkyawar fahimta saboda kowanne dan adam akwai nashi kalar kaddarar sannan idan kinga Allah ya saukar miki da kaddara karki tunanin cewar wai ko don kinyi lefine ko kuma wani abu daban kinji kawai kedai kiyi imani da Allah kuma ki sani cewar kowanne tsanani yana tare da sauki,gaban khushi ne yaci gaba da faduwa a hankali ta daga kanta alamar ta gamsu da maganar da ake fada mata,ajiyar zuciya aunty salamatu tayi tace kinsan cewa najeeb ya fasa aurenki?a firgice khushi ta kalli mum cikin tsananin tashin hankali ta fara girgiza kanta alamar ah ah tace bansaniba aunty daga nan hawaye ya fara zuba daga fuskarta,tunda ta fara kuka su mum ke rarrashinta amma hakan besa ta dena kuka ba mikewa tayi ta karasa dakinta da gudu bayan ta kulle kofa taci gaba da kuka wani irin tsananin son najeeb takeyi wanda bata taba jin irinsaba tunda suke tare,wayarsa taci gaba da kira amma banda rejecting babu abinda najeeb yakeyi at the end ya turo mata text message cewar tayi hakuri ta dena kiransa shi kam ya hakura ya fasa aurenta babu abinda zeyi da yar lesbian,sake fashewa tayi da kuka tare da tsananin tsanar aneesa a zuciyarta,tuni khushi ta fara hada kayanta cikin kuka gaba daya ta tsani gidan sanadiyyar zuwanta gidan gaba daya rayuwarta ya sanja komai nata ya lalace,gaba daya ta tsani aneesa ta tsani ganin aneesa,bayan ta hada gaba daya kayantane ta nemi izini gurin mum cewar ta bata dama don Allah tanaso taje gida,bayan mum ta kira dad shima be musa ba aka hadata da driver ya dauketa suka tafi wannan shine rana ta farko data fara regretting zuwanta duniya komai na duniya baya yi mata dadi addua takeyi Allah ya dauki ranta yanzu ko zata huta da wannan masifar na duniya aneesa ta cuceta ta cuci rayuwarta,tun a hanya ta sanarwa umma gatanan tana zuwa itama umma bata nuna wata damuwa ba akai tunda ta bangarensu najeeb ya sanar dasu cewar ya fasa auren meenal din
"Kamar mahaukaciya haka aneesa ke ihu tana birgima a kasa duk kuwa da tarin alluran bacci wanda akeyiwa mahaukata akeyi mata da tarin magunguna amma sam basayi mata komai sedai idan tayi bacci ta dora daga inda ta tsaya,hankalin mum da dad yayi matukar tashi anan aka basu shawarar cewar su gwada maganin gargajiya kona aljanu,bayan dad ya yiwa abokinsa magana ya hadashi da mallam buba babban malamin addini wanda yayi popular wajen cire aljanu anan ne aka bashi damar shiga wajen aneesa don gwada nashi kalar maganin,sai daya dauki almost 40 minutes kafin ya fito bayan sun zaunane yayi gyaran murya yake fadawa su dad cewar aljanune sukayi nasarar shiga jikin aneesa kasancewar tana wasa da addininta sannan bata yin sallah akan lokaci wani zubin ma yin sallar be dametaba,shiyasa aljana ta shiga jikinta bayan ta hadu da khushi take matukar son khushi din,saboda rashin maida hankali wajen ibadarta da addua hakan yasa rauni cikin imaninta take jin bazata taba iya rayuwa da wani namiji ba idan ba khushi ba,sosai dad da mum sukeyin mamaki cikin tashin hankali dad yace yanzu mallam kenan haka zamu xuba mata ido muna kallo?murmushi mallam buba yayi yace a,a yanzu munyi nasarar raba ta da aljanun da suke sanyata duk wasu abubuwan da takeyi sedai idan har bata maida hankali gurin neman yafiyar ubangijiba da kuma yin ibada yanda ya kamata to zasu dawo suci gaba da bibiyar rayuwarta.......bayan dad ya bawa mallam buba kyautar kudi masu yawa sannan yayi masa godiya sosai
"Bayan kwana 2 aneesa ta samu sauki sosai duk lokacin data tuno kalar rayuwar da tayi a baya wani irin bakin cikine yake damunta tare da danasani yanzu gaba daya ji takeyi bazata iya hada ido da khushi ba saboda kunyar khushi takeji,bangarensu meenal suma basu wani damu sosaiba akan fasa aurenta da najeeb yayi saboda sun san hakan zai iya faruwa tunda najeeb ya samu labarin su khushi,kullum meenal cikin kuka take har sai da ta tabbatar najeeb bazai taba aurenta ba tukunna ta hakura ta maida lamuranta ga Allah.......sai da aka dauka lokaci me tsawo tukunna su mum da aneesa sukazo gidansu khushi bayan sun nemi yafiyar juna akan misunderstandings da suka dinga faruwa tsakaninsu dukansu sun yafewa junansu ita kanta khushi har mamakin aneesa takeyi ganin ta nutsu
"Bayan 8 months aneesa ta samu miji tayi aurenta sedai har yanzu khushi tana nan dai zaune bata samu mijin aureba duk wanda yayi kokarin cewa ze aureta da an kwana 2 sai an samu masu fada masa cewar yar lesbian ce daga nan bazai sake dawowa ba........Lol bariki ba riba wlhy
Alhamdulillah rabbil alamin
I have no words to thank you guys for the love and support that you shown toward this book nagode sosai Allah ya saka da alkhairi
Sai mun hadu a sabon littafi mai suna
MU'AMALAT
(Happy ending)
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top